Showing 3001 words to 6000 words out of 11084 words
Chapter 2 - YAR ZAMAN DAKI Complete Hausa Novels by Ameera Adam.txt
ta zo ta same ka."
Khalid duk irin buguwar da ya yi bai sa ya karaya ya ce, "Wai uban waye yake son shiga tsakanin ma'aurata a daren amarcinsu? Babu inda za ni kowanne matsoraci ne ya fito mu yi gaba da gaba." Khalid tun bai rufa baki ba sai ji ya yi an yi saman fanka da shi, ƙafafuwansa na jikin fanka kansa yana ƙasa yana reto. Tsoro azaba da wuya ta sa ya sako fitsari daga sama ba tare da ya sani ba, Zarah na ganin an tasamma halaka mijinta ta sa kuka tana faɗin:
"Don Allah ku ƙyale shi karku kashe min mijina." Zarah bata rufe baki ba sai ji ta yi an turo ƙofar ɗakinsu an shigo, Khalid yana daga saman fanka idanunsa suka hango masa wata ƙatuwar kaza, tsayi da girman kazar za su iya yin girman yaro mai shekara huɗu. Cikinsa ne ya fara kaɗawa cikin rawar murya ya ce, "Wayyo Zarah Kazaaaaaa."
Zarah na shirin yin magana Kazar da take tafe tiƙis tiƙis ta karɓe zancen da cewar, "Haba Mijin kaza zuwa na yi da kaina ba aike ba, na tafi da kai mu ɓarje amarci ko na biyo ka sama Angona." Khalid ya fara saka hannuwa yana kare jikinsa ya ce, "Don Allah ki koma ni wallahi ba mijinki ba ne." Khalid tun bai rufe baki ba Kaza ta hau saman madubin Zarah tana tafe tana wata irin girgiza za ta ɗafe saman fanka, Zarah na daga zaune Cinyar kazar ta ce mata:
"Zarah ki bani haɗin kai ko na yi kidinafin ɗinki."
Khalid na ganin Kaza ta tunkaro shi gadan-gadan ya sake ƙwallah ƙara yana faɗin, "Zarah kazaaaaaaa, wayyo za ta min fyaɗe." Zarah ita ma ta kanta take yi don haka ta ce, "Khalid Zakara zai yi kidinafin ɗina." Kaza na hawa saman fanka ta yi tsallake ma maƙale hannun Khalid yana cewa, "Angonaaaaaa."
NI MA SAI NA CE NA BARKU LAFIYA KU TAFI CETO KAR KAZA TA HAIKE WA ANGO, NA YI NAN BYEEEEEEEEE😂😂😂
Ummou Aslam Bint Adam🌚*'YAR ZAMAN ƊAKI*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️
7&8
Khalid na jin yanda Kaza ta cafki hannunsa ya ware murya cikin tashin hankali ya ce, "Wayyooooo Allah Kaza za ta haike min." Kazar ta ra gwaɗar da kai tana girgiza tozonta ta ce, "Angona yau fa ranar farinciki ne ka taimaki kanka ka ba ni haɗin kai." Tana gama maganar ta miƙa bakinta wurin saitin fuskar Khalid ta ce, "Matso na sumbace ka masoyi." Khalida ta juyar fa kai gefe yana tofar da yawu. Kazar ta tashu sama firrr kamar tsuntsuwa tana kaɗa fukafukanta, bata dira a ko'ina ba sai kan tafin ƙafar Khalid da suke can saman fanka. Khalid na jin Kaza a daidai ƙafarsa ya fashe da wani matsanancin kuka tare da faɗin, "Wayyo za ta mayar da ni Zakara, wayyo Zarah Kaza za ta mayar da ni zakara." Kaza ta sa faratan ƙafarta ta shafo gwiwar Khalid tana faɗin.
"Me ya yi saura Angona da kai da Zakara duk ɗaya ne a wurina."
Zarah na shirin yin magana ta ji cinyar kaza ta ce, "Amaryata ki ba ni dama kar ba tafi da ke a neme ki a rasa." Zarah na jin haka ita ma ta fashe da kuka don wannan karon ta kai maƙura, ta gama saddaƙarwa rayuwarta. Suna cikin wannan halin wayar Zara fara ringing, ringtone ɗinta karatun alƙur'ani ne, yana fara ƙara duka suka nemi komai suka rasa daga kazar har cinyar kazar da take iƙirarin ita zakara ce.
