Showing 3001 words to 6000 words out of 22904 words

Chapter 2 - MAJANUNI BOOK 3 BY BINTA UMAR ABBALE.txt

ya bashi tsoro lallai baya shakka ta samu labarin abinda yake faruwa; sai kawai ya sunkuyar da kansa 'kasa ya san takaicin abin ke damun zuciyarta.

Aikuwa ya tsinkayi maganarta. "Baba wace irin rayuwa ka jefa kanka a ciki? wace irin rayuwa kake so ka jefe mu a ciki shin wai baka tausaya mana ne?"

Shuru yayi bai ce komai ba.

Ta ja majina! tare da cigaba da cewa ." Gabadaya ka zubar da kima da mutumcinka a gari, babu wanda bai san irin harkar da kake ba, shifa arziki na Allah ne, wallahi ubangiji ba zai ta'ba azurtaka da haram ba! ko ya azurtaka din 'karshen nadama da jin kunya! shin meye ribar abinda kake? gashi ka jefa kanta cikin masifa da bala'i ka jefe mu a ciki, a yanzu ina muka ga miliyan daya da rabi? babban tashin hankalinmu wannan gidan da ya rage maka shima ka sarayar dashi yanzu da mu da kai ina zamu kama?"
[11/17, 8:09 PM] Bintu: _••MAJNUN!••_
*'BOYAYYAN ATTAJIR!*🛩️
~~~~~
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRTS ASS*
~~~~~
Tukwici ne gare ku mutana ne💕
_*1-AUTAR MANYA*_
_*2-ZEEY KUMURYA*_
_*3-AYSHA BARNO*_

Pege
41&42
Cike da fuffuka! irin wacce ya saba ya nuna ta da yatsa da fadin." Kada ki yi min maganar banza da wofi mana; don uwaki ni za ki zauna kina tsarawa magana, ke din guda nawa kike? me ki ka sani a rayuwa da har zaki zo kina kawo min 'kabli da ba'adi, to wannan shine gargadi na dake na karshe! kada wani abu ya sake faruwa ki zo kina min wasu zantuka ranki sai yayi mummunan 'baci! wallahi."

A sanyaye ta ce." Kayi hakuri Baba." tsawa! ya daka mata ya nuna mata hanyar fita da fadin." Fita ki bani guri shashasha kawai."

Da sauri ta fito tana share hawaye! Talatu ta ja tsaki da fadin." Aikin banza yarinya kina wahalar da hawayenki a wofi wannan mahaifin naku ai ya riga yayi nisa domin ba zai ta'ba gane hanya ba, don haka kowacce ta nemi madafa don duk wanda ya dogara da Jamilu 'bacin rai ne zai kashe shi."

Hadiza ta ce." Talatu duk lalacewarsa ubanmu ne babu yanda za mu yi dole mu shiga damuwa."

Ta ce." To ai sai ku yi karo karo ku biya masa bashin da ake bin sa shashashai kawai ana nusar da su suna baud'ewa."

To in ban da rigima irin ta Talatu ya za suyi ? za su je su rufe shi da duka ne? ai ya riga ya gama yi musu illah! a rayuwarsu dole kuma suyi hakuri su cigaba da yi masa addu'a domin ba a canzawa towo suna.




A na kiran sallar isha'i mai adaidaita sahu ya sauke ta a bakin titi.

Kud'insa ta bashi ta fara kokarin tsallaka titin da nufin shiga layinsu, dan gabadaya Hankalinta yayi gida ganin garin yayi duhu, gashi babu wani cikkaken haske akan titin. tana kokarin tsallakawa kawai ta ji ana jan gefen hijab d'in ta.

A razane! ta juyo sai tayi saurin ja da baya tana kallonsa gabanta na wani irin fad'uwa!

Yana nan yanda yake sai dai an samu sauyin tufafi a jikinsa, amma fuskarsa tana nan cike da 'kasumba sumar kansa ka a cukurkud'e!

Yana sanye da tazarce na shadda bulu sai dai ta kod'e sosai tayi haske sai wani takalmi sosa a kafarsa shima ya sud'e! amma babu datti a tare dashi.

Murmushi kawai yake mata yayin da yake mata wani irin kallo.

