Showing 1 words to 3000 words out of 90881 words

Chapter 1 - Wata Soyayya Complete Hausa Novels by Maryam Ibraheem Aleeyu.txt

Haske writer's association
[Home of expert & perfect writer's 💡]

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Da sunan ALLAH mai rahma mai jin k'ai, tsira da aminci da dukkan yabo su tabbata ga shugabanmu ANNABI MUHAMMAD ( sallallahu alaihi wa alihi wasallam), ALLAH ina rok'onka yadda nafara book d'in nan lafiya kabani ikon gamawa lafiya.







*WATA SOYAYYA*♥️🩸♥️


Writer: Oum Hanan

Free pages
Fiction story

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare duk wnd yy using set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali😘just start placing ur orders dearies DNT be left behind
Available product👇
Herbal whitening black soap:3k
Beauty kit:11k
Blacksoap/molato whitening soap: 3500
Bridal kit:20k
Muna maraba da masu siyan daya ko sari
Chat
08062991549
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀?

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan munada frames masu kyau shima siyan daya ko sari 07046881166
08062991549

Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549
Mungode🤝

01


SHIMFID'A.

Malam Abdullahi Modibbo madugu haifaffen garin yola ne bafulatanine usul iyaye da kakanni yayi shura sosai wajen noma da kiwo kamar yadda ya gaji sana'ar a wajen mahaifinshi Ard'o Modibbo, ahalinsu babban ahali ne ta yadda kowa ke son had'a zuri'a dasu.
Abdullahi yayi aurenshi tun lokacin iyayenshi na raye ya auri wata yarinya mai suna Dije a wata ruga dake mak'oftaka dasu.
Lokacin da Dije tayi haihuwarta ta farko a lokacin ne ALLAH ya d'auki ran mahaifin Abdullahi wato Ard'o Modibbo sakamakon ciwon ciki daya turnuk'eshi rana lokaci d'aya ya rasu, bama iya rugarsu ba rugogi da dama sunji rasuwar shi musamman iyalanshi mai d'akinshi Asiya tafi kowa jin mutuwarshi inda daga baya ta fawwalawa ubangiji lamuranshi.
Abdullahi sun cigaba da rainon yaransu mai suna Basheer inda suke bashi cikakkiyar kulawa gefe d'aya kuma yana cigaba da kula da mahaifiyar shi da kuma kasuwancinshi na noma da kiwo.

Tsakanin Ard'o Modibbo da mai d'akinshi Asiya duka baifi tsiran wata biyar ba itama ALLAH ya karb'i abarshi, daga nan Abdullahi yazama ba uwa ba uba sai y'an uwa da abokan arzik'i, ta b'angaren haihuwa kuma tun daga kan Basheer ko b'atan wata Dije bata k'ara yiba saida Basheer yayi shekara takwas lokacin ma harya fara makaranta dayake Malam Abdullahi yanason karatun boko dan haka lokacin da yaji wasu suna saka yaransu a makarantu shima yasa Basheer duk da a lokacin ana gudun karatun bokon, saida yayi shekara takwas sannan kwatsam Dije taji alamun ciki a jikinta dan har sun fitar da ran sake wata haihuwar saikuma ALLAH ya kawo musu wani cikin Malam Abdullahi yayi murna k'warai ya kuma yiwa ALLAH godiya itakuma Dije kunya ya hanata bayyana nata farin cikin amma cikin ranta tayi farin ciki mara misaltuwa tana kuma addu'ar ALLAH yasa ta haifi mace saboda tun kafin tayi aure take sha'awar yara mata.
Cikin ikon ALLAH kuma data tashi haihuwar sai ALLAH ya bata d'iya macen, sunyi murna sosai sunyi godiya ga ALLAH yarinya taci suna Maryam inda mafi yawancin y'an uwa ke kiranta da mairo, anan suka cigaba da kula da yaransu har itama Maryam din ta taso suna matuk'ar k'aunar juna itada d'an uwanta Basheer. Tunda ta taso itama ta nuna sha'awar irin karatun da yayanta yake dan haka Malam Abdullahi yayi mata alk'awarin insha ALLAHU itama zatayi shi idan ta isa sawar.

