Showing 60001 words to 63000 words out of 91747 words

Chapter 21 - INUWAR GAJIMARE Book Complete By Oum Nass.txt

oum Nass   

17 Oct 2025

3218

fuzgar da iska mai zafi a bakinsa, da labari aka bashi cewar zai ga mummunan rana irin wanan to kuwa da zai musanta labarin yace babu ita a cikin duniyarsa.
  A yau da mutane za su ganshi da tsaf za su masa kallon sabon mahaukaci.
Duba bayan motar yayi cikin sa'a ya samu kaya kasancewar basu rabo da tafiye-tafiye hakan yasa ko yaushe suna ajiye kayan sawa a cikinta.
  Wani lallausan yadi yasa fari ƙal da shi, marar nauyi an kuma yi masa ɗinki zamani da hannu rabi a jikinsa.
  Sanan ya sa shimfiɗa dardumar sallah ya zero sallolin da ake binsa da shi. Ya daɗe zaune a wajen yana addu'a yana kuka, akan Allah ya dube shi ya tsayar masa da damuwarsa iya nan. Kada ya jarrabi ɗiyarsa da abun da ya aikata da hannayensa, ya tashi kafaɗunta ya buɗi idonta lafiya!"
  Anan ya kifa kansa yana kuka har ya fara jiyo assalatu a garin, hakan ya sashi shiga cikin motarsa ya nufi cikin garin, da yawa mutane basu fara fitowa sallah ba, haka ya shige cikin masallacin zuciyarsa cike da nauyi.
  Duk wanda ya fito a sallah sai ya tsaya ganin motar da ke wajen, da yawansu suna mamakin abun da ya shigo da mota cikin garin nasu a wanan lokaci, hakan ya sa su shiga massalacin, amma kuma basu ga alamun baƙin mutane ba, har liman ya tada iƙamar sallah suma suka ɗori bayansa.

  Bayan an idar da sallah ne wasu suka fara tashi suna fita, yayin da Aabid ya haɗe kai da gwuiwa yana tunanin ta ina zai fara tambaya? Toma da wani suna zai ce ya zo neman yarinyar da ya lalatama rayuwa?

  "Yaro kana lafiya dai?" Ya tsinkayi wata dattijuwar murya na tambayarsa me cike da kamala.

  Ɗagowa yayi a hankali ya kalli Mutumin, da yake sanye da manyan kaya, kansa kuma naɗe cikin rawani, hakan ya sa ya fahimci shine limamin garin.
  "Subhanallah! Kuka kake ai samari! Me ya faru da kai haka?"

  "Nazo neman wata yarinya ne da aka yima Fyaɗe shekaru shida da suka wuce!" Ya faɗa cikin rawar muryar da ta sha kuka ta more.

   Sakin kafaɗarsa Malam Liman yayi yana kallon fuskarsa "Me yasa kake nemanta yanzu?  Ka santa ne Yaro?"

  Kai ya gyaɗa masa "Eh na santa! Dan Allah ka sa akaini wajenta, ina son naga yanda take ne."
  Shuru Malam Liman yayi yana nazartar yaron da ke gabansa, can kuma ya buɗe bakinsa "Kana son ganinta saboda wani dalili?"

  Shuru yayi yana tunanin amsar da zai bashi, shi bai san me zai ce masa ba "Ko dai kai ne ka mata Fyaɗen?"

  Da sauri ya ɗago da kansa saboda jin maganar da yayi a bazata, kai ya gyaɗa sanan ya girgiza cikin rawar murya "A'a ba ni bane?"

"Ya akayi idan ba kai bane ka riƙe shekarun da aka yimata fyaɗen? Waye kai? Kana ina a lokacin da aka mata abun?"

   Kai ya shiga girgizawa jikinsa duk ya shiga rawa, maganar mutumin tana ratsa jikinsa, yana jin sabon tsoro da shakkarsa na shigarsa.

    "Kai ne mutumin da ka lalatama Khadijatu rayuwa! Duk tsawon wanan shekarar ba zo ka waiwayi rayuwarsu ba sai yanzu?"
  Jikinsa ne ya shiga rawa kafin yayi magana yaji wata kakkausar murya na dukan dodon kunnensa "Malam Liman me ke faruwa anan? Da gaske wanan yaron ne ya yima Khadijatu fyaɗe?"

  "Bai yi magana ba har yanzu ran kai daɗe! Ya zo ne yana nemanta dai."

