Showing 3001 words to 6000 words out of 19091 words

Chapter 2 - SAINA AURI MATAR NOVEL COMPLETE BY HAJARA ABLA.txt

18 Nov 2025

747

kada ka makara."

Ado ne tayi zumbur ga mik'e sanan yace" aa MALIYA kaine da sassafe haka,lallai ne kace baka ma manta da ranar tafiyar ba ashe,ahhhh lallai dagaske kake."

"Ohhhh wai daman kai ka d'auka da wasa nake lallai ado yanzu dai abinda za'ayi ka tashi ka shirya mu wuce."

"Kaiii MALIYA yanzu dai ka tawo da kud'i mai yawa dafatan?"

"Ahhhhh karfa ka damu indai,kud'ine babu matsala dan kuwa ni zan d'auki nauyin mu har muje,ammm wane gari ma kace zamu?"

Ado ne ya washe bakin jin cewa MALIYA ya tawo da kud'ad'e" ai kano zamuje,yanzu dai ka zauna ka huta dan kuwa motar kano bama ta tashi sai sha biyu na rana dan haka kabari na shirya a nitse."




Haka MALIYA ya zauna zaman jiran ado har lokaci ya k'arsa suka nufi Tasha dan hawa motar kano.



Zuwan su keda wuya kuwa suka sami mota nan da nan suka hau mkta ta cika ba b'ata lokaci suka d'auki hanyar kano.......




Haajar abla ce.✍🏻
[11/16, 18:23] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/


*Page 7_8*

Tafiya ce sosai ba k'aramar tafiya ba,dan kuwa har saida sukayi bacci suka farka ana tafiya sai wajan yamma liss sanan suka sauka a tasher kano line dake garin kano...


Bayan sun fito daga tasha sai zare idanuwa suke kamar shege a raban gado,haka suka hau d'an sawu yakaisu unguwar da ado ya tab'a zama wato fagge. Ado ya zauna a fagge har yayi sana'oi kala² kuma gashi duk abin da yayi insha Allah ana siya shiyasa ma zaaman unguwar yayi masa dad'i. Wani shago ne na wani mutum da yake bada haya saidai hayar shagon da tsada sosai hakan yasa shi ado ma alfarma aka masa suke kwana da wani,sai gashi bayan magrib shi da ba'ko da kaya nik'i ² a hannu,direct ado a wanan shagon ya sauka inda ya nemi alfamar ad'am k'arb'i ba'konsa sanan zai bada kud'in zama kamar na wata d'aya,haka kuwa akayi da yake MALIYA akwai y'an kudad'e a jikin sa hakan tasa ya bada kud'in hayar sanan aka samu masalaha,haka suke cakud'uwa su uku suke kwana a d'akin duk a takure....


Washe gari MALIYA ya bud'e waya yaga fall network nan take dad'i ya cika sa,har ya zauna ya bud'e y'ar datar sa zai hau Facebook ado yace ai ba zama yakamata suyi ba,tashi yakamata suyi suje su samu aikin yi,dan baza su zauna haka nan babu wan ba 'kanin ba...



Haka kuwa akayi sun fita suna d'an neman na kalaci,dad'i kamar ya kashe MALIYA gashi a birni abin alfaharin ma gashi a tsakiyar birni yau har yayi kwana d'aya woooowwww Allah kenan,wanan al'amari tabbas ya nuna masa akwai nasara a tafiyar sa d'ari bisa d'ari....




Haka suke ta gararambar yawo lungu da sak'o shiga nan fita nan,da yake shi ado yasan unguwar hakan baiyi masa wahala ba wajen shige da fice,shida MALIYA da za'ace ya koma gida to da lalllai tabas sai ya b'ata,ko wacce budur wa idan tazo wuceaa sai ga kalle ta sai dai kallo d'aya yakewa wasu matan baya kuma wa,idan yaga budurwa ta tawo a titi fara soll da ita yana duban k'afarta sai yaga kuma ashe bak'a,to y'ar bleaching ce,sai kuma yaga mace da gashi har gadan baya sai ya k'uraa ido sai kuma ya tab'o ado wanan tana da gashi kamar India ado yace dallah ware d'an k'auye ( har kura ce zatace da kare maye) wanan ne gashi kana ganin gashin doki... Haka dai ranar suka gama gararanba daga can zuwa nan batare da sun samu aikin ko na shara ba....