Koda lokacin data isa shiga makarantar yayi, Malam Abdullahi yafara maganar nan Dije wadda suke kira da Ayyah tayi tsalle ta dire tace ita sam batasan zancen ba ba za'a saka mata d'iyar ta mace a makarantar kafirai ba namijin ma dayake yi ALLAH ya yafe musu. Sada aka sha artabu sosai tsakaninta da Malam Abdullahi sannan ta yarda shima d'in bawai da son ranta bane fin k'arfi akayi mata.
Y'an uwa ma a lokacin sukayi ta k'ananun maganganu Malam Abdullahi ya toshe kunnuwanshi baibi ta kansu ba, yasa Maryama a makarantar su Basheer suka cigaba da tafiya tare kuma masha ALLAH suna da k'wak'walwar gane abinda ake koya musu ba laifi.

Lokaci ya cigaba da tafiya kuma har lokacin Basheer da Maryam suna karatunsu na boko gefe d'aya kuma gata allo da dama suka bud'i Ido sukaga suna zuwa dan tun basu san inda kansu yakeba ake zuwa dasu.

Basheer yasamu kammala primary school d'inshi inda yabar Maryam na cigaba da zuwa, ya shiga secondary school ya cigaba da karatunshi.

Bayan wani lokaci Maryam ta kammala primary d'inta, Malam Abdullahi ya fara shirin tafiyarta secondary a nan fa Ayyah ta tubure ita yarinyarta bazataje gaba da primary ba d'iyar ta aure zatayi tunda ga manema nan sunata b'arkowa tako ina ga kuma surutan jama'a da suke tayi na cewa yak'i aurar da ita, to tarihi dai ya maimaita kansa dan a nan d'inma Malam Abdullahi ya nuna mata shine gaba da ita kuma a k'asanshi take haka nan kuma surutan mutane ba damuwarshi bace ya samar mata secondary ta d'ora daga inda ta tsaya, kan dole Ayyah ta kawo idanu ta zuba musu dan sanin kanta ne Malam baya d'aukar wargi duk boren datayi bai hanashi bin ra'ayinshi ba.

Maryam ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali, har zuwa lokacin data gama k'aramar secondary wato j.s.s 3, taso ta d'ora zuwa senior amma Malam ya hanata dan zuwa lokacin shima yaga dacewar tayi aure saboda shekarunta sun ninka ma yadda suke aurar da yaransu mata duk yadda ta dinga masa nacin ya barta ta cigaba yak'i yace idan tayi auren in ALLAH yasa mijin data aura mai sha'awar yin karatun ne saitayi a gidanshi. Ita dama Ayyah murna fal cikinta, haka Maryam ta hak'ura a hakan ma ta godewa ALLAH da wanda ta samu d'in ta cigaba da zaman gida. Duka cikin masu neman auren natama bamai rabo a ciki dan wani can daban yazo tayi kuma na'am dashi, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba magabata suka shiga maganar, lokacin shi Basheer yana jami'a, anyi biki lafiya an tashi lafiya an kaita gidan mijinta dake nan cikin yolan.

Tsiransu ba yawa da Basheer dan shima auren wurin yayi saboda iyayen wadda yakeso d'in da suka nemi ya turo saboda aure zasu yiwa d'iyar su idan bai shiryaba zasu aurarwa da wani gashi kuma suna masifar son junansu hakan yasa ya uzzurawa su Malam Abdullahi shifa lallai aure zaiyi gashi baima yi wani nisa sosai a karatunshi na jami'a daya fara ba.
Da farko dai Malam bai yardaba sai daga baya sannan ya amince, akasha bikinshi da Hafsat k'anwar abokinshi.
Anan gidan yafara zama inda ya gyara d'aki akasa amarya a ciki.

Ya cigaba da karatunshi gefe d'aya kuma yana d'an tab'a kasuwanci, dama kuma business yake karanta a school.

Haihuwar farko da Hafsat tayi ta haifi 'ya mace wadda taci sunan Ayyah wato Khadeejah, har lokacin suna nan a cikin gidan, Khadeejah tanada shekara uku Hafsat ta k'ara samun wani cikin zuwa lokacin Basheer yasamu cigaba harya gina musu d'an k'aramin gida suka koma ciki.
Namiji ta haifa lokacin da cikin ya isa haihuwa, akasa masa Ameen sunan baban Hafsat kenan.
Har zuwa lokacin itakuma Maryam ALLAH bai bata haihuwa ba.
Shima Ameen shekararshi uku ta k'ara samun wani cikin.









