Showing 15001 words to 18000 words out of 19045 words

Chapter 6 - Dan Karuwa Romantic Hausa Novels By Zahra Surbajo.doc

09 Dec 2025

1661

da nana,koda kuwa bayan ranka ne,don Allah kadena wannan mgnr,nana na sonka kaima kana sonta don Allah ku zauna lfy,inde nine wlh kwanannan zanyi Aure kowa ya huta"

Hakade sukai ta tattaunawa akan matsalar,daga karshe me martaba,ya umarcesu dasu bashi guri ze huta.

Se Anjima suka masa sannan suka fice daga gidan hydar ya raka fahad gida sannan ya kara duba jikin nanar.

Koda zuwansu a zaune suka sameta a falo tana kallon tv hankalinta kwance

Tana ganinsu ta saki wani murmushi me sanyaya zuciya.

A hankali ta furta.

"Fahad abun Alfaharina,Aliyu hydara baban Sultan,jinin sarauta kun wuce reni"

Dukansu basu san sanda suka fashe da dariya ba.

Fahad ya karasa kusa da ita,ya rukota yana dariya yace.

"Farincikin ki ne burin hydara,shiyasa ya zaba miki miji fahad wanda ze iya baki rayuwarshi domin ki farinciki,"

Hydar cikin dariya yace.

"Lalle kin samu,ba karya,wannan kirarin duk namu mu kadai,gaskiya yadace abaki tukuici"

Dariya tayi ta kwantar da kanta ajikin fahad tace.

"Tukuicin da zaka min shine ka yi Aure nan da watanni biyu,masu zuwa shine kawai dadin dazanji na tukuicin da ka bani"

Dariya yayi yace.

"Angama uwargida sarautar mata,ki dauka nayi ma"

Daga haka hira suka shiga yi na duniya,koda wasa basu bata labarin abinda ya rabasu da hydar ba,dan hydar ya roki fahad kan kar ya bari tasani.

Amman sun fadimata hajiyace silar kaddarar data fadamata,yan haka ma ga abinda ya samu ita hajiyar.

Sosai nana take kuka dakyar suka shawo kanta tai shuru.

A falo ya tafi ya barsu,dan haka nana zamewa tayi ta kwanta kan cinyar fahad ta mika hannu tana wasa da gashin sajensa.

Tace cikin sanyin murya.

"Sultan fushi fa yake damu"

Kara rukota yayi jikinshi yace cikin sigar rarrashi.

"Karki damu dashi,yaje ya karata da ubanshi hydar,muma mu dage mu samu wani mu kyaleshi"ya karasa mgnr yana kashe mata ido.

Duka takai mushi a kirji,tace.

"Dan de bakasan zafin haihuwan bane yasa kake wannan mgnr,to nide faskiya banida lfy"

Dariya ya tuntsire da ita yace cikin dariyar.

"Allah baki lfy baby na hakan baze hanani nuna miki ni lfy ta lau ba"

Da sauri ta mike ta bar inda yake da gudu ta haura sama zuwa dakinta.

Mikewa yayi ya mara mata baya.

Tana ganinshi ta fara rokonshi cikin shagwaba tace.

"Wlh wanka zanyi don Allah ka kyaleni zanyi wanka ne"

Be saurareta ba ya sureta zuwa toilet din ya taimaka mata tai wankan shima yayi suka fito.

******************

Hydar yana barasu gida ya nufa,yayi wanka ya huta,yaci abinci,sannan ya nufi gurin me martaba yaga ko zuwa lokacin ya samu natsuwa.

Koda ya shiga dakin kwance yaganshi kan dardumar sallah alamun ya idar da sallah ne bacci ya kwasheshi agurin.

Hydar be tasheshiba ya samu guri can gefenshi ya zauna zaman jiran ya tashi.har zuwa lokacin sallar magrib.

Ganin be tashin bane yasa hydar matsawa kusa dashi yafara kokarin tashin shi ta hanyar kiranshi yana dan matsa masa kafa.

Ganin be motsa bane yasa hydar ya fara kiranshi da karfi yana girgizashi.

Shuru,agigice hydar ya dagoshi yana kiranshi ganin yadda idonshi ya juye ne yasa hydar fahimtar me nartaba fa rai yayi halinshi.

