Showing 39001 words to 42000 words out of 76019 words
ashe kinzo garin gidan Lalai kika sauka ne? Islaha tace ae,yace Ja'ira gari duk danginki amma mu baza ki dinga sauka a wajen mu ba,mufa yan uwanki ne na kusa ba na nesa ba,Islaha tace ai na dawo nan da zama gaba daya ba Aunty ce ta aiko ni ba.
Gali yace toooo....fada kuka yi? Islaha tace itace tace ta gaji dani,Gali yace kece kika mata rashin kunya Islaha,laifinki ne,ba ruwan Auntynku mutuniyar arziki ce,ku yaran yanzu baku iya samun waje ba,yar banza kina zare ido kamar na uwarki, Gwara ma da kika sauka gidan Lalai din ni nan baza mu shirya ba,kuma ki fidda miji kinji na fada miki.
Islaha tace a bani kuli inji Lalai,Matar Gali ta karbi kudin a wulakance ta kawo kulin ta bata tace ki gaida Lalai,Islaha ta juya tayi tafiyarta,a ranta tace nina jawowa kaina da ban lallaba Aunty ba da tuni ina Lagos abina,ashe Aunty dai duk da haka tayi kokari ta iya rike ni,inci insha duk da itama irin lalai ce sai naci aiki ake bani ga zagi ga gori amma da dama aikin nasu ba irin na kauye ba,idan nayi sati ina wannan aikin sunan na tashi a aiki na zama tsohuwar karfi da yaji bazan iya ba idan na gaji guduwa zanyi wlh.
A haka ta dawo gidan Itace ta daka kulin Lalai ta kwashe rogo shi suka ci suka koshi sannan ma ta samu tayi sallah.
Maheera tana can suna jinyar Mama kullum su Sohail sai sunje asibitin dubiya har Mama ta samu sauki aka sallame su,amma Zayna da su Adnan an fada musu ko ya me jiki basu ce ba,Ibrahim kuwa ya tafi kano gida wurin Daddy har yanzu bai dawo ba tunda suka tafi tare da Amal bai ma san Islaha bata gidan ba sai yau da ya dawo da yamma,ya gaji ya tambayi Maheera tace ai ta tafi garinsu,yace ina ne? Tace Taraba kauye,wanne kauyen? Tace ban sani ba,yace baki da hankali duk zaman da kuke yi baki tambayi address dinsu ba ya ja tsaki ya fara gwada kiran Islaha number bata shiga.
Bai gaji ba yace amma indai ta taba kunna layin a garin da take ai masu tracking number zasu gano zanje na bincika har kauyen da take zanje.
Sohail dai yana ta zuwa aikinsa gwanin sha'awa Alhaji Saminu ana ta samun ci gaba a kamfani mugun kaunar Sohail yake yi sun saba sosai,bangaren da Sohail yake basai me karatun boko me zurfi ba,sannan akwai wani a kusa ko da haukar zata motsa.
Gidan an zuba furniture da komai na bukata flat house ne me kyau,dauke yake da 3 bedrooms sai parlo,ga katon kitchen da Dining area daban,gaba daya estate din irin ginin kala daya ne komai kai daya kowa da wajen parking da komai, ko ina yaji fulawoyi kamar a turai,basu bar gidan su Adnan ba amma kullum sai sunje sabon gidan kuma watarana su kwana acan watarana su yini su dawo gidan su Adnan su kwana haka suke sintiri.
Motar ma kusan Sahil yafi Sohail hawa,Kayan abinci da duk wani nauyi Sohail ya daukewa Maheera na gidansu bata musu komai yanzu,gashi bai taba zuwa gidan ba,sai daga baya tunda yasan gidan ya dame su da zuwa, Mama ce ta kira Maheera a waya,bayan sun gaisa tace Maheera nifa yaron nan da yake ta mana hidima ya kamata ace idan soyayya kuke kin fitar da shi tunda yana da aikin yi,kuma yana da hankali ni na yaba da shi gaskiya,indai kin san soyayya kuke yi banga amfanin zaman haka ba,Maheera tace to ni dai mutunci muke yi da shi Mama,ban tabbatar da so na yake ba.
