Showing 3001 words to 6000 words out of 8675 words
Chapter 2 - SHA'AWA DA JARABA COMPELET HAUSA NOVELZ.txt
a hakan ba, yai janyeta daga jikinsa, kana ya wuce toilet, tana kwance a lulluɓe da blanket, ya fito ƙugunsa ɗaure da pink towel, da wani siriri a hannunsa, sumar kansa da take sheƙi tayi yalaf, ya fara gogewa, cikin sauri tare shiryawa, tana kwance tana kallonsa, "zanyi miki transfer.."
Ya faɗa yana ɗaukar key car ɗinsa ya fice,
A gajiye ta miƙe ta shiga toilet ta tsarkake jikinta kana ta fito, doguwar rigar da tazo da ita a jikinta ta saka, ƙananun kayan ta ninkesu sosai sannan tasa a bag irin ta zuwa school, wacce ke ɗauke da littafai a ciki, ciro farin ribom ɗin da yake ɗaure da gashinta tayi, ta sake gyara gashin wanda ya saukar mata har gadon baya, kulle ɗakin tayi, kana ta sauko ƙasa hannunta riƙe da school bag da key wanda, wata wacce take tsaye a reception ɗin ta bawa, wacce dama sun riga sun saba tun farkon zuwanta da doctor Muzaffar,
Kai tsaye ta fice zuwa bakin titi ta tari mashin, kai tsaye gidan yayarta ta wuce,
Bayan mai mashin ya sauketa ta fara nocking a bakin get na gidan, mai gadi ya leƙo dan ganin mai nocking ɗin, sannan ya buɗe mata, gaishesa tayi cike da girmamawa saboda shi ɗin dattijo ne, ta ƙarisa ciki, Door bell ta danna, kana ta tsaya jira na buɗe mata, yayar tata ta buɗe ƙofar fuskarta ɗauke da murmishi, ga tace "yau ina kika tsaya ko baku tashi da wuri bane?"
Resh tace "anty Zubaida ai yau ba ƙaramin wahala nasha ba gurin karatu"
Anty Zubaida na riƙe da mararta tace "dan Allah tashi ki ɗora min abinci tun safe nake kwance babu lafiya, gashi Yazeed baya gari tun jiy"
Resh tayi mata sannu, tana cire hijab ɗin jikinta tace "baki je hospital bane?, wannan babyn yana wahalar dake, kafin ki haifeshi kin gama galabaita"
Anty Zubaida tayi murmishi kafin tace "Resh sai aka ce miki shikenen dan mutum ya samu ciki bazai warke ba kafin ya aihu?"
Resh ta shige ciki tana taɓe baki, da gyaran kitchen ta fara, kana ta gyara ko ina tsaf-tsaf sannan ta fara hidimar ɗora abinci, parlor ta dawo ta samu Anty Zubaida tayi barci, ga shi tana son tambayarta me take son a dafa, komawa kitchen ɗin tayi ta gyara kayan miya sannan tayi blanding ɗinsu kana ta kunna electric stove sannan tasa tukunya da mai ta soya albasa bayan sun soyu Harda su spices da su maggi ta zuba soyayyen kifi wanda ta gama cire masa ƙaya, kana ta rage wutar sosai, sannan ta juye couscous ɗin ta fara gaurayawa bayan ta gama ta zuba masa tafasasshen ruwa iya adadin yawan couscous ɗin ya rufe, ƙarar shigowar massage da taji a wayarta dake parlor a cikin bag yasa tai saurin zuwa parlon ta zuge zip na jakar ta ɗauki wayar sannan ta koma kitchen ta ɗauko warmer mai kyau ta juye abincin ta gyara ko ina kana ta dawo parlor duba massage,
Alert ta gani na 50k, tayi murmishi tana mai maita sunansa a cikin zuciyarta "Doctor Muzaffar" matashi mai jini a jiki mai ji da kansa.
lokacin da ya shigo da motarsa cikin gidansu, yai parking kana ya fito ya fara taku cikin ƙasaita ya isa ciki, Diyana da Fateema ne a zaune, ko wacce tasha kwalliya da hand bag a saman cinyarta, sallama yayi kana ya nemi guri ya zauna, "Yah Muzaffar Barka da shigowa.."
Suka faɗa cikin haɗa baki, "Barka.." ya amsa yana ciro wayarsa da tai ƙarar shigowar saƙo, a tare suka tashi dan basa ƙaunar zama a inda yake zaune, bedroom ɗinsu suka wuce Fateema ta murza key, tare da jingina da jikin ƙofar murya ƙasa-ƙasa tace "shikenen mun shiga uku, wannan ba zai barmu mu fita ba"
Diyana tace "kina nufin bazamuje birthday din ba kenan.?"