Khalid da yake maƙale a saman fanka sai ji kake faaaaaaaf ya faɗo kan gado, zumu-zumu ya yi saboda yadda ya galabaita. Ya juyar da kansa ya kalli Zarah murya a shaƙe ya ce, "Zarah yai muna ganin rayuwa." Zarah ta goge ƙwallar idonta ta ce, "Khalid wallahi gari na wayewa zan bar maka gidanka, kana gani cinyar kaza wannan ƙaramar hallita tana cewa za ta min fyaɗe." Khalid ya shafa wurin da Kaza ta taɓa ya ce, "Ki gode wa Allah Kaza ba ta haike min ba, kina ji fa wai kaza ce za ta min fyaɗe."
Zarah bata kula shi ba ta ɗauki wayarta, za ta bi kiran da aka yi mata daga can ƙofar ɗaki suka ji takun tafiya ƙwas ƙwas ƙwas. Da sauri Khalida ya wawuro zanin gado ya zagaya ta gefen Zarah ya ce, "Zarah ki ɓoye ni wallahi ta dawo, daga ji Kaza je wallahi haike min za ta yi."
Kafin Zarah ta yi magana daga bakin ƙofar suka ji an ce, "Kun ci sa'a amma babu komai a juri zuwa rafi." Jikinsu ba ƙaramin sanyi ya sake yi ba, Khalid na son yin waya yana tsoron tashi daga wurin. Dabara ce ta faɗowa Zarah va shiri ta saka wayarta a Airplane mode ta kunna karatun Alƙur'ani, tun suna jin taku a bakin ƙofar har suka daina.
A hankali Khalid ya janyo doguwar riga ya saka sannan ya ɗauki wayarsa ya wuce wani ɗakin da aka ware don hutawarsu. Yana shiga ya ciro wayarsa ya nemo wata lamba sai da ya kira sau biyar aka ɗauka, tun ba a fara magana ba Khalid ya fara magana bakinsa har rawa yake.
"Mai turakar Aljanu akwai babbar matsala fa. Yau daren amarcina amma Kaza da zakara sun hana ni walawa, yanzu haka da ƙyar na sha wai ni Kaza za ta yi wa fyaɗe..."
Khalid bai rufe baki ba kukan Walida a ƙofar ɗakinsu, wani dogon tsaki ya Khalid kamar zai yi kuka ya ce, "Mai turaka don Allah ka yi wani abu wallahi ina cikin damuwa." Daga can ɓangaren aka bashi amsa da cewar, "Khalid ka ji da yarinyar da take yin kuka idan ka daidaita nutsuwarka sai mu yi magana." Khalid ya guɗe baki zai yi magam ƙit ya ji Mai turakar aljanu ya katse.
Khalid tsabar takaici bai san lokacin da ya fashe da kuka ba, yana tafe yana hawaye ya isa bakin ƙofar ya buɗe. Walida na ganin Khalid ta goge hawaye ta ce, "Uncle na kasa bacci." Khalid baƙinciki ya sake kama shi a daƙile ya ce, "Mu ma ai ba mu yi ba."
Walida ta fara shinshine-shinahine ta ce, "Uncle ƙanshin zakara nake ji." Khalid ya fisgi hannun Walida cikin ɗakin yace, "Sai ki ci idan kin gan shi."
Zarah na hango Walida ta kashe karatun ta diro gabanta fuska a haɗe ta ce, "Ke! Me ya hanaki bacci." Ta haye kan gadon Zarah ta kishingiɗa tana lumshe ido ta ce, "Uncle bacci zan yi."
Zuciya ta ɗebi Zarah ta kai wa Walida duka ta ce, "Ɗaga min gado ko na ci uwarki wallahi." Khalid ya zaburo a fusace ya ce, "Ke Zarah me ye haka?" Walida ta fice daga ɗakin tana kuka ta nufi sashen da Khalid ya fara kaita, da gudu Khalid ya rufa mata baya sai da ya je tsakiyar gidan ya ji fuurrrr a saman kansa. Yana ɗago kai ya hangi Kaza tana ɗaga fuka-fukai ta ce, "Yau babu mai hana ni abin da na yi niyya, ƴan uwa ku kawo min ɗauki." Tana rufe baki sai ga tawagar kaji sun dira a kan Khalid masu danne hannuwa na yi masu danne ƙafa na yi.
