Showing 3001 words to 5639 words out of 5639 words
Chapter 2 - MUTUM DA ALJAN 2 By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
idanu yayi arba da fuskar macen
tagwayen
a wannan lokaci yaga irin tsananin kyawun da
Allah ya bata wanda bai taba ganin irinsa ba
kuma
yaga cewa tabbas sarki kasheta zaiyi kuma ya
kashe dan uwanta sai ya zabura cikin bakin zafin
nama ya janyesu daga inda suke kwance tamkar
shaho ya suri yan tsaki yayi jifa dasu izuwa cikin
wata korama dake can gefe daya.Ai kuwa sai
Sarki
Alkasim ya soki kasa da makaman nasa
maimakon
ya sami nasarar soke cikinsu.Koda Namrita da
Zaihas suka fada cikin wannan fadama ruwa ya
jikasu sai nan da nan suka farfado daga suman
da
sukayi suna bude idanuwansu sai suka hango
sarki
Alkasim ya nufo su da gudu a sama tamkar ya
kasance kibiyar da aka harbo daga cikin baka
saboda karfin gudun nasa.Saura baifi taku uku ba
kacal ya sake samun nasarar soke su sai yaga
sun
daidance sun zama kamar kwayar zarra sun shige
cikin karkashin kasa sun bace bat.
★MUTUM DA ALJAN★!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part C .
★A-Haleefah Physicist★
SUN SHIGE CIKIN KARKASHIN KASA SUN BACE
BAT.Sarki Alkasim ya diro kasa bisa kafafuwansa
fuskarsa cike da kaduwa gami da mamaki yana
dube dube amma ko alamun tsagwayen bai gani
ba.Duk irin ilmin tsafin da sarki Alkasim ke dashi
bai taba sanin irin wannan lakani dasu Namrita
sukayi ba.Nanfa ya shiga amfani da karfin Sihirin
nasa na tsafi domin ya gano inda suke amma sai
abu ya faskara.Al'amarin da yayi matukar
fusatashi
kenan ya juyo ya dubi Yarima yana mai daka
masa
harara irin wacce bai taba yi masa ba har saida
Yarima yaji ya firgita hantar cikinsa ta
kada.Kawai
sai sarki Alkasim ya daka masa tsawa yana mai
cewa akan wane dalili ka tserar da rayuwar
makiyana?Shin ka gaji da ganina ne ka kosa na
mutu ka haye kan karagata?Koda jin wannan
tambaya sai nan da nan idanun Yarima suka
kada
sukayi jawur har hawaye ya zubo masa,kawai sai
ya durkusa bisa guiwoyinsa biyu yana mai
sunkuyar da kansa kasa ya bude baki cikin
sanyin
murya yace tabbas na aikata babban kuskure
kuma
babban laifi wanda ya zame mini abin nadama a
halin yanzu.Ya kai Abbana maza ka takobinka ka
sare kaina.Idan zubar da jinina zai sa zuciyarka
ta
huce daga zafin dana aikata Maka.Koda yarima
Kamsus yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki
Alkasim yayi sanyi bai san sa'adda ya mayar da
makamansa cikin kufe ba sannan yazo gaban
yarima ya kama kafadunsa ya tashe shi tsaye
suka
dubi juna ido da ido sannan yace yakai dana
hakika ka aikata mini babban laifin da bazan iya
yafe maka ba.Ka sani cewa bazan iya kasheka ba
a matsayinka na dana guda daya jal tilo wanda
nake tsananin SO da KAUNA fiye da komai amma
ya zama wajibi nayi maka horo bisa wannan laifi
daka aikata mini domin ya zamo izina a kan
dukkan jama'ar dake karkashina su san cewa
babu
wanda yafi karfin fuskantar hukuncina muddin ya
aikata laifi tunda gashi na hukunta dana na
cikina.Zaka fuskanci horo na dauri a cikin rana na
tsawon yini uku ba ci ba sha.Koda gama fadin
hakan sai sarki Alkasim ya juyawa yarima baya
sannan ya fiddo wani karamin kaho daga cikin
aljihunsa ya busa.Faruwar hakan keda wuya
saiga
shugaban dakaru Uzaila tare da dukkan yaransa
da
kuma hadiman sarki sun rugo da gudu izuwa cikin
sansanin.Da zuwansu sai sarki ya bayar da
umarnin a gyara masa tantinsa kuma a dawo da
sauran abokan tafiya.Ba tare da bata lokaci ba
aka
cika wannan umarni kuma aka sanya tsaro mai
tsauri a sansanin irin na farko.Da yake sauran
abokan tafiyar basu san abinda ya faru ba sai
sukayi ta mamakin abin da yasa sarki ya sauya
shawara haka nan da nan.
