Showing 54001 words to 57000 words out of 90881 words

Chapter 19 - Wata Soyayya Complete Hausa Novels by Maryam Ibraheem Aleeyu.txt

a rufe wani tsananin son mijinta na k'ara ratsata ada gani take ba yadda za'ayi Yah Abdallah yasota har taji dad'in zama dashi sai gashi kuma alhmdulillah komai yazo mata cikin sauk'i batada matsalar komai dashi sai wanda ba'a rasaba wanda kuma zaman aure ya gaji hakan zo mu zauna zo mu sab'a tana fatan ta rayu da mijinta har k'arshen rayuwarta.
Daga nan kuma salon labarin yafara canzawa ya d'auketa cak suka nufi bedroom ganin suna shirin zubewa k'asa.


√^√^√^√^√^√•••••••?
Rayuwa ta cigaba da tafiya da dad'i ba dad'i dama haka rayuwar ta gada watarana zuma watarana mad'aci ayi kuka ayi dariya da haka har lokacin da kowa zai amsa kiran ubangiji subhanahu wa ta'alah ubangiji ALLAH yasa mudace yasa ranar mutuwar mu tazama ranar farin cikinmu ALLAH kasa mu cika da Imani yabamu sa'ar tafiya alfarmar sayyadil wujuud sallallahu alaihi wa alihi wasallam (Amin ya Rahman).


Mrs Salees Mu'az 💝
3/5/22, 18:41 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*💝

Page 32.
Paid book

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*.

© Oum Hanan

Tun kafin cikinta yafara girma ya kaita ta ziyarci y'an uwa Yola suka fara zuwa suka sauka gidan Momy Maryam taga y'an uwa ta zazzagaya sosai kwanansu biyar anan Yolan suka wuce Kaduna gidansu Janaan.
Tunda sukaje Abdallah yake gumawa Jauhar takaici iri iri rashin kunya kala kala kuma tasan da biyu yake hakan,su Mama kuwa sai sallamawa zaman falon sukayi Hajiya Yaya ce ma wani lokacin takan ce baza'a takura mata da zaman bedroom ba ta fito falon ba jimawa kuwa zata gudu tana faman mita Abdallah na mata dariya. Gaba d'aya Jauhar ta k'osa sutafi kafin zuciyarta ta buga duk da dai bata gaji da ganin y'ar uwar tata ba amma mijinta yaja mata, ita kanta Janaan d'in yana matuk'ar bata kunya saidai ba yadda ya iya dashi a haka suka gama kwanakin su suka tafi.

Shak'uwa ce mara misaltuwa ta k'ara shiga tsakanin Madugu da Janaan duk wanda ya gansu dole yayi mamaki saboda sanin halin shi sai gashi kuma yabawa marar d'a kunya irinsu Aunt jamila da sauran y'an team d'inta 😄 bani na fad'a ba🥲.



•••••••••••••?
A haka Janaan ta cigaba da rainon cikinta wanda tun yana y'an watanni da basu wuce hud'u ba yayi girma sosai idan mutum yagani sai yace yayi wata biyar koma shida school d'inta kuwa tuni ta ajiyeta gefe saboda laulayin datake kullum batada cikakkiyar lafiya hakan yasa dole ta hak'ura duk da yadda takeson karatunta sosai. Sosai Abdallah yake bata kulawa taban mamaki wanda kowa yagani sai abin ya d'aure masa kai wai Abdallah ne yake yiwa mace haka?.