Ita kuwa gabanta sai bugawa! yake tana kallonsa tana so ta tabbatar da cewa shine ko kuma aljani ne domin al'amarin ya 'bata tsoro mutuka!

Maganarsa ta dawo da ita hayyacin ta. "Shahida ni ne Baban-baba kina mamakin gani na ko?" da d'an k'arfi yayi maganar saboda ya san lalurar ta.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke har yanzu da ragowar tsoro a tare da ita ta ce.'' Baban Baba kai ne da gaske ko dai idona ne yake min gizo."

Ya sake matsowa kusa da ita a nutse ya ce." Ni ne dai masoyinki na san kin yi kewata ko? nima ina can hankali na yana kan ki."

Wasu hawaye masu zafi suka 'kwace mata ta ce." Alhamdulillahi Allah Na gode maka daka 'kar bi addu'a ta."

Yana murmushi ya ce." Ai d'azu akan idona kuka fito tare da wata abokiyar ki sai na ga fuskokinku cike da damuwa! ganin haka ya sa jiki na yayi sanyi na ce lallai akwai abinda yake faruwa, wannan dalilin ya sa na ce sai na zauna na jira dawowarki kafin na tafi."

Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta.

Ya dan sake matsowa daf da ita da fad'in." Ko ba zaki iya fad'a min damuwarki ba."?

Ta kalle shi tana girgiza kai.

Ya tausasa murya da fadin." Ina sauraranki ki sanar dani abinda yake faruwa domin ganin ki cikin damuwa da tashin hankali ya sanya ni cikin wani hali."

Ita dai a tsorace take dashi dan sai waiwayen bayanta take.

Shima ya fahimci hakan ya ce." Kina jin tsoro na ko."?

Zuciyarta ta karye sai kawai hawaye suka shiga gangarowa ta sanya hannu tana sharewa wasu na biyo baya! sai jan majina take.


Wani irin ciwo zuciyarsa take masa. tuntuni ya tsani zubar hawayen ta ita ce ba ta fahimci hakan ba.

Ya rasa yanda zai yi a gurin yana jin kamar ya rungume ta ya rarrashe ta, sai dai ya daure ya shirya kalaman rarrashi ya fara kwantar mata da hankali har ya samu ta daina kukan.

Ta kalle shi; nan ta fahimci cewa yana cikin damuwa da kukanta, sai ta sassauta fuskarta ta d'an yi kasa da kanta ta ce." Ka fara fad'a min ya akayi rayuwarka ta sauya ? wani almajiri dai ya tabbatar min da cewa an tashe ka daga gurin da kake rayuwa to tun daga lokacin ba a 'kara ganin ka ba. shin dama kai din ba mahaukaci bane?"


Murmushi yayi, ya ce." Ni ba mahaukaci ba ne Shahida." Da sauri ta kalle shi tana mamakin furucinsa, koda yake ba abun mamaki bane a gurinta tunda dama can ita ba ta yi masa wannan kallon.

Ya cigaba da cewa " Rayuwa ce ta mayar dani haka amma yanzu alhamdulillhi na gode Allah tunda ya mayar min da alkairi ya had'a ni da uban gida wanda ya dauke ni aiki a garin abuja, ina masa gadin gidansa ni nake kula da masu shiga da fita! wannan shine ya sauya min rayuwata na dawo cikkaken mutum kamar kowa tunda bani da fargabar ci da sha da kuma gurin kwanciya komai ya d'auke min, nutsuwa ta zo min ban yi tunanin kowa ba sai ke domin ina ganin zaki iya amincewa mu rayu a inuwa d'aya."

Hannu tasa ta rufe fuskarta kunyarsa ce ta rufe ta.

Ya raunata murya da fadin." Ko kina ganin nayi miki tsufa ne? ko kuma kina gudun kada 'yan uwanki da 'kawayenki su yi miki dariya."?

Hannunta ta cire tana girgiza kai ta ce." A'a wallahi bana shakka kuma bana jin kunyar mutane su gan ni tare da kai! so na gaskiya nake maka, kuma wallahi zan iya rayuwar aure da kai a cikin kowane hali, ina rokon Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninmu."

Ya amsa cike da walwala da farin ciki.