"Eh mana ko kin manta waye Yah Muzaffar?"
Diyana ta sauke ajiyar zuciya kafin tace "Fateemah ki samo mana mafita dan ko gurin momy mukaje bazata taɓa bamu goyon baya ba tunda ya shigo, dama bai shigo bane"
Suna tsaye suna shawara sukaji anyi nocking,
Kowacce sai da ƴan hajinta suka kaɗa, Fateemah dake tsaye a jikin ƙofa ta matsa da sauri, Diyana tace "kamar da wannan nocking ɗin ba irin na Momy bane"
Fateemah tace "wa kike tunani?"
Diyana tace "na tabbatar da Yah Jawad ya tafi gurin aiki, kai wannan bugun ƙofar na yah Muzaffar me saboda wlhi komai nasa daban yake"
Ko wacce tayi tsuru-tsuru da idanu, suna gudun aikata laifi saboda shi baya raina duk ƙanƙantar laifi sai ya hukunta mutum dashi,
Fateemah ta murza key ƙofar ta buɗe, tsaye yake a bakin ƙofar idanunsa na kan wayarsa da yake daddanawa, sarai yaji buɗe ƙofar tasu, bai kalli gurin ba kuma bai ce musu komai ba, bakin Fateemah na rawa tace "mun..mun..buɗe...gamu.."
Har yanzu bai kulata ba, dan tayi tunanin bai jita bane, zata sake magana Diyana ta taɓata tayi shiru, ɗago fararen idanunsa yayi kana yace "kuje kitchen ku yimin farfesun naman rago kuma bana son ƙazanta, kafin ku taɓa kayan miya ko wacce ta wanke hannu, idan kun gama a kirani" ya faɗa yana barin gurin.
Wani irin takaicin baƙinciki suka ji dukkansu, fuskokinsu babu walwala suka amsa da cewa "toh" dole kowacce ta cire kayan ta, suka saka riga da wando t-shirt da jeans da hula a kansu, kitchen suka wuce, shi kansa naman yayi ƙanƙara a cikin frizer, suka fito dashi suka wanke, Diyana ta ɗauko turmi ta daka ɗanyar citta da su tattasai, ta ɗauko tumaturin leda, nan fa suka shiga aiki gadan-gadan wai duk dan suyi sauri su gama su tafi tunda dai ya fice, Fateemah tace "mun manta mu tambayesa manja ko mangyaɗa?"
Diyana tace "Mu saka manja kawai, saboda Momy yawanci na manja takeyi"
Fateemah tace "hmm Wllhi ina tsoron hukuncin yah Muzaffar inda kasan yayi rayuwar cikin sojoji, amma dai bari inje parlo in ɗauki waya in kirashi in tambayeshi"
Fita tayi zuwa parlor ta ɗauki wayar tafi da gidanka ta kirashi, baya wasa da ganin kiran gidansu, dan haka ya ɗaga da sauri, Fateemah tace "yah Muzaffar manja za'a saka ko mangyaɗa?"
"Mangyaɗa"
Ya faɗa yana katse kiran,
Fateemah ta dawo ta gayawa Diyana, a tare suka sauke ajiyar zuciya suna cewa Allah ya taimake su, sun mugun gajiya kafin su kammala, Diyana tace "yau kashinmu ya bushe a gurin classmate ɗinmu"
Fateemah tace "ba wata matsala ai mun kammala kawai ki juye masa sai a kirashi a waya, ki fito mana da kayan da zamu saka da bags sai mu wuce, shigowa yayi ya samu Siyan ta ajiye Warmer ɗin a saman table na parlor, ya kai hannu ya buɗe "good" ya faɗa yana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, Please ku dafa jollof ɗin shinkafa yanzu abokaina sun kusa ƙarasowa, sannan ayi musu juice, ayi abincin har dare tunda yamma tayi, Hajiya ma ta kusa dawowa,
Suka wuce kitchen, Fateemah ta fashe da kuka marar sauti, haka ma Diyana kuka ta farayi...!