Ganin yadda take matuk'ar shan wahala yasa Ammi da Ayyah suka nemi Abdallah ya maidata gabansu lokacin cikinta yanada wata takwas amma idan mutum yagani zai iya rantsewa ya shiga cikin na goma bama tara ba saboda yadda yayi mugun girma ga kumburi datake fama dashi, Nan fa Abdallah ya k'ek'ashe k'asa yace sam shi babu inda zaikai matarshi ko haihuwa tayi ba inda zata saidai azo a zauna musu saida Ammi tayi masa jan ido sosai harma da Abbie wanda Ammi ta fad'a masa ya kuma ga dacewar Janaan d'in ta dawo gabansu, haka nan dai bawai da son ranshi ba ya maida ita da siyayyar kayan baby daya uban jidosu kamar hauka.
Kwana d'aya biyu shima sai gashi wai yadawo gidan da zama bazai iya zama acan ba matarshi ba, haka yasa aka gyara masa side d'in daya bari ya zauna a ciki. Sosai su Ammi kejin dad'in irin d'imbin kulawar da Abdallah yake bawa Janaan duk da dai harda rashin kunya yake had'awa saidai su kauda kai amma suna jin dad'in hakan sosai.
Yauma suna bedroom d'in data sauka bayan zuwanta kusa dana Ammi, yana zaune a tsakiyar gadon ya jingina bayanshi da pillow ya mik'e k'afafunshi dogon wando ne a jikinshi plain ruwan zuma da farar riga mai gajeren hannu, Janaan na kwance kanta akan cinyarshi hannunta cikin nashi hannun yana mammatsa mata su saboda kumburin da sukayi suma hatta fuskarta ta d'add'aga matuk'a gaya yake tausayawa matar tashi ko ba'a fad'awa mutum ba yasan tanajin jiki ya matsu yaga ta haifar masa da abinda ke cikin nan nata kota huta da wannan wahalar.
"Yayanah". yaji muryar Janaan ta ambaci sunanshi cikin sanyin muryarta wanda a yanzu ta k'ara yin sanyi sosai saboda wahalar ciki.
"Na'am MAI SANYIN". yace shima a hankali bayan ya sunkuyo da kanshi saitin kunnenta, murmushi tayi jin sabon sunan daya mak'ala mata kuma yau dama kullum da kalar sunan dayake fad'a mata wani ma idan ya fad'a sai abin yaba mutum dariya.
Bata bud'e idanunta da suke a lumshe ba tace
"Idan na haihu wani suna za'a sawa babyn?".
"Kibari ALLAH ya saukeki lafiya mana Baby saurin me kike uhmm?".
"Nidai kawai inaso inji ne Yah Modibbo". tace cikin muryar shagwab'a, murmushi yayi yace
"Idan namiji ne zan maida sunana ne idan kuma baby girl ce zataci sunanki ok?".
Da mamaki tace
"Sunan mu fa Yayanah?".
"Basuyi bane?". ya maida mata da tambaya maimakon amsa yana d'age kafad'a daga zaunen dayake.
"Nikam gaskiya dai.....bai bata damar k'arasa abinda yayi niyyar fad'a ba ya sunkuyo tareda zura bakinshi cikin nata ya shiga bata zazzafar sumba daga nan kuma ya shiga ragewa kanshi zafi cikin dabara batare daya takurata ba dama a kusa yake an kwana biyu ba'a had'u ba 🙃.


Tunda cikin Janaan ya shiga watannin haihuwar shi su Ammi suke zuba ido amma shiru haka dai suka cigaba da jiran haihuwa da kuma addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya Abdallah da kanshi yake kashe ayyukan gabanshi ya kaita asibiti ganin likita da kuma yin awo. Lokacin da akayi scanning aka tabbatarwa da Abdallah twins ne a cikin Janaan, tamkar zaiyi hauka saboda tsabar murna suna dawowa kuwa ya fesawa su Ammi labari suma sunyi murna sosai tareda fatan sauka lafiya.


