Showing 15001 words to 18000 words out of 35560 words
Chapter 6 - TAWA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN SHAKUR.txt
da mijinta.
Isma’il yace yanzu a ina zamu sauka?? Thariq yace y not mu sauka a hotel, anjima da yamma sai muje gidansu yayan dad din nawa, kaga tundasu sun dade a zamfara watan kilan susun alh shuibu din ko ya kace, isma’il yace hakane.
Suka kama daki biyu a hotel shi daya isma’il daya, karfe biyar suka shirya suka tafi gidan, hj amina na ganinsu tafara murna wai wai wai likita bokan turai, kainake gani ko mafarki nakeyi?? Thariq yay dariya yace zoki mintsileni sukadayi wasa da dariya aka zauna anata fira, hj amina tace kaga bari nakira hajara tazo kuhadu batasankaba, kaima batasankaba tadau waya.
Bayan mangariba wata hadaddiyar mota ta faka a tsakar gidan. hj amina tace ai gatachan ta iso ma, hajara tafito ta kulle mota tabude back sit tafito dawasu kyawawan yara maza daga ganinsu twins ne tariko hanunsu suka shiga ciki.
Sallama tayi saida kirjin thariq yabuga wacece haka da muryan shukra?? Bude labule tayi ta shigo twins da gudu sukaje suka dane jikin hj, itakuma ta karaso cikin falo
Isma’il da thariq suka mike tsaye ganin wata irin mata wanda babancinta da shukra shine ita wanan daga gani ta girmama shukra nesa bakusaba, thariq ne yasamu bakin magana yace hj wacece wanan??… ……
Maman shakur 😘
mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE 37 to 39TAWA CE!!! 45 to 46 →
TAWA CE!!! 40 to 44
Posted on November 9, 2015 by mamanshakur
[09/11 8:02 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣0⃣
Hj Amina tace ai itane hajara yata mana. Zama yayi akasa hj tace lpy thariq?? Ya share gumin daya zubo mai, yace hj dalilin daya kawomu zamfara munzo neman maman wata yarinya ne mai suna shukra.
Hajara ta rude tace shukra ta?? A ina ?? Ina take?? Plz ka kaini wurinta tareda babanta??hj dama nafada miki shukra bata mutuba, Thariq yay shiru yana kallon yanda hajara ta rude. Yace anty tana gidana, nan yabasu labarin komi har da na dad, bayan ya karake ya kalli hj yace hj maisa zaki raba uwa da ya?? Maisa zaki raba miji da mata?? Why??
Hj da tuni hawaye ya wanke mata ido tace Thariq wlh son zuciya da tsanan talaka kuma nai nadama,*****bayan na kori baban shukra da shukra, ko kwana biyu ba’a yiba hajara tafara ciwo kaman zata mutu, hankalina yatashi kullum magananta shine indawo mata da mijinta da yarta. Nayi matukar shiga tashin hankali dan hajara tafara haukacewa har India nakaita amma a banza bataji saukiba, nazo nafara nadaman abunda nayi dan banason na rasa hajara ita kadai gareni, ana sallamanmu muka dawo Nigeria nai mata alkawari zansa a nemo baban shukra da yarta shukra.
Babu inda ba’a nemesuba a zamfara amma babusu, nikuma ganin ba’a gansuba hankalina yakara tashi nazo nacema hajara ance sun mutu. Ranan hajara tai kuka ta kallen tace mama wlh inaji ajikina shukra da babanta na raye. Da kyar nasamu hajara ta dawo dai dai shekara uku dayin aurenta wayan nan twins din hassan da Hussain sune yaranta *******
Hajara tadau waya takira mijinta hello honey kazo yanzu, nan da nan yazo yaga matarshi na kuka rungume yayi yana lallashi.
Hajara tace ina shukra ta ku kaini wajenta wlh bazan iya bacci ba yau, Alh tafawa (mijinta ) yace honey cool ur mind gobe in sha Allah direct zaria zamuje kiga shukra ki.
