Showing 3001 words to 6000 words out of 6100 words

Chapter 2 - Mutum Da Aljan Book 5 By Abdulaziz Sani Madakin Gini.doc

tafiyarmu duk
inda
kika ga nasa kafata kema ki saka
naki
ina gama fadin hakan saina nufi kan
karshen
gefen kogin tabon naci gaba da tafiya
akan
kogin hankali kwance tamkar ba
akan kogin
tabo nake ba
ita kanta luslaiya sai abin ya daure
mata kai
ta kamu da tsananin mamaki sai da
na fara taka
inda nake takawa sannan na gane
cewa ashe
bushashshen tabone a wajan ba
danye ba
duk da haka luslaiya bata yadda taci
gaba
da yin gudu ba akan busashshen
tabon
a hankali ta rinka tafiya har muka
tsallake kogin
tabon gaba daya
muna fita saita sake falfalawa da
gudun gaske
nima saina rufa mata baya sai da
muka yini
muna gudu ba tare da mun tsaya ba
ko mun
hadu da wata matsala ba ko kishirwa
ta kama daya daga cikinmu
sai dai ya daga battar ruwansa yana
cikin
gudun ya dan sha kadan yaci gaba da
gudu a binsa
A wannan lokacine nayi tunani na
gane cewa zamu gane kuskurenmu
anan gaba
tunda bamuyi guzurin abinci ba sai
guzurin
ruwan sha shi kansa ruwan shan ba
zai ishemu ba a cikin tsawon
kwanaki
taran da zamu yi muna wannan gudu
to wai shin
idan yunwa da barci
suka kamamu a cikin wannan gudu
ya zamuyi?
Amsar da na kasa baiwa kaina kenan
haka muka
ci gaba da gudu har gari ya soma
duhu koda
luslaiya taga gari ya soma duhu bata
ganin gabanta
sosai saita daga hannunta na hagu
sama nan
take fitilar ice ta bayyana a hannunta
nima sai nayi irin tsafin da tayi
na samu fitilar
Wohoho ! Ba a sanin maci tuwo sai
miya ta kare kuma
ba a sanin jimrau sai idan ba a san
karshen wuya ba
haka dai muka ci gaba da gudu a
cikin dajin ba sassauci tamkar
jikinmu bana jini da tsoka bane
domin babu alamar
cewa zamu sare
ba wai gajiyar bace babu a jikinmu
tsabar juriyace
kawai da sabo, sai dare ya soma yi
sannan
yunwa da barci suka fara damunmu
amma saboda naci muki yarda
mu sare ko mu tsaya hutawa ko yada
zango
Al amin Ahmed Misau
Guyson
Lokacin da luslaiya taji cikinta ya
fara murdewa
saboda yunwa saita fara tunanin
mafita
nima a wannan lokaci na fara shiga
irin wannan
hali da ta shiga don haka burina
kawai shine
naga ta sare na fadi kasa nima sai
kawai na zube
kasan don haka dolenemu yada
zango a wajan
ba zato ba tsammani sai kawai naga
luslaiya
ta daka tsalle sama izuwa kan wata
bishiya
ta cafko wani tsuntsu tana dirowa
kasa taci gaba
dagudunta
tana cikin gudun ta kafawa tsuntsun
hakoranta
akan makoshinsa ta cisge masa
wuya kawai sai
ta kama shan jininsa
bayan ta gama tsotse jinin saita
kama fige
gashin tsuntsun tana gama figeshi ta
kama cinsa
danye a haka ta gama cinyeshi
Koda ganin abinda luslaiya tayi sa
nayi koyi
da ita amma fa sai dana ji kamar
zanyi kumallo
domin ban taba cin danyen nama ba
a rayuwata sai a sannan.
Zidane
Mutum Da Aljan
Littafi na biyar (5)
Part C.
.
Marubucin littafin:
Abdul aziz sani madakin gini
Typing by'
Al amin Ahmed Misau Guyson
Contack: 08064594218 for more
Doka' ban yarda a sarrafa wannan post ba
inbada izinina ba.
