Showing 15001 words to 16885 words out of 16885 words

Chapter 6 - Mijin Kwaila Complete Document .txt

jikinta yagama yin sanyi ta'amsa da "Allah dai yasa abin yazo da sauki".
Ameen"
Abba yace yasakai yafice hankali tashe,
Tuni mutane suke tambayar umma ba'asin dake faruwa kowa yaji halin da'ake ciki saigaka jikinshi yayi sanyi.
Kai tsaye abba yafito waje yasamu kebewa da alhaji saifullahi yana sanar dashi abinda ke faruwa da zahra,abba yaci gaba dafad'in"anawa ganin kawai a dakata da d'aura aurennen harzuwa yanda hali yayi Allah yaga zuciyata banyi niyyar hana isha'q auren zahra ba.amma babu yanda na'iya da kaddara haka Allah ya nufa dole ce zata saka inhana isha'q auren zahra don bazan kaimashi wahala ba."
Ya tsagaita idanuwansa jajur,
Alhaji saifullahi kallon abba yakeyi da matu'kar mamaki akan fuskarshi yace da abban"amma malam adamu kabani mamaki kwarai da gaske,yanzu don *wata jarabta*tasamu zahra har kake tunanin zan'iya hana isha'q zama da ita?
Tokasani koda mungoyi da bayan hana isha'q auren zahra isha'q bazai lamunta ba,shine yaga zahra yaga tamashi a hakanta yake sonta na tabbata isha'q yanama zahra soyayya ta gaskiya yanama zahra *so d'aya tak*son da babu kiyayya koda yaya zahra takoma,zahra ta isha'q ce abadan da'iman don haka matu'kar dai babu wani dalilin personal acikin ranka to kawai a d'aura aurennan inyaso zahra taci gaba da samun kulawa daga maman ta wato *dr.ru'kayya*."
Abba ya gyd'a kai cike da gamsuwa,yana sake godiya ga Allah daya hada zahra da surukai na gari yanakuma fatan Allah ya tashi kafad'un zahra yabata ikon yima iyayen mijinta dama mjin shi kanshi biyayya.
Haka kuwa akayi take aka sanarma liman yakuwa dage ya tamke igiya uku ras tsakanin zahra da isha'q aurekam ya d'auru bisa sadaki mafi karanci don aure yafi albarka da karancin sadaki.
Umma tana cikin gida taji ana shafa fatiha sai lokacin wasu zafafan hawaye suka sauka akan kumatunta,wato dai shi tsautsayi baya wuce ranarshi.
Yanda isha'q ya kid'ime yasaka sadi'q binshi da mota yakara mashi motar yasha gaban isha'q duk suka fiffito daga cikin motar suna rokon isha'q yayi hakuri yabi komai a sannu,
Kasa motsawa yayi kamar wanda ya daskare haka yakejin jikinshi indai ba bayada rabon aure a duniya ba,mezaisa yarasa zahra akaron farko yad'auki dangana awannan karon yakuma sake rsa zahra?anya wannan kaddarar dake watangaliliya da rayuwwarshi kuwa.
Haka kawai yasakejin soyayyar zahra kamar ana ninka mashi ita,tabbas soyayya ba karya bace kuma amana ba wasa bace,