Mama tace shike nan tunda haka kika ce amma ni bazan so ace yana kashe mana kudi a haka ba gaskiya kawai kisan yanda zaki ko ki dakatar da shi ko ki tsaida shi a mijin aure kawai,Maheera tace to,Mama tana kashe waya sai ga Sohail yayi parking motarsa sanye yake cikin sky shadda ya zuba kyau,gidan ya shiga kai tsaye,Mama ta amsa sallamarsa tace Sohail kaine kazo? Sohail ya sosa gashinsa daga bakin kofa yaki shiga kuma yana daga tsaye ya leko da kansa yace Mama Ina yini? Baza ka shigo ba kuma yau? Ai ka zama dan gida,Sohail yace kunyarki nake ji kunyar surukai nake yi,Ammar yayi dariya kamar me,Yace dan Allah ka shigo? Sohail yace wallahi Allah bazan shugo ba yau kullum sai nazo na shigo, nazo ina raina sirikata,Mama dariya ta kamata,tace yau naji shashan yaro kai kuwa kalau kake?
Sohail yace ki fadawa Maheera Mama ta dawo gida nayi nayi taki ta dawo ai ba mutunci bane ta zauna cikinmu,gwara zayna ita tana da miji,Amma mu maza mu hudu ne a gidan ita budurwa ta hakura da aikin nan zan mata komai ni kadai kudina ya isa,amma taki sai Iyayi take min wani ita ai kaza kaza ya gwada yanda Maheera take magana,Mama tana daga palo yana daga bakin gate a haka suke zancen,Mama tace to ka turo iyayenka indai sonta kake suje dangin ubanta a nema maka aurenta na gaji da wannan soyayyar in ka tabbatar sonta kake kayi magana,Sohail yace zan dai tabbatar, zan tafi,yau Mama bazan baki kudi ba Ammar zan bawa,Mama tace to ai abin naka yayi yawa ni kyautar ma taka ta ishe ni,Sohail yaji dadi ya kira Ammar ya bashi kudi ya juya ya tafi yana murna yace yawwa dama nace Mama sai ta shiga uku da kudi gashi tace kyautar har ta isheta,sai nan gaba ma, ya shiga motarsa ya tafi.
Shi da Sahil kaya iri daya yake musu komai iri daya,kasancewar ma basu saba rike kudi ba sai suyi ta shawarar me zasu yi da kudin.
Washe gari Sohail ya kwanta ya bawa Sahil Amt dinsa da key din mota yace kaje ka kai Maheera shopping duk abinda take so ta siya,Sahil yace ka isa ka aikeni wato kayi kudi ni zaka aika ko? Kaje ka dauke ta ka kaita ni karka dameni tunanin Islaha nake yi na kasa dainawa,ban san a halin da take ciki ba,nayi kuskure,Sohail yace bani naje na kaita marar mutunci akan nace zan huta ka kaita duk kudin ba mu dai nake nemowa ba,Sahil yace jeka dai bazan je ba Islaha ta tafi ita yarinyar nan Allah bai yita da yar karamar sanwa ba,Duwunta kadai tallaja guda ne inji larabawa suka ce Tallaja,aba ba kadan ba yanzu ta kama hanya ta tafi duk wanda ya ganta ya kenan,Sohail yace Allah ya kiyaye kar tayi aure ma,Wanda ya sameta kuwa zai sha kallo,Sahil ransa ya baci yace bani key din naje na kai Maheera din ina dan dubawa gari ko zan dace na ganta.
Ba musu ya bashi key din ya fita.
Ibrahim kuwa tracking aka dinga masa yana biyan kudi sai da aka gano inda take har gidan da take,ya cika da farin ciki washe gari a .mota ya tafi ma da kansa sabo da shiga kauyen,ya dinga sharara tafiya yana bin location har garin da Islaha take.