Maman shakur 😘
[09/11 8:28 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣1⃣
Suka danyi hira hajara kam kuka sosai take, twins sunzo suna share mata hawaye, mijinta ma hankalinshi dukya tashi yanda yar matarshi ke kuka, Thariq da isma’il suka mike zasu tafi hj tace ai wlh a gidanan zaku kwana hakanan suka hakura.
Alh tafawa yadau matarshi da yaranshi suka tafi gida ranan hajara takasa bacci sai hada kaya take.
Da sassafe karfe 8 suka diro gidan ita da twins sai alh tafawa tare akayi break fast sanan akadau hanyar zaria, tun ahanya isma’il yakira Amina yace su gyara gidan da kyau za’ayi baki.
Suna shiga zaria gaban hajara yadinga faduwa haka suka kai gidan lokacin shukra na daki tana duba assignment da Amina tabata dayake tana mata lesson, Thariq yace su zazzauna hajara sai waige waige take ko zataga shukra, isma’il yakira Amina tafito suka tafi gidansu.
Thariq ya shiga daki shukra na ganinshi tayi wani ihu ta daka tsalle ta rungumeshi sai kuka, ya dagota yana share mata hawaye, tace yaya thariq shine kayi tafiya ka dade ko, inata missing dinka, yace ai bagani nadawo ba kinga yanda kika kara girma da kyau kuwa ta rufe fuskanta da hannu, yace kina cinyemin abinciko saisa kikai katuwa, ya kamo hanunta yanzu dai kinga anjima mayi fira munzo da baki fito kiyi serving dinsu abinci da drinks tai murmushi tace to, harzai fita tace yaya wlh ni kaman kirjina na ciwo sai bugawa yaketayi yau zoka duba kaga, tana kokarin zage zip din riganta.
Yace ke mehaka zaki cire riga kuma?? Tace yaya zan nuna maka kirjin ne wlh yau tun safe yaketa bugawa ni bansan maisaba, murmushi yayi yace sako hijabi muje falo anjima inya cigaba da bugawa saina duba tace to ta sa hijab ta rike hanunshi gam suka fita falo,
Alh tafawa shiya fara ganin fitowansu mikewa yayi tsarki ya tabbata ga ubangijin hallitu wacece wanan mai kama da matarshi haka?? Saidai kawai ta nunama matarshi karamin jiki?.????
Maman shakur 😘
[09/11 8:57 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣2⃣
Hajara ma ta mike bakinta na rawa, hj amina ko dukar dakai tayi dan wani irin kunyan shukra taji tanaji, shukra tasaki hannun thariq taje wurin twins da gudu tana laaaa yaya ikon Allah jibi wasu yan biyu masu kama dani, farare masu kyau, dago kanta tayi lokacin dataji ance shukra, saida taja baya da gudu yaya wacece wanan tayi kama dani haka?? Takuma kara dawowa gabansu tace ku zauna bari nakawo muku ruwa, ta kalli hajara tace wlh ina sonki saboda muna kama tawuce tatafi kitchen ta kawo musu drinks tazuba akofi ta mikama hajara.
Hajara ta hada kofin da hanun ta rike ta cire kofin ta ajiye a stool ta dago shukra ta rungumeta sosai tana kuka, shukra ta janye jikinta daga nata tace mai haka zaki rungumeni?? Kuma mena miki kike kuka?? Murya na rawa hajara tace shukra nine mamanki, am ur mother shukra am ur mother!!!.
Shukra komawa tayi da sauri inda thariq yake azaune yana kallonsu tace yaya wai da gaske itace mamana?? Thariq yace eh.