Ya ce." To yanzu ya za a yi nayi magana da mahaifinki domin jibi nake so na koma bakin aiki na."

Shuru tayi tana Nazari!

Ya ce." Shahida akwai matsala ko?"

Kanta ta d'aga murya a sanyaye ta ce." Mahaifi na yana cikin matsananciyar damuwa da rashin lafiya! gashi bama jituwa da juna kullum cikin yi min tsawa! yake tunkararsa da wannan maganar zai yi wuya domin bashi da fahimta, ita ma Baba Asabe tana da tata matsalar.

Ya ce." Ko zan iya sanin matsalar."?

Shuru tayi tana jin nauyin fad'a masa! dole duk d'an halak yayi kishin iyayansa.

Ya ce." Ki daina shakkar fada min damuwarki Shahida ni dake mun riga mun zama d'aya."

Shuru tayi ta kasa magana.

Ya d'anyi murmushi da fadin." Ki fad'a min kada kiji komai, ni mai rufa miki asiri ne a kowane yanayi."

A sanyaye ta fara bashi labarin abinda yake faruwa.

Shuru yayi na minti uku kafin ya ce." Ina ganin wannan ba a abun damuwa bane insha Allahu, ni zan yi iyakar bakin 'kokari na akan al'amarin ina da alfarma sosai a gurin maigida na zai nemi alfarma a gurinsa insha Allah ba za ku tozarta ba."


Ta ce.'' Kudin fa suna da yawa." yayi murmushi da fadin." Ba zai gagara ba insha Allahu rabbi.''

Ta dinga kallonsa ta na tunanin yanda za ayi har a samu a biya wannan kudi masu yawa, to amma tunda ya ce Allah ya gama magana.


Har 'kofar gida ya rakata suna tafe suna hira ta fahimtar juna sosai ta saki jikinta dashi, ta kuma samu sassauci a kan fargaba da tashin hankalin da take ciki.
Sai dai har yanzu tana mamakin sauyawarsa.


Cike da farin ciki biyu ta shiga gidan.
Sai kawai ta riske su a tsaitsaye a tsakar gidan har da kawu Musa a cikinsu, da alama akwai maganar da suke.

Gabanta ne ya fadi! ganin fuskokinsu babu walwala ko kad'an!

Kafin ma tayi magana ya rufe ta da fada! ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.

Sai kawai ta fashe da kuka ta durkushe a gurin tana shashshe'ka!

Baba Asabe ta ce." Ka kyale ta haka tunda dai Allah yasa ta dawo lafiya shikkenan magana sai ta wuce."

Ya ce." Idan gidan uban nata take so ta koma ai sai ki had'a mata kayan ta, amma idan ba haka ba mai zai sanya ta dinga wahalar damu, kawai ina zaman zamana an taso ni a tsaye 'karfe goma na dare idan ba shashashan uba ba waye zai bar 'yar sa tana gantali a hanya irin haka."

Ta ce." Na ce ya isa haka don Allah kada mak'ota su ji abinda yake faruwa, tunda dai ta dawo magana sai ta mutu."

'Kwafa! yayi da girgiza kai ya kalle ta da fadin." Ni zan tafi gida sai da safe."

Ta ce." To Allah ya tashe mu lafiya"

Ya kama hanya ya fita da takaicin abin a cikin ransa.

Saliha kuwa bayan fitarsa tsaki ta ja ta shige daki tana surutai!

Ya rage da ita sai Baba Asabe a tsakar gidan.

Ta ce." Ai sai ki tashi kuma kukan da kike bashi da amfani domin sai da na ce miki kada kiyi dare duba da yanayin garin da kuma lalurarki idan shi Jamilun bashi da hankali to mu muna dashi"

Cikin b'acin yanda suke cin fuskar mahaifinta ta ce." Baba ku daina daukar alhakinsa haka don Allah."

Sai ta ri'ke baki da mamaki a tare da ita ta ce." 'Karya akayi masa kenan?"

Girgiza kai tayi ta ce." Tuntuni na dawo fa babu ruwan Babanmu shine ma ya ce na tashi na tafi kada dare yayi min."


Ta ce." To a ina kika tsaya har goma na dare."

Kai tsaye ta ce.'' Ina tare da Baban Baba."