Washe gari ma haka suka tashi dan neman aiki fad'a nan fad'a can amma kamar dai jiya babu abin da suka k'aru dashi,a rana ta uku ne sun sha wahala sosai kafin su samu wata mai abinci da yau 'yan aikinta basu samun damar zuwa ba tace suzo suyi mata aiki....


Bayan isha'eh a gajiye suka dawo gida,dan kuwa kowa jikin sa ya fad'a masa saboda wahalar ma da sukayi kafin su samu aikin yin...



Ado ne yaja dogon numfashi bayan sun gama cin abinci sanan ya kalli MALIYA yace" MALIYA kasan Allah raba k'afa zamuyi,kana gani dai abin da yake faruwa idan muka fita mu biyu kamar wasu masu bak'in jini sai muk'i samun abin yi,kana ganin yau dakyar Allah ya taimake mu muka samu mai abincin nan ta rab'amu,ahhhhh dan haka gaskiya bazaiyiyuba kawai asan abinyi ,domin kuwa idan ni kad'ai ne wallahi tuni nake samun aikin yi...."




"Haba kai kuwa ado to mene kuma abin d'aga jijiyoyin wuya,nifa daman badan wai inason nayi aiki ko dan na samu kud'i ba nake fita nidai kasan kawai kudirina d'aya ne dan Allah yasa nayi gam dakatar na had'u da MATAR NOVEL amma badan inzobina bi kwararo² sak'o² wai dan in nemi kud'i....."



Ado ne ya juyo cike da k'osawa da wanan haukan nasa yace" to kai wai barin in tambaye ka tayaya baka da kud'i sanan ka lissafomin daman sufoffin matar novel d'in to ka fad'a min taya zaka aureta bayan baka da abin da zaka aureta dasu."

"Kaiiiii ado share kawai,ni ina ji a jikina dole zan aure ta,ai matar mutum kabarin sa dan haka idan nine mijin ta tofa tabbas zan aure ta."




Ado ne cike da mamaki yace"tofa naga yanda za'ayi tusa ta hura huta."

"Aaa ado kada mu zo nan dakai,Annabi (S.A.W.) yace falyakul khairan aliyasmut,kafad'i Alkhairi ko kayi shiru da bakin ka to idan kasan sharri zaka fad'a dan Allah kayi shiru da bakin ka banson ji nagode....


Ado shikam yaga abin da yafi k'arfin sa dan haka yace" to shikkenan Allah ya baka hak'uri..
..



Yau satin MALIYA biyu da zuw akano amma tun daga kwana na ukun nan bai sake zuwa ko nan dacan ba saboda shi ba wanan ne ya kawosa ba,anasa tunanin....



Haka dai kamar wasa kwanaki suna shud'ewa watanni suna k'ara tafiya,sai yazamana cewa yau shekarar MALIYA d'aya a birinin kano fad'a nan tashin can fad'a can,gashi tun yana wata na uku yagama da wad'anan kudad'en na hannunsa nan fa ya fara fafutukar sana'ar yi,abin haushi gashi har ya gaji da had'a numbobima ya h'akura,haka ya samu ya fara zuwa gareji ana koya masa gyara mota yana kuma wankin mota.

Shi daman tuni ado yake zuwa k'auye kuma yana dawowa yana yin k'wadagon sa. Y'an k'auyen su MALIYA kuwa tun suna sa ran dawowar sa har sun fidda rai dashi kowa ya fawalawa Allah,sundai Sani indai ba mutuwa yayi ba insha Allah watarana zai waiwayo gida watarana zai dawo....



Kamar kullum yau yayi aiki ya gaji ya dawo makwancin sa ya kwanta kenan har ya fara bacci yaji ankawo nefa,sai yaji yana son yasa caji a wayar tasa haka kuwa akayi yasa caji ya kwanta barci har wayar tasa ta cika,yana tashi da safe bayan ya shirya ne yaga misscall na ado daman baya gari to yana ga da alamar zuwan sa dan haka sai yasa d'ayar number adon da niyar ya kira,yana kira ta shiga har ta gama rigin ba'a d'aga ba,ya sake sawa ya k'ara kira saida ta kusa katsewa ne sanan yaji an d'aga,daga d'ayan b'angaren wata sassanyar muryace tace"hello,hello ana magana da Ashfa mudassir."

Ashfa mudassir! Take anan ya daskare dajin wanan ni'im taciyyar muryar, wowwwww gaskiya wanan murya ta had'u duk da cewa baison ko wacce ba amma tabbas wanan murya ta mace mai aji ce... Kauda tunanin sa yayi da sauri yace"Amincin Allah ya tabbata AGAREKI Ashfa mudassir ina fatan kin tashi lafiya?"