*Al'amarin jaruma Namrita da dan uwanta Jarumi
Zaihas kuwa lokacin da suka tsira da rayuwarsu
daga sharrin sarki Alkasim ya zamana cewa sun
zama kwayoyin zarra sun shige cikin karkashin
kasa basu bayyana a ko ina ba sai a can cikin
wani daji dake can bayan wanda su sarki Alkasim
suke.Tazarar dake tsakaninsu takai tafiyar sa'a
uku.A galabaice suka baje a kan kasa suna
numfarfashi kamar ransu zai fita.Saida suka
shafe
yan dakiku suna hutawa sannan suka mike zaune
a lokacin da suka dawo cikin hayyacinsu sosai.A
wannan lokaci ne kowannensu ya fada cikin
sabon
kogin tunani.Shidai jarumi Zaihas ba komai yake
tunani ba face mamaki irin tsantsar jarumtakar
sarki Alkasim gami da bajintarsa ta iya yaki.A
zatonsu shekaru bakwai da suka shafe shi da yar
uwarsa suna neman ilmin tsafi gami da karbar
horon yaki a wajen jarumai kala kala sun sami
damar da zasu iya kashe sarki Alkasim amma sai
gashi sun kasa don haka lallai aikin dake
gabansu
bana wasa bane dole ne su sake yin sabon shiri
gami da sabon tunani.Ita kuwa Jaruma Namrita
ba
komai ta fara tunowa ba face fuskar yarima
Kamsus a lokacin da ya ceci rayuwarsu sa'adda
sarki Alkasim ya fado kansu zai tsire cikinsu da
makamansa.Wai shin a kan wane dalili yarima
Kamsus ya ceci rayuwarmu?Alhalin yasan cewa
mu
makiyan mahaifinsa ne?Wane irin kallo ne yayi
mini a lokacin?Shin ya kamu da SO na ne shi
yasa
ya ceci rayuwata data dan uwana?Amma dai ya
cika SAUNA idan har saboda SOYAYYA ya tserar
da rayuwar MAKIYANSA.Koda Namrita tazo nan a
zancenta na zuci sai taji zuciyarta ta ta buga da
karfi a karon farko a rayuwarta.Kawai kuma sai
taji
babu abinda take so sama data sami damar da
zata sake saduwa da yarima Kamsus har su
zauna
suyi yar hira domin tasan gaskiyar abinda yake
cikin ransa.Ayyana hakan keda wuya sai
hankalinta
ya dugunzuma ainun saboda ta fahimci cewar
akwai alamun itama ta dan kamu da son Yarima
Kamsus.Tana cikin wannan tunani ne Zaihas ya
dubeta yana mai katse mata hanzari yace yanzu
wane mataki ya kamata mu dauka tunda dai
munyi
gumurzu da sarki Alkasim gaba da gaba babu
nasara?Koda jin wannan tambaya sai Namrita ta
kawo gwauron numfashi ta ajiye sannan tace ai
komai ya dagule a halin yanzu,tabbas ba zamu
iya
kashe sarki Alkasim ba a cikin wannan tafiya.Dole
mu hakura har a isa can birnin Sarki Masarul
Anjana.A can ne kadai zamu iya kashe shi kuma