Ayi haƙuri da typing errors
Mom Islam 08141799224
[12/5, 4:11 PM] Mom Islam: 💋💋💋
*SHA'AWA DA JARABA*
(Love and Romantic story)
💋💋💋
Mom Islam
Page 9-10
Duk saurin su gurin ganin sun kammala girkin da wuri hakan bai yiwu ba, lokacin da suka kammala ana kiran sallahar magriba harda juice ɗin, kowacce idanunta yayi jajir tsabar kuka, suka fito da abincin a warmers biyu manya, Dinning area suka kai suka ajiye kana suka wuce ɗakinsu, kowacce zuciyarta na ƙuna, alwalah sukayi kana suka kabbara sallah a tare, bayan sun idar, Diyana tace "Sis Teema wlhi Yah Muzaffar azzalumi ne baya ƙaunar yaga mutum ya huta.."
Fateemah tace "nifa hatta muryarsa naji sai zufa ya tsatsafo min saboda tsananin tsoronsa da nake ji, suna cikin gulamrsa ya kirasu cikin ɗaga murya yana zaune a parlor shi da abokansa biyu, dawowarshi kenan daga ɗauko Momy daga gidan biki, suka kirashi wai sun iso ya fita ya tarosu,
Kowacce tana sanye da hijabi suka fito, suka durƙusa a gabansa, "kun kammala komai?"
"Eh" suka ce,
Yace "ku ɗauko ku kaimin ɗakina"
Cikin bin umarninsa suka wuce kitchen suka ɗauko kyakkyawar warmer ɗin sai sheƙi take da spoon da Plate da Glass jug da kofunansa, kasancewar lemun abarba da kankana sukayi, kai tsaye ɗakinsa suka kai kana suka fito suka ce masa sun kai, yace "good" tare da miƙewa, suma abokan nasu suka miƙe kowanne idanunsa na kan Fateemah da Diyana,
Bayan shigarsu ɗakin ya haye lallausan Royal bed ɗinsa tare da ɗaukar system ɗinsa, "ku ci abinci ku ƙoshi.."
Doctor Muzaffar ya faɗa yana saka gilashi a idanunsa,
"Ikon Allah Muzaffar gaskiya kazo ka zuba mana.."
Cikin isa yace "duk shegen da bazai ci ba ya barshi inhar nine zan zuba muku abinci"
Dole dai ɗaya ya ɗauki ragamar zuba abincin suka fara ci suna hira, shiko hankalinsa sam baya gurinsu,
Ɗayan mai suna Abubakar yace "Muzaffar Please ƴan matan da na gani ƙannenka ne..?"
"Yea mai ya faru?"
Muzaffar ya amsa masa a taƙaice,
"Ina ciki ne idan babu wanda ya rigani.."
Doctor Muzaffar yace "aiko ba zaka samu ba saboda dukkansu ba yanzu zasuyi aure ba karatu sukeyi."
Khalil yayi dariya, kafin yace "idan ban da abinka Muzaffar ai cewa kana son budurwa ba shine zai hana ta yin karatu ba"
"Okay abinda ya kawoku kenan?, to ku tafi mun gode nace basa tsayuwa da samari ko ana dole?"
Abubakar dai bai sake magana ba, sai Khalil da yace "Allah ya huci zuciyarka"
Ba suci abincin da yawa ba, suka fara shirin tafiya, Muzaffar ya sauko daga bed, ya rakasu har compound inda motarsu take, ido biyu sukayi da Diyana da Fateemah sun fito daga garden kowacce hannunta riƙe da abin fifita,
Abubakar da Khalil suka zuba musu idanu, idanun Muzaffar ne ya sauka a kansu ya kalli su Abubakar sannan ya kalli Fateemah da Diyana da suke tafiya a hankali basu ma san Muzaffar ɗin na kallonsu ba, cikin daka tsawa yace "daga ina kuke" ba ƙaramin gigicewa sukayi ba, suka ƙara da gudu basu bashi amsa ba, Abubakar da Khalil suka shiga mota sukayi masa sallama, dan ko bari su gaisa da momy da ta shiga Sallah beyi ba, ya ɗaga musu hannu motarsu tabar gidan,
Cikin ɗaga murya yake ƙwala musu kira tun daga ƙofar shigowa parlor, basu fito ba suna bedroom ɗin Momy sunata haɗata da Allah akan ta bawa yah Muzaffar haƙuri bazasu sake fita ba,
Momy tace "kunsan halinsa mai yasa ba zaku dinga kiyaye duk abinda zai zame muku matsala a tsakaninku dashi ba"
Suka ce "bazasu sake ba"
Momy ta fito parlor ta sameshi yana zaune a saman Sofa mai zaman mutum ɗaya, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya fuskarnan tasa babu wani annuri, Momy ta zauna kafin tace "Doctor Dan Allah ka rage zafin zuciya yara nan ba wani guri suka je ba, garden suka je dan Allah kayi haƙuri irin haka sai su dinga tsoronka.."