  "Ku fito min da shi waje!" Mai gari ya faɗa cikin muryarsa mai amo kamar zai tada masallacin.

  Kafin yayi magana wasu masu fushi da fushin wani suka kamo Aabid suka fito da shi waje, jikinsa babu ƙarfi babu kuzari, shi ya manta ma cewar shi ɗin soja ne balle ya ƙwaci kansa.

    "Yaro kada ka ɓata min lokaci, ka faɗa mana gaskiya shin kai ne ka keta haddin Khadijatu ko kuwa?"

  Bashi da wani zaɓin da ya wuce ya amsa, saboda a yanzu zuciyarsa ta riga da ta bushe, abu ɗaya yake so ya ga yarinyar ya bata haƙuri, shi idan bata haƙura  bama a shirye yake da ya aureta.

   "Eh ni ne nazo na bata haƙuri ne, na kuma aureta!" Ya faɗa cikin ƙwarin gwuiwar da ya masa saura, saboda a tunaninsa idan suka ji zai aureta za su ji daɗi su amince da shi nan take.

  Kallonsa duka mutanen garin suke da mamaki ya cika su  "Duk waɗan nan shekarun baka zo ka bata haƙuriba sai yanzu? Yanzun ma na tabbata ba ka zo haka ba ne sai dan wani abu na son zuciyarka. Da kace kuma ka zo zaka aureta sai na fahimci manufar da ta kawoka ka zo ne dan ka ƙarasa mata sauran rayuwarta da ta rage mata! Ka zo ka ƙara kassara mata duniyarta da ta fara haska mata daga baƙin fantin da kayi." Hawaye ne ya taru akan fuskar Mai gari.
  "Ashe dama kai ne ka sa na yanke hukuncin da har yau bai daina caccaka min zuciyata ba! Kai ne ka hautsina mana  kyakkyawan garinmu, ka rusa mana amincin da ke kwance male-male a cikinsa. Duk baka zo ba sai a yanzu da muke ta ƙoƙarin dawo da martabar da ka gama zubar mana da ita."

  Kallon matasan garin yayi "Me kuke jira da la'anannen nan, kuyi ta dukansa har sai numfashinsa ya ɗauke."
   Dukansa suka farayi tun ƙarfinsu kamar Allah ne ya aikosu, tun yana daurewa har ya fara ihu, duk ƙoƙarinsa akan ya ƙwace daga ruƙonsu ya gagara ƙwacewa.
  Shi ba wanan ne damuwarsa ba, idan da sun nuna masa yarinyar to ashirye yake da su ɗauki rayuwarsa mutuƙar ya nemi yafiyarsa.

   Da ƙyar yaja numfashi jini na zuba ta hancinsa da bakinsa "Dan Allah kafin ku kasheni ku nuna min Yarinyar na nemi yafiyarta! Daga baya sai ku kashe ni."
  Basu tsaya sun saurare shi ba haka suka ci gaba da dukkansa, har idanuwansa ya fara janyewa daga kallonsu da yake, numfashin da yake ta ƙoƙarin ƙarfafashi ya gaza riƙe shi "Dan Allah kada ku kasheni ku barni da nauyi mai yawa akaina! Ku barni na roƙi yafiyarta, dan Allah!" Ya faɗa yana yin luuuuu da dukkanin gaɓɓan jikinsa.

"Ku ƙyaleshi haka!" Liman ya faɗa sai dai ina numfashinsa ya riga ya ɗauke, lokaci ya ƙure musu, suna sakinsa ya taho ya kifa ta kan fuskarsa, take jini ya ɓalle a hancinsa da kuma bakinsa, idanuwansa suka rufe ruf.. ..

  *******
KADUNA, NIGERIA.

  A hankali ta ke sauƙowa daga matakallan benin, jikinta sanye da doguwar rigar shadda gizna mai kalar  sararin samaniya, ta yane kanta da baƙin gyalen da ya haske kyakkywar fuskarta, mai zubin larabawa duka shekarunta ba za su wuce ashirinba, amma kana ganinta kasan ta amsa sunan mace, idanuwanta farare masu ɗauke da gashin ido da ke rufesu akai-akai.
  Babu wadatacciyar kwalliya a fuskarta kamar yanda ta saba, iyaka tasa kwalli a idonta sai man laɓe fari.
  Tunda ta sauƙo hankalin mutanen da ke palon ya koma kanta, yayin da ita kuma hankalinta na kan agogon da ke saƙale a hannunta.
   Zama tayi kusa da Ammu ba tare da ta kalleta ba, ta danna maddanan wayar da ke hannunta sanan ta kara a kunnenta, kamar wadda bata son magana ta fara yamutsa kyakkyawar fuskarta tana lumshe idanuwanta "Kana so nace ka makara ne?" Ta faɗa cikin sanyin muryarta da ba kowa zai san ta yi magana ba, sai idan ya lura da motsawar da bakinsa ya ke yi.
 