Shukra tace dama inada mama?? Ni nadauka babana ya haifeni, tunda nataso babana nasani shike goyani, yay min wanka, yabani abinci, ya koyamin salla, yamin kitso yamin tsifa yamin komi takara kallon hajara dake kuka sosai tace where were you?? Ina kika shiga lokacin?? Why did u abandon me?? Tace bansankiba, karki kara cewa ke mamata ne, banda mama ni, babana shine mamana, sai kuma yaya thariq babana nabiyu, nisu kadai nakeso, suna sani, su suka raineni, bana sonki, kuma karki kara kiran kanki da mamana cos i dont have, tawuce ta shiga bedroom ta banko kofa bommmmm…
Maman shakur 😘
[09/11 9:12 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣3⃣
Hajara tamike zata bita alh tafawa yakamo hanunta yana girgiza mata kai, yace honey shukra needs to be alone yanzu, put ur self in her shoes kusan 16 years batasan wani gatan uwaba, batasan mamanta ba, rana daya wata tazo tace ita maman tane yazakiji? dama dole kiga tai reacting haka, is normal yanzu kiyakuri ahankali zatazo ta koyi sonki harku saba ya kalli thariq koba hakabane Doc?? Thariq yace hakane anty shukra nada saukin hali zata sakko.
Kuka sosai hajara take ta juyo ta kalli hj amina tace mum kinga abunda kikaja ko?? Are u happy now?? Alh tafawa yace banason haka, yajawota jikinshi yana lallashinta twins ko sai wasansu suke.
Wuraren karfe 5 sukace zasu wuce,thariq ya kalli yanda hajara ke cikin damuwa yace Anty next week shukra zata fara waec dazaran sun gama zan sanar daku saboda muhadu a kano ayi komi achan, kafin lokacin in sha Allah shukra zata sauko kinga saiki tafi da ita zamfara ko?? Hajara ta share hawaye ta ce Nagode thariq, tnx 4 taking good care of my daughter Allah bar zumunci, tace bari nama shukra sallama key mota ta karba tafita waje tafito dawani sabon trolley akwati mai shegen kyau.
Duk suka bita da kallo bude dakin tay ta shiga shukra ta mike tsaye tana turo baki mai haka zaki shigomin daki?? Hajara tai murmushi dayafi kuka ciwo ta matso kusa da shukra tabata akwatin tace dan Allah ki karba kinji yar baba, shukra ta kalleta da sauri, hajara tai murmushi tace kina mamaki ne?? Tun randa aka haifeki babanki kece miki yar baba, takai bakinta taima shukra kiss a goshi tace i luv u daughter tajuya tabar dakin.
Maman shakur 😘
[09/11 9:33 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣4⃣
Shukra jikinta yay sanyi sosai, ta zauna kan gado tabude akwatin Bra ne masu bala’in kyau sai pants sanan english wears sai abayoyi da kayan makeup, tashi tayi tana gwada komi kaman an aunata sun mata das saidai bra din sun mata kadan 38 ne, itakuma 41 tai tsaki tace naba Amina dama naga 38 take sawa maida kayan tayi tarufe tace in yaya yadawo na nuna mishi.
Sai bayan magrib ya shigo gidan yazauna a falo yana amsa waya, aikuwa ta kinkimo akwatin har falo ta bude, saida yagama wayan tace yaya jibi kayan datasiyomin ya kalli kayan dayake su abaya ne asama yace sunada kyau yacigaba da latsa waya, kwaso duka bras din tayi kala 5 ta daura akan cinyanshi tace yaya kagafa bra dinan hardasu tasiyomin kumani sunmin kadan, dago kanshi yayi ya kalli bra din wani kunya yaji yakamashi kaman ya nutse a wurin, yace to meruwana da sun miki kadan ki maidasu cikin jaka, wanan kayan mata ne ai,
Tace yaya to ta kallesu mana, dama inaso naba Amina kanwar isma’il ne, kaga ita 38 take sawa nikuma 41, ya kalleta ya kalli bra din ita bama tasan yanayin dayake cikiba, yace 4 god sake ki kwashe abunan daga jikina mana shukra, tace to ai yaya inaso ka kaini naba Amina ne, yajuyar da kanshi najito anjima na kaiki, yanda taga yana magana kaman yana fushi yasa ta tsaya tana kallonshi shikuma sai kauda kai yake, Ahankali yaji tace yaya yanzu wai kunyar kallon bra kake?? Wani zabura yayi yamike aiko da gudu tayi daki tana dariya sosai yaya mai kunyar bra.
