Showing 1 words to 1898 words out of 1898 words
Chapter 1 - TURBAR GASKIYA Book 7 by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf
TURBAR GASKIYA
Part 7
Rubutawa
MADAKIN GINI
bi su da tsananin harbin kibiyoyi yanda za mu rage yawansu idan ya so kafin su ankara damu
sai mu juya da baya mu gudo"
Koda Sadauki Askam ya ji wannan shawara daga yaronsa Kuffura sai ya yi aminci da wannan
shawara nan take ya yi umarni da a ci gaba da bin bayansu, sannan ya yi umami kowa ya fitar
da masunsa.
Nan take dakarun suka bi umaminsa suka nikata abinda ya umarce su da su yi.
Koda suka dunguma zasu fara tafiya sai suka ga mutum a bayansu, su duka suka waiga. Suna
waigawa sai su ka yi ido biyu da gimbiya Shadilat, sune ganinta suka gancta kamar yanda ita
ma ta gane su, ba komai yasa suka shaidata sai ganin kamanin da su ka yi da Sarki Abu
Zaiyan, nan take sai Askam ya kyaikyale da dariyar mugunta, Sakamakon dariyar da yake yasn
daukacin jama'arsa su ma suka kaure da wannan shu'aumar dariya.
Gimbiya Lushmaira tana tsaye da jaririn Zakinta a hannunta tans binsu da kallo cikin tsananin
mamakinsu
Nan suka kuma daina dariya da kansa
Sadauki. Askam ya yi kanta da niyar ya kamata, amma kafin ya isa gareta sai kawai ya ji wani
irin ibu yana ta shi daga bayansa, kukan fitar rai ko da ya waiga sai yaga at tini an ei karfin
sama da motum duba a cikin dakarunsu
Yana duban Dakarun nasa suna sulatewa kasa suna faduwa, amma ya kasa ganin wanda yake
musu wannan barnur saboda tsananin zafin namar mai aikata kisan, bai ankara ba ya ga gaba
daya dakarun duk an karkashesu, ya zama dan kauye sai waige yake yana son ganin wani
mala'ikan daukar rai ne ya zo yake girbar masa Dakaru.
Ba shi ba hatta Gimbiya Lushmaira kallon mamaki take, cikin tsananin faduwar gaba Yarima
Zaiyan ya bayyana a daf da shi, wanda saboda tsananin firgici Sadauki Askam sai da ya saki
fitsari a wandonsa.
Gimbiya Lushmaira tsananin mamaki ya hana bakinta rufawa saboda irin jarumtakar da Yarima
zaiyan ya yi amfani da ita wacce bata taba ganin ya yi irinta ba.
Sadauki Askam ya dubi Yarıma yana Rirma ya zuba giwowinsa a kas, yana neman yafewa
Koda Yarima ya dube shi sai ya tsar ta masa yawo a fuskarsa.
"Ahir dinka da a ke kiranka da gwarzon Sadauki kuma har yake jagoranta wadansu Dakaru dan
aiwatar da wani shiri na karkashin Rasa, ina son ka sani duk kan shirin ku mun fara saninsa
daga fara shigowa cikin wannan dajin haka zalika ko da aka fita daga cikin dajin nan ni ban fita
ba ina nan ina son na ga sabon shirin da zaku kulla.
Dajin wannan batu sai jikin Sadauki Askam ya kara rawa, yana makyakkyata, shi kuwa sai
Yarima Zaiyan ya dube shi cikin fushi ya ce, ka dauki daya bayan daya ka dora dukkan dakarun
da na salwantar akan dokinsa ina nan ina jiranka.
Aikuwa nan da nan Sadauki Askam ya fara aikin cikin sauri-sauri gudu-gudu, kafin wani lokaci
har ya kwashe su duka, ya na gama dora su a bisa dawakan kowannensu sai Yarima Zaiyan ya
dube shi ya co.
Ya kai wannan sakaran jarumi kasan abinda ya sa na sa ka aikata haka,?"
Cikin rawar jiki Sadauki Askam ya ce, "ya shugabana ban da masaniya akan bakan.?" Da jin
haka sai Yarima Zaiyad ya yi
murmushi ya cc, "Abinda hakan ke nufi shi no za ka jagoranci gawarwakin izuwa sansaninku ka
labartawa sakaran Samkanku yanda aka yi aka salwantar da rayuwakan wadannan dakaru, ka
basu labari ni ne Yarima Zaiyan daya daga cikin dakarun cikin birnin Baitul Haural ina so ka
sanar dasu cewa guguwar bala'i tana daf da isarsu kuma duk irin shirin da suke tunanin za su yi
a kanmu mun riga mun gama da ku, fatanmu mu hadu a fili daga mu gidaddabaku in har ba
zaku bi TURBAR GASKIYA BA.