, kuma wani ikon ALLAH wannan cikin yafi bata wahala akan sauran guda biyun sosai take laulayi danma Ayyah na taimaka mata da yaran dan kusan can suke yini wani lokacin ma har kwana suke a can hakan yasa ayyukan gidan nata suka ragu. A daidai wannan lokacin ne itama Maryam tasamu nata cikin zokuga murna wajen bayin ALLAHn nan suka yiwa ALLAH godiya tasha gata sosai a wajen mijin da sauran y'an uwa ta cigaba da rainon cikinta cikin kulawa.
Ranar da Hafsat ta haihu a ranar ALLAH ya yiwa Malam Abdullahi rasuwa, dama ya d'an kwana biyu yana fama da jikin, sunyi matuk'ar girgiza da rasuwar nan ta Malam Abdullahi, saidai dole mutum ya d'auki dangana dan ita mutuwa rigar kowa ce kowa saiya sanyata sai abin ya had'e musu biyu ga farin cikin samun k'aruwa ga kuma gagarumin rashi da sukayi a familyn su na madugu.
Da ranar suna ta zagayo sai aka maidawa jaririn sunan Malam wato ABDALLAH.
Tsiran Hafsat da Maryam duka sati biyu itama ta haifo yaronta namiji bayan doguwar nak'uda datayi, itama d'in dai sunan Malam d'in aka maidawa yaron.

Rayuwa ta cigaba da tafiya da dad'i ba dad'i har Basheer ya kammala masters d'inshi ya d'ora harkokin kasuwancinshi.

Bayan wasu shekaru.
Arzik'in Basheer wanda yazama Alh a yanzu ya hab'aka sosai ubangiji ya sawa kasuwar shi albarka, yayi fice sosai sunanshi kuma ya zaga ko ina, daga kan Abdallah Hafsat bata k'ara haihuwa ba saida akayi shekara biyar sannan ta k'ara haihuwar d'iya mace mai suna Hauwa'u daga Hauwa'u saikuma Mabrookah saikuma twins datayi duka mata wanda daga sune bata k'ara wata haihuwar ba.

Maryam ma bayan nata Abdallahn tayi Zakiyyah, Hameedah, Kulthum da Hannah wanda itace y'ar auta itama domin daga kanta ne haihuwar ta tsaya.

Tun tasowar Abdallah Ammi (Hafsat) ke fama dashi saboda rashin jin maganar shi ga surutu gashi duk maganar datazo bakinshi fad'ar ta yake ba abinda ya dameshi.

Ganin harkokin kasuwancinshi sunfi a kano shi Alh Basheer d'in yasa ya siya gida ya tattaro iyalan nashi gaba d'aya suka dawo kano. Har Ayyah yaso tahowa da ita tace a'ah ita sam bazata biyoshi ba zata zauna gurin danginta, amma har a yanzun yanada burin d'auko mahaifiyar shi ya zauna tare da ita hankalinshi zaifi kwanciya idan tana gabanshi duk da can d'inma akwai d'iyar k'anwar ta dasuke zaune tare bazawara ce batada aure.


Alh Basheer ya mallaki manyan kamfanoni a cikin birnin kano dama Nigeria gaba d'aya sannan yanada hannun jari a kamfanunnuka da dama na gida dama na waje. Ya k'ara gina wani k'aton gidan a unguwar nassarawa G.R.A. part daban daban suka tare a ciki.
(Sauran haife haifen da Hafsat tayi duk a kano tayisu Khadeejah, Ameen da Abdallah su kad'ai aka haifa a yola).

Bayan dawowarsu kano Khadeejah tasamu miji anan tayi aure yaranta biyu ma a yanzu haka Afnan da Nu'aym sai Amin da ake shirin bikinshi a halin yanzu.

Ameen tun yana yaro yake da sha'awar yazama banker dan haka gaba d'aya karatunshi akan aikin banki yayi shi kuma Abbie kamar yadda suke kiran Alh Basheer dashi bai hanashi ba saima k'warin gwiwa dayake bashi duk da dai yaso ya karanci business kodan yasamu mai taimaka mashi amma bai tauyeshi ba yabashi damar zab'in ambition d'inshi tunda ga Abdallah shi saiya karanci business d'in, kuma Alhmdulillah burinshi ya cika na zama banker d'in.

