Showing 9001 words to 12000 words out of 15331 words
Chapter 4 - Subul Da Baka Book 1 Complete Document by Zul.txt
yana bayani?shi kawai nake
kallo. Ya fiddo wani abu a gaban
aljihunsa. Sai wannan allura ce idan ba zaki
damu ba zan yi miki ita yanzu ta
kwana 3 ce yau,gobe,sai kuma jibi a hannu
akeyi".
Na kara yi masa kallo 'likitane ? Na tambayi
kaina,dama 'ya'yansarauta na
karatu?shin yarima TAUSAYI gare shi ko kuwa
KIRKI? "Me zai hana yarima,wlh ayi
mini ina so,na kuma gode,Allah ya biya".inna ta
fada. Ya taso hr kusa da ita, abn
mamaki sai naga ya rage tsawo. Yana gamawa
ya dan kalleta ckn murmushi, "
Inna da zafi? " Ckn -yar dariya ta girgiza kai. Ya
mike tsaye yana fadin. " Don
Allah a sha maganin akan ka'ida.Mu kwana
lfy".Ya juya abinda. Na yi saurin
mikewa na bi bayansa tun kafin inna ta
gargadeni. Har ckn Lungu na bishi nufina
sai zai shiga mota snn na bashi hkr, amma sai
na ga ya dan tsaya are da juyo wa.
"Za ki bi ni ne?" Na yi turus! Ba motsi. "Idan
Zaki bi ni ne, to mu tafi. idan kuwa
ba Zaki bi ni ba ne koma gida".Ya nuna mini
hny da yatsa. Na yi wani dummy!!!
kunya ta kamani ainun, shin mai zan kira hkn
da ya yi mini, dizgi ko wulakanci? Ya dawo baya,
"mu je!!"Da sauri na juya hr bakin kofa ya Kai ni
ba tare da wani
abu ba, ya juya kawai abinsa. "wnn Yaro
Humaira Allah ya dasa masa
tausayinmu".Maganar da Inna ta tare ni da ita
ke nan. Na yi murmushi kawai.
"Tunda yazo ashe abin na damunsa, wlh mun
gode, Allah ya nuna mana aurensa
da Gimbiya".Na ce,"Ameen".Ckn rai. Kasa cin
taliyata na yi, na rufewa su Aisha da
safe su dumama. Yau na dan makara sbd lkcn
da na isa kusan 7.30 hr ta gota. Na
tarar da 'yan aikin safe an tara su a falo maza
da mata. Gabana ya fadi, ko a
gabansu zai koreni? Nima na yi hanzarin
shigowa tare da samun wuri na durkusa.
Sanye yake cikin shiga ta alfarma,wata
rantsatsiyar alkyabba ce ya saka ciki kana
hango kayan sakin da ya zuba kansa da hula irin
ta sarakai,yau ya fito a
matsayinsa na (PRINCE)wato yarima mai jiran
gado a kowane lokaci.
Gabana ya fadi lokacin da muka hada ido nayi
saurin saukar da kaina kasa.yau
mulkin yake ji,ya dago hannu,dogarin sa dake
tsaye yace. "Yarima na amsa
gaisuwarki". Duk muka sunkuyar da kai alamar
godiya. Ya dan gyara murya.