√•√•√•√•√•√•√•√
A firgice Jauhar ta farka daga wani mummunar mafarkin datayi a daren ranar ganin y'ar uwarta cikin wani hali marar dad'i kai tsaye bazatace ga yanayin da Janaan d'in take ciki ba kawai dai ta ganta cikin wani hali mai wuyar fassara gaba d'aya sai jikinta yayi sanyi taji gabanta sai fad'uwa yake addu'o'e ta k'ara yi ta k'ara komawa ta kwanta da k'yar barci ya d'auketa bayan dogon lokaci data d'auka idanunta biyu ta kasa komawa barcin.
Washegari kuwa tana idar da sallahr asubah ta dokawa Janaan kira a waya, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da taji Janaan d'in tayi picking kuma muryarta lafiya lau sai lokacin hankalinta ya kwanta sosai Janaan ta shiga tambayarta lafiya kuwa kira da asussuba haka? kawai cemata tayi ba komai kawai ta kirane dai taji lafiyar ta daga nan sukayi sallama.
Tun daga lokacin Jauhar taji gaba d'aya hankalinta ya koma kan y'ar uwarta burinta tasa ta a idanunta duk hankalinta yayi Kano dan haka tasamu Mama da maganar tanason zuwa Kano, Mama tayi mamaki k'warai ta tambayeta dalili tace kawai ita haka nan take so taje taga Bloody d'inta, da farko Mama bata yardaba tace ta bari Janaan d'in ta haihu tunda ta kusa amma ta shiga yimata magiyar dan ALLAH ta taimaka ta barta tunda sun samu hutu a school da k'yar Mama ta barta tace zata fad'awa Daddy aji ta bakinshi.
Da dare take fad'awa Daddy zancen tafiyar da sukayi da Jauhar baija da nisa ba yace ALLAH ya kiyaye hanya ayiwa Ja'afar magana ya kaita.
Kwana biyu da yin maganar Jauhar ta shirya inda driver ya tafi kaita saboda Ja'afar aiki yasha masa kai a office hakan yasa bai samu kaita ba. Sai ganinta kawai sukayi katsam dan bata sanar da kowa zuwanta ba itama kuma Mama da sukayi waya da Ammi ta manta bata fad'a mata ba.
Rungume juna sukayi sosai lokacin data k'araso cikin tsananin murna da soyayyar y'an uwantaka dake ratsa jininsu, ta tausayawa Janaan sosai ganin yadda takoma kamar ba itaba tamkar tayi mata kuka, nan suka had'u a bedroom d'in Janaan d'in har da Hassana da Hussaina sunata hira a haka Abdallah ya shigo ya samesu tun kafin ya shigo d'in k'amshin shi ya bayyana musu mai shigowar hakan yasa su Hassana duk suka mik'e tsaye suna jiran ya shigo su fita Jauhar kam tana nan a inda take kusa da Janaan tasan shi dinne saboda yadda bugun zuciyarta ya canza lokaci d'aya gabanta sai wani fat fat yake tamkar zai fasa k'irjinta ya fito waje batasan meyasa hakan ba kokuma dan ta dad'e bata ganshi bane oho murmushi kawai Janaan take saki tun kafin shigowar shi ALLAH sarki Yah Abdallah gaskiya wanda bai zauna dashi ba bazai tab'a fuskantar shiba yanada dad'in zama ga wanda bai saniba kuma yanada hawa kai da addaba itadai a yanzu batada kamar shi kulawar dayake bata ko auren soyayya sukayi sai haka ba abinda zatace sai alhmdulillah ubangiji ya karb'i addu'arta yabata zaman lafiya da nutsuwa a gidan aurenta.
Yana shigowa Hassana da Hussaina suka fita daga bedroom d'in kansu a k'asa sudai duk da ake cewa Yah Abdallah ya canza har yanzu basu tabbatar ba dan zagin dayake musu bai dainaba yadai d'an ragu ba kamar da ba. Farar rigace a jikinshi long sleeve mara nauyi sai wandon jeans blue black saita gadon tashi wato P.cap white color dake kanshi idanunshi kyarr akan Jauhar da tun shigowarshi ta had'e rai sosai itama idanunta cikin nashi kowa da abinda yake sak'awa cikin ranshi yayin da kowa ya kasa fassara irin kallon da d'an uwanshi ke jifanshi dashi, sai taga duk ya canza mata kamar bashi ba yayi y'ar k'iba abinshi sab'anin da dayake sai uban tsayin kawai kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin tarin nutsuwa da kwanciyar hankali gashi ya k'ara fari akan wanda yake dashi da masha ALLAH musamman da bak'i sid'ik d'in sajen daya k'ara k'awata fuskar tashi da gemunshi na gayu wanda suke shan uban gyara da mayuka masu matuk'ar kyau da tsada. Ido ta runtse gam zuciyarta na wani irin rawa lokaci d'aya ta saki y'ar k'aramar ajiyar zuciya dako Janaan dake kusa da ita bata jitaba.
A hankali ya shiga takawa inda suke zaune bayan ya soke hannayenshi cikin aljihun wandonshi, yana takowa ne yayin da bugun zuciyarta ke k'ara tsananta tayi ta maza ne kawai ta basar ta juyar da kanta gefe tana girgiza k'afafunta data d'ora d'aya kan d'aya, k'erere yayi musu akai yayi musu tsaye idanunshi akan Jauhar data juyar dakai wani side d'in.
Rai a had'e ba alamun wasa a muryar shi cikin harshen fulatanci yace
"Ke tashi ki fita zanyi sirri da matata".
Da sauri ta juyo ta kalleshi tanajin tamkar ta tashi ta daddalla masa mari saboda mugun haushin daya bata.
"Bazaki fita bane? ko bakya jin yaren danayi magana dashi?". yace still dai da fillacin yana zaro hannayenshi dake aljihu ya kama k'ugunshi da duka hannayenshi, a fusace Jauhar ta mik'e tsaye sama da k'asa ta kalleshi itama cikin fulatanci tace
"Dan ALLAH idan ka tashi ka cinyeta gaba d'aya k'arewar sirri mtwss". taja k'aramin tsaki ta nufi k'ofar fita bedroom d'in.
"Cinyewa ta nawa kuma? ki zuba ido kiyi kallo had'iyeta zan dinga yi ina dawo da ita tsabar yadda nake sonta kwarkwar d'in yarinya kawai". Tsaye tayi a bakin k'ofar bayan ta janyo k'ofar da k'arfi duk yadda taso hana hawayen idanunta zuba saida suka zubo zafi zuciyarta keyi mata tarin tambayoyi ne cike fal cikin ranta amma batada wanda zai amsa mata su, jin takun tafiya kamar an nufo wajen tasan baya wuce Ammi ko Ayyah.