Wata gigitacciyar kara,ya saki gami da futa da gudu zuwa gurin fadawan me martaba.

Kiransu yayi kan suzo su duba mishi mahaifinshi.

Ana tsaka da wanban Fahad ya iso gidan dan duk dare a masallaci dada suke sallar magrib da isha.

Koda ya samu labarin abinda ke faruwa,agigice shima yayi shashin mahainasa wanda zuwa lokacin likitansa ya zo ya duba yaga meke damunshi.

Likitan na gama duk bincikenshi ya gano zuciyarshi ce ta buga,wanda hakanne yazama silar rasuwarsa.

Fahad da hydar kan gawar sukayi suna kuka suna kiranshi.

Dakyar aka rarrashesu.suka shiga yimishi addua.

Direba fahad ya tura yazo mishi da nana,dan batasan meke faruwa ba.

Kan kace me gaba daya kasar ta dauka sarki ya mutu.

Nana seda ta iso gidan tasamu lbr,kuka take kamar ranta ze fita anata rarrashinta.

A daren iyayen nana da sultan suka iso kano.

Sabida da safe zaa masa jana'iza.

Ranar kwanan bakinciki sukayi agidan kowa ka duba idonsa inbanda kuka ba abinda yake.

Gari na wayewa kofar fada ba masaka tsinke alumma sun taru domin yimasa sallah

Fahad da hydar ne suka shiryashi suka masa sutura.

Sannan aka fito dashi aka sallaceshi aka kaishi gidanshi na gaskiya.

Bayan an dawone jamaa suka fara tambayar ina hajiya babba.

Ba musu hydar ya bude kofar dakin da suka rufeta.dan yayi imani bakin cikinta ne ya kashe mahaifinsu.

Ayko da gudu ta fito cikin mutanen tana ta zage zage.gamida tonawa kanta asirin duk abinda tayi.

Kowa yashiga yimata tofin Allah tsine.itako se dariya take tana shewa.

Yar tace ta yi kokarin kamata amman ina tafi karfinta.

Tanaji tana gani hajiyar ta fice agidan da gudu cikin hauka.

Dan kowa be tausaya mata ba bare akamota.

Muje zuwa

Surbajo for life<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?
*DAN KARUWA*
<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?

*writen by zahra surbajo*

*page 22*

Haka suka ci gaba da zaman makoki cike da bakin ciki da takaicin rashin mahaifinsu.

Bayan sadakar Arbain din me martaba ne majalisar fada ta zauna domin nadin sabon sarki wanda kowa ya tsaida fahad kasancewarshi shine babba.

Ana gama tsaida magana daya aka sa ranar nadin sarkin.

Hydar sosai ya taya shi murna gamida fatan alkhairi agareshi.

Shide fahad jinshi kawai yakeyi yana amsawa.

Ranar nadin sarkin tazo dukansu sunci ado irin na sarauta.

Nan fa aka fara shirye shiryen nadin.

Fahad ne ya bukaci abashi abin mgn zeyi mgn,ba musu aka bashi.

Sannan yafara da addua kamin yace.

"Nayi matukar farincikin zabata da akayi dana zamo sarki awannan jiha tamu me albarka,sede inada wani uzuri dazan sanar da ku.nida Aliyu hydar duk dayane,yanada hankali da ilimi da zurfin tunani,Aliyu yayi muamala da talakawa yasan me sukeso yasan menene basa so sabanin ni da bansan hakanba,Aliyu in abu ya faru se yayi bincike kan yay hukunci sabanin ni dase nayi hukuncin sannan nake binciken,dan haka na janyewa Aliyu na yarda ba wata damuwa anada Aliyu amatsayin sarki,Allah ya tayashi ruko"yana kaiwa nan ya ajiye abin mgnr ya koma gurin zamanshi ya zauna ranshi fess dan shima so yake yayiwa kanin nasa irin sadaukarwar da yake masa.

Nam fa guri ya dauki kabbara,hydar ko gaba daya rudewa ma yayi,dan betaba zaton hawa kujerar sarki ba se gashi yayanshi ya yarje masa.

Haka aka kirashi aka nada masa rawani,gamida bashi sandar girma.

Nan akaita bushe bushen algaita.da kirari ga sabon sarki.