Cikin wata irin kasalalliyar murya tace dashi" lafiya,wa yake magana?" Ta tambaya a tak'aice.

Da sauri yace"wani bawan Allah ne da yayi damdakatar a yayin neman wata number aka samu akasi ya sab'a number to ashe rabon nayi gamo ne dake."


Wani farrr tayi da ido tamkar tana ganinsa,hmm wanan kuwa akwai kalamai,tafad'a a zuciyar ta a fili kuma tace"ok shikkenan ngd." Daga haka bata k'ara cewa komai ba k'it ta kashe wayar...


Cike da murna da jin dad'i a hakan ma yayi mutuk'ar sa'a harma ya samu rabon Jim sunan ta ASHFA ya maimaita yana dad'a rungumar wayar sa...



Tashi yayi,yayi wanka yasa kaya ya nufi gareji. Kamar kullum yaje ya gudanar da aikin sa yanda ya kamata ya dawo gida ya tarar har ado yazo kuma bacci ma yake. Bayan ya tashi suka gaisa sosai da tambayar y'an k'auye ya sheda musu kowa yana lafiya,MALIYA bai tsaya iya nan ba,har saida ya bawa ado labarin had'uwars da wanan Ashfa yau d'inan bayan ya gama bashi labari ne ya k'ara da cewa" kai daga jin sunan ta da irin muryar ta wallahi kasan cewa irin matar da nake burin aure ce wayyo Allah na,Allah yakai damo da harawa kobaiciba yayi birgima."


Tun ba yanzu ba ado ya gano MALIYA yafi so ayita fasa masa kai da k'arya da k'arairayi aikuwa tuni ya ringa masa famfo yana 'Kara zurmasa...




Tafiya yake zuwa wajan aikin sa,wata kyakkyawar mace ya hango daguwa ce amma ba can ba,gata fara tass da ita ta sha doguwar rigarta ruwan kuka,hakan ya k'ara fito da ainahin kyanta tsaye take a gefen titi da alama motar tace ta mutu tana jiran bakanike....





Hangota yayi,dan haka da sauri ya matsa wajan domin ya taimaka mata,yana zuwa ya gaishe da ita kamar haka"ina yini Hajiya naga kamar motar kice ta samu matsala idan bazaki damu ba ni bakanike ne ko zan iya duba miki." Ba tare da tace komai ba tayi masa nuni da hannu ai tuni yaje ya fara aikin duba mata motar,da yake kuma Allah ya bashi basira kafin mintuna goma har ya tashi motar.. Godiya sosai tayi masa sanan ta ciro kud'i ta bashi yak'i amsa ta takura akan sai ya amsa haka ya amsa ita kuma ta shiga mota ta tafi....


Kashhhhh ya fad'a a zuciyar sa,naso ace ta fad'amin sunan ta gaskiya wanan k'arshe ce a matan novel d'in ma ohhhh ni yanzu ina ji ina gani gashi tatafi...


Haka ya k'arsa gareji yayi aikin gyaran mota ya gama washe gari kuma wankin motoci ogan sa ya bashi,ya wanke motoci guda biyu a ta ukun ce kuma yaga wanan ai itace motar da ya gyarawa wata budurwa kwana biyu da suka wuce,kenan nan take kawo wankin mota...




Cike da tunani ya shiga ya fara aikin wanke mota sai da ya gama tsaf yaje yana hutawa kenan yaga wanan hajiyar,wato budurwar nan ta sauka a keke napep dan tafiya da motar ta,da sauri ya k'araso ya gaishe da ita cike da ladabi. Amsa masa tayi sanan tace "aana kake aiki kenan."
"Ehhh madam anan nake aiki."
"Murmushi tayi sanan tace niba sunana madam ba sunana AFNAN....."





SHARE IT FISABILLILAH.
[11/16, 18:25] Ablaaa: *🦋SAINA AURI MATAR NOVEL*🦋


*BY*
*Haajara abla*



*💫💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION.*💫
(Annuri is the best.)


https://facebook.com/groups/743377583724957/


*Page 9_10*

Ogan su ne ya k'araso cikin sauri cike da fara'a yana mai furta"sannu da zuwa Hajiya Afnan,ga motar nan har an wanke ta angama komai. " yafad'a yana irin washe baki...