400 ne 1&2 gaba daya
0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gtbank
Yan Niger
+22790795939
AsmaBaffa
08061929616
[7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸
31-35
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM
Page naki ne
Bestynbeelat
Ibrahim yana tafiya a motarsa yace chaiiii wannan kauye haka wanne iri ne,dama har yanzu da irin wannan kauyukan a kasar nan,wannan kauye kaddara ce ta kawo ni ace kamar ni Ibrahim ina son yar wannan garin zuciyata baki kyauta min ba, 'yar wannan garin kamar ni za ace ina son yar nan kauyen Allah ya kiyaye ba mayu bane ma duk tabi ta lashe mana kurwa sai dai aga muna ramewa a rasa dalili.
Amsa ya bawa kansa yace ko ma mayyar ce haka zan aura duk su Sahil ta lashe min su.
Wasu yara suna ta faman wasa da kasa Ibrahim yana dan tsayawa kusa da yaran da niyyar tambayar su suka watse gaba daya da gudu suna cewa barayi barayi ne...sabo da sunga mota, a kauyen ana musu huduba in sunga mota su gudu barayi ne,Ibrahim ya dinga mamaki yana daga cikin mota.
Abdulrazaqu ne ya dawo daga gona da ganyen zogale da yawan gaske zai kai gida,Ibrahim ya fito daga mota tare da yi masa sallama,Hannu Ibrahim ya mika masa,Abdulrazaqu yaki bayarwa yace kawai na baka hannu mu bace tare mu gaisa daga baya baya.
Ibrahim yayi murmushi shaddarsa tana sheki tana daukan ido arsh ga jiki ya ji hutu dole Abdulrazaqu su firgita,Ibrahim yace dan Allah gidan su Islaha nake nema, Abdulrazaqu yace yayanta ne ni ma da kake gani na,Amma kai na ganka baki bakwa kama,gaskiya da kamarka tayi sai dai a auri Islaha a garin nan.
Abdulrazaqu yaji haushi yace amma kai baka da ilimi sam kazo garinmu ka tare ni kana min tambaya sai ka dinga chaba min magana ko ance maka so shi a kyau yake? Duk ga ba munana nan ba sunfi auruwa sunfi samun mazaje na gari kuma kyawawan maza suke aura,sai kayi mamaki kace me ya gani a jikinta shi gashi kyakyawa,kuma kyakyawa mace kaga tana ta fadawa hannun mazaje munana,kaga mace hadaddiya mijinta ficika baza a siye shi ba,shi so da aure ai ba ruwansa da kyau malam ka gyara kalamanka,daka ganni bakin ba Allah ne yayi ni ba,a gidanku aka kirkireni? Ko kai farin ne gaka nan wankan tarwada kai a wankan tarwadar ma da alama kanti ka shiga ka dawo haka dama ai munji labari yan birni mayuka suke shafawa har mazan,mu kuwa mun tsaya yanda Allah yayi mu,ka ganni nan ko vaseline sai na shekara ban shafa ba,watarana ma mangyada nake shafawa da sanyi amma gani dakaukau dani aikin da nake baka isa kayi shi ba.
Ibrahim yayi dariya yace shi yasa ai gaka nan kamar an tonoka daga rami abokina maida wukar ka kira min Islaha idan tana nan,idan na sameta na maka alkawarin jari me tsoka ka fara kasuwanci zan maka gida me kyau a kauyen nan da babu kamarsa.
Abdulrazaqu yana jin haka yace da ina son Islaha nima amma na bar maka ita zan tsaya tsayin daka ko da tsiya sai ka aure ta ka kaddara ka sameta an gama.
Ibrahim yaji dadi yace na gode jeka zan bika a baya da mota,Ibrahim maimakon yace Abdulrazaqu ya shiga mota su tafi baya so ya shigar masa mota kar kamshin ta ya canja ya bata masa mota,a haka suka tafi shi yana daga cikin mota Abdulrazaqu yana tafiya a kafa har kofar gidan Lalai.