Nan aka shiga zuwa gaida sabon sarki,fahad ma mikewa yayi ya isa gabanshi yana shirin zubewa ya kwashi gaisuwa,se ganin hydar yayi shi ya zube agabanshi ya rike masa kafafu ya dukar da kai alamun girmamawa.

Fahad dagoshi yayi suka rungume juna.hawaye nabin fuskarsu.

Fatam alkhairi fahad yay masa sannan suka rabu kowa ya koma gurin zamanshi.

**************

*BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR*

Abubuwa da yawa sun faru aciki harda auren sarki hydar inda har matar tashi ta haifi ya tamace me sunan mahaifiyarsu amman suna kiranta da Sabrina,

Fahad ma da nana sun kara haifar yan biyu duka mata wanda suke saanni da sabrina,sunan su najwa,da jadwa.

Yayinda acikin shekaru nana itama ta rasa iyayenta duka biyu,se fayan Allah yay musu rahama.

Rayuwar duka gidajen biyu rayuwace me cike dajin dadi da so da kaunar juna

Tuni Sultan ya koma hannun hydar da zama,gata ba irin wanda be gani agurin uncle din nashi.

Wanda a halin yanzu yanacan kasar england ya kammala karatu afanni lafiya,amakarantar cambridge.inda kuma yasamu ayki acan.

Duba daya zakawa Sultan kasan shi me kyaune.

Matashine me matukar miskilanci,wanda in ze wuni beyi mgn ba hakan baya damunsa.

Sam bashida hayaniya,shiyasa ko aboki bedashi se guda daya,Safwan shine kawai abotarsu tai lasting dan ya karanci halayen sultan din shiyasa yaci maganin zama dashi.

Sultan dan kimanin shekaru talatin da haihuwa,ko kadan zina ba halinshi bace,dan aduniya ya tsaneta tsana me girma tunda iftilainta ya fadawa mahaifiyarshi.

Yana da kamala da tsoron Allah ga kwarjini bana wasa ba.

Muje zuwa

Surbajo for life.<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?
*DAN KARUWA*
<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?


*writen by zahra surbajo*


*page 23*



Fahad zaune shida hydar a lambun gidan fahad din suna tattaunawa,kai da ganin yadda suke mgnr kasan me muhimmanci ce.

Fahad ne ya gyara zama sannan yace.

"Yade kamata kayiwa danka magana ya fitar da matar daze aura,zamanshi haka beda maana kullum shekarunshi gaba suke yi"

Murmushi Hydar yayi sannan yace.

"Yaya insha Allahu zaa masa nafiso in tazo gida se muyi maganar dan a waya baze yiwuba"

"Hydar ay daga kai har shi din jirginku daya,kaima daya muka samu kai auren,nide kawai ka matsa masa yazo gida,"

Dariya hydar yayi sannan yace.

"An gama babban yaya,insha Allahu zanmasa magana kuma insha Allahu zaayi kamar yadda ka bukata"

Haka de sukai ta magana daga karshe fahad yay masa rakiya zuwa gurin motoci da fadawan da suka rakoshi.

Sallama sukayi ya tafi shi kuma yashige cikin gida.

************

Sultan zaune a dakinshi yana kallon wasan arsenal da bercalona kasancewarshi masoyi ga kungiyar arsenal shiyasa ya maida hankalinshi kan wasan.


Wayarshi ce tai kara.


Yana dubawa,yaga number uncle dinshi,da sauri ya kashe tv gaba daya sannan ya daga kiran.

Durkusawa yayi har kasa yana gaisheshi vikin nutsuwa zaka dauka agabanshi yake.

"My Boy,se yaushe zaka zo gida ne?"hydar yatambaya cike da kulawa.

Kara rusunawa sultan yayi sannan,yace.

"Daddy ban tsaida lokaciba,"

"Haba sultan yanzu fa shekarunka goma rabonka da kasar nan,sede mu muzo mu dubaka,ya kamata ka ajiye duk abinda kakeyi ka taho gida haka,muma munason ganinka,ga kannenka duk basu sanka ba ka daure kazo gida haka"

Ajiyar zuciya yayi sannan yace cikin nutsuwa.

"Daddy karshen watannan inanan zuwa insha Allahu,kuyi hkr"

Sosai hydar yaji dadin maganar sultan din,dan haka albarka yashiga sa masa sannan sukayi sallama kowa ya ajiye wayar.