M&S 💝
3/7/22, 21:16 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*💝

Page 33.
Paid book.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*

© Oum Hanan.

Da sauri tasa hannu ta goggoge idanunta sannan tabar wajen cikin sassarfa ta nufi bedroom d'insu Hassana.

"Yah Modibbo wai sai yaushe ne zaku daina y'ar tsama da Bloody dan ALLAH?". Janaan tace tana kallonshi.
"Ranar datayi hankali". yabata amsa kai tsaye yana zama kusa da ita.
"Da da yanzu fa ba d'aya bane Yah Modibbo yanzun surukar kace fa".
"Idan ban bige miki baki ba kice......kukan shagwab'a tasa masa wanda yasa ya kasa cigaba da maganar ya janyota jikinshi yana fad'in tayi masa shiru zai gaisa da baby's d'inshi.

Tunda Jauhar ta fahimci abin na Madugu wulak'anci ne saita daina shiga bedroom d'in Janaan dan bayan wannan ya k'ara zuwa ya sameta suna zaune suna hira da Janaan lokacin su su Hassana suna school ranar ma kam baiyi mata magana ba sai gani tayi ya rungume Janaan d'in yasa bakinshi cikin nata ita kanta Janaan d'in abin yazo mata unexpected, abin yayi matuk'ar k'ona mata rai tashi tayi ta fita tanata faman masifa harda cemasa jarababbe da cikin ma bazai bar mata y'ar uwa ta huta ba ( Hajiya Jauhar 🤣).
Tunda daga lokacin ta janye shiga bedroom d'in saidai su had'u a falo dasu Ammi ayi hirar cikin jama'a tasan dai duk iskancin shi da rashin kunyarshi bazaiyi a gaban su Ammi ba amma abinda ya bata mugun mamaki rannan a gaban Ayyah yayi hugging d'in Janaan ya k'ara mata da peck a goshinta Ayyah sai kauda kai tayi k'arshe kuma ta tashi ta bar falon tun daga nan ta sallamawa Madugu da aikinshi lallai a hakane har ake cewa yayi hankali? indai hakane kam da sauranshi ALLAH ya shiryashi.