Ibrahim yana parking a gindin bishiya ya fito yace ai a nan gidan Islaha take? Abdulrazaqu yace ae a nan take,yace cab,Shigo ciki gidan tsohuwa ce ba wani abu ta riga ta tashi a aiki, shigo ko a wanne hali ka kalleta ba komai,Ibrahim yayi murmushi suka shiga kai tsaye gidan,Lalai tana jikin katangar kara tana leken mota a kofar gidanta riga daban zani daban.
Islaha tana zaune a gindin murhu tana ta faman iza wutar tuwo ta hada zufa idonta yayi ja sabo da hayaki.
Mamaki ya kamata ganin Ibrahim a tsakar gidan su yazo, Abdulrazaqu yace Islaha kinyi bako daga birni ai kin sanshi ko? Lalai tace sannu da zuwa maraba, ta fada daki ta dakko tabarma sabuwa ta shimfida masa a kasan bishiyar mangoro dake gidan,Ibrahim ya cire takalminsa me kyau ya zauna,tare da gaishe da Lalai,Islaha haushinsa taji da yazo amma bata nuna masa ba tunda gidansu yazo kuma dan ita yazo,mikewa tayi sanye cikin riga fitted gown ta atamfa green,komai ya fito chass,Ibrahim ya kare mata kallo irin na wayayyun yan birni kamar ba kallonta yake ba,karasowa tayi tace sannu da zuwa ina yini,kazo lafiya,ya hanya? Ta furta a jere.
ya amsa lfy Alhmdllh,shine kika taho ba sanarwa,murmushi tayi,yace ba sallama ba komai ko dan zaman tare ai kya yi mana sallama,Islaha tace ai wanda naje dominsa yasan na taho.
Kishi ne ya cika zuciyar Ibrahim yace ai shi bai damu dake ba,da ya damu dake ai da yazo,ko ya zo ne? Twins basa soyayya ba masu lafiya bane baza su iya inganta rayuwar kansu bama bare su inganta ta wani,gagararrun Aljanu ne da su, bakaken aljanu kuma masu gulma ma su suka hau kansu,da cutar aka haife su,kinga wanda aka haifa da cuta ai baya warkewa,tsoro ma muke ji kar nan gaba su fara duka ko su fara tsince tsince a bola.
Islaha tace Allah baya sa ba inshaallah zasu warke baza su taba zama hakan ba,kaima idan kun san farkon ku ai baku san karshen ku ba,Ibrahim yace Allah ne ya dora musu ba ni ba,mu bar wannan maganar muyi abinda ya kawo ni, Lalai ce ta fito da ruwa da abinci ta kawo har da hado fura ta kawo masa, Islaha tana kallon ikon Allah yanda Abdulrazaqu da Lalai suke wani nan nan da Ibrahim kamar zasu cinye shi.
Lalai ce ta kalli Islaha ta gasa mata harara tace ki zauna mana kuyi hira wajenki yazo kin wani tsaya masa kerere a ka,Islaha ta zauna tana jin haushi a ranta,Ibrahim ko ruwan su bai sha ba,bare yaci wani abu nasu ma.
Islaha ya kalla yace kina shan wahala a nan kizo mu koma gida dan Allah wannan garin bai dace da irinki ba,ke ba kalarsu bace,idan ma baza ki koma gidanmu ba muje zan kama miki hayar gida idan ma so kike zan siya miki gida naki na kanki sannan zan baki jari na bude miki wani abun na Business ki dinga yin abinki,idan ta kama har Dubai zan nuna miki yanda ake shugo da kaya ki dinga samun kudi,Islaha a ranta tace gwara a bani Sahil na kare a talauci na,a fili tace na gode ni nan yafi min idan kaga na bar nan to nayi aure.
Ai me sauki ne sai na turo manya a nemar min aurenki,Islaha tace ban shirya aure ba yanzu ni soyayya ma gaba daya bata gabana,murmushi Ibrahim yayi yace a ransa a hankali zaki shigo hannu ne yarinya,a fili kuma yace ba komai zan jiraki ni,ya dan dade yana hira tana amsawa sama sama sannan yace Alhmdllh tunda na san inda kike yanzu hankalina ya kwanta zan tafi,tace a yau zaka koma Abuja? Yace a cikin gari zan kwana a hotel gobe sai na wuce,tace yafi dai,mikewa yayi zai tafi tace ka gaida gida.