Tv shi ya kunna yaci gaba da kallon wasan.



Hydar ko suna gama wayar fahad ya kira ya shaida mishi yadda sukayi,shima yaji dadi amman be nunawa hydar dinba sabida kara.



Tuni gidajen biyu suka rikice da murnar dawowarshi.

Kowa se shirin tarbarshi yake dan sunyi kewarshi.

Sabani Sabrina wacce hayaniyar da akeyi sabida ze dawo din ke bata mata rai,dan batason hayaniya ko kadan.


Suko su najwa ko ajinsu.
*************


Jirgin safe ze biyo dan haka da wuri ya isa airport,

Duk abinda yadace yayi yayi,ya gama jiran shiga jirgin kawai ya rage masa.


Ji yayi anzauna kusa dashi,da sauri yakai dubansa gurin.


.wata kyakkyawar budurwace sanye cikin shigar mutunci dake nuna ita musulmace kuma yar nigeria.

Dauke idonshi yayi akanta yaci gaba da danna wayarshi.

A hankali yaji tace masa cikin sanyayyan murya.

"Pls are you a nigerian?"


Dago kai yayi ya dubeta yayi murmushi sannan yace.


"Ofcourse,is something happen?"

Murmushi tayi sannan tace.

"Sunana hamra,daga kano state,nazo hutun makarantane nan gurin Aunty na,yau zan koma gida."

Murmushi yayi sannan yace.

"Sannu hamra,Sultan Fahad,my name from kano state, "

Murmushi tayi tashiga yimishi labarai ta kunsan halin gogan naku tun yana amsa mata har koma yaba banza ajiyarta dan ta soma sa mishi ciwon kai.



Ba abinda yayiwa hamra dadi gani kujerar su daya ita dashi,dan ganin farko da tai masa ta kamu da sonshi.

Dan haka zatai duk me yiwuwa taga ta samu numbershi.

Jirginsu na dagawa,sama,hamra ta fara surutunta=??,

"Sultan a kano a wacce unguwa kukene?"

Yatsina fuska yayi sannan yace.

"Nasarawa"

"Wow nice to meet you,nima acan nike"


Murmushi kawai yay mata.

Can kuma se tace.

"Ka bani numberka mana mudinga gaisawa"

Kallonta yayi ido cikin ido akaro na farko da yaji wani abu ya daki zuciyarshi,dakyar ya furta.

"Na jima rabona da nigeria banida numbar nigeria,amman ki bani naki inna sauka gida zan kiraki "

Yana gama yimata bayanin ya tsinci kanshi da mamakin kanshi da yayi maganar.

Ba musu hamra ta bashi numberta yayi saving.



Da laasar suka sauka a malam aminu kano airport.


Duk family din sun hallara suna jiran isowarshi,

Yana fitowa ya hangesu,da dan saurinsa ya isa garesu suka rungumeshi cike da murnar ganinsa.

Nana da sabrina ne kawai basu zo tarbarshi ba.


Hamra ko bace mata yayi yasa bata ganshi ba,ba haka tasoba amman tarasa abunyi haka tabi yan gidansu itama ta wuce gida.

Sultan ma haka suka dunguma zuwa gida kowa na cike dajin dadi.

Gidan uncle dinshi ya sauka.

Nan yay wanka ya sauya kaya sannan yayi zaman cin abinci,bayan ya gama


Suka taba hira da mutanen gidan kadan,sannan ya mike yacewa matar hydar wacce yake kiranta,mummy.

"Mummy zanje na duba umma,abanj key."

Da sauri tasa najwa ta dauko masa ta bashi.sannan suka fice shida su najwa din dan sui masa jagora.

Suna isa gidan yayi parking.masu gadi nata zubewa suna kwasar gaisuwa har ya shige cikin gidan.

Zaune nana take,kan kujera yayinda sabrina ke kwance akan kafarta sanye cikin kayan bacci riga mara hannu sa gajeren wando wanda ko cinyarta be gama rufewa ba.


Muje zuwa


Surbajo for life.<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?
*DAN KARUWA*
<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?

*writen by zahra surbajo*

*page 24*

Kallo sultan yabita dashi,na mamakin girmanta.