Abokanshi wajen biyar suka rufar mashi da rokon bude motar hakan ysakashi budewar kuwa,yanda yafito saika rantse yasha giyane saboda yanda jiri yake kwasarshi dakyar ya'iya furta"sad'iq zahra tazama tawa kokuwa ayauma nasake rasa zahra?"
Wani irin tausayin isha'q ya tsilga dukkan abokan nashi,
Dafa kafadarshi sadi'q yayi"haryanzu zahra adam ta isha'q ce,banga dalilin dazaisa afasa kulla auren da Allah yanufi saiya wanzu ba,isha'q bana tunanin akaf duniya akwai wanda yafi dacewa da zahra kamar ka.already zahra tana karkashin kulawarka isha'q".
Wata ajiyar zuciya isha'q yasaki,sai lojacin yasamu kwarin gwuiwar shiga motar da su sadiq suke sauran abokan suka shiga motar isha'q sukayi gaba suna sake kwantar da hankalin isha'q din.
.
Duk tarin yawan mutane gidan baihana dr.ru'kayya ficewa dag gidan ba, sakamakon kiran gaugawa data samu daga dr.haisam akan wata yarinya dawani yakad'e wadda take bukatar agajin gaugawa inma da haki sunason saka hannun dr.ru'kayya wajen fitar da yarinyar zuwa kasar cairo.
Jin yanayin matsalar yasaka dr.ru'kayya zura fara kal ta rigarta gami da saka hijabi tafice dasauri tana barma dr.aysha sallahun cigaba dakula da bakinta kafin ta'iso.
Rafiyar mintuna ashirin tasadata da babbar asibitin,dakanta take driving abinda harta mance rabon datayi kenan.
Parking tayi inda aka tanada domin hakan,tafito dasauri dai-dai lokacin da A'a yake mikama dr.haisam hannu don tafiya wajen cukuiniyar visa.
Dakatar dashi dr.ru'kayya tayi,tana tambayar koshine yakad'e yarinyar?
Dr.haisam ya amsa "shine hajiya"
Tayi d'akin da aka kwantar da zahra,tura dakin tayi cike da kwarewa takutsa kai dakin idanunta suka sauka akan zahra wadda take kwance batare datasan waye akanta ba.
Dasauri dr.ru'kayya ta karasa tana dudduba fuskar zahra,lokaci guda ta shaida atamfar jikin zahra wadda itace dakanta tabada d'inki iri d'ayane dana hanan.
Saikuma y'ar siririyar sarkar gold mai kwad'on da'akama designed da harafin Z wato farkon sunan zahra tabbas zahrace to why meyasamu zahra garin yaya hakan ta kasance?
Bata tsaya 'bata lojaci ba,ta fito a hanzarce tana shaidama dr.hisham yarinyarta ce ma ashe,yasha mamakin jin maganar don ayaranta babu wanda bai sani ba.
Sai dai basuda lokacin neman karin bayani ayanzu dasuke cikin hali na tunanin hanyar kubutar da rayuwar zahra daga halaka.
Kusan manyan likitoci hud'u suka nufi d'akin xahra da kayan gwaje2 don dr.ru'kayya tace sufara jaraba tasu sa'ar kafin ayi tunanin fitar da zahra kasar waje......
October 9,




Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah ��
4 comments 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN 'KWAILA*
_jinjina ga masoya lbrn mijin kwaila'gsky bnsan yama zan fasalta matsayinku awajena ba_ =luv yhu guys=��
editing aisha T.fulani.




*by maman meenat*










Chapter 17.






Cikin abinda baishige mintuna goma ba dr.ru'kayya tagama had'a kayan aikinta tare da kwararrun likitoci sundu'kufa akan zahra don gano ko tasamu matsalane a brain d'inta,
Abinda suka binciko shine yad'anso daga hankalin dr.ru'kayyan bawai matsalar zata shafi lafiyar zahra dun-dun-din bane,saidai hakan zai iya haifar da barazana ga lafiyar kwakwalwarta amma kuma muddin tana samun kula akwai tendencies na zata iya warkewa cikin kankanin lokaci.
Dukkan wani abu daya kamata likitocin suyima zahra sungama cikin ikon Allah kan natane kawai yasamu matsala ayanayin nasu binciken zata iya farkawa akowanne lokaci so abu d'aya dai dasuke ganin mafitane gareta shine idan tafarka tafara kallon abu mafi soyuwa agareta,wanda akowanne lokaci takeson kallo.
Saikuma abu na 'karshe wanda takalla bawai kallo na razanarwa ba,watakila tahakanne zaisa ta'iya tunano abunda yafaru abaya,kenan bazata samu matsalar tunani ba.
Wannan kenan....
Isha'q kam dukkan bincikensu baikaisu ga gano ainahin inane zahra ta kurd'a ba,hakan yasaka shi kifa kanshi ajikin kujera zuciyarshi kamar zata tsage kirjinshi tafito don tashin hankali da damuwa,
Soyakeyi hawaye sufito daga idanunshi watakila zaisamu sassaucin tashin hankalin dayake ciki.
Abinda yafi daga hankalinshi baishige yanda zaisake rasa zahra akaro na biyu a rayuwarshi ba.
Yakira wayar mummy yafi a 'kirga tana ringing sai dai babu amsa,sosai suka shigarda report wa police don binciko zahra.
Acan gidansu zahran ma hankalin duka atashe yake,kusan kowa zakaga babu natsuwa a tattare dashi,duk shirmen zahra a irin wannan halin datake ciki yakamata kowanne mai imani da hankali ya tausayamata.
Abba kam da aminanshi basu samu zamaba,bazama sukayi neman amarya zahra dafatan komai zaizamo cikin sauki da salama.
Sai wajen uku na yammacine motar dr.ru'kayya tayi fakin cikin harabar katon gidan nasu maicike da jama'a yan biki,dayawa sunamata sannu dazuwa dakuma tambayar maijiki takan amsa kawai sai dai babu natsuwa ko d'igo a tattare da ita.
Dakin dady tanufa da telephone din dake kan dan teburin tsakiyar dakin tasamu damar lalabo lambar dady wanda harzuwa lokacin yana fama da ba'ki,
Ganin kiran matarshi yasakashi kebewa gefe guda yana amsa sallamar datakeyi,
Cikin damuwa dr.ru'kayya takecewa dashi"abban hanan kana inane?"
Yabata amsa"inatare da ba'ki ince dai lafiya?"
Tad'anyi kokarin kauda damuwar dake tattare da'ita tace"kalalaboman number isha'q yanzu inason magana dashi ne".
Dady yad'anyi jimm saikuma yace"akwai matsalane mummyn hanan,kidai bari in karaso gidan,don aurenma da har mahaifin yarinyar yace afashi kawai."
Itama abinda takeson sanar dasu din kenan tawatso mashi tambayar"anfasa kokuwa ya'ake ciki?"
"and'aura mana,mezaisa afasa".
Cikin raunanniyar murya tace"abban hanan matsala babba nahangowa isha'q,yanzu haka amaryar tana asibitina a kwance tasamu accident yuwuwar samun lafiyar kwakwalwarta shine abu mafi wahala,bana zato ko tsammanin cikin kankanin lokaci zata zama normal koda miliyan nawa aka barnatar don lafiyarta din,shikenan zamu zubama isha'q idanuwa yazama sakarai akan macene?inada tabbacin akwai zahra ko babu zahra isha'q dole zai iya rayuwa"
Tad'anyi jim tanason jin abinda maigidan nata zaiic Jin baitankaba yabata damar cigaba da maganarta"nikawai atawa shawarar a d'age bikinnan harzuwa lokacin da zahra zata samu lafiya,inyaso sai ayi auren shikuma isha'q yasakama zuciyarshi dangana tunda dama aurene kawai na jeka nayika bawani abu zai tsinta jikin yarinyar ba."