Dogari ya yi saurin cewa. "Magana ta 2 kowa ya
nutsu inji yariman gimbiya". A
tausashe yace,Na hana zuwan maza cikin gidan
nan iyakarku waje,saboda aikin
cikin gida na mata ne. Ina sane da ta6arar da
ake aikatawa". Nan da nan mutane
na ido ya raina fata. Ya kara da
cewa.""ma'aikatan abinci Ina son daga yau a
kara
yawan abin da ake ba ni, ya na yi min
kadan".Duk suka amsa da, "An gama
yarima " ya mike tare da shigewa ciki, kowa ya
tashi tare da kama tsaginsa. Na
gama da ko'ina snn na shiga ciki, yana zaune
dirshan saman kafet da takardu baje
a Kasa, shigowata wayarsa ta fara kuka. Ganin
ya kanga a kunne yasa na shige
kewaye kafin na karasa shima ya gama na Kai
gaisuwa tare da ban hkr. Aiki nake
yi, amma Ina jin hirar tasa wadda na tabbatar
da mahaifiyarsa yake yi, sbd jin ya
ambaci MAMEE. "kun tashi lfy?"Ya kara narkar
da murya yana shagwaba ya ce, "Ni
kam Klum Mamee... wlh har yanzu bana jin
sonta. ,Don Allah a nemar mini afuwa gurin mai
martaba a janye auran nan. Da yake ba
na jin abinda ta ke cewa,ya kara shagwa6ewa
har ina mamakin kato dashi da
shagwa6a. "Mamee HAMEED din ki ne fa,don
Allah ki taimaka,wallahi ba ta da
kunya.kullum sai ta kai karata ga sarki. Na
jinjina kai tare da maimaita sunan
'HAMEED'wato sunansa ke nan. Ni dai mamee
kiyi wani abu,bana so!!! What? Ya
fada da karfi,wallahi mutuwa zan yi ko na gudu
na bar muku kasarku...o.k... O.k,to
shi kenan,mom ina jira fa". Yayi murmushi,bye
love you!!" Tare da ajiye wayar. Ya
koma ta baya ya kwanta tare da rufe idanunsa
duka,hannayensa yayi filo da su ba
tare da ya motsa ba. Na dawo wurin kansa daga
nesa na durkusa. "Brk da asuba".
Da sauri ya bude idanunsa, sun yi jawur ga su
tubarkalla ya dallo mini su tare da
maidawa ya rufe.Na daure na cije sbd ni ce
Kasa, na ce." Yrm !!!"Da sauri ya tashi
zaune yana mai kara shigar da kallonshi gare ni.
Na yi Kasa da kai, na kara yin
yaki wajen furta klmr. "Don Allah ka yi hkr
jiya..."sai kuma mgnr ta makale ta Kasa
fitowa. Ya jinjina kai,"Uhum? "Alamar na ci gaba
yana saurare. "Ban San cewar kai
ne ba wlh, a tunanina irin samarin unguwarmu
ne da ke damuna". Ya daga kafadu
tare da watsa hnn yana tabe baki alamar bai
damuba. ,Na tashi kawai na fita tare da hado
kalaci. Yanayin yadda ya ke cin abincin ya
bani dariya a cikin rai,mutum sai ka ce
mace,wallahi ko macce ta yi yangar yarima
tayi kokari,sai yatsina yake yi abin har ya zamar
masa jiki. Ya ture kayan har zan
dauka yace,zauna ki ci a nan! Na dafe
kaina,wannan mutumin na neman haddasa
mini fitinar Gimbiya,ga shi ba a yi masa
gardama. Na dan cusa kwan da dankalin
tare da satar kallonsa. Na ce, na koshi". Ya kada
kai kawai. Har nakai bakin kofa
ya ce idan kin juye ki dawo". Nace to. Kawai na
fice da sauri. Wata wayar na tarar
yanayi sa'adda na dawo,amma yanayin wannan
ya tabbatar mini abokinsa ne. Na
yi tsaye na jingina da bango kaina a kas har ya
gama. Dakin ya dauki shiru na
wani lokaci.
,"Humaira".Ya kira sunana a hnkl. Na yi saurin
dago kaina.ya shigar da idonsa
sosai ckn nawa."Magana tana yi miki wahala
ko?"Na girgiza alamar a'a. ya yi
murmushi, ckn KASAITA ya ce. "Bata yi miki? Na
daga kai alamar, 'eh'.Murmushi
ya kara yi ya ce."To bani lbr..."Da sauri na
kalleshi ya daga min gira yana bin
fuskata da kallo. ana sunkuyar da kaina Kasa
Ina wasa da 'yan yatsun hnn. Zuwa
can na dago ido, ashe ni din yake kallo.Muka yi
arba da juna ya kara saka mini
murmushi, nayi saurin dauke kai. "Humaira ". Ya
kara kirana a karo na 2.Na dago
Kai ban yrd mun hada ido ba.yace,miskilancinki
da jan aji har ya fi na 'ya'yan
SARAUTA,da ana sauyi yau da kin koma
GIMBIYA,ita kuma na mayar da ita BAIWA
ta zama barorinki kamar yadda kika zamanto a
cikin nata a yanxu. Gabana yafadi
matuka. Ba zaki yi mini magana ba?.Nace zan
yi. Yanayin yadda na fadi maganar
ya sanya shi fahimtar gab nake da yi masa
kuka. "Kin takura ko? Ya fada...