!
Labari ya isowa guyson cewa...
Hakika dole kanwar naki ce domin inda banci
wannan danyen tsuntsun ba da tabbas yunwa
zata iya min lahani
hakika a cikin wadannan kwanaki tara naga
abubuwan al ajabi a tare da jaruma luslaiya
babban abin da yafi burgeni da ita shine
yadda take iya yin barci a lokacinda take cikin yin gudu
ba tare da tayi karo da bishiya ba ko dutse
da zarar ta tunkari bishiya ko dutse saitazo daf
da su saikaga ta goce musu ta wuce lafiya lau
ni kuwa sai da na rinka yin karo da bishiyoyi da duwatsu
ina jin ciwo da faduwa tsabar naci da juriya
ce tasa ban sare ba naci gaba da gudu a hakan
a wannan lokacine na tabbatar da cewa luslaiya
ta samu horo da ni bani dashi hakika munsha
bakar wahala a cikin wadannan kwanaki
tara tamkar zamu rasa rayukanmu amma har
lokacin ya cika ban sare ba
a ranar kwana na taran ma a jere muka iso
farkon wani daji wanda ke cikin nahiyar kasar
teheren da yammaci ne muka iso farkon dajin
kawai sai naga luslaiya ta zube kasa bisa
guiwoyinta tana haki nima sainazo na zube
kasa daf da ita
kawai saita dubeni tace tabbas na yarda kai
jarumine na gaske domin kaine mutum na
farko daya jure irin wannan wahala tare dani
tsawon kwana tara ba tare da ya rasa rayuwarsa ba
yanzu ka tsallake matakin farko na gasarmu
amma ina mai tabbatar maka da cewa babu
yadda zaka iya tsallake mataki na biyu bare
har ka kai kan mataki na uku
yanzu ne zamu yada
zango mu huta kuma mu kwana sai gobe da
safe zamu ci gaba da tafiyarmu koda gama fadin
hakan sai luslaiya ta zare addarta guda dake
kan cinyarta ta hagu ta yunkura zata wuce ta
gabana a zatona ni zata kawowa hari don haka
nima saina yunkura na zare takobina amma sai naga
kawai ta wuce ta nufi inda wata bishiya take
mai dogayen rass ta fara saranta da yake
masu iya magana sunce idan kaje gari kaga
kowa da bindi kaima saika daurawa kanka sai
kawai nima naje na taya luslaiya aikin da takeyi
nan da nan muka saro rassan bishiyoyin da yawa
muka tarasu a waje guda daga nan kuma sai
naga taje ta kama yanko wadansu busassun
jijiyoyi na bishiya masu kwari gami da wadansu
irin manyan ganyaye na wata bishiya ta musamman
masu fadi nidai sai naci gaba da yin koyi
da ita bayan mun gama tara wadannan kyayyakin
sai luslaiya ta shiga gina daki kawai saina tayata
muka kammala ginin har da kofa da rufi kai
kace kwararrun magina ne suka yi aikin abin
gwanin ban sha awa saiga kyakkyawan karamin gida a tsakiyar dokar daji
tunda muka fara wannan aiki da yammacin
bamu kammala aikin ba sai da dare ya soma
a sannan ne wata irin matsananciyar gajiya ta riskemu kuma kwasam
sai hadari ya gangamo aka fara tsawa da walkiya
nan take luslaiya ta shige cikin wannan daki da muka
gina ta turo kofa zata rufe saina kare da hannuna
nace ya ya zaki shige kuma ki rufe min kofa
koda jin wannan tambaya sai luslaiya tayi min.
Wani irin kallo mai nuna tsantsar kiyayya tace
wane ne kai a gareni har da kake tunanin zamu
kwanta tare a cikin daki guda
hm Guyson sunana wannan abun ya ban mamaki..