   Ɗan murmushi tayi kaɗan "Ka yi zamanka ba sai ka zo ba." Ta faɗa tana kashe wayar da ke hannunta.

   "Aikin banza mu za'ayi gulmarmu muna zaune goɗai-goɗai da mu!" Ammu ta faɗa tana bankama Khadijatu harara.
  "Kina nan dama?" Ta faɗa tana kallon sashen da mutane falon suke.
  "Aysha!" Ta faɗa da muryarta da har lokacin bata da ƙarfi.
  "Ubanwa zai ji wanan maƙalalliyar muryar taki! Kamar da aka sa ki magana dole. Ni na rasa wanan maganar yarinya shekaru sun tura amma har yanzu bata iya buɗe baki tayi magana irin ta mutane ba."
  Tashi Khadijatu tayi daga kusa da ita, ta koma kusa da Abbu Yasir da Ummi da suke ta dariya "Wanan matar ku nema mata magani." Ta faɗa cikin sanyin muryarta.

   "Wai nikam ya kuke magana da Nabil ne? Shi naga yana da surutu ke kuma gashi magana ma haushinta kike ji " Abbu Yasir ya tambayeta yana kallon fuskarta, da take murmushi bata ɗago ta kalle shi ba, balle yasa ran zata amsa masa.
   Duka ya kai mata da hannunsa wanda ya sata tashi da sauri tabar falon gaba ɗaya " 'Yar butar uwa! Da kin tsaya da na sauƙe sheɗanun da suke kanki." Ya faɗa cikin jin haushin share shin da tayi.

  Ummi kuwa mi zata musu banda dariya "Kuma bakwa gajiya wallahi, kuce dole sai kunsa ta magana, bayan kunsan ko shekara kukayi kuna mata magana da ƙyar ku samu amsa ashirin a lokacin. Ni wallahi har tausayama rayuwarta nake, ace magana kamar ana ƙwatota a bakinta.  Ni kam idan akwai inda za'a samu maganin wanan  cutar shuru ɗin nata muje a dubata, ko bakinta ke da matsalar magana."
  "Gaskiya nima abun ya isheni haka, dan tunda ta samu lafiya shikenan magana ta ɗauke mata." Ammu ta faɗa tana zabga tagumi.
  "Bari Imran ya zo sai mu tambaye shi ya nema mana wata asibitin da zamu kaita." Abbu Yasir ya faɗa.

    Dariya sukaji an kwashe da ita, wanda ya sasu saurin juyowa, Wasu Kyawawan samari biyu ne suke musu dariyar sai budurwa guda ɗaya da har ciki ta ke ruƙewa dan dariya.

   🌷🌷🌷

Barka da hantsi....[10/14/2020, 3:49 PM] +234 703 602 1861: IG

 

  0000430000

   "Kuji sabon shashanci kuma. Me ye abun dariya a maganarmu?" Abbu Yasir ya faɗa cikin tsuke fuska.
  Ƙarasowa falon suka yi suka zauna akan kujera "Wai sai yaushe zaku daina takurama Khadijatu na! Ko yaushe kuka zauna magana ɗaya kuke akanta dole sai ta muku surutu kamar radio."