Koda Yarima Zaiyan ya gaba sanar da Sadauki Askam wannan sako sai ya juya da niyar ya yi
gaba ya barsu a nan da Gimbiya Lushmaira.
Nan take gimbiya Lushmaira ita ma ta yi gaba batare da damuwa da shi ba. Yana tafiya kawai
ya ga ta zo ta wuce shi ranta kuma в басс
bata ko kallonsa, ga jaririn Zakinta a hannu Koda Yarima Zaiyan ya dubeta sai ya yi sauri ya ya
sha kanta, ita ma ta tsaya su ka yi
cirko cirko suna kallon juna na tsawan lokaci a farko kallon kurillar da sukewa junansu, basu
san a irin matsayin da suke ba, domin kuwa kowannensu wani tunanin ya tafi na daban.
Yarima Zaiyan ya dawo haiyacinsa ya yi saurin dubanta kamar bai shiga wani hali na tsawon
lokacin da ya yi yana dubanta ba, ya ce cikin kakkarfar murya kamar yana doka mata Isawa.
Take ita ma ta dawo haiyacinta ta dube shi da shakka, tana saurarensa.
"Yake wannan karamar yarinyar mai shirin zama jaruma, hakika a yanzu na tabbatar da cewar
kin yi kokarin da idanuwanki za su iya jure ganin irin gagarumin gumurzun da zamu kwafsa
tsakaninmu da makiyanmu, tabbas, bana da haufi ba zaki tsorota ba a yayin da idanuwanki
suke kallon wannan gumurzu, sakamakon wannan bajintar da kike na dauko jariririyar dabba."
Yana zuwa nan a cikin zancensa sai ya juya da niyar ya wuce gaba, da ganin haka sai Gimbiya
Lushmaira ta dakatar da shi da cewa.
"Kai kuma a yau ne na fara tunanin dinbin
shekaru da ka dauka kana kowan yaki, duka ka yi su ne a banza, domin kuwa ka bani mamaki
da har kake fada na shammata, duk wani jarumi mai ji da tumbatsarsa jarumtarsa, baya yaki da
wanda bai shirya ba, dan haka akwai saura rina a gabanka."
Tana zuwa nan a jawabinta sai ta cilla masa jaririn Zakin ta yi gaba cikin gudu kafin ya dawo
daga mamaki kalamanta tuni ta yi nisa.
Cikin sanyi jiki ya baro cikin dajin Shi kuwa Askam tuni ya dauke hanya yabi wata siririyar hanya
wacce ta zagaya ce ya tura dawakan da matattun dakarun da suke kal
Koda Gimbiya Lushmaira ta isa cikin tawagarsu ta yi sauri karasa inda sahunsu yake ta tarar da
Shadilat a cikin sahu tana tafiya, koda Shadilat ta ganta sai mamaki ya rufeta har ta kasa yin
hakuri ta kamo hannun gimbiya Lushmaira ta cc.
"Ya ke 'yar uwata shin yaya a ka yi kika kamo a cikin wannan tafiya, da tuni na cire rai dake.?"
Da jin haka sai Gimbiya Lushmaira ta yi murmushi tun daga lokacin da tafi kawo irin
waggwarmayar da ta yi da Zakunan zuwa lokacım da Yarima Zaiyan ya ise ya yi yaki de Dakaru
sama da duhu goma da irin bajintar da ya yi, ta kuma dora irin yanda Yariman ya gwasalets a
cikin tafiyarta da kwazonta sannan ta Kare da ita ma irin gwasale shin da ta yi, duk ta sanar da
ita
Da jin wannan bayani sai Shadilat ta ce, "A gaskiya kin yi kokari kuma na yaba da irin kwazonki
domin kuwa ban yi tsammanin samun nasararki ba, ni kuwa yanzu a hali da nake ciki na fara
tsanar jarumtakata, kai in takai ce miki na duda da duk wani Rudiri nawa.
Gimbiya Cikin tsanenin mamaki Lushmaira ta dubi Shadilat ta ce.
"Ke kuwa akan me yasa?"
Shadilat ta yi wani kayataccen murmushi ta dubi Gimbiya Lushmaira ta ce.