Ni ba kowa bane a gareki kuma bazan taba
kusantarki ba amma ina da ikon kwana a cikin
wannan daki tunda dani aka ginashi
luslaiya ta sake hade fuska tace gani kayi ina
aikin ginin wannan daki ka tayani amma ban
gayyaceka ba don haka daki nawane ba naka ba
idan ka matsa saika shigo saidai muyi yaki
mu baje dakin gaba daya tana gama fadin
haka saita bangajeni nayi baya taga taga
kuma ta banko kofar dakin ta kulle abinta
faruwar hakan keda wuya aka fara yin wata
irin iska mai karfin gaske sannan kuma aka kece
da ruwan sama tamkar da bakin kwarya
nan take na jike sharkaf, kawai sai naga luslaiya
tana lekena ta cikin tagar dakin nata tana yi
min murmushin mugunta haka dai ruwa yaci
gaba da dukana inaji ina gani ga inda zan fake
amma babu dama ba komai ne yasa naki
matsawa akan saina shiga dakin ba face nasan
cewa ruguza dakin zamuyi a banza alhalin
mun sha wahalar gaske wajan ginashi
baya ga haka ni har a cikin zuciyata bana son
abinda zai sa luslaiya ta sha wuya ko zuciyarta ta
sosu saboda soyayyata a gareta ta gaskiyace
hm So kenan '
lokacin da ruwan saman yaci gaba da dukana ga
iska mai dan karan sanyi na kadawa sai nan
da nan zazzabi ya rufeni jikina ya kama karkarwa
nan fa na fara tunanin neman mafaka kawai sai na ruga
izuwa gabas da yamma kudu da arewacin dajin
ina neman inda zanga wani kogon dutse na shige
cikinsa amma ko alamunsa ban gani ba
nan take na gane cewa luslaiya mugunta ta
shirya min dama tasan cewa babu mafaka a ko ina cikin
dajin kawai sai naji raina ya baci zuciyata ta
fara ayyana min cewa kawai na koma wajan
luslaiya na fasa kofar dakin na shiga da karfin
tsiya in yaso kome zai faru ya faru har na
yunkura zanje na aiwatar da hakan sai na
tuno da nasihar mahaifina cewa na jure duk irin
wahalar da zan sha a cikin wannan tafiya
tawa tare da luslaiya don haka
Haka saina fasa kawai na dawo kusa
da dakin nata na haye kan wata bishiya na kwanta
ina mai takure jikina a lokacin da ruwan saman
yaci gaba da zaneni ina ta karkarwar jiki
saida aka shafe kusan sa a hudu ana tafka wannan
ruwan sama sannan aka dauke dif
A sannan ne zazzabin jikin nawa ya kara zafi
ainun gashi kayan jikina a jike suke sharkaf
kuma gashi duk itatuwan dajin sun jike babu
damar na kunna wuta naji dumi A wannan
lokaci alfijir ya keto don haka har gari ya waye
sosai ina cikin mugun yanayi na rashin lafiya
sannan ga tsananin yunwar dake damuna domin
rabonmu da abinci tun jiya da rana sa adda
muke gasar tseren gudu na tsawon kwana tara
sa adda kowannenmu yaci danyen naman tsuntsu
kwatsam saiga luslaiya ta fito daga cikin
wannan daki a shirye cikin nutsuwa da cikar lafiya a hannunta akwai
cinyar wani katon tsuntsu gashashshiya tana ci
Al amarin dayayi matukar daure min kai kenan
na cika da tsananin mamaki na tambayi kaina
a cikin zuciyata nace yaushe ne luslaiya ta
farauto tsuntsu har ta gasashi ban sani ba
koda nayi tunani mai dan zurfi saina gane
cewa lallai yaudarata tayi dama can ta tanadi
wannan nama a cikin jakar guzurinta ban sani ba
kuma tana sane taci naman danyen tsuntsu don kada nasan tana da
wani guzuri a boye
kawai sai naji wani irin takaici ya rufeni na sake
tambayar kaina nace akan wane dalili luslaiya
ta tsaneni haka har take son ta cutar dani
matuka ga ya Alhalin ni ban taba zama abokin
gabarta ba amsar dana kasa baiwa kaina kenan
luslaiya ta taho gareni a lokacin da nake bisa
wannan bishiya cikin halin rashin lafiya
jikina nata tsuma
kawai saita dago kai ta dubeni cikin murmushin
mugunta tace lokacin gabatar da gasarmu ta biyu yayi sai ka sauko domin mu
kama hanyar zuwa birnin Arnan daji inda zamu
sato gunkin da suke bautawa
koda jin wannan batu sai hankalina ya
dugunzuma ainun na dubeta cikin mamaki
da fushi nace Shin bakya ganin halin da nake ciki ne
na rashin lafiya da matsananciyar yunwa?