Gabanta yayi mummunan fad'uwa!"

Baki na rawa ta ce'' Baban-Baba kuma?"

Ta amsa da "Eh." tana kokarin tashi tsaye. Ta cigaba da cewa." Ya zo ne saboda ni, kuma mun tattauna maganganu masu muhimmanci! wallahi Baba baki ga yanda rayuwarsa ta sauya ba dama na ce miki ba mahaukaci bane."

Baba Asabe jikinta yayi sanyi sosai kawai ta dinga kallonta ta gaza cewa komai, mamaki da al-ajabin al'amarin kawai take.


A daran ranar dai da 'kyar Baba ta iya rintsawa tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki na al'amarin yarinyar da wannan mutumin da take zargin wani abu a kansa.


Mamakin ta ya kara tsananta lokacin da Shahidan take sheda mata irin maganar da suka tattauna dashi. wato Maganar aure da kuma taimakawa mahaifinta da zai yi."

Ta kalle ta da fadin." Shahida anya kina da hankali kuwa.?

Kafin tayi magana Saliha ta kyalkyale da dariya da fadin." Ras! take tsabar iskanci ne wallahi! amma Baba ki kyale ta kawai jiki magayi ta je ta aure shi jikinta zai gaya mata."

Baban ta girgiza kai da fadin." A'a Saliha ba za ayi haka da ni ba, domin yarinyar nan amana ce a hannuna ban bari ta an aura mata Saminu abbatuwa ba to kuwa ba zan bari ta auri mahaukaci ba."

A hankali suke maganar dan kada ta ji."

Ta kalle su ranta a masifar 'bace ta ce." Baba na san duk kokarin ki kada nasha wahala a rayuwa! wallahi nayi imani da Allah mutumin nan ba zai azabtar dani ba, yana sona ina sonsa mai zai sanya ki dinga mugun tunani akan al'amarin, ni dai mutukar kina so ki ga farin ciki na to ki amince da abinda nake so kuma ki bini da addu'a.

Sai kawai tayi shuru tana kallonta gabadaya jikinta ya mutu ta rasa yanda za tayi ta kamo bakin zaran.
[11/25, 10:02 AM] Bintu: pege
43&44
"Ranka ya d'ad'e wannan mutumin da ka sa nayi maka binkice a kansa har ila yau magana d'aya ce kamar dai wancan lokacin; ma'kotansa da jama'ar unguwa ba su ba da kyakykyawar sheda a kansa ba, duk wanda zai bud'e baki yayi magana baya fad'in alherin sa, ranka ya da'de wannan shine labarin da nasa mu a kansa cewa d'an ca-ca ne wasu ma suna zargin yana harkar bariki."
Cikin ladabi ya 'karasa maganar da yake tafe da ita.

Jaridar dake hannunsa ya ajiye a gefansa, ya mayar da hankalinsa gare shi ya ce." Sule ka tabbatar da Gaskiyar maganar nan? kasan duniya ta lalace mutane basa kunyar sharri! yarda da amincewa ne yasa na sanya ka gudanar min da wannan binkicen, ba naso daga baya wata magana fito."

"Ranka ya dad'e hakane wallahi ba za a ta'ba had'a baki dani a cutar da kai ba, duk maganar da na fada gaskiya ne akan Hujaj sai dai ma'kotansa sun bada sheda arziki akan mahaifinsa, sun tabbatar min da cewa shi mutumin kirki ne domin har ya rasu bai ta'ba aikata alfasha ba."

Ya ce."To godiya nake Sule za ka iya tafiya."

Har ya niyyar tashi sai ya koma ya zauna yana d'an shafa 'keyarsa tare da sinne kai.

"Sule Ya akayi ne? da alama akwai magana a bakinka ."

'Dan murmushi yayi ya ce." Ranka ya dad'e na jima ina mamakin al'amarin tun a karon farko da ka sanya ni wannan aikin, sai nake tunanin wani abu, na ce kodai mun kusa samu uwar d'aki ne?"

Maganar ta sanya shi dariya ya ce." Sule ai na d'auka za ka bukaci zuwa gida ne domin dubo iyali ashe ba hakan bane.?"