Gyaɗa kai kawai yayi ba tare da ya cewa momy komai ba, ya tashi ya fita, ta sani sarai haushi yaji, kuma gaskiya ta faɗa masa, cikin ɗaga murya Momy tace "Diyana Fateemah kuna ina?"
Suka fito da sauri suna leƙo ko Yah Muzaffar ɗin ya fita, ganin baya nan yasa su fitowa da gudu suka zo parlon suka zauna a saman Sofa suna kallon Momy kowacce tayi tsuru-tsuru da idanu, kuma ankare suke dan suna ganinsa rugawa zasuyi.
Momy tace "wlhi ku kuka da kanku ransa ya ɓaci, sakamakon faɗan nayi masa"
Shiru sukayi basu ce komai ba, Momy tace "ashe kunyi girki"
Nan suke bata labarin birthday ɗin da aikinsa ya hana su zuwa dole sai haƙura sukayi,
Momy tayi murmishi kana tace "sai kunyi haƙuri, ya kamata tunda kuka san abinda baya so sai ku kiyaye"
Momy ta tashi zuwa yin sallar isha'i, suma suka wuce bedroom ɗinsu, sun rigata fitowa dan haka sukai saurin zuwa kitchen suka kwaso plate da spoon da sauran abubuwan buƙata gudun kar ya fake dasu yayi musu hukuncin da zai huce a kansu,
Momy ce ta fito daga bedroom ta nufi dinning area, ta ƙwalawa su Fateemah kira, amsawa sukayi kana suka ɗan leƙo suga ko Yah Muzaffar ya dawo, ganinsa sukayi yana zaune a saman kujerar Dinning table ɗin yana daddana waya, suka koma saɗaf-saɗaf suka kullo ƙofa,
Tunda momy taga basu zo ba, ta ƙyalesu saboda tasan kwanan zancen.
Jawad yace "momy lafiya kuwa me yaranaki sukayi?"
Momy tayi murmishi kafin tace "hmm basa jin magana ne rabu dasu kawai"
Jawad na gama cin abinci ya fice shiko yah Muzaffar har yanzu ko loma ɗaya bai kai bakinsa ba, sannan gefe kuma farfesun da yasa su Diyana sukayi masa ne, koda Momy ta gama cin abincin, ta dubesa kafin tace "Doctor abincin zai yi sanyi ko a rufe maka ne?"
"No momy ina wani abu ne yanzu zan ci"
Momy taja kujera baya tace "ni zan shiga ciki gobe dai Dadynku yana hanya"
Yah Muzaffar yace "Masha Allah Ubangiji ya dawo dashi lafiya"
Momy tace "Amin ya rabbi" ta shige ciki.
Yana zaune a gurin bai ci abincin ba har ƙarfe 9:30pm idanunsa na kallon screen ɗin waya, sai yanzu ya ɗauki spoon ya kawar da abincin sannan ya ɗauko warmer na farfesun kana ya zuba, ya fara ci a hankali,
Acan ɗakinsu Fateemah yunwa ta addabesu, dama tsabar zumuɗin zuwa birthday yasa basu ci abincin rana ba, yanzu kam ko wacce ta fara raina kanta, gashi sun leƙo parlor sun hangoshi yana nan a zaune yanzu nema ya fara cin abincin, Diyana tace "Abu mafi sauƙi ko tea suje kitchen su haɗa"
Fateemah tace "kina ganin bazai ganmu ba, sannan tea dame zamu haɗa?"
Suka yanke shawarar zuwa kitchen su dafa indomie ko hungry man guda ɗaya ce, sun fito keman sukayi ido biyu da Yah Muzaffar yana shirin fita ya dawo da baya..!