Kauda kai yayi ya nemi guri ya zauna,sannan ya duka yagaida umman tashi cike da girmamawa.

"Idonka kenan sultan,haba kai har se an fada maka baka kyauta ba,taya mutum ze zauna akasar da ba tashi ba sannan ba tare da iyaliba,kayiwa kanka fada fa sultan"

Murmushi yayi ya sosa keya,sannan yace.

"Umma zanyi ne kinsan komai lokacine ki tayani da addua"

Harara tabishi dashi alamun ya raina mata wayo shide be kara mgn ba.

Sabrina ko ido take binsu dashi bata da alamun sakkowa ta gaisheshi.

Wanda hakan sosai ya bata masa rai yaji yarinyar sam bata masa ba,ji yayi zuciyarshi na mishi zafi.

Mikewa yayi yayiwa umman sallama yafice daga gidan yanufi gidan sarki.

Bangarenshi ya wuce,yana shiga daki ya haye kan gadonshi se huci yake shi kadai.

Sosai yaji tsanar sabrina acikin ranshi.dan shi mutum ne me shegen son girma.

Bacci ne yayi awon gaba dashi be farkaba se gab da magrib,da sauri ya fada toilet yayi wanka ya daura alwala ya fito ya kintsa cikin kayanshi da suka dace da kirar jikinshi.

Masallaci yaje yasamu jam'i sannan suka wuce falon hydar tare dashi.

Hirar yaushe gamo suka shigayi,kamin hydar yafara mgn cikin kulawa.

"My boy,kullum kara girma kake,shekarunka karuwa suke ba raguwa ba,yakamata babba kamarka ka ajiye iyali,hankalinmu be kwanciya, zamanka a can batare da iyali ba"

Murmushi sultan yayi yakara rusunawa sannan yace.

"Insha Allahu daddy zan nemo matar auren,inyaso kan na tafi se a daura auren mutafi tare."

Sosai batun nashi ya faranta ran hydar yashiga sa mishi albarka.

***********

Wasa wasa yanzu sultan kimani watanni uku kenan da dawowarshi,kuma tun da ya dawo sannu bata taba shiga tsakaninshi da sabrina ba,

A wannan lokacin sun shaku sosai da hamra wacce ta rikide ta zama budurwarshi,

Sosai yake sonta dan yanason mace me wayewa.kuma hamra na dashi dede gwargwado.

Soyayya suke me tsabta,inda takai kowa na gidan su hamra yasan da sultan haka shima gidansu ansan da ita.

Abokanshi da suke nace masa jin ya dawo yasa suka bibiyeshi.

Safwan kawai yakeba fuska dan yasan halinshi kuma ya iya zama dashi.

Sultan ganin sun fuskanci juna da hamra ne yasa ya shaida mata ta fadi agudansy ze turo iyayenshi.

Bayan hamra ta sanar agidansu se aka bashi dama.

Ba bata lokaci ya tura iyayen nashi,

Bayan sun nemamasa aurenta,iyayenta suka shaidamusu cewa zasuyi bincike akanshi kamin atsaida ranar auren.

Kudin gaisuwa suka bada sannan suka tafi da zummar in an gama binciken zaa kirasu.

Hamra diyace ga mininstan tsaro,Alh habu dogon karfe,so gidansu babban gidane itama.

Mahaifin hamra baza mutane yayi su binciko masa waye sultan.

Cinkin sati biyu shaidun komai suka bayyana,inda daga karshe de suka bashi final result da cewa.

"Ranka ya dade DAN KARUWANE FA, bashi da wata tarbiyya duba da wacece mahaifiyarshi,kasani ma ko can gurin yawonta ta samoshi,batun gaskiya bedace da hamra ba".

Ran mahaifin hamra in yayi dubu ya baci kasancewarshi me saurin fushi.

Kwalawa hamra kira yayi ya zayyane mata komai gameda sultan.

Sosai taji ta tsaneshi,kuka ta fashe dashi na bata lokacin kulashi da tayi.

Janta mahaifinta yayi se gidan su sultan .

Ranar jummaa ne duka suna harabar gidan azaune.

Fahad ya dauko nana sun kawowa hydar ziyara gidanshi,

Su sabrina kuma suna gefe ita da su najwa suma suna tasu hirar,hydar kuma yana tare da iyayenshi ana tsara yadda bikinshi ze kasance.