Nayi shiru ina kallon babban yatsan kafata,
Humaira! Gabana ya kara faduwa
wai me yakeji idan ya ambaci sunana? Ko kuwa
duk salon wulakancin ne zai ta
takura min? Jin ya taso yasa nayi saurin dagowa
kwalla ta taran min nace yanzu
zan baka wllh yallabai lbrn nake
hadawa....amma saida ya matso gabana gashi
gab dani kamshinsa yana dokar hancina jikina ya
dau kyarma addu'a nake Allah ya
karemu daga sharrin shaidan ya sunkuya dab da
fuskata yace kina da sarauta?
Nace a'a to meya sanya kin cika TAKAMA? Nace
kayi hakuri.Yace to bani lbr koda
tarihinki ne yau sai naga miskilanci irin naki...
Yace gaba na fiki rashin son mgn da
miskilanci tunda na ajiye girman kai harna
tambayeki dole ki gaya min har gidan
ku naje amma kika kasa tambayata dalilin
zuwana. Ya dalli bakina oyya am
waiting.... Na kalleshi idona taf da kwalla nace ai
kaga gidanmu ko? Ya kanne ido
daya yace ban kula ba sbd duk na gama tsorata
dashi... Mu kenan babanmu ya
rasu ya barmu 6yrs kenan muna da yan'uwa da
yawa a nan garin. Ya kalleni kin
gama? Nace umm yace to saura ni na dago da
sauri saura kadan mu hada fuska
sbd ya dan duko, donAllah ka matsa na fada ina
fidda kwalla. Baki so? Ya fada cikin maraitacciyar
murya. Na ce,"eh". Sai ya koma saman
gado ya zauna. "Ki shiga kowaye ki wanke
fuskarki,kada ki fita a haka,ko kuwa ba
komai ? Na yi hanyar fita. Zan wanke a kicin.
Zaune nake dirshin ina tunani ban ga
wurin aiki a nan ba,saboda idan haka halin
yarima yake lallai shima yana layin 'yan
unguwarmu. Har na tafi gida bai kara sanya ni a
ido ba,duk tsanarshi tashiga
zuciya ta.Da daddare na yiwa inna karyar barci
zan yi da wuri don haka lokacin da
ya zo da daddare yiwa inna allura sai ta ce ya
shigo kawai. Ina jinsu ya share wuri
ya yi zaune inna na yi masa labarai wanda shi
ne ke mata tamboyoyin,sun dade
kafin ya tafi. Da safe na yi shiri kamar na tafi na
zame gidan su Amira na yi mata
karyar daga can nake ba ni da lafiya shi ne aka
ba ni izini ga shi inna ba ta nan
tana gidan yini,ni kuma sai anjima zamu tafi
party sai 2 na koma gida. Da daddare
yazo,inna ta fada masa muna wurin walima.
Washegari na wuce gurin walima
abina. Wasa wasa sai da nayi kwanaki 4 banje
ba,kullum ba ya tadda ni sai yau.
Ina alwalar magriba na ga mutum a tsakar gida
yana sallama. Gabana ya yanke ya
fadi,tuni inna ta kabbara sallah. "Wurinki na zo.