Da murmushi a tare dashi ya ce." Da wannan maganar ma Alhaji amma ina bu'katar ka bani wannan amsar idan babu damuwa."

Shuru yayi na minti biyu kafin ya ce." Hakane maganar ka Sule, yarinyar mutumin nan nake so na aura insha Allahu."

Da walwala a tare dashi ya ce." Ma sha Allah Alhamdulillhi ranka ya d'ade Allah ya sanya alkairi yasa za ayi damu Allah kuma yasa abokiyar arziki ce."

Ya amsa da "Ameen suma ameen."

Shuru gurun yayi na minti biyu kafin ya ce." Amma Alhaji baka ganin hakan zai janyo maka wata matsalar duba da cewa uban yarinyar bashi da kirki! akwai ma'kiya wad'anda suke jiran 'kiris su samu abun yayatawa a gari."

Murmushi yayi ya ce." Sule kada ka damu da hakan, insha Allahu alkairi ne zai biyo bayan al'amarin, ba mu nufi kowa da sharri ba, duk wanda ya nufe mu dashi to babu shakka sharrinsa zai koma kansa."

Ya ce." Wannan haka yake fatan alkairi Alhaji tabbas idan hakan ta kasance za mu fi kowa farin ciki."

"Ma sha Allah." Abinda ya fada kenan; ya dauki jaridar da ya ajiye ya dan kishingida kan kujerar da yake zaune, ya ce." Ina fatan ka shedawa Labaran cewa bayan sallar la'asar za mu fita."

Yana k'o'karin tashi ya ce." Eh Alhaji na sheda masa umarinka tuntuni."


To bayan fitar Sule da minti goma kira ya shigo wayarsa.

Koda ya ga wanda yake kiran sai ya ajiye ya cigaba da abinda yake.

Sai da ta kira sau uku tukkuna ya daga, shuru yayi bai ce mata komai ba.

"Daddy ina kwana." ta fada cikin rawar murya.

A dakile ya amsa.

Sai ta fashe da kuka tana bashi hakuri "Daddy don Allah kayi hakuri ka ji."

Gyaran murya yayi babu walwala a tare dashi ya ce." Shukura kin zama mara ji ko? Fatima ta na yi miki hud'ubar banza kina dauka, kamar ni ubanki na baki umarni ki tsallake! ki fita ba tare da izini na ba, har na fita baki dawo ba shin me kike so ki zama?"

A sanyaye ta ce." Daddy wallahi ba 'kin bin umarnin ka nayi ba, tsoro nake na fad'a maka gurin da zan je, na san ba zaka bari ba shiyasa na tafi amma ai Hajiya ta sani na fad'a! mata.

"Shukura saboda kin san bana tsallake maganar Hajiya shiyasa ki ke had'a ni da ita ko?"

"Ba haka bane Daddy."

Ya ce." Nayi 'karya kenan."

"A'a Daddy ba kayi 'karya ba kawai dai na ga itama Mamana tana da hakki a kaina babu laifi idan na je in da take."

Ya ce." Ok to ki tattara kayanki gabad'aya ki koma gurinta kada na dawo na same ki a gidana."

Tana kuka take bashi hakuri!

Ya ja tsaki! da fad'in." Wallahi kiyi hattara da wannan uwar taki bata da kirki! sannan magana ta dake ta 'karshe shine kiyi gaggawar fito da mijin aure a cikin masu sonki domin ba zan lamunci sakarci ba."
Yana gama maganarsa sai ya kashe wayar ya ajiye ransa a 'bace!


Shiru tayi da wayar a hannunta tana tunanin abinda zai biyo baya, ta san halin mahaifin ta kaifi daya ne, baya magana biyu, mutum ne shi da bai yarda da shiriri ta ba, ita kuwa a yanzu dai babu wani wanda zata nuna a matsayin wanda za ta aura domin har yanzu ba ta samu wanda yayi dai-dai da rayuwarta ba, tunani mai zurfi ta shiga domin nemo hanyar warware matsalarta.


****
"Baba yau fa zai zo da daddare ku gaisa sannan kuma mu je da shi can gidanmu su gaisa da Babanmu domin gobe yake so ya koma gurin aikinsa."

Ta ce." Waye zai zo?" domin ita har ga Allah ta manta da maganar da sukayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login