Ta yaya zan iya ci gaba da yin wannan gasa a haka
kodajin wannan batu sai luslaiya ta bushe da
dariyar mugunta lokaci guda kuma ta hade fuska
tace ashe kenan ka yarda na lashe wannan gasa
tabbas baka cika jarumi ba wannan ya nuna
cewa na fika karfi da jarumtaka
kafin luslaiya ta gama rufe bakinta tuni na duro kasa
daga kan bishiyar da nake kwance na duro
bisa kfafuwana na tsaya cak a gabanta nace
har abada namiji yana gaba da mace yunwa
da rashin lafiya ba zasu saki lashe wannan gasaba
mujezuwa mahaukaci ya hau kura zamuga inda zata kaishi.
Koda jin wannan batu sai luslaiya tayi min
murmushin mugunta ba tare da ta sake cewa dani
uppan ba saita juya ta falfala da gudu izuwa cikin daji
ai kuwa nima saina ware na bita a guje muka kasa tsere
tamkar babu wata lalura a tare dani amma ni
nasan abin da nakeji
tabbas nasan cewa ba karamin ganganci nayi ba
domin idan har yaki ya balle a tsakaninmu da Arnan
dajin da zamujewa ina cikin wannan hali komai
zai iya faruwa a gareni tun da babu cikakken karfi
da kuzari a jikina.
Kash! Tabbas rashin sani yafi dare duhu
ashe wani babban tarkon mugunta luslaiya
ta shirya min wanda ta tabbatar da cewa indai
na fada cikinsa babu makawa saina hallaka
ni kuwa gogan naka sai naci gaba da tsala gudu
kokarina kawai na risketa mu jera tare in yaso duk
masifar da zan shiga mu shiga tare sai da
muka shafe sa a daya da rabi muna ta tsala azababben gudu a cikin dajin tamkar zamu tashi sama a wannan
lokacine naji jiri ya fara dibata ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????saboda muguwar
yunwar da nakeji gami da rashin lafiyar dake addabata
amma saboda bakin naci irin nawa
gami da juriya irin ta manyan mazaje sai naki
sarewa.
Ita kanta luslaiya tayi tsananin mamaki bisa
ganin yadda nake iya yin wannan gudu da dukkan karfina tamkar bani da wata lalura
muna cikin yin wannan gudu ne ba zato ba
tsammani naga wani wawakeken rami a gabanmu
mai tsananin fadi da zurfi gashi babu damar muyi turjiya mu hana kanmu fadawa
cikin ramin,
kawai sai naga luslaiya tayi wuf ta zaro wata doguwar
igiya daga cikin jakar guzurinta mai kugiya a karshenta tana
sama ta cilla igiyar izuwa can karshen ramin ta sakalo dutse sai gani nayi ta tsallake ramin da dire can samansa
ni kuwa saina fada can kasan ramin ina mai
kwala uban ihu saboda na tabbatar da cewa mutuwace tazo da sauri
luslaiya ta rugo izuwa bakin ramin ta leko
lasansa amma saboda tsananin zurfin ramin ko
hangoni batayi kawai saitayi murmushin farin ciki
saboda ta tabbatar da cewa na halaka
ita kuwa ta lashe wannan gasa cikin murna ta
juya tayi gaba ta kule cikin daji
Al amarina kuwa lokacin dana fada kasan wannan
mugun rami mai tsananin zurfin gaske ina
kwala ihu cikin karayar zuciyar saina fara kokarin
ceton ratuwata ta hanyar amfani da karfin
sihirin tsafi amma sai tsafin nawa yaki tasiri
Al amarin daya kara tabbatar min da cewa
lallai ajalina ne yazo ban isa karshen wannan
rami ba sai bayan kimanin dakiku dubu daya
da dari shida saboda mugun zurfinsa.