Mrs Salees Mu'az 💝
Maryam Ibraheem Aleeyu
[Ummee]

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
2/14/22, 08:38 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* ♥️🩸♥️

HASKE WRITER'S ASSOCIATION
(Home of expert & perfect writer's)

Writer: Oum Hanan
The writer of DR SAIF

Free page
Fiction story


02

Shikuma Abdallah tun tasowar shi yakeda sha'awar zane zane koyaushe zaka ganshi da pen da paper yana zana bishiyoyi, gidaje, da tsuntsaye flowers,da sauran zane, ko assignment aka basu a school indai na drowing ne shine yake winning shikuma saiya taso da son yazama architecture.
Lokacin da Abbie ya zaunar dashi ya tambayeshi nashi ambition d'in kai tsaye yace masa mai zane yakeso yazama, cikin rarrashi Abbie ya nuna masa ya karanci business administration dan ya taimaka masa kan harkokin kasuwancinshi ba wani b'oye b'oye dan tun yana d'an mitsitsinshi bai iya b'oye abinda ke ranshi koma meye fito dashi yake koda kuwa wanda zai gayawan bazai masa dad'i ba yacewa Abbien shi wllhy zane yakeso kuma shi zaiyi idan kuma aka takura masa karatun ma zai bari gaba d'aya 😡🤣 sanin halin darunshi yasa Abbie yace me yayi zafi? yaje yayi ALLAH ya bada sa'a, dan baya d'aya daga cikin iyayen dasuke takura yaransu kan abinda sukeso ko yaushe yana duba maslahar yaran ne sannan nefa aka samu zaman lafiya. Kamar Ameen din shima yasamu cikar burin nashi alhmdulillah yaje yayi karatun kuma ya fito da good results

Arch. Abdallah Basheer Madugu kenan inkiya Modibbo, mutum magananne ba ruwanshi da wani miskilanci irin na Mr hukunci😂 ( Dr Saif) ga masifa da neman tsokana halayyar nan tashi dai tun yana yaro bata sauya ba, saurayine d'an kimanin shekaru 30 kyakkyawa ne na ayi kwatance dashi kunsan dai fulani tubarkallah akwai baiwar kyau, dogo ne sosai kuma sam bashida jiki sai afkin tsayin da faffad'an k'irji da ALLAH yayi masa baiwa, mugun d'an hayagaga ne idan kuma ka ganshi ya nutsu yana zane saika rantse da ALLAH bashi bane saboda yadda yake maida duk wani attention d'inshi kan abinda yake, tamkar hawainiya haka yake wajen canza kala yanzun nan zaiyi abu saikuma yakoma tamkar bashi yayiba kokuma wani tym d'in ka ganshi yazama wani silent kamar bashi ba.


Akwai yayar Ammi da suke uwa d'aya uba d'aya datake aure a garin kaduna da nata iyalin tanada 'ya'ya sosai dan yaranta sun kusa goma maza da mata amma duk sunyi aure mazan da matan sai guda uku ne yanzu a gabanta Ja'afar dayake saurayi kusan sa'an Abdallah saidai Abdallahn ya girmeshi da wata biyu, saikuma twins d'inta itama wad'anda zasuyi kusan sa'anni dana Ammi dan familynsu akwai y'an biyu sosai, matane dukansu Hassanar Janan ake kiranta itakuma Hussaina Jauhar identical twins ne su dan in bakayi musu cikakken sani ba to kuwa bazaka iya bambance su ba , ba kamar na Ammi da sam basu kama kamar ba twins bama idan ba an fad'awa mutum ba. ta b'angaren halayyar sune kawai ake ganesu dan ita Janan tanada sauk'in kai da sanyin hali ga hak'uri da kawaici sab'anin Jauhar datake matsiwaciya ga rashin kunya da d'an banzan surutu, suna first year d'insu ne a higher level inda Janan take kano gidansu Abdallah tana karatunta a B.U.K wato Bayero university Kano itada Hassana da Hussaina, itakuma Jauhar acan Kadunan take nata karatun a poly. Sunada kyau mai d'aukar hankali ga diri da ALLAH yayi musu da kyan sura komai nasu iri d'ayane.


Itama Maryam wadda suke kira da Momy a yanzu ta aurar da Zakiyyah Hameedah da Kulthum d'in sai auta Hannah datake gabanta a yanzu tana karatu saikuma Abdallahnta da shima baiyi auren ba yake aiki a wani babban company na babansu wanda ake sarrafa fata.

Wannan shine tarihin madugu family a tak'aice ga kuma su Jauhar dasu Abdallah suka had'a alak'a ta jini dasu ta b'angaren Ammi.


A yau alhamis Abdallah yake dawowa daga k'asar Italy wani course dayaje duka na wata biyu duk akan aikinshi na zane a yaune kuma yake dawowa k'asar.

Tun safe Hassana da Hussaina ke kaida kawowa wajen yin girke girke kasancewar basuda lecture ita Janan tun 7@m tabar gidan.
"Dan ALLAH sis ya kikaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login