Ya fada tare da juyawa ya fita
waje. Na zuro hijabi na kalli inna,na ce "inna
yarima ke kirana a waje". Tayi gyaran
murya,wanda na gane umarni ne ta bani na je
din. Na sameshi waje ya harde
hannayensa yana tsaye. Barka da isowa. Na
fada a hankali. Ya kalle ni,zuwa na yi
bada hakuri da neman afuwa,ina kuma biko don
Allah a koma aiki na tuba idan
halina ne kuma zan kara. Nayi shiru kawai ina
mamakin mutum mai GIRMA
matsayi yazo bani hakuri. Allah ya baki hakuri
ya kuma huci zuciyarki Humaira, acikin raina
nace yana
kaunar sunan nan nawa. Kin jahilceni Humaira
zuciyarki tana gaya miki karya lalai
da kinsan waye yarima da baki shiga rudani
haka ba but am sorry pls, shiyasa
nakeson ki sami sakewa cos shiru shirun naki is
too much kada ki sami wata cutar
amma na daina kiyi hakuri 'bakomai' itace
kalmar dana fizgo daga bakina na fada
yayi murmushi to acikin abnd ya faru meya bata
miki rai dani? Nayi shiru donAllah
kiyi min magana ko sai munyi sallah? Da sauri
na daga kai, to kawo min buta, na
tsya ya gama alwalar yaceDako min tabarma
nayi ta anan".Na zaro ido Ina
murmushi har bakina ya dan bude kadan, sbd
ya bani dariya, na ce."Gafa masallaci
can".Na nuna masa da yatsa.Ya sosa keya kawai
ya wuce yana murmushi.Na rasa
abinda zan cewa inna akan zuwan Yrm, abin ka
da wnd yasan hali sai kawai ta
share ni.Ana karasa sllr isha'i ya dawo, na
dakko tbrm a kusa da katangar tana
kallon dakin inna, sbd bani son ta ji hirar har ta
ganoni. Na leka nace "shigo ciki
yallabai". Karshen tbrmr na zauna nesa kadan
shi kuma ya zauna bisa daga farko.
Ba tare da ya kalle ni ba ya ce, "kin fi sha'awar
zama hakane, ko kuwa kina ckn
takura?"nayi saurin kai guwoyina Kasa.ma'ana
na durkusa. Ya dago Kai.... Ke nake sauraro,ko
sai kin gama jan ajin? Na yi shiru saboda na
rasa ta inda
zan fara masa. Ya kuran ido wataKe nake
sauraro... Nayi shiru sbd narasa ta ina
zan soma yu kuran ido ga wata me haske kamar
lantarki.. Uhm....uhmm...u
hmmm..daman... Kai wani kaya sai amale wasu
na fama da magana wasu kuma
wahala take musu duk maganar nan bata wuce
kalma uku ko hudu ba sbd iyakar
zancenki kenan idan mutum ya matsa amma kin
kasa furtawa, kinga dare yana
karayi kada ki jawo min wata masifar bana son
yawan korafi, nayi kasa da kai
nakara rage murya nace kasan aikina yana da
hadari kuma ance inda duk mace da
namiji suka kebance na ukun su shedanne kuma
gashi naga....... Kinga me? Nayi
shiru bakiji? Ya maimaita.Uhm me kikace? Duk
daya san ban yi magana ba. Ganin
ka taso daga kan gado yasanya na tsorata,
nafada kamr zanyi kuka yadan matso
kan tabarmar tare da juyowa ya fuskanceni
sosai ta hanyar jingina da bango, ya
sassauta muryar nan tasa mai taushi "saurara
kada kiyi kuka inna zata zargeki
kota sani?" Nayi saurin girgiza kai yayi murmushi
don Allah ina neman alfarma a
dinga ce min e ko a'a tunda basu da tsayi kinji?
Nace to da kyar, kiyi hkri bazan
kara ba shikenan? Na sunkuyar dakai kawai naji
kunya ko bakiyi bane? Nace nayi.
Ina jin sautin murmushinsa ya kalleni inaso ki
fahimceni zan fada gsky ba don
na kare kaina ba wllh Humaira ko Qur'ani kika
dauko zan dafa na rantse, duk me
ya kawo haka na tambayi kaina, na girgiza kai,
zaki amince dani? Na girgiza kai to
wllh Humaira ban taba yin zina ba na rantse da
Allah a turai nayi karatuna saida
nayi 9yrs amma budurwata 1 itama hi hello ne
tsakaninmu muna gama karatu
muka rabu dama ita take damuna lokcn dana
dawo kuma na tarar an hadani da
Fareeda wato gimbiya a matsayin wacce zan
aura ba don kuma ina sonta ba ganin
ina kaukauce wa alamarin yasa aka yi min
wannan kofar ragon,ga shi zuwan bai
wani amfani ba domin ya kara min tsanarta
maimakon na ji sonta. Wallahi ba ta
cikin tsarin macen da nake son aure,ko mun
dace? Nace,uhm. Ya kalle ni,nayi
saurin daukar da kai. Uhm fa kika ce? Nayi
murmushi. Magana zaki yi,domin
shawara na zo mu yi ko ban isa ba? Kai isa
mana,amma kayi hakuri zan yi
tunani". Yanayin yadda ya tabbatar min da
maganar ba karamin dadi tayi masa ba.