Shima dariya yayi ya kwashe bra din yabude akwatin alokacin yaga harda pants ma yay maza yasa ya kulle.
Maman shakur 😘
mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE!!! 40 to 44TAWA CE!!! 47 to 53 →
TAWA CE!!! 45 to 46
Posted on November 9, 2015 by mamanshakur
[09/11 9:57 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣5⃣
Sai bayan sallan isha ya leko dakin tako mike tsaye tana dariya ciki ciki, ya daure fuska ke wakikema dariya ta turo baki to ai badakai nakeba dakaina nake, yace oya mutafi gidan isma’il din kiyi sallama da Amina gobe zata tafi, komawa falo tayi ta kwashe bras din tasa a leda da wasu kayan makeup suka tafi.
Databa Amina aiko ta dinga murna tana mata godiya sai wuraren goma suka bar gidan, thariq yakawo kudi mai yawa yabama Amina da kyar ta karba tai godiya.
Suna komawa gida shukra ta shiga dakinta sai bacci.
Washe gari da sassafe thariq ya shirya zai tafi asibiti shukra ta dinga kuka, yaya dan Allah kaje dani, tuntuni fa kai tafiya sai jiya kadawo plz go with me, yace jekiyi wanka to, daki taje tai wanka tazauna tayi kwalliya sosai dan zama da amina yasa ta iya make up yanzu.
Daya daga cikin dogayen rigunan da hajara takawotama tasa, pink ne sai akimai kwalliya da black stones tadau gyalen tayafa gashinta takama amma still saida yazubo har tsakiyan bayanta tadau black flat shoe tasa sai kamshi take.
Fitowa tayi ya tsaya yakura mata ido, yaushe shukra ta iya gayu haka?? Murmushi yayi yace zama da amina mana. Kallonta yayi yace bakiga ana ganin gashinkiba ta tsaya agabanshi ta juyamai baya yaya dan tusamin gashin nakasa.
Hanunshi na rawa yakamo jelar gashin wani taushi yaji da santsi yay rolling sanan yatusa aiko ya shige sanan suka fito ya kulle gidan suka tafi.
Suna shiga sai kallonsu ake sunyi bala’in matching, wata doc mace shukra taga tanata hararanta, tace yaya wacece wanchan ya kalleta yace ohhh wata doc ce sunanta JAMILA amma muna cemata JAMCY..
My dear jamcy mai kwankwaso sau🙊 lot of luv jamcy ina sonki.
Maman shakur 😘
[09/11 5:29 PM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣6⃣
yakamo hanun shukra suka shiga office dinshi.
Telephone din office din ya dauka yakira secretary yace akawo mana min abinci plates biyu.
Suna zaune shukra sai tabe tabe take shikuma sai Kallonta yake, aka kawo abincin saida sukaci tai nak sanan yace ki zauna a nan karfa kije ko ina bari na shiga na duba patients tace saika dawo.
Yana fitowa jamcy tabiyo bayanshi ranta abace tace Thariq wacece yarinyar chan?? Wani kallo ya jefeta dashi batare daya bata amsaba, kagafa abunda na tsana dakai kenan wanan miskilancin naka. Ya kalleta ok jamcy ne
duk macen dakaika gani dani sai kinsan ko wacece? Tace haba thariq ka tausayamin ina sonka wlh, kishinka nake. Yace jamcy banasonki plz stay away 4rm me.