Dady ya katseta dacewar"to naji naki batun idan shawarace ko umarni duka ina tayaki jimamin rashin samun karbuwarsu don yanzu haka anrigaya da andaure aure tsakanin zahra da isha'q,sannan koda cikin mafarki banzaci bakinki zai iyafurta wannan maganar ba,mutanen dasuka yimaki hallacci saboda batashi sukayi aurar da yarinyar suba,ganin kima da mutunci dakuma halinda isha'q ka'iya fad'awa yasaka suka aminta da aurar mana da ita amma kisani idan za'akai zahra turu 'karewar hauka tofa bazamu dage dai-dai da second daya na biki ba.
Tunda har da lafiyarta iyayenta suka bashi ita,yakumace yaji yagani to lallai madamar ta warware zata tare d'akinta inyaso yayi jinyarta sannan banason nakuma jin bakinki akan maganar matsalar da isha'q zai shiga,idan yaro yadauki gatari rikemashi kota akeyi."
Bai saurari mai zatace ba yadatse wayar,
Tafi minti uku tana kallon kan telephone dib dake hannunta kamar shine yake mata maganar,tagyad'a kai ita sam dady bai fahimci manufarta ba,idan soyayya ce bazai nunamata kaunar zahra ba amma abu daya dabazata dauka ba shine fadawar danta cikin wahala haka kawa.
Tana niyyar fitowa daga d'akin dr.aysherh tana kutso kai atare suka kalli juna,aysherh tafara magana"nadad'e ina sauraron shigowarki ga baqi sunata zuwa sai akace kina dakin dady bayan naga fitarshi tun dazu,ince dai lafiya?"
Tayi tambayar idanunta sunakan dr.rukayya,
Sauke ajiyar zuciya rukayya tayi dacewa"matsalar isha'q bansan har tsawon lokacin da zata dauka kafin warwarewar taba,"
Aysherh tace"sanar dani komai qawata,abokin kuka ba'a boyemashi mutuwa."
"Hakane"
Dr.ru'kayya tafad'a lokaci guda tana warwarema aminiyar tata zare da abawa.
Wani mugun farin cikine ya ziyarci zuciyar asherh saitake ganin lokaci yayi dazata cilla kibiyarta wajen farauto ma tilon d'iyarta aneesa zuciyar isha'q wanda aneesan tayi matukar macewa akan kaunarshi.
Cikin kwarewa da hila dr.aysherh ta langwa'be kai dacewa"ayya gaskiya na tausayama zahra,sai dai kokusa isha'q yafi tsayamun araina yanda baligin mutum kamar isha'q zai tsaya a rayuwar kila wa kala don natabbatar matsalar zahra matsalace da take daukar lokaci kafin warakarta kobayaga haka abinda zaifi tayar da hankalina yanda kamalin mutum kamar isha'q wannan matsalar ka'iya kaishi ga aikata sabo na zina donshi ma lafiyayyene kamar kowa yanada feelings akan mace.sai dai na tabbatar matsalar zahra bazata ruguje komai ba Allah yabata lafiya ".
Shiru dr.ru'kayya tayi tana juya maganar aminiyar tata cikin kwanyarta,for how isha'q zai tsaya zaman jiran lafiyar zahra bayan jiran girmanta?
Anya tayi nazari wajen amincewa da zahra yarinyar da kwakwaran wayo baigama zama ajikin ta ba? Mafita daya dazata nemawa isha'q take tunani amma wacece mafitar,tadaisan ko hauka take bazata taba iya tunkarar iyayen zahra da maganar su rike zahra harsai tasamu lafiya ba,kuma shi kanshi isha'q din bazai lamunci rayuwa babu zahra ba.
Kenan menene mafita?
Mafita...mafita..abinda take nanatawa kenan tana kirga tsawon shekarun da kamilin yaro irin isha'q zai dauka na jiran gaibu,don zahra gaibu ce ayanzu adai wannan halin datake ciki.
Tafara matsar yatsun hannunta tana jeranta awanni zuwa sekonni kwana zuwa sati kai matsalar isha'q abin iyaye suyi nazari ce gaskiya.
Jin andafata yasata tunawa dacewar akwai kawarta dr.aysher tana kallonta suka sakarma juna murmushi lokacin da dr.ayshe take cewa"mafita akwai mafita,mafitar d'ayace amma wahalarta yafi ace kizagaye garin kaduna akafa,mafita itace auree".
"aure?"
Dr.ru'kayya ta tambaya fuskarta akwai alamun mamakin jin maganar kawar tata,
"of course,aure zaki karama isha'q shine hanya mafi sauki dazata bashi dama dakuma ikon kula da kanshi dama ita zahran gaba daya".
"nooo,ican't aysher"
Cewar dr ru'kayya"haryaushe xan'iya kallon idanun mahaifan zahra inmasu wannan butulcin?"
Aysherh tadage kafad'a"bazaki iyaba muddin bakya kaunar farin cikin danki isha'q......
turkashi!!!nayi nan...








*real mum meenat*��
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)




WHATSAPP NO:
+2349030159301

4
5
6

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login