Nidinne Dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
First Admin na
zauran labarai
page 2017
Zidane
Mutum Da Aljan
Littafi na biyar (5)
Part D.
.
Marubucin littafin
Abdul aziz sani madakin gini
typing by
Al amin Ahmed Misau Guyson
contack: 08064594218 for more
Doka' banyarjeba a yi edit na post dina....
.
Labari ya isowa guyson cewa..
Ashe acan karshen ramin kasusuwane na matattun dabbobi, tsuntsaye da mutane bisa rashin sa'a
kuwa sai na fado akan kashin wata dabba mai tsini
take kashin ya sokeni a gefen cikina ya faso
ta gadon bayana nidai kawai naji ganina dajina sun dauke
duf,
ban sake tuno da komai ba sai bayan wadansu
sa'o'i sannan na farfado daga dogon suman da nayi
koda na bude idona naga katon kashin dabba
a cikin cikina har ya bullo ta gadon bayana kuma
ga jinina ya zuba da yawa a kasa sai na kamu
da tsananin mamakin abinda ya hanani mutuwa
cikin tsananin juriya da karfin hali na yunkura
ina mikewa sama kashin na fita daga cikin cikina
a sannanne na rinka kwarara uban ihu gami da
kururuwa mai ban tsoro saka makon mugun zafi da radadin da nake ji a cikina
aikuwa ina gama zare kashin daga cikin cikin
nawa na sulale kasa mutuwa nayi ko suma ban sani ba
lokacin da jaruma luslaiya ta barni a cikin
wannan rami wanda ta tabbatar da cewa na gama
halaka sai ta nufi wata hanyar daban wacce
zata kaita can birninsu na taheren a maimakon
ta nufi birnin Arnan daji inda zamu yi
gasarmu ta biyu
har tayi nisan zango Arba'in a cikin tafiyar tata
sai wani tunani ya fado mata a rai ta tsaya cak
a inda take ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tace
yanzu idan na isa gida da wacce hujja zan
gamsar da mahaifina cewar nice na lashe wannan gasa
wacce mukayi nida yarima Alkasim lallai idan
ina son ya gamsu dolene na koma can bakin ramin
nasan dabarar da zanyi na shiga cikinsa na dauko
gawar Alkasim na tafi da ita
gama ayyana hakan keda wuya sai luslaiya ta
juya da baya da gudu ta nufi inda ta baroni bata
iso ba sai bayan sa'o'i
da isowarta bakin katon ramin sai tayi turjiya
koda ta leko kasan ramin a karo na biyu taga
baata iya hango karshensa ba
saboda tsananin zurfinsa sai hankalinta ya
dugunzuma kuma zuciyarta ta buga da karfi tace
kai kada nima fa naje na hallaka a banza a kokarin
shiga wannan rami tunda kowanne irin tsautsayi zai iya faruwa a gareni
wata zuciyar kuma sai tace da ita to ai baki
da wani zabi wanda yafi ki shiga cikin wannan rami
ki dauko gawar sarki alkasim inba haka ba kuwa
duk wannan wahalar da kika sha a baya ta
zama ta banza domin baki da hujjar da zaki
tabbatar da cewar kece kika lashe wannan gasa
taku a wajen mahaifinki
sarkin mafarauta na birnin taheren koda gama ayyana hakan sai ta fara
tunanin irin dabarar daya kamata tayi don shiga
kasan wannan mugun rami ai kuwa bata dade
tana tunanin ba dabara ta zo mata
wannan igiyar tata mai kugiya ta sake fiddowa
ta sakalata a jikin wata bishiya mai kauri ta sulala
izuwa kasan ramin sannan ta runtse idanunta
ta fara yin wani irin sihirin tsafitake igiyar ta ringa karawa kanta tsawo
tana sauka izuwa kasan ramin nan fa luslaiya