sai mun hada kai da masanin sirrinsa.Koda jin
wannan batu sai Zaihas ya murtuke fuskarsa ya
dubi Namrita cikin alamun tsananin fushi yace
wannan kuma wace irin maganar banza ki keyi
haka?Kina nufin kice ba zamu sake jarraba
sa'armu
ba a kansa?To kiyi sani cewa abinda muka kasa
yi
anan ba zamu iya yinsa a cikin birnin sarki
Masarul Anjana ba,saboda birninsa ne birnin da
yafi ko ina a duniya tsaro.Ke dai kawai ki gaya
mini gaskiya idan kin sauya shawara ne a cikin
zuciyarki domin na fuskanci kin yaba da abinda
yarima yayi mana.Koda jin wannan batu sai
Namrita tayi farat tace ni babu wani abu dana
sauya a cikin zuciyata kuma ni Yarima Kamsu bai
★Abubakar Haleefah Physicist★
burgeni ba amma ya bani mamaki,shi yasa kaga
ina kallonsa domin banga dalilin da zaisa ya ceci
rayuwarmu ba alhalin yasan cewa so muke mu
kashe mahaifinsa.Sa'adda Zaihas yaji wannan
batu
sai yayi murmushi yace nima nayi mamaki amma
kuma ta wani fannin banyi mamaki ba,tunda inda
zaki iya tunowa tun muna yara lokacin da sarki
Alkasim ya kashe mahaifinmu Yarima Kamsus ne
kadai ya tausaya mana harma saida ya zubar da
hawaye,kinga kenan shi yafi mahaifinsa adalci da
tausayin talakawa,don haka baya goyon bayan
irin
abubuwan da yake aikatawa.Ina miki gargadin
cewa kada ki kuskura ki bari zuciyarki ta sami
rauni akan wannan gagarumin buri dake gabanmu
na daukar fansar ran mahaifinmu domin ko yaya
son yarima ya darsu a cikin zuciyarki to ba zamu
taba samun nasara ba.Sa'adda Jaruma Namrita
taji
wannan batu sai jikinta yayi sanyi ainun tayi shiru
tana mai sunkuyar da kanta kas kuma tayi shiru
har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai
ta
dago kai ta dubi Zaihas cikin murmushi tace ka
kwantar da hankalinka yakai dan uwana,kayi sani
cewa babu wani mahaluki walau MUTUM ko
ALJAN
wanda zaisa na fasa aiwatar da wannan babban
aiki dake gabanmu.Ko mutuwa nayi ruhina ba zai
kwanta ba a cikin kabari face ya dauki wannan
fansa,tunda zaluntar mahaifinmu akayi aka kashe
shi ba bisa laifinsa ba sai bisa kuskure da rashin
sani.Koda gama fadin hakan sai zuciyar Namrita
ta
karaya idanunta suka ciko da kwallah bata san
sa'adda ta fashe da kuka ba.Koda ganin haka sai
shima Zaihas zuciyarsa ta karaya don haka sai
ya
kamo Namrita ya rungume ta uana mai
rarrashinta
a lokacin da shima idanunsa suka ciko da
kwallah.