Zuwa yaushe?"Jibi. Na fada. Yace, A'a,zan jira ki
gobe da safe idan kin zo. Na yi
shiru kawai ko ba zakizo ba? Nace ,insha Allah
zan zo". ,yayi murmushi wai ke baki iya karrama
bako bane humaira ko dan ruwa?
Narasa inda zansa kaina kamr na tsaga kasa na
shige don kunya, zan mike yace
a'a zauna saida na roka Allah ko kin kawo bazan
sha ba. Nasan dama barazana ce
ba zai iya shan ruwan gidanmu ba kamr ya
karanci hrt dina naji yace gobe ki
tanadar min fura mai dadi na sha kinji? Nace
uhm! Sbd tunanin bazai iya cin
abncnmu ba yasa ko ruwa bana bashi. Ya mike
zan wuce naga inna ta shiga ciki
watakila ma tayi bacci ko bakya bacci da wuri?
Inayi fada tare da mikewar nima,
yar gayu' kalmar ta tsaya min arai ina ce yan
gayu sune masu hira ba bacci da
wuri ba? Muna kaiwa bakin motar nace Allah
bamu alhair da sauri yace kezonan!
Kibari na bashi fitila mana ko kinason fadawa
kwata ne? Da rana ma mutum bai
tsira ba balle dare wann lungun naku(kai yarima
a hakan dai!) Ya mikon wayarsa
na zare ido ki haska gobe kya taho min da ita,
na juya baka gajiya zo humaira na
tsaya batare dana juya ba ya karaso gabana
natsani gardama donAllah ki daina
ungo wayar nan ko wllh in yarda, jin ya rantse
yasa na karba hannuna yana rawa
jikina yana kyarma kirjina naci gaba da faduwa,
kinji dadi? ,Nace uhm amma cikin raina fal
haushi maimakon yabarni na koma sai cewa
yayi zomuje mota nai miki kyauta ko bakya so?
Maganar gsky idan haka halin
yarima yake to banaso sbd banason yawan
takura dayawan tambaya (kunji
kinibabbiya) ace duk maganar da mukayi saiya
nemi na bashi amsa kamr yasan
zuciyata saiya dan duko yace kona dameki? Na
bata fuska kabarshi kawai
bakyaso? Na kalleshi cikin takaici na wuce wajen
motar kawai sbd na tabbatar
yarima mutum irin mai naci ya biyoni lalala!
Ashe kin iya harara haka irin wann
harar ai saikisa na kasa bacci a yau. Maganar
tashi tayi min tsaye naita
luguiguitata cikin kwakwalwata. Abin takaici sai
naga ya fiddo da cakulet kwaya 1
ya mikomin harga Allah bansan sanda nayi
dariya ba wacce har yaga hakorana
shin ko dai yarima auta ne? Shima ya kara kura
min ido yana murmushin nan nasa
na kasaita mai kunshe da nishadi marar
misaltuwa yace. "I can't express my
feelings bcos of this beautiful laughing thank U
so muc!" Duk cikin wann dogon
turancin da yayi thank u din kawai na fahimta,
na juya kawai jikina ya bani kallona
yake bai tafin ba har na kai karshe layi zansha
kwana na juya sai naga ya dago
min hannu yana dariya. Inna na zaune na shiga
tace yau kam ya dade lfy ko? Na
zauna nace inna yarima na bani tsoro, tsoro
kamar yaya Humaira? ,Wai inna shawara yazo
na bashi akan gimbiya fareeda wai shi baya
sonta, inna
ta zare ido baya sonta humaira? Haka yace
inna. Naci gaba da bata lbr da irin
yawan tambayoyin da yake min. Zan baki
shawara 1 goben ki gaya masa yayi
biyayya da iyayensa shine kawai mafita don
bazasu sashi hanyar dasuka san bata
da amfani ba ita kuma gimbiya a matsayinsa na
namiji shi zai nuna mata yanda
yakeson tayi sbd mu mata muna da rauni da
karamar kwakwalwa duk zurfin
iliminmu kuwa. Nayi murmushi nace amma inna
ngd da wann shawarar wllh dama
narasa me zance masa. Ki yi wa kanki godiya da
kin yi shiru kinga ai ba zan sani
ba bare na ba ki shawarar. Shi yasa ake son duk
abin da yaro zai yi ya shawarce
magabatansa. Na langwa6ar da akai ina
fadinada mata irin abubuwan da yake yi
min. Ta yi murmushi har sau biyu,sannan ta
kalle ni. Kin san abin da ake nufi da
HADUWAR JINI? Na girgiza kai ta kara
murmusawa. ,Abin da akae nufi shine,kauna ta
cikin jini,haka kawai Allah ya hada bayinsa
cikin hikima tasa. Ma'ana yarima Allah ya hada
jininku ba don komai ba,saboda
hakan Allah ya rubuto. Wallahi ina mai tabbatar
miki,da yana tausaya mana ne
kawai na farko yafi karfinmu nesa ba kusa ba.