ta rinka ganin zurfin ramin a cikin idanunta
ai kuwa igiyar bata isa can karshen ramin ba sai bayan sa a uku al amarin
daya yi matukar dugunzuma hankalin luslaiya kenan
amma da yake bata da wani zabi dole ta kama
igiyar ta fara sauka kasan ramin kafin luslaiya ta isa kasan ramin saida ta shafe
tsawon sa a ukun ta sha bakar wahala kuma babu yadda bata yi ba ta isa
kasan ramin da sauri bisa karfin tsafi amma abu ya gagara
koda ta dira a karshen ramin sai tayi arba da gawata a kwance cikin rub
da ciki ga ramin da kashin dabba yayi min
a gadon bayana
cikin farin ciki ta matso daf dani ta tsugunna tana haki
sakamakon muguwar gajiyar da tayi don
haka dolene ta huta tsawon lokaci sannan ta dauke
gawata ta saba a kafadarta ta kama igiyar ta hau tayi sama
wannan tunani da tayine hankalinta ya dugunzuma
ta tuno da wahalar da tasha ita kadai bare kuma
yanzu ga dakon gawa
sai da luslaiya ta shafe sa aguda tana huce gajiya
dake jikinta sannan ta mike tsaye ta kama gawata
da nufin ta dorata akan kafadarta
kwasam ba zato ba tsammani sai taji nasa
hannuna na tunkudeta ta fadi can gefe daya
cikin tsananin juriya da zafin nama na kama rigar jikina na yageta sannan na
daure ramin raunin jikin nawa kuma na
mike tsaye bisa kafafuna na dubeta tana daga zaune a kasa dirshan gaban
kwarangwalolin dabbobi da mutane nace
har yanzu ban mutu ba don haka gasa bata kare ba saimu ci gaba
saboda tsananin kaduwa da mamaki luslaiya kasa yin magana tayi da motsi
kawai saita bude bakinta tana kallona kawai
daga can saita bushe baki tace kai mutun ne ko Aljan?
Yaya akayi ka rayu baka mutu ba alhalin
ga wannan mugun rauni a cikinka mazajen
kwarai basa faduwa a banza domin ransu
tamkar na karfe ne
Ina gama fadin hakan sainayi wuf na finciko
jakar guzurinta na budeta na fiddo ragowar wannan
gasasshshen tsuntsu data boye na kama ci har
saida na koshi
ina gamawa na zura hannuna a cikin aljihuna na fiddo wani
kullin garin magani na zazzagashi akan raunin
cikin nawa
take wajen ya kama turon da hayaki tamkar wuta
aka zuba masa na rinka ihu da kururuwa saboda tsananin zafi da
Radadin da naji har saida raunin yayi baki
kirin kuma ramin ya toshe tamkar wajan bai taba
hujewa ba sannan na daina ihu da kururuwa
kawai saina dubi luslaiya nace tare zamu
hau wannan igiya taki mu fice daga cikin
wannan rami don bazan yarda ki rigani fita ba
koda sarki Alkasim yazo nan a cikin labarin
da yake baiwa yarima kamsus sai ya daga
masa hannu yana mai dakatar dashi yace
tsaya haka yakai Abbana nifa gaba daya kaina
ya daure da jin abubuwan da suka faru a cikin
wannan labari naka
Wai shin kana son kace dani sai da kuka kammala
wannan gasa kenan? Anya kuwa zaka gama bani
wannan labari kafin mu isa birnin sarki
Masarul Anjana?
.
SHIN ME ZAI FARU A CIKIN TAFIYAR YARIMA
ALKASIM DA JARUMA LUSLAIYA? KAFIN SU KAMMALA
GASARSU HAR TA KAMU DA SONSA SUYI AURE KUMA
MENENE SANADIN AJALINTA? IDAN AKA ISA GARIN
SARKI MASARUL ANJANA ME ZAI FARU TSAKANIN
GIMBIYA ZULFULAIFA DA YARIMA KAMSUS
KUMA MAI ZAI FARU A TSAKANIN

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login