*A can sansanin su Yarima Kamsus kuwa lokacin
da sarki Alkasim ya shiga cikin tantinsa ya
kwanta
domin yayi bacci sai ya kasa sakamakon takaici
bisa ganin yadda Zaihas da Namrita suka iya
guje
masa suka bace masa da gani ya neme su sama
da kasa ya rasa.Abinda ya daure masa kai kenan
ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace yanzu
kenan akwai kalar sihirin da bani dashi a cikin
wannan duniya alhalin ina ganin cewa babu wani
boka wanda ya fini ilmin tsafi ko kuwa wannan
bacewa dasu Namrita sukayi bada sihirin tsafi
bane?Ai kuwa idan haka ne yanzu za'a iya
samun
wanda ya fini karfin sihirin tsafi anan cikin
duniyarmu ta bil'adama,ashe idan muka isa
birnin
Sarki Masarul Anjana zan iya jin kunya ko kuma
na raina.Haka dai sarki Alkasim ya cigaba da
wannan tunani da zulumi daga karshe sai kawai
ya
manta da komai yayi kwanciyarsa yaja mayafi ya
lullube jikinsa sakamakon sanyin da ake
busawa.Lokacin da gari ya waye sai aka kawowa
sarki Alkasim abincin buda baki,maimakon ya
zauna yaci abincin sai ya fito daga cikin tantin
nasa da sauri a fusace ya kwalawa shugaban
dakaru Uzaila kira.Nan da nan sai ga Uzaila ya
iso
da gudu.Da zuwansa sai ya zube a kasa gaban
sarki ya kwashi gaisuwa sannan yace ya
shugabana me kake da bukata?Koda jin wannan
tambaya sai sarki ya dubi Uzaima a fusace yace
maza ka debo dakaru kuje tantin Yarima ku kamo
shi da karfin tsiya ku kai shi tsakiyar sansanin
nan
ku daure shi a jikin Dirka yadda rana zata kare a
kansa kuma duk wanda ya bashi ruwa makwarwa
daya ko abinci kwatankwacin kwaya guda ni da
kaina zansa takobina na sare shi.Koda jin
wannan
umarni sai mamaki ya turnuke Uzaila da dukkan
dakarun dake kusa dashi amma sai Uzaila ya
mike
tsaye da sauri yana mai cewa an gama ya
shugabana.Nan take Uzaila ya zabo karti shida
majiya karfi daga cikin yaransa suka durfafi tantin
Yarima.
★MUTUM DA ALJAN★!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part D
★A-Haleefah Physicist★.
SUKA DURFAFI TANTIN YARIMA.Da shigarsu cikin
tantin sai suka iske Yarima a zaune yayi tagumi
yana mai hada kansa da guiwa kuma yana rike
da
takobinsa da hannunsa guda.Koda ganin yarima
a
cikin wannan hali sai hankalin su Uzaila ya
dugunzuma ainun suka firgita domin a zatonsu
Yarima yakarsu zaiyi kuma sun san cewa a cikin
dakiku kadan zai hallakasu su duka.Bisa wannan
dalili ne jikinsu ya kama karkarwa aka rasa
wanda
zai kusance shi bare yayi yunkurin
kamashi.Kwatsam sai sukaga Yarima Kamsus ya
dago kai ya dube su cikin murmushi sannan yace
yakai Uzaila ku kwantar da hankalinku kuyi sani
cewa babu yadda za'ayi na yake ku.Ina mai
umartarku daku cigaba da aikinku.Inason ku
kamani a wulakance kuna jana a kasa tamkar
bawa
ku kaini har can tsakiyar sansanin kuyi duk yadda
aka baku umarni don kada fushin sarki ya tabbata
a kanku.Koda jin wannan batu sai Uzaila yaji ya
kamu da tausayin yarima amma sai ya dubeshi
yace ka gafarceni ya shugabana ba'a son raina
haka zata faru ba.Yana gama fadin hakan sai ya
dubi wadannan karti shida yayi musu inkiya.Nan
take suka make yarima ya fadi kasa har lebansa
ya
dan dare jini ya zubo,kawai sai suka kama shi
suka rinka jansa a kasa tamkar tsumma suka fice
dashi daga cikin tantin.Uzaila na biye dasu har