Lalai ta tsomo baki au baza ki raka shi ba? Mayafinta ta yafa tabi shi suka fita,Ibrahim sai dadi yake ji shi gani yake ma ya samu Islaha an gama,50k ya ajiyewa Lalai sabo da ya siyeta da kudi, Abdulrazaqu ma haka ya bashi 20k,sai murna suke yi,Ibrahim yace idan na dawo za a rakani gidajen yan uwan Islaha na gaishe su,Lalai ta yashe baki tace Allah ya kaimu dan nan kaji,an gode Allah ya tabbatar da alkhairi gashi kayi dace dama bata da saurayi bata kula kowa a sadaka zaka sameta,Ibrahim yace na sani ai ya wuce abinsa.
Suna zuwa jikin mota ya bude motarsa ya dakko ruwan roba ya balle ya sha abinsa,wato bazai sha na gidan ba,Islaha tace shine mu kaki shan ruwanmu ka dakko naka ai ba so bane wannan,Ya kalleta yace Typoid masifa ce sabo da ina son budurwa kawai sai na cuci kaina Typoid ta kamani ko na sha tsutsa a cikina ta hayayyafa ta cika min ciki, Typoid bata jin maga ni.
wato mu ta kashe mu kenan?cewar Islaha,Ibrahim yace ku ai kun saba ta saba da jininku ta sanku,baki ta tabe ya shiga mota sannan ya sauke glass ya miko 50k itama yace gashi kya samu ki dinga siyen wani abin,Islaha tace ina da kudi na ance maka bana ci ina koshi ne..
Nasan kina koshi mana amma garau garau gashi nan naga kin kara cikowa ma,Karki wa kanki ki karba karki koma gida kina cizon yatsa,Islaha taki karba fafur tace ina so na fada maka karka dawo wajena ni dai da Sahil nake soyayya sabo da haka bazan kula yaya na kula kani ba.
Ya kalleta cike da kishi yace Sahil baya sonki ki daina batawa kanki lokaci bai san ma kina yi ba harkarsa yake ya manta da ke ma,Islaha tace na ji duk da haka,kai fa bai ma dace ko da wasa ka kulani ba sabo da kaninka tunda tare ka ganmu,Ibrahim yace idan kika ga na hakura to kice an daura miki aure,Ba ruwana da wani Sahil kanina ne yazo muyi takara wanda ya samu shike nan ba abinda ya dameni,Islaha ta gaji tace to ka gaida gida na gode ta juya ta shige gida ko sisinsa bata karba ba.
Islaha tana komawa gida Lalai ta fara masifa tace ina lekenku kina fada masa magana,har ya baki kika karba to ubanwa kike so yaro kyakyawa da shi ga kudi dan birni,Islaha tace to ni bana sonsa kaninsa nake so karki dameni,Lalai tace to kuwa matukar baza kiso wannan ba sai dai ki bar min gida wlh,yaro dan mutunci ga kyauta,Islaha tace ae naji zan tafi bazan taba sonsa ba wlh ni bana sonsa,sabo da ya baku kudi ni zaku cuceni.
Lalai ta fara ruwan bala'i kizo gidana in ciyar dake amma nace kiyi abu kice a'a ai kuwa baki isa ba kici ki sha kice zaki rainani,Islaha tace iya na aikin wahala ta naci kyauta kika bani ba aiki nayi ba sannan aka bani,tuwon da rogo sai dambu ko danwake shine ake ta min gori sabo da ni bazan baki abin duniya ba,nidai na fada miki bana sonsa gwara na bar gidan kuma da bana gidan ai da baku samu kudin ba,zan iya danne ki na kwace kudin nayi tafiya ta gwara ki kyale ni kaka Lalai,ni talaka na nake so kaninsa,ba wanda yake