Kazar ta fara rangwaɗa ta ce, "Bari fara salon jan hankali don na birge Angona." Rufe bakinta kw da wuya sai ga gashin jikinta na salewa. Khalid bai yi aune ba ya ganta a sulluɓe ba shiri ya ƙwallah ƙara yana faɗin, "Zarah Ki zo wallahi za ta haike min ta mayar da ni Zakara."
ANGON KAZA A SHA AMARCI LAFIYA, GOBE MAJE GANIN AMARYA DA ANGO😂
AYI HKR DA ERRORS BAN YI EDITING BA.
Ummou Aslam Bint Adam🌚*'YAR ZAMAN ƊAKI*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️
9&10
AMNASH BAKERY PRACTICAL CLASS
Mun ɗaura ɗamarar koyar da sana'o'in gashe-gashe da girke-girke kamar: VANILLA CAKE, DOUGHNUT, CHINCHIN, MEATFIE, COOKIES, CHICKEN NUGHET, BIRTHDAY CAKE, CAKE PERFAIT da sauran girke-girken sari a farashi mai rahusa 5K kacal domin masu farawa daga farko.
ADDRESS: NO EA70 TITIN ADAMU ƊAN KURA GANDU KAFIN GIDAN BASHIR TOFA OPPOSITE MASALLACIN ƘADIRIYYA. KANO STATE MUNINCIPAL L.G
PHONE NUMBER: 07038826617 for watsapp and call.
KU GARZAYO KU KARƁI SAMI FORM ƊINKU DON KAR WANNAN DAMAR TA WUCE KU.
Zarah na daga wurin da take a zaune kan gado ta ji yo ihun Khalid nan take hantar cikinta ta sake kaɗawa, takurewa ta yi a lungun gado tana karanto duk wata addu'a da tasan ta taɓa biyata a bakinta don lamarin ba ƙaramin kaɗamata ciki ya yi ba. Saboda tsabar tsoro ta karanta addu'a har da ta hawa abin hawa tun bata direta ba sake ɗaukan wata.
Kaza na jin abin da Khalid ya faɗa ta waiga tana ɗaɗɗaga ƙafa ɗaya ta ce, "Haba Angona wa za ka kira mana a wannan yanayin da muke ciki." Khalid ya fara ja da baya yana kallon sauran kajin da suka haye kan hannunsa sannan ya ce, "Don Allah ki rabu da ni wallahi ni ko da mace bil'adam ƴar uwata ban taɓa yin zina ba, me ye haɗina da ke kina Kaza ina mutum."
Kaza ta turo masa ciki gaba sannan ta ce, "Wannan cikin da ka gani sai da ya ɗauki cikin mazan bil'adam bakwai. Kai ne na takwas kuma duk namijin da na yi mu'amala da shi Zakara yake komawa, kalli can."
Kazar ta yi magana tana nuna masa kusurwar bango nan take Khalid ya kai idanunsa, bai yi aune ba sai gani ya yi zakaru na fitowa ɗaya bayan ɗaya daga cikin kusurwar bango. A tsorace ya zaro ido yana shirin yin magana zakaran farkon ya buga tsalle sai da ya yi sama sannan ya fara buɗa fuka-fukai sannan ya miƙa wuya gaba ya ce, "Kukkurukuuuuu." Khalid ya saki baki yana kallon ikon Allah don duka jikin zakarun a saɓule yake babu gashi, zakaran yana gama cara ya kalli Khalid ya ce, "Ɗan uwana ina yi maka murna da shirin fara sabuwar rayuwa, don nan ba da jimawa ba kaima za ka dawo zakara kamar mu. Ni sunana Bala Mai leda yau shekarata huɗu a cikin siffar zakara."