zuwa tsakiyar sansanin.Da zuwa sai aka haka
rami
aka binne wata dirka mai gwafa sannan aka daga
Yarima Kamsus aka daure shi tamau da
murtukekiyar igiya a jikin dirkar.Kawai sai aka bar
shi anan kowa ya cigaba da harkokinsa.A gaban
Yarima akayi kalaci aka ci abincin rana dana dare
amma ko digon ruwa ba'a sanya masa a cikin
bakinsa ba.Har ma saida sarki yazo gabansa
yasa
aka gasa masa barewa ya rinka ci yana shan
ruwan inibi a gefe daya kuma ga wadansu
kuyangi
suna tika rawa sarki Alkasim nata faman kyakyata
dariya abinsa ko kallon yarima sau daya baiyi
ba.Har saida aka dauki lokaci mai dan tsawo
anayin wannan bidiri ya zamana cewa gari ya
soma duhu.A wannan lokaci yarima ya galabaita
ainun,lebansa ya bushe saboda kishirwa kuma
idanunsa har lumshewa sukeyi saboda yunwa da
jigata.Kawai sai akaga sarki Alkasim ya mike
tsaye
ya juya ya nufi inda tantinsa yake.Koda gamin
haka sai Uzaila ya ruga gareshi ya risina yace ya
shugabana zaka tafi kuma baka bayar da
umarnin
a kwance Yarima ba a bashi abinci da ruwa
ba.Koda jin wannan batu sai sarki Alkasim yayi
murmushi yace ku kyale shi sai nan da cikar sa'a
guda tukunna.Dajin haka sai Uzaila ya dubi sarki
cikin kaduwa da firgici yace haba ya shugabana
shin so kake lafiyar yarima ta tabu ne?Bai
kamata
kayi masa horo da yunwa ba ko kishirwa.Koda jin
haka sai sarki ya turbune fuska ya dakawa Zaihar
tsawa yace ka fini sonsa ne?Dana ne fa kuma shi
kadai gareni a wannan duniya.Laifi yayi mini
kuma
sai dana gargade shi a kan kada ya aikata laifin
amma yabi son zuciyarsa.Ta wannan hanyar ce
kadai zansa ya gane kuskurensa kuma ya kori
gaba.Kowa ya tafi yabar shi a wannan wuri sai
bayan sa'a guda ka aika kuyangi su kwance shi
sukai shi cikin tantinsa.Sarki Alkasim na gama
fadin hakan sai ya juya ya nufin cikin tantinsa
yaje
ya kwanta,shima shugaban dakaru Uzaila ya
gyada
kai ya tafi izuwa inda nasa tantin yake.
* A can dajin dasu Jarumi Zaihas suke kuwa
lokacin da gari ya soma duhu bayan sun bude
jakar guzurinsu sun dauko abinci sunci sai
Namrita ta dubi Zaihas tace amma fa ya kamata
muje sansanin su sarki Alkasim muyi LEKEN ASIRI
domin musan halin da suke ciki saboda babu
mamaki ya kasance suma suna shirin kawo ma
harin bazato kamar yadda muka kaiwa
sarki.Sa'adda Zaihas yaji wannan batu sai yayi
ajiyar numfashi gami da gyada kai yace tabbas
maganarki gaskiya ce amma kuma akwai hadarin
gaske mu sake kai kanmu sansanin sarki Alkasim
a yanzu domin babu mamaki sunyi mana mugun
tanadi bisa tunanin cewa zamu sake kai wani
hari.Namrita tace hakan zai iya faruwa amma ai
tunda kasan cewa na kware ainun a iya leken
asiri
fiye da kai babu wani tarko wanda dakarun sarki
Alkasim zasu iya dana mini ya kama ni.Rashin
sanin shirin da sukeyi a kanmu yanzu yafi komai
hadari a garemu.Ka kwantar da hankalinka ka
barni naje nayi wannan leken asiri nayi maka
alkawarin cewa babu abinda zai sameni kuma zan
dawo gareka lafiya lau cikin koshin lafiya.Lokacin
da Namrita tazo nan a zancenta sai dan uwanta
Zaihas yayi shiru yana tunani gami da nazarin
abinda ta fada har izuwa lokaci mai dan tsawo
daga can kuma sai ya dago kai ya dubeta yace
shi
kenan yar uwata na amince ki tashi kije kiyi
wannan aiki amma ki sani cewa idan sa'a hudu
ta