Friday morning.
Tun bayan sallahr asubah Janaan takejin jikinta ba daidai ba ga ciwon baya da mara kad'an kad'an dake damunta idan suka murd'a mata saikuma su saki. Abdallah daya shigo lokacin dazai fita office yaga yanayinta duk ya rud'e ya dinga tambayarta ko tanajin wani ciwo ne cikin dauriya ta nuna masa ba komai batason tun yanzu ta nuna gazawarta ta tayarwa da mutane hankali, tsugunawa yayi yayi kissing d'in cikin ya tashi yayi kissing d'in goshinta ya gangaro kan dogon hancinta sannan ya dire kan bakinta doguwar sumba ya bata sannan ya saketa saidaya k'ara yin hugging d'inta sannan yayi mata sallama yana fad'in ta kular masa da kanta.
K'ofar daya fita tabi da kallo fuskarta d'auke da mad'aukakin murmushi tana matuk'ar son Yah Abdallah yazama wani b'angare na rayuwarta a yanzun ALLAH ya bata ikon cigaba dayi masa biyayyar aure ninkin ba ninkin akan wadda take masa a da, siririyar k'ara ta saki tareda dafe k'asan mararta wadda ta tsinka mata idanunta ta rufe gam tana ambatar sunan ubangiji so take ta d'aga k'afar taje ta zauna amma ta rik'e da k'yar taja k'afafun nata da sukayi mata matuk'ar nauyi ta nufi bakin gado ta zauna tana cije baki.
Ajiyar zuciya ta saki lokacin da ciwon marar ya saketa, nan ta cigaba da zama sai yayi kamar ya saketa saiya k'ara dawowa k'arshe dai k'asan tiles ta sauko ta durk'ushe nan k'asa tana salati idanunta a runtse, cikin haka ALLAH ya shigo da Ammi dan ta dubata taga halin datake ciki nan taga yadda Janaan take da sauri ta k'arasa inda take hankalinta a tashe ta dafa kafad'arta tana tambayar ta abinda ya sameta sam Janaan batayi magana ba sai cije baki datake ta faman yi na azaba hakan ya tabbatarwa da Ammi lallai nak'uda ce, da sauri taje ta sanar da Ayyah suka taho tare Ayyah tace kamata yayi a tafi asibiti dan haka zataje ta sanarwa driver ya fito da mota itakuma Ammi ta shirya kayan da za'a tafi dasu.
Hakan kuwa akayi Ayyah ta fita Ammi kuma ta fara shirya kayan baby's dana Janaan d'in da duk wasu abubuwa datasan za'a buk'ata acan a rud'e take yin komai cikin hanzari tana faman jerawa Janaan sannu wadda har lokacin take durk'ushe a k'asa idanunta a rufe tana ambaton ALLAH batayi zaton abun zaiyi worsting haka tun yanzu ba, sam Jauhar batasan bikin da akeba sai lokacin da Ammi ta kamo Janaan zasu fita itama ta fito falon suka had'u sosai hankalinta ya tashi ta shiga tambayar Ammi meya samu Janaan d'in Ammi tace mata haihuwa ce zasu tafi asibiti ne zasuje itada Ayyah itakuma ta zauna a gidan, Jauhar taso binsu Ammi ta hanata tace suma ba dad'ewa zasuyi ba insha ALLAH suna fatan ace da sunje ta haihu haka suka tafi suka bar Jauhar cikin jimami na ganin halin da y'ar uwarta ke ciki.

Suna zuwa aka karb'i file d'inta dama inda take zuwa ante natal ne aka shiga da ita labour su Ammi na zaune gaba d'aya hankalinsu a tashe yake indai kanada mai nak'uda dama hakane hankali bazai tab'a kwanciya ba har sai kaga ALLAH ya bud'i ido lafiya fatansu ALLAH ya sauketa lafiya ya kawota mai sauk'i kuma.
Tunda aka shiga da Janaan take faman abu d'aya haihuwa shiru ba ita ba alamunta sai tsabar wuya datake sha, a hakan kuma tayi matuk'ar dauriya duk da haihuwar fari ce sam bata irin ihuce ihuce nan sai salati da ambaton ALLAH kawai take amma fa tana shan azaba wadda tunda uwarta takawo ta duniya bata tab'a jin irin misalinta ba.
Ammi batayi niyyar kiran Abdallah ba karta tayar masa da hankali so tayi sai an haihu sannan ta kirashi tayi masa albishir amma ganin lokaci yanata k'ara shud'ewa abu yak'i ci yak'i cinyewa har lokacin bata haihu ba yasa Ammi tace ta kirashi ta fad'a masa nan kuma ta dinga neman number tashi switch off sai Abbie ta kira ta fad'a masa.
Meeting d'in daya shiga yasa ya kashe wayoyin nashi bayan fitowar tashi kuma bai kunna wayar da wuri ba sai bayan wani lokaci daya kunna yaga kiran Ammi rututu har dana Abbie 2miscal, Ammi yafara kira ta sanar dashi suna hospital Janaan zata haihu sosai hankalinshi ya tashi nan da nan ya tattara duk abinda yake ya ajiye a gefe kasancewar dama yasan asibitin dama nan yake kaita ake duba lafiyar ta.
Da gudu ya figi motar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login