Zakaran farko na gama magana sauran suka riƙa gabatar da kansu, na ƙarshen cikinsu ya yi girgiza sannan ya : "Jikinka zai ɗau raɗaɗi fatarka za ta saluɓe kafin ka koma Zakara zan gaya maka gaskiya ka yi ta kanta don fyaɗen wannan kazar ba alheri ba ne. Ni nan da ka ganni Harisu sunana Bakanike ne shekarata ɗaya a haka..." Kazar na daga wurinta ta bugawa Zakaran da ya ke magana tsawa na take ya katse sauran maganar da yake yi.
Khalid wani wawan kuka ya saki ba tare da ya shirya ba, ya dubi Kazar da ta yi ƙerere a gabansa, tana banƙaro ƙirji gaba ya ce, "Yanzu waɗannan da gaske mutane ne kamar ni?" Kaza ta kai tsinin bakinta za ta sunbaci bakin Khalid da sauri ya goce. Zakaran da yake gefe ya ce, "Ɗan uwa ka yi duk mai yi wa ka tsira da kanka."
Khalid na jin haka ya zabura ya watsar da kajin da suka danne shi, ya riƙa surarsu ɗaya bayan ɗaya yana buga su da ƙasa. Duk wacce ya buga da ƙasa sai dai ka ji ta girgije ta ce, "Ka tsokanowa kanka wallahi nima sai na ɗana bayan uwar gayya ta gama da kai." Kaza na shirin faɗo masa gadan-gadan ya yi sufa da gudu ya faɗa ɗaki haɗe da danno ƙofa ya sakar mata sakata.
Da gudu ya faɗa gefen Zarah ya riƙo hanunta sai kawai ya fashe da kuka. Zarah ita ma kukan ta saka masa don rayuwarta gabaɗaya a dagule take, cikin kuka ta dubi Khalid ta ce.
"Khalid wannan wacce irin rayuwa muka samu kanmu a ciki?"
Khalid ya matse ƙallar idonsa ya ce, "Zarah yau na ga mutanen da suka koma Zakaru da idona, yanzu haka ni kaina kaɗan ya rage Kazar cen ta haike min, da tuni na koma zakara angon kaza." Saboda takaici Zarah shiru ta yi suka ci gana da zurawa sarautar Allah ido, suna nan zaune sautin karatu na ci gaba da tashi daga nan har bacci ya yi gaba da su.
PLS SHARE 🌚
Ummou Aslam Bint Adam🌚*'YAR ZAMAN ƊAKI*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️
11&12
AMNASH BAKERY PRACTICAL CLASS
Mun ɗaura ɗamarar koyar da sana'o'in gashe-gashe da girke-girke kamar: VANILLA CAKE, DOUGHNUT, CHINCHIN, MEATFIE, COOKIES, CHICKEN NUGHET, BIRTHDAY CAKE, CAKE PERFAIT da sauran girke-girken sari a farashi mai rahusa 5K kacal domin masu farawa daga farko.
ADDRESS: NO EA70 TITIN ADAMU ƊAN KURA GANDU KAFIN GIDAN BASHIR TOFA OPPOSITE MASALLACIN ƘADIRIYYA. KANO STATE MUNINCIPAL L.G
PHONE NUMBER: 07038826617 for watsapp and call.
KU GARZAYO KU KARƁI SAMI FORM ƊINKU DON KAR WANNAN DAMAR TA WUCE KU.
Washegari.
Asubar fari Zarah ce ta fara farkawa daga bacci, da sauri ta ƙarasa ta fara tashin Khalid da ya saki baki da hanci yana shaƙar bacci. A firgice ya tashi yana faɗin, "Zarah! Zarah ina kazar?" Zarah ta yi ƙasa da murya ta ce, "Khalid gari ya fara wayewa ka tashi mu yi sallah ka buɗe ƙofar mu fita, wallahi ni da ka gani ba zan sake wuni a gidan nan ba." Khalid ya fara muttsuka ido yana dube-dube ya ce, "Zarah ina nan yadda nake ko?" Zarah ta dube shi da mamaki tana faɗin, "Ban gane ba."