"Ungo amshi nan." Abbu yasir ya aika masa da daƙuwa "Kai ai ba haka kake ba! Wanan tsaf mijinta zai yi ta cutarta ba zata tanka masa ba."
"Ai kuma tana magana da shi sosai fa. Inaga yanda take zagewa tayi hira da shi ko da Yayanmu bata yi." Macen ta faɗa tana ƙunshe dariyarta.
Harara ya buga mata "Ki fita idona Aisha. Nabil ba zai taɓa samun hirar da Khadijatu zata min ba har abada."
"La'ilaha illah lahu! Kuji min wani saɓo! Anya ƙalau kake Isiya? Miji fa ake magana. wa ya damu da kai." Ammu ta amshi maganar.
Nan Aisha ta ƙara kwashewa da dariya ita da sauran mutanen da suke falon.
"Ai gaskiya na faɗa, ba ta yanda za'a yi wani ya maye guna a wajen Khadijatuna, kema Ammu sai dai ki faɗa dan adawa.
Ku zo ma kuga zahiri." Ya faɗa yana tashi daga kujerar da yake zaune, tashi suka yi suma suka bi bayansa har zuwa ɗakin da Khadijatu ta ke.
Sai da ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, sanan ya tura ya shiga "Khadijatu nah!" Ya faɗa cikin sanyin muryarsa yana baza idonsa a kanta.
Murmushi tayi tana kallonsa ba tare da tayi magana ba,zama yayi kusa da ita "Bani labari ƙanwata!"
"Wani labari kuma Yayanah?"
"Uhm kamar labarin duniya, soyayya makaranta da kuma ƙawayenki."
Murmushi tayi tana kallon fuskarsa "Ni ai duka bani da sabon labari akan waɗan nan, komi da ke cikin duniyata ka daɗe da saninsa tun kafin na sanshi."
"Harda soyayyar Nabil?"
Fuskarta ta rufe da hannunta yana dariya mai sauti "Wanan ai bai shiga cikin labarina ba, saboda da kanka ka zamar da shi zanannen al'amari.
Ina jin soyayyarsa a raina tun lkcn da ban san kaina ba, amma kuma ban bari ya girmi al'amarina ba har sai da na samu yardarka a kansa."
"Idan nace yanzu ki barshi na samo miki wani kenan zaki haƙura da shi."
Kanta ta kwantar akan kafaɗarsa "Ba iya soyayyata ba ma, ko rayuwata ka buƙata zan baka ita muddum kana buƙatarta.
Nasan duk abun da zaka bani mai kyau ne wanda ke ɗauke da lu'u-lu'un hikima da kyakkyawar gobe a gareni."
Hancinta ya lukuce mata yana jin zuciyarsa na karyewa da maganarsa "Duk abun da kike so shine soyayyata a gareki, idan baƙi kika kawo min kikace fari ne nima kallon fari zan masa Khadijatu nah.
Nabil ya can-canci soyayyarmu, ba zan iya musauya miki wani a madadinsa ba, a tare da shi nake son ganin murmushi a kyakkyawar fuskarki."
"Uhmm hakan zai faru ne Yaya idan kaima ka cire mikin da ka ɓoye a zuciyarka!"
Ido ya fiddo waje "Me na ɓoye a zuciyata?"
"Gaskiyar da idanuwanka suka kasa ɓoyeta. Al'amarin da idanuwanka basa jure ɗaukesu! Labarin soyayyarka da kake ta yaƙi a cikinta, kada ka tsaya kallon kwaɗo yayi maka ƙafa, kada garin jira kaji kiranye na riskar kunnuwanka, kada garin jinkiri kaji lokaci ya ƙure maka!"
"Lokaci ba zai ƙure min ba ƙanwata! Ina ta auna lokaci da killace ko wata sa'a a cikin zuciyata, na tabbata nima ina da kyakkyawan dashen da ruwa bai ɗaukewa daga gareshi."
"Ka yarda da kanka da yawa Yayanah!"
"Fiye da yanda ake kiran Yarda ma ƙanwata."
Dariya suka yi a tare dai-dai lokacin da su Ammu suka turo ƙofar ɗakin "Da kyau wato mu kika rainama wayo shi yasa bakya mana magana ko?" Ummi ta faɗa cikin ruƙe haɓa.

"Ai ga zahiri ba sai kin ja ba, mune dodonninta.Bari Imran ya zo yau a yita ta ƙare a gidan nan." Ammu ta faɗa tana fucewa a ɗakin kamar kububuwa, suma bayanta suka bi suna ƙwafa.
Dariya ta yi tana kallon Ishaƙ da hannu "Banyi komi ba!" Ya faɗa yana wara hannunsa da langare kansa.

Kai ta girgiza kawai tana kallon Indo da a yanxu ta koma Aisha "Kina jinsa ko?"
"Kun fi kusa ai, wace Aisha da shiga maganar yaya da ƙanwarsa."
"Ya Anwar harda kai!"
"Ki barshi da ni, na samo masa wata budurwa zan haɗa shi da ita."
"Haba mana Yaya! Ya zaka mun haka!"
"Ai an gama magana kuma." Ya faɗa suna tafawa da Khadijatu.
Fuska ya haɗe daga nan ya fice a ɗakin bai ƙara magana ba suna binsa suna kiransa.

********


  ƘAUYEN TONI.