Turo kofar da akayi da karfine yasa duka suka maida hankalinsu gurin.

Hamrace tafe ita da mahaifinta cikin fushi.

Da sauri sultan ya mike ya isa gurinsu,yana tambayarsu lafiya de ko.

Muryar mahaifin hamrane ya katseshi.

"Dalla can munafuki kaida iyayen naka Allah ya tona muku asiri. Kunzo zakumin angulu dakan zabo,ashe kai din Dan karuwane!!!!! Dan karuwa ko taya ze kasance me tarbiyya"

Runtse ido sultan yayi,da karfi jikinshi na rawa.

Nana zamewa tayi ta zauna jagwab,wasu zafafan hawaye nabin idonta.

Fahad ko mutuwar tsaye yayi ya kasa magana.

Hamrace ta amshi maganar da cewa.

"So kake in aureka nima asamu karuwar acikin yayana to aniyarka ta bika Allah ya tona ma asiri wlh nafi karfin zama sirikar Karuwa,mata ga DAN KARUWA!!!!never wlh"

Tasss taji an dauketa da mari mw shiga jiki wanda seda taga wuta sabida hasken marin.

Da sauri takai dubanta kan wanda ta maretan.

SABRINA ce rike da kugu tana huci.

Cikin fushi hamra tace.

"Ke yar gidan uban waye da zaki mareni?"

Dauketa tayi da wani marin sannan tace.

"Gimbiya Sabrina ce agabanki ba sako ba,ke har kin isa keda wannan me dattin hular ku shigo mana gida kuci mana mutunci,wlh kunyi kadan,daga ke har uban naki duk shegen daya fasa Allah ya tsinewa uwarshi albarka,"

Daga hannu baban hamra yayi ze tsinke sabrina da mari,da sauri ta rike hannu,tace cikin fushi.

"Hattade dattijo,nasan darajar furfura shiyasa ban kwasheka da mari ba atun farkon shigowarka,amman wlh ka kuskura ka tabani senasa karnukan gidannnan sun farauceka,marasa mutunci kawai ku fice mana agida."

Hamra gaba daya tsorom sabrina ne yakamata yasa batayi yunkurin ramawa ba.

Kowa binta yake da ido cike da mamakin masifar tata wacce ba wanda yasan ta iya.

Baban hamra ganin take taken sabrina gab take da kifeshi da marine yasa ya wurga musu kudin gaisuwarsu yaja hannun yarsa suka fice cike da alwashin se ya dauki mataki.

Muje zuwa

.surbajo for life.<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?
*DAN KARUWA*
<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?

*writen by zahra surbajo*

*page 25*

Kowa bin sabrina da ido yake,an rasa me magana acikinsu.

Da gudu ta juya zuwa gurin Nana ta fada jikinta tana kuka tana fadin.

"Umma kice karya sukeyi,su dena ce miki karuwa ke ba ita bace su dena umma in suna fadi wlh zan iya mutuwa"tasake rushewa da kuka.

Rungumeta Nana tayi cikin matsanancin kuka itama.

Fahad ne ya mike ya usa gurinsu a hankali ya zare sabrina daga jikin nana ya ka ma nanar suka wuce gurin motarsu,kai tsaye ya zauna mazaunin direba,yajasu suka bar gidan zuwa nasu.

Hydar kasa cewa komai yayi ya wuce cikin dakinshi.

Matarshi tabishi abaya domin kwantar masa da hankali.

Sabrina kuka take iya karfinta,dan sosai ranta ya baci.

Jiki a sanyaye sultan ya isa gurinta yace cikin taushin murya.

"Kiyi shuru kaddarace kuma tana kan kowa,"

Afusace ta dago tana dubansa tace.

"Kaddara a ina,kode mugun son zuciyarka,taya zaka kwaso karuwa amatsayin matar aurenka,in kana dadironka kayi iya waje mana,taya zaka sa azo har gida azagar mana iyaye.to wlh ni ba ruwana duk wata yar kutumar uban karuwa data.... "

Tasss taji an dauketa da mari.

Agigice take kallonshi ranshi abace yace yana nunata da yatsa.

"Zaki iya zagin komai na kyaleki amman bazan taba bari ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login