Mom Islam
[12/5, 4:11 PM] Mom Islam: 💋💋💋 SHA'AWA DA JARABA (Love and Romantic story) 💋💋💋 Mom Islam Page 11-12 Kafin ya furta wata kalma suka ruga da gudu bedroom ɗinsu suka yiwa ƙofar key, ƙwafa yayi ya fice. Sai dare yayi sosai, sannan suka leƙo suka tabbatar da baya nan, kana suka shige kitchen suka yi girkinsu, bai ƙarasa nuna ba suka sauke suka wuce bedroom, Kowacce na mayar da numfashi, san sun san idan har ya damƙesu tabbas sai sun sha baƙar wahala. Washe gari, tun bayan da sukayi sallahar Asbha suka fito aka fara gyare-gyaren gida, kasancewar dady zasu dawo yau, sun gyara ko ina tsaf sai ƙamshi ke tashi, daga nan suka wuce part ɗin Hajiya Mariya, suna kiranta da Umma, da sallama suka shiga, suka samu tana zaune ita da autanta Abdul yana wasa a saman carpet, zama sukayi kana suka ce "Umma munzo gyara miki gidane, tunda yau Abba yana hanya" Cikin fara'a da sakin fuska tace "aiko ina maraba daku wlhi, saboda dama aiyuka sun yimin yawa" Da bedroom ɗinta suka fara, kana suka wuce kitchen ɗinta suka gyara tsaf sannan suka wuce dinning table suka goge, kana suka saka turaren wuta mai ƙamshi, sukayi mata sallama saboda su ɗin ba ma'abota son yin girki bane bare suce ta kawo suyi mata, Part ɗinsu suka wuce, basu tsaya a parlor ba suka wuce bedroom, Diyana ce ta fara shiga wanka, bayan ta fito Fateemah ta shiga, Fateemah na fitowa ta zauna a gefen bed tana goge gashin kanta tace "Diyana wane irin kaya ya kamata mu saka?" Diyana tace "abayar da Abba ya siya ma lokacin da sukaje Egypt da Daddy" Diyana ta Ciro musu abayar, kala ɗaya ce komai iri ɗaya Black color ce sannan tasha adon duwatsu golden da ja, mayafan abayar sunada ɗan girma, bayan sun gama shafa mai sukai makeup wanda ya sake fito da ainihin kyawunsu, gasu dama farare tass, Kowacce tasa tata, sukai rolling Vail ɗin sosai sukai kyau, ga wani uban sarƙa da ɗankune da suka saka da zobe da warwaro, Masha Allah, parlor suka fito lokacin 9:am Momy ta gama breakfast takai dinning ta ajiye, suma suka wuce dinning ɗin suna yi mata sannu da aiki, suna zaune ya Muzaffar ya shigo, yana sanye da dakakkiyar farar shadda sai sheƙi take, ya ɗora hula a saman kansa, hular ta sake fito da ainihin kyawunsa, hannunsa sanye yake da tsadajjen agogo ga wasu kyawawan zobuna a yatsuntsa na tsakiya, Masha Allah yah Muzaffar yayi kyau sosai, "Momy Barka da safiya" Ya faɗa yana wucewa dinning table ya zauna, Momy tace "Barka ya aiki" "Lpy" ya amsa a taƙaice. Diyana ta kalli Fateemah, suka gwalo idanu yanzu dai babu halin guduwa dan haka ko wacce ta saita tunaninta, ɗaya bayan ɗaya suka gaishe sa, bai amsa ba sai can momy ta zuba masa faten dankalin turawa da yaji hanta da kifi, bayan ya zare spoon a bakinsa yace "lafiya kun gama gudun?" Suka wani zazzaro idanu, cikin haɗa baki sukace "dan Allah kayi haƙuri bazamu sake ba" Bashi da isasshen lokaci, dan haka bai wani bi ta kansu ba, sakamakon kiran gaggawa da akai masa, a gurguje yai breakfast ɗin ya miƙe yana cewa "momy sai ya dawo" Fatan nasara gami da Ubangiji ya tsareshi tayi masa ya fice, Diyana ta gyara zama tana cewa "kaii Masha Allah gidan har yayi ni'ima" Momy ta ware idanu tana kallonsu, kafin tace "bazaku tabbatar da gata ake yi muku ba sai zuwa nan gaba" Fateemah ta turo baki kafin tace "wlhi ina tausayawa wacce zata auri yah Muzaffar shifa kowa bai ƙyale ba har abokansa inda kasan wani sarki ko yarima" Momy tace "ya isa haka, da ace yana nan ƙwaƙwaran tari babu mai yi, da yake kunga baya nan shine bari kuyi gulamrsa ko?" Sukai shiru suna dariya, Diyana ta kwaɓe fuska kana tace "Momy dan Allah ki bari muje gidan Granny wlhi mun kwana biyu bamu jeba, bazamu daɗe ba muna gaisheta zamu dawo saboda muga dawowarsu Abba da dady" Momy tace "Allah ya kiyaye hanya, idan ma kun daɗe wlhi babu ruwana, dama cewa take wai nice nake hanaku zuwa gurinta, amma ku gama cin abincin" Godiya sukayi mata kana suka fice kowacce ta ɗauki hand bag ɗinta, suka dawo parlo, momyn bata parlor suka wuce bedroom ɗinta, da sallama suka shiga, momy ta kallesu gami da yin murmishi tace "ƴan matana kunyi kyau sosai" Fateemah tace "momy bamu da kuɗi..."