Tsarinmu da shi ya sha bamban da
sa.kuma ya fahimci hakan. Shawara daya zan
baki. Kiyi kokarin inga ba shi amsa
gamsasshiya a duk lokacin da yayi miki
tambaya,hakan zai sanya ya daina
damunki tunda halinsa ne.Yarima ba yaro bane
don akalla zaiyi 38yrs ke kuwa
duka fa yanzu kike 15 kawai daiya dauke a
kanwarsa ko yar cikinsa a tunani. Jin
tayi shiru nace to inna yace gobe zai dawo na
dama masa fura, fura? Ta tambaya
tana kallona nace uhm tayi tagumi to bamusan
abnd Allah zaiyi goben ba na mika
mata wayarsa daya bani aro ta karba itama
hannunta yana kyarma don kyaunta
ga wani kamshi da yake fita ta juyata ta kara
juyata Allah sarki humaira yaron nan
tausayi gareshi adana masa zuwa safiya na
amsa ita kuma ta juya ta fara bacci ni
kuma yau baccin sama-sama ne sbd kamshin
yarima daya addabeni (kuji mayya
lol) kamshin da yake a jikin wayarsa harta
hanneyana ma kamshin sukeyi. Saina
tsinci kaina cikin faduwar gaba ina tunanin irin
halayensa. Tun daga kofar shiga
falon na fara fahimtar yau gidan babu lfy kowa
ka gani yayi tsuru-tsuru yana zare
idanuwa ba mazan ba ba matan ba kowa yana
cikin fargaba. Jikina ya dauki rawa
don bana kaunar tashin hnkli a dunia. Takun
farko dazan shiga cikin falon najiyo
muryar gimbiya tana balbala masifa abnd
kunnena ya jiyemin saura kadan fitsari
ya zubo min nayi saurin komawa ta kicin tare da
lafewa a jkin bango ina saurare.
Duk abnd kake takama dashi nima ina takama
dashi yanda kake dan sarauta haka
nima ubana yake sarki na gaji da wann cin
kashin da kake min tun zuwanka! Kullum da irin
salon wulakanci da rainin wayon da zaka 6illo
min da su kana
kunyata ni a gaban BARORI nah! Ya zama dole
ka amsa min tambayar nan INA
KAKE ZUWA KULLUM CIKIN DARE? Na tambaye
ka jiya bayan ka dawo kace min
bacci ka ke ji. Yo yanzu kuma fa? Da kai nake
kayi banza dani,ko za kayimin
izgilanci ne da kasaitar da ake yi maka kirari da
shi? To ka tuna cewa,nan ba
masarautarku bace,don'yan magana na
cewa,sarki a gidan wani sarkin sunansa
BAWA....Ba za kayi magana ba? Lallai zaka amsa
kira a fada yanzun nan,idan ka
raina ni ina ganin sarki yafi karfin raini a
wurinka. Ta banko kofa,tuni kowa ya
kama aikin karya kada ta gane ana sauraronta.
Na makale wayar a siket dina,kada
ma wani ya gani. Kallo daya zaka yi min ka gane
ina cikin tashin hankali. Aiki
kawai nake amma Allah Allah nake ta dawo a
aiko kiran yarima fada nayi amfani
da wann damar na hamzarta kammala tare da
ajiye masa wayarsa koda a
karkashen carpet ne tunda ba mai shiga dakin
saini amma