wuce banga kin dawo ba zan biyo bayanki domin
zanyi zaton cewa kin fada tarkon makiya.Koda jin
haka sai fuskar Namrita ta fadada da murmushu
tace na yarda da hakan.Tana gama fadin hakan
sai
ta mike tsaye zumbur ta dauki MAKAMANTA na
YAKI ta dauresu a jikinta kuma ta rufe fuskarta
da
wata bakar hula yadda idanunta,hancinta da
bakinta kadai ake gani,kawai saita rungume
Zaihas
tana mai yi masa sallama sannan ta juya ta
falfala
da azababben gudu izuwa cikin daji.Wani irin
gudu
ne na ban al'ajabi Namrita keyi wanda saidai a
kwatantashi da gudun tauraruwa mai wutsiya a
cikin gajimare.Nan da nan kuwa cikin kankanin
lokaci Namrita ta iso sansanin su sarki
Alkasim,nan take tayi girgiza ta zama wahainiya
ta
cigaba da tafiya a kasa tana giftawa ta gaban
dakarun sarki Alkasim ba tare da kowa ya ganta
ba saboda kalar jikinta ta saje da ciyawar
kasa.Kwatsam ba zato ba tsammani Namrita na
cikin kalle kalle da dube dube a cikin sansanin
tana nazarin komai da kowa dake wajen sai ta
hango yarima Kamsus tsaye
★Abubakar Haleefah Physicist★
kuma a daure jikin dirka a tsakiyar
sansanin.Al'amarin da yayi matukar daure mata
kai
kenan ta tsaya cak a inda take tana tunani inda
tace a cikin ranta anya kuwa wannan ba wani
tarkon bane ba aka dana mini?A daidai wannan
lokaci ne ta hango yadda bakin Yarima Kamsus
ya
bushe kuma ta lura da irin mugun daurin da aka
yiwa hannayensa da kafafuwansa.Take ta gane
cewa tabbas abin da gaske ne.To waishin akan
wane dalili sarki Alkasim zai yiwa dansa irin
wannan danyen hukunci?Kafin Namrita ta baiwa
kanta amsar wannan tambaya sai ta cigaba da
tafiya da sauri akan ciyawa a cikin siffarta ta
hawainiya ta nufi inda yarima Kamsus ke
daure.Da
zuwa sai ta daka tsalle ta dira akan kafarsa ta
cigaba da tafiya a kan kafar tasa har ta iso kan
kafadarsa.Tun sa'adda yarima yaji alamun tafiyar
wani abu a jikinsa sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun saboda yasan cewa koma mene ne abinda
ke hawa jikinsa zai iya cutar dashi tunda ba zai
iya
kare kansa ba sakamakon cewa hannayensa da
kafafuwansa a daure suke tamau.Koda Yarima
yayi
arba da hawainiyar data taho kan kafadarsa sai
yaji
tsigar jikinsa ta tashi gaba daya kuma tsoro ya
kama shi domin yaji a jikinsa cewar wannan ba
kwaro bace saidai MUTUM KO ALJAN.Kwatsam
ba
zato ba tsammani sai yaga hawainiyar ta rikide
ta
zama jaruma Namrita zaune akan kafadarsa ta
kura
masa idanu tanayi masa murmushi.Kafin ya bude
baki yace wani abu sai ta dafa kansa da
hannunta
na hagu.Take igiyar data daureshi ta kwance
kanta
suka bace tare daga sansanin.Basu bayyana a
ko'ina ba sai a can wani bangaren daban na
dajin.Kawai sai ta cire battar ruwa a jikinta ta
mika
masa tace maza kasha wannan ruwa idan ba so
kake kishirwa ta kasheka ba.
ME ZAI FARU A YANZU TSAKANIN YARIMA
KAMSUS DA JARUMA NAMRITA?
SHIN SU JARUMI ZAIHAS ZASU SAMI NASARAR
DAUKAR FANSA A KAN SARKI ALKASIM?
YAUSHE NE ZA'A ISA BIRNIN SARKI MASARUL
ANJANA?
WADANNE ABUBUWAN MAMAKI NE ZASU FARU A
FADAR SARKI MASARUL ANJANA?KUMA WANE
IRIN
DAUKI BA DADI ZA'AYI?
WAYE ZAI DACE YASA GIMBIYA ZULFULAIFA
DARIYA KUMA WANE LADA ZAI SAMU?
Mu Hadu A Mutum Da Aljan.
Littafi Na Uku Don Jin Cigaban Wannan Labari.
Mene Hasashen ku game da wadannan
tambayoyi?