 
  Salati mutanen garin suka fara ganin yanda mai gari yasa ya kashe mutum nan take "Kun sake aikata wani kuskuren Yallaɓai! Kamata yayi mu bari muji uzurin da ya kawo shi, tunda har ya iya jure dukan da ake masa, amma duk da haka alfarma ɗaya yake nema a nuna masa inda KHADIJATU take. Bamu san me ya dawo da shi a yanzu ba bayan wasu shekaru, kai tsaye bai kyautu mu yanke masa hukunci ba, tunda mu ba masana gaibu ba ne." Malam Liman ya faɗa cikin tausayawa Aabid da yake kwanci cikin jini.

Jikin Mai gari ne yayi sanyi da kalaman da Malam Liman ya masa "Kaina ne ya ɗauki zafi Liman! Zuciyata na tafasa akan abun da wanan mutumin ya aikata mana. Ka kalleshi da kyau, duk inda ya fito ba ƙarmin mai kuɗi ba ne, amma ya rasa wa zai cuta da yin lalata sai marainiyar yarinya, 'Yar ƙauye! Duk yanda karuwai suka gama cika gari a duniya bai neme su ba sai ita."

   "WANAN Amsar a bakinsa kaɗai zamu jita." Malam liman ya faɗa yana kara hannunsa a hancin Aabid, amma bai ji alamun numfashiba, hakan ya sashi ya riƙe tsintsiyar hannunsa.
  "Ku kawo ruwa."

  CIKIN Sauri aka kawo masa ruwa ya kwara masa da iya ƙarfinsa a fuska nan take yaja doguwar ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Sake kwara masa ruwan Malam Liman yayi anan ya fara ƙoƙarin buɗe fuskarsa "Dan Allah kada ku kasheni! Ku barni na roƙeta gafara!" Ya faɗa cikin raunin murya irin ta wanda ya sha duka ya ƙoshi.

   "Ba zamu kasheka ba, har sai ka faɗa mana dalilin da yasa ka lalata mana rayuwar yarinyarmu."

  
  Numfashi yaja da ƙyar, yana jin yawun bakinsa ya ƙafe a bakinsa "Dan Allah ku taimaka min da ruwa na sha."
  Miƙa masa ruwan  Liman yayi, karɓa yayi jikinsa duk yana rawa ya tashi zaune, ya fara shan ruwan kamar zai ɓace da hannunsa, nan take ya ƙware ya fara zuba ta hancinsa da bakinsa. Ƙirjinsa ya riƙe da yake ji kamar zai fice saboda tsananin zafin da yake jin yana masa.
  Dukan bayansa suka fara yi suna kiran "Luff! Luff! Ka huce yaro!" Dukan da suke masa yasa shi ɗauke hannunsa daga kan ƙirjinsa ya shiga kare bayansa da yake ji suna barazanar burma masa shi.
  "Ku ƙyale shi haka mana!" Malam Liman ya faɗa musu cikin tausaya masa.

  Bayan wani ɗan lokaci ya samu nutsuwa anan ya kalli mutanen garin da suka masa cirko-cirko kamar za su cinye shi ɗanye. Ko wanne a cikinsu ya zazzaro idanuwa yana shirin jin ta kwana.
  'Ikon Allah! Banda ƙaddara bai taɓa tunanin wani abu zai sake kawo shi wanan garinba, shi ya daɗe da manta sunan garin da abun da ya haɗa shi da shi.
  Sai gashi kuskure ɗaya tak da yayi a cikin rayuwarsa ya wargaza masa farin cikinsa.'
  "Kai muke sauraro samari." Mai gari ya faɗa cikin ƙosawa da zaman da suke.
  "Da fari dai sunana Aabid Isma'il Maitama. Ni babban soja ne a cikin hukumarmu. Shekara shida data wuce munzo munyi bikin abokinmu anan a garin Haɗejia muka haɗa da murnar ƙarin girman da aka bani a lokacin.
  Kasancewata Babba a wajen suka fara gabatar mana da kayan ciye-ciye da shaye-shaye dan girmamawa a gareni. Da yawa a cikin mutanen waɗanda ba musulmai bane suka fi yawa, duk da cewa shan giya ba wani abune mai wahala ga sojojinmu ba, amma ni bana da ra'ayin shan koda sigari, kamar yanda bani da sha'awar yin tarayya da ko wata mace muddum ba halaliyata ba ce.
  A wanan lokacin kuma, bikina ya rage kwana uku ne kacal, hakan yasa suka ce dole sai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login