**Jamcy doc ce tana bala’in son thariq shikuma bayasonta dan jamcy tama girmeshi she is 36 yanzu.**
Wucewa yayi yabarta a wurin, jamcy azuciye takoma, office dinshi ta wuce direct tana zuwa taga shukra gaban laptop dinshi tasa farin coat din thariq yanda kukasan doc, jamcy ta daka mata tsawa ke tashi dan ubanki, mezakisa coat din Doc Thariq??. Shukra ta mike wlh karki kara zaginmin babana yamutu.
Jamcy tace ance dan ubanki din, shukra ta kalleta sama da kasa sanan tace mai KWANKWASON SAURO kawai. wani super jamcy tayi tazo ta shake wuyan shukra….nikuwa nasa gudu nafito dan nakira thariq 🏃🏻🏃🏻
Maman shakur 😘
mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE!!! 45 to 46TAWA CE!!! 54 to 59 →
TAWA CE!!! 47 to 53
Posted on November 10, 2015 by mamanshakur
[10/11 8:29 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣7⃣
Secretary dinshi ce taji alamun kaman kokawa a office dinshi kuma tasan baya office shine tamike tabude kofa gani tayi Doc jamcy ta shake shukra wanda idanunta sun soma juyawama, karasawa tayi da gudu ciki duk iya kokarinta nata kwace shukra takasa. Fita tayi da gudu tatafi word, tana zuwa takoga Doc Thariq naduba wata, da gudu takarasa tace sir jamcy zata kashe bakuwarka, a tsorace yatashi yace wot Tace mai muje kawai yabi bayanta. Yana shiga ya fizge jamcy ya wullar da ita shukra kam sulalewa tayi a kasa.
Yakoma kan jamcy yace kasheta zakiyi?? Idonshi duk sun juya yaso ya shaketa itama amma sai yay tunani kawai ya jata ya wurgar da ita wajen office dinshi, yakoma kan shukra wanda fuskanta yay jaa abunku da farar mace hawaye kawai ke fita daga idonta.
Ya rungumota jikinshi sorry shukra am here, ya duddubata yaga bawani matsala murya ciki ciki tace ni ka kaini gida tashi yayi ya mikar da ita yacire mata coat dinshi sanan yakamo hanunta duk kuka take suka shiga mota sai gida.
Suna kaiwa gida ta zauna afalo tana kuka, ya zauna kusa da ita duk hankalinshi atashe, yace wai meya hadaku?? Tace ba ita bane tace zata ci ubana ba, shine nacemata mai kwankwason sauro, shine ta shakemin wuya, ta nushe ni, takuma hambareni. kaji su shukra da sharota lol😜, kuma ni wlh sai ka ramamin.
Dariya ma tabashi amma ya gimtse toke shukra mena cemata mai kwankwason sauro?? Tace wlh yaya ai batada kiba, kaman tsinke take koni nafita kibafa. Thariq yay dariya aiko shukra takara fashemai da kuka da kyar ya lallabata tai shiru.
Maman shakur 😘
[10/11 8:44 AM] Aishat muh’d: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
4⃣8⃣
Yau monday yaune ranan da shukra zata fara waec dinta anan DEMONSTRATION samaru thariq yabiya mata. tun safe ta shirya tadau wayanta tasa a jakan dan tanaso tai waya da nazir yau.
Karfe 8 thariq ya sauketa tareda bata kudi mai yawa taci abinci, yace intagama zaizo ya dauketa dayake 12 zata fito.
Yana barin makaranta taciro wayanta ta kunna takira Nazir aiko kaman jira yake yace hello baby na wai maiya sami wayarki ne?? Tace yaya na yadawo kasan inya kamani dakai zai dakeni, nidama inason nafadama karka kara zuwa plz. Nazir yace yanzu kina nufin bazamu kara haduwaba?? Tace nidai ba yanzuba sai yaya yakarayin wani tafiya.
Nazir yace kinfara waec dinne?? Tace eh, yace to gaskiya randa kika gama paper zanzo plz zan baki gift din gama exam, tace to shikenan na yarda idan yatafi asibiti sai kazo , daganan suka cigaba da firan