Murmushi tayi batare data sake magana ba ta ciro kud'i a hand back d'inta ta mik'awa ogan nasa,sanan ta kalle sa tace"ya sunan ka?" Da sauri MALIYA yace sunana MALIYA." Amsar tasa ta d'an bata dariya dan haka sai tayi murmushi sanan tace okya nagode MALIYA. "
"Ahhh Hajiya Afnan ai nine da gdy." Batare da tasake tanka masa ba direct ta nufi inda motar tata take ta shiga ta kunna ta sanan tabi wajan..


Kurar data tashi a wajan ya k'urawq ido yana kallan motar har ta b'acewa ganin sa,a zuciyar sa sak'e sak'e yake kala²,ya sak'a wancan ya kwance wance a haka dai ya cigaba da aikin nasa...




Bayan ya dawo daga wajan aiki yana zaune a bisa y'ar k'aramar katifar sa yana ta tunanin duniya saiga ado ya shigo,zama yayi kusa da abokin nasa sanan yace" SAIKA AURI MATAR NOVEL ya garin, ya kuma har kokin,waiiii shiru babu labarin matar novel kodai har yau da kake had'a number's Allah baisa kun had'u da juna ba..."

"Uhmmmm basar kawai aboki na har yau fa babu wani labari amma duk da haka ban karaya ba... Ohhhhh na tuna." Ba tare da ado ya San mai MALIYA ya tuna ba MALIYA ya jawo wayar sa ado dai ya bishi da ita yana ta kallon sa cike da mamaki...


Daining wata number yayi wacce yayi saving da ASHFA MUDASSIR sai da ya kira wajan sau uku sana ta d'aga cikin wanan murya tata dai mai kala da wacce take jin bacci...

Da sauri yace"hello Ashfa ina fatan kin yini cikin k'oshin lafiya."

A b'angaren ta kuwa tana kwance saman wata k'aramar katifa tana wani juya ido a wani k'aramin d'aki,saidai ko ina na d'akin a gyare komai a mahaillinsa yake,k'ara juyi tayi a saman katifar sanan tayi magana" lafiya kalau Alhmdlh, am wane ke magana. "

Cike da jin dad'i MALIYA yace" am Ashfa sunana MALIYA."

Ita kuwa ashafa wani d'an zaro ido tayi taji yace maliya, ita dai tasan idan ana kiran mutum da wanan sunna to tabbas yaci ya tada kai." Cike da tsayuwa ta k'ara narkar da murya" ok amma ban gane kaba."
"Hakane ashfa mundai tab'a yin waya sau d'aya dake amma kuma har yau zuciyata bata daina mararin da zumud'i sake jin muryar ki a karo na biyu ba,sai gashi Allah ya bani sa'a kin d'auki wayata har nayi nasarar samun jin wanan murya mai d'auke da abubuwa da dama."

Ita kuwa ashfa a b'angaren ta ta d'auka wani hamshaj'in ne,ta d'auka dai irin yana da cancinsa ,shiyasa ma ta zak'e suna ta fira,bayan sunyi sallama kuma ta adana number sa a ma'adanin akwatun wayar ta,inda tayi masa saving da suna MALIYA.





Wata matace zaune a sa'kar gida ta shimfid'a k'aramar tabarma tana zaune tana Jan sharbi,ganin farko da zaka mata zakaga bata haura irin sheraa 40 d'inan ba... Tana zaune tana ta salatin ta naji ra kwallawa ashfa kira.." Ashfa,Ashfa ki taso kizo ina kiranki."

Ashfa data k'ara kishingid'ewa a k'aramar katifar ta bayan sun gama awaya da MALIYA tace wa Maman nata"wallahi mama duk nagaji,mai zanyi."

Cike da k'osawa da lamarin Ashfa matar tace"wallahi Ashfa ki kiyaye ni,ni kike cewa kin gaji,to wai ma uban me kikayi tun tashin ki a gidan,ina nina yi komai da komai amma har kike kira kin gaji,kin daina zuwa makaranta tunda kikai y'ar diploma d'inan kika ajje karatu kin ajje karatun islamiyya,kina ganin dai y'ar uwar ki ASHNA kullum tana hanyar makaranta y'ar Albarka bata gajiya,tana dawo wa zakiga tana taya ni aiki harta Khalid da yake k'arami yana tayani wasu abubuwan amma kekam saidai ki kwanta ko ki shirya ki tafi yawan gidan k'awa,to wallahi zamu sa k'afar wando d'aya dake."



Zuwa wanan lokacin duk fad'an da mama takewtakewa Ashfa yasa ta taso tazo ta zauna cike da wata kalar shagwaba tab'as ta zauna akan tabarmar sanan tace" gani mama mai zan miki." Duk dai ba'asan ranta take maganar ba.