Hannunta ya janyo shafa mata a jikinsa sannan ya ce, "Don Allah a mutum nake ko na koma Zakara? Kin san zakarun nan fa suma har magana suna yi." Zarah ta yi guntun tsaki ta ce, "Idan so kake ka koma Zakaran sai ka bari idan na tafi gidanmu ba zakara ba ko Toro (Mijin agwagwa.) Sai ka koma." Ta ƙarasa maganar tana janyo jarkar faro ɗaya, ta fisgo bargon da yake kan gadonta, ta shinfiɗa a ƙasa ta fara yin alwala a kai. Khalid ya kalle ta ya ce, "Zarah ga banɗaki me kike yi haka?" Zarah ta yi masa kallon sheƙeƙe ta ce, "Jiya ina jinka da ƙyar ka ƙwaci kanka amma za ka ce min na shiga banɗaki, wallahi ko kashi na ji kafin na tafi gidanmu a nan zan yi." Shiru Khalid ya yi Zarah ta ci gaba da alwala.
Tana gamawa shi ma ya suri robar ruwa ɗaya, ya gabatar da alwala suka yi sallah. Bayan sun idar Zarah ta dubi Khalid ta ce, "Khalid ka leƙa idan babu komai a waje ka buɗe mana na tafi gidanmu wallahi ba zan ƙara kwana a nan ba." Khalid ya riƙo hannun Zarah cikin shauƙi ya ce, "Haba my love amma ai ko raya darenmu ba mu yi ba." Zarah ta haɗe fuska ta ce, "Khalid!" Yanda ya ji ta kira sunansa ya sa ya tsaya tsam yana sauraronta.
Ta nuna masa ƙofa ta ce, "Wallahi ba dare ba ko safiya ba za mu raya ba, da na samu na kwaci kaina a hannun zakara yana ƙoƙarin haike mun. Ni tun da nake na taɓa ganin masifa irin wannan? A ce kaza da zakara sune za su yi wa mutum fyaɗe wai har da kidinafin." Ta miƙe tsaye ta ɗaura ɗankwalinta ta je wurin ƙofa ta ce, "Don Allah ka zo ka buɗe min na tafi." Khalid ya haɗiyi yawu makwat sannan ya ce, "Haba Zarah ango nake fa ki tausaya min kina ganin baƙar wuyar da na ci hannun kaza kafin na tsero ɗaki."
Zarah ta ɗaga kafaɗa ta ce, "Yanzu ma dama na wurinka ka zauna sai ku kashe amarcin kai da amaryarka kaza, amma wallahi wuni ba zan ƙara a gidan nan ba." Zarah da Khalid haka suka yi ta ja'inja har gari ya waye suna ɗaki kowannensu na tsoron buɗe ƙofa.
Suna nan cikin ɗaki Walida ta ƙaraso bakin ƙofar ɗakin ta fara bugawa, ta window Khalid ya leƙa ya ce, "Walida kin tashi." Walida ta yi miƙa haɗe da hamma ta ce, "Wallahi Uncle na tashi don ma jiya ban samu bacci da wuri ba." Zaro ido Khalid ya yi suka haɗa ido da Zarah don shi a tunaninsa ko abin da ya faru tsakaninsa da kaza ne ya hanata bacci, ya tattaro murmushin ƙarfin hali ya ce: "Me ya hana ki bacci Walida?" Walida ta sake sakin hamma sannan ta ce, "Ga jikina duk tsami yake na so huce gajiyata amma haka bata samu ba, amma zan sake gwada sa'ata anjima." Khalid na shirin yin magana wayarsa ta fara ƙara.
Lambar mahaifinsa ya gani da mamaki ya ɗauka don lokacin ko tara bata yi ba. Cikin girmamawa ya ɗauka da sallama, tun bai rufe baki ba Mahaifinsa ya rufe shi da faɗa.
"Kai wanne irin mara hankali ne? Kai ka haifi kanka da ba za a gaya magana kaji ba? Tsabar ka raina mutane ba sai da nace maka yarinyar nan babu inda za ka da ita amma ka mayar da ni ɗan iska ko? Wallahi tun wuri ka haɗa kayanta ka dawo da ita ina dalili ka ɗauki son duniya ka ɗorawa yarinya, a daren aurenka ka ce za ka tare da ita." Khalid ban da gyaɗa kai ba abin da yake yi. Sai da mahaifinsa ya gama magana sannan ya