"Ke kuwa mai kike tunanin zai saka ni a cikin irin wannan hali in ba soyayya ba, ya ke ananiyata
ina so ki sani a cikin 'yar gajeriyar tafiyar da muke, sakamakon rashinki a tare da ni, sai Yarima
ya ke zuwan min lokaci lokaci yana aya ni hira, a wannan lokaci han yi sune ba
tsananin soyayyarsa ta shuga cikin raina"
Kafin Shadilat ta gama zuwa Kurshen maganaria gaban Gimbiya Lashmaira ya yanke ya fadi
want iris kashi ya turnukata, da kyar ta iya kawar da damuwarta ta dubi Shadilat cikin mma
rashin damewa ta ce
"Amma dai ke kuwa kin yi asara a kan soyayya ki zubar da irin burukanki tabbas na yi dana
sanin Kulla Kawance dake, domin kuwa a tafiyata bana son sakarci ni kuwa ban dauki soyayyar
komu face sakarci in har zaki yi soyayya to babu shakka ke sakaryace."
Wannan magana ba Karami bakantawa Shadilat rai ya yi amma sai ta yi murmushi ta ce, Ko da
zaki rabu dam, ha zan ji takaici ba tun da dai ina tare da gwarzon namijn duniya kuma shugaba
ga wannan tafiya ina so kuma ki yi sani, Yarima Zaiyan ne kadai zai iya yin nasara akan
dukkanin Kudirinki domin kuwa a yanzu a kaf cikin wannan nahiyar babu sadauki mai karfinsa
da kwarjinsa dan haka kada kı taba tunanin ke ce zaki iya soke daya idaniyar Maciyar Burukul
Kursum, kuma shi ne zai zama gwarzon kami a cikin wannan gagarumin yaki da za a kwafsa,
tabbas idan ya zamo abin gabarki a yanzu zai zamo abin son ki a nan da wani dan lokaci mai
zowa, ina mai shawartarki da ki yi biyayya a gare shi domin ki samu saukin bakin cikin rugaza
miki kudiri da zai yi
Koda gimbiya Lushmaira ta ji wannan ba tu sai ta fusata ta cire hannu daga rikon da Shadila ta
yi mata ta bar gun cikin tsananin fushi, tana barın gun kuwa ta shiga wani sahu a na ci gaba da
tafiya.
A dai-dai wannan lokacin kuwa aka tsaya yin sallar Azahar, wannan damar ce ta sa Gimbiya
Lushamaira ta samu guri ta zauna dukkanin abubuwan da Shadilat take sanar da ita nan take
ya dinga dawo mata, wani tsananin kishinta ta ji, tabbas a yanayin jarumtakar da Yarima yake
nunawa zai iya zamowa gwarzon Karninmu dan haka abinda ya kamata ta yi shi ne ta ta yi
kokarin da zata zamo itama za a yabeta tana da masaniya ko da bata kai Kokarinsa in har ta
zamo masa na biyu to bai isa ya yi mata wani kuri ba, da wannan tunanin Gimbiya Lushmaira ta
ta shi ta tafi ta yi alwala, sai dai lokacin da ta dawo daga yin tsarki sai ta hango Shadilat da
yarima Zaiyan suna hira har da kyalkyalewa da dariya, wannan abu ba Karamin yi mata ciwo ya
yi nan take wani tukokin kishi ya rufcta
Koda aka idar da sallah za'a ci abinci bata bari ta je inda Shadilat take ba saboda yanzu
haushinta ma take ji, a haka aka ei gaba da tafiya
A can kuma san sanin su Sarki Madhan lokacin da suka iso bakin filin da za yi wannan yaki sai
suka isaya da tafiya nan take kuma aka kama kafa tantun domin a samu hucewa kafin.su samu
sako daga jama'ar Sarkı Abu Zaiyan.
Koda aka kammala da kafatuntunan su Sarki sai Sarki Madham Sarki Tarma da kuma Sarki
Husaka suka kadaice a cikin nasu tantin da dubu da irin abubuwan da yake gabansu
Koda yin shiru na dan wani lokaci kowannensu yana tunanin abin da zai faru, sai Sarki madhan
ya yi ajiyar zuciya ya dubi Sarakan gudu biyu ya ce.
"Ya ku Sarakai 'yan uwana yanzu ya kuke tunanin jama'armu da muka turo don yin
Mu hadu a part 8 littafin Yaki