Mamace tace"uwaki zaki min kinji,nace uwaki zaki min,to ki shiga d'akina ki d'akko naira hamsin kine wajan Shamsu mai itace ki siyo min kafin ya'kare.."



Zaro ido Ashfa tayi kamar zasu fad'i barakalla abinka gamai idon,"waiiii mama icce fa kikace,mama haba haba mama,yanzu ni zanje suyi icce."

"Ahhhhh to karki du idan ke bazakije ki iya siyowa ba ni bari intashi in tafi da kaina."

Cike da k'uk'uni Ashfa tace"haba mama amma yanzu misali idan wani ya ganni ina sayen ice wallahi mama ajina duka zubewa ma zaiyi."

"Dan ubanki nikek fad'awa ajinki zai zube,to shikkenan shiyasa nace ki barni naje da kaina nida bani da aji sai na siyo.."


Zuwa lokacin kafin mama tak'arashe zancen ta tuni taje d'akin nata gefen gadon nata ta d'akko naira hamsin ta fito tare da saka hijabi da nik'af ta saka,mama dai tana kallon ta haka ta fita.saboda kar wani ya sheda tama bataje wajen mai iccen da suke kusa dashi ba,na wani layin taje,amma a hakan ma ba dakanta ta k'arasa ba wani yaro ta gani ta bashi ya siyo mata sanan ta masa godiya tasa icen a hijabin ta ta koma gida....



Tana zuwa gida ta ajje icen a wani d'an k'aramin kitchen d'in nasu sanan ta shiga d'aki ta cire kayan ta tayi d'aurin k'irji ta fito ta d'auki botiki zatayi wanka wai a lallai ta gaji kuma icen data d'aukko na hamsin ya gajiyar da ita..tana fitowa ta samu k'annen nata duk sun dawo Ashna itace ke bi mata yarinya ce mai ladabi da biyayya tana da mutuk'ar tarbiyya tana girmama na sama da ita,a zaune ta samesu suna y'ar fira su da mama. Kallon Ashna tayi sanan tace'k'an wata dan Allah d'aura min ruwan zafi,kinga na siyo coal na gawayi saboda ita bama tasan yarda zata hura itacen ba,dan Allah ki d'aura ruwan wanka." Batare da musu ba Ashna ta tashi taje ta hura gawayi nan da nan ya gama ta d'aura nata ruwan yayi zafi ta sauke mata sanan ta zuba mata ta kai nata band'akin su,sana tazo ta sameta a d'akin tare da fad'in" Anty Ashfa gashi can na had'a miki ruwan wankan yana ban d'aki."
"Murmushi tayi sanan tace" sannu da k'ok'ari nagode k'anwarka Ashna idan nayi aure dake zan tafi gidana muje can mu more rayuwar mu...


Itadai fitowa tayi tana murmushi, haka Ashfa ta tashi tayi wanka tayi alwalar magrif,ana kiran sallah tayi sallah sana ta koma saman katifar tata tana janyo wayar ta,nan da nan ta kunna data ta hau online tafara chating direct group d'in MATAN SIRRI NA HAAJAR ABLA ta nufa,dan kuwa anan tafi kauri saboda babu abin da take so a yanzu a halin data ke ciki sama da ayi mata aure,amma takasa tsayar da miji saboda ruwan idon ta,ita lallai sai mai kud'i ko kuma d'an gidan masu dashi,bayan ta gama duba sak'on matan SIRRI taga abubuwan da zai amfaneta da yawa sai kuma ta koma HAAJARA ABLA HAUSA NOVEL nan taga LITATTAFAI kala² su Maman Zahra ana ta posting HAAJARA ABLA ma anan kuwa taje tana ta zuba karatu da comments.....




"Kaiii kana jin muryarta ma zaka San y'ar gata hutu ya zauna a jikin ta,kai bakaji muryaba wallahi,kainifa daga ji ma kasan yarinyar ta had'u,kana jin sunan ta irin na matan novel d'inan sunan ta fa Ashfa."

Ado ne ya zaro ido tare da dagewa ya tafa da MALIYA da 'karfi sanan yace" wuuuuuuu MALIYA ikon Allah wanan ne abin da ake cewa koda kud'in ka saida rabonka wuuuuuuu."


Haka ado ya ringa zuba MALIYA suna ta hauka.....







Share and share fisabillilah.✍🏻
[11/16, 18:26]

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login