Showing 6001 words to 9000 words out of 96677 words
Chapter 3 - GOYON KAKA(1 to End) Complete Document Writing by Umma Yahya Musa.txt
*11*
Harhada kayansu sukayi a jaka,da gudu islam ta fice a gda gidansu hanne taje tararwa tayi innar hanne tana mata fada akan y kamata ta gyara halinta inba so takeyi ta rasa mijin aure a kauyen ba.
Sallama islam tayi tace hanne naxo nayi miki salama yau xamu koma birni gidansu babana ko nasaka ta na wala da yadda kowa y sakamin ido,innar hanne ce ta girgixa kai tace Allah y shiryaki islam to ina kudan yake balle romonsa da har xakice an saka miki ido,murguda baki islam tayi tace yanxu ke inna baki gani ba umh hanne xo muje gidansu ilah da yusufa nayi musu sallama,da sauri hanne ta tashi innarta tana kiranta kota kanta batabi ba suka fice.
A hanya hanne tace yanxu shikenan islam in kin tafi binni xaki manta damu ko,wata dariya islam tayi tace mai xaisa na mantaku kunefa abokanai na na hakika kuma ba ai Abba yace xamu naxuwa hutu washe baki hanne tayi tace Ashe nima wataran xani birni islam tace sosai a kofar gidan su ilah suka tarar da ilah da yusufa anan islam ta sanar dasu tafiyarsu birni suma basuji dadi ba suka dunguma suka tafi raka islam.
Acan bayan sun gama saka kaya a mota daddy yace to ina kuma islam din,kaka ce ta kama baki tace la'ilah ha illallah in ka bibiya ta tafi gidansu hanne yi musu sallama amma mu jirata.
Xaman jiran islam sukayi harna tsahon 10 minute amma shiru ba ita ba dallinta tsaki Aslam yayi yace amma yarinyar nan yar raunin wayoce in ba rainin hankali ba tasan jiranta mukeyi xata tafi yawo kaka ce ta hararesa tace to sai taki yiwa abokananta sallam...,bata karasa ba suka hango islam itada su hanne,Aslam yaja dogon tsaki yace saboda yarinya an batata wai har abokanai ne da ita maxa kaka ta hayayyako masa tace saika fadi waya batata kai wlh da badan islam tanason komawa birni ba kuma baxan iya bari ta tafi ita kadai ba wlh da ba inda xani,daddy ne yace hajiya dan Allah kiyi hakuri y kalli Aslam yace be carefull in ba haka ba kuma y girgixa kansa.
Islam ta karaso ta shiga mota daddy y bawa su hanne kowa 100 ganin da gaske islam tafiya xatayi suka hau ihu da kuka suna bin mota,islam itama ihu takeyi kaka ma harda goge kwallahπ’.
πππ
*daga* *sisin* *mama*
πππ
[11/12, 8:54 PM] βͺ+234 703 443 5155β¬: (7/10/2016 3:00pm)na umma yahya musa
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON* *KAKA*
*12*
Aslam ne yaji kukan islam yayi yawa kuma su Abba sunata rarrashinta taki yin shiru,tsawa y daka mata yace da Allah kiyiwa mutane shiru kin cikawa mutane kunne ke gaki mai kawaye ko,dago fuskarta tayi shabe-shabe da gawaye ta murguda masa baki tace to ina ruwanka in baxaka jiba ka toshe kunnanka da wanda ya tilasta maka dole kaji kukana xaro ido yayi yakai mata rankwa shi ta goce,daddy yace Aslam y kake wasa da rayuwarmu ne Aslam yace I'm sorry dad,sannan yace mamana rabu dashi kinji ta washe baki kamar ba ita take kuka ba tace toh.
Tunda suka tafi take surutu komai ta gani sai tayi magana na tambaya kuma ta tambayi Aslam ko kallanta bayayi sai tayi tsaki tace daddy ko Abba menene wannan saisu fada mata.
Aslam kuwa duk haushinta yakejin ganin yarinya karama tana shirin rainashi yadda kowa yake girmama shi a gdan amma yanxu xataxo da nata salon na daban murmushi yayi daya tuno da irin axabar da xaiyi mata har saitayi biyayya tsinto ihunta yayi ta kwalla kara tana yeah kiiiii yaja birki saura kadan y bugawa motar gabanshi dan ma Allah y nufa babu mota a bayansa da hatsarin da xasuyi ba kadan bane.
Kaka firgigit ta farka daga gyangyadin daya dauketa tana salati,su Abba ne suka kalli islam sukace ihun me kikeyi ko kinaso muyi hatsari mu mutu daddy yace kai Aslam kai kuma tunanin me kakeyi,kaka tace so yakeyi y kashemu kawai dama bai damu da rayukan muba.
Islam tace nifa tsoron wannan nakeyi gani nake in mun hau xamu fado,dariya Abba yayi yace islam rigima wannan fa gadace da ana fadowa ai da bakiga wasu motocin suna biba(nikuwa na kyalkyale da dariya nace kai aradu kauyanci baiyi ba yanxu hawa gadar takewa ihu hakaππ).
Aslam kuwa wani bakin cikine y turnike shi a ranshi yana watako ita duk iskancin nata ma tsoron mutuwa takeyi aikuwa xakici ubanki y figi motar,islam kuwa idanunta ta runtse sai da suka sauka akan gadar ta bude idonta.
πππ
*daga* *sisin* *mama*
πππ
[11/12, 8:54 PM] βͺ+234 703 443 5155β¬: (8/10/2016 4:00pm)na umma yahya musa
ππππππ
ππππ
ππ
π
*13*
*GOYON* *KAKA*
Tafiya sukeyi har suka karasa gda horn Aslam yayi gate man y wangale katon gate din gidan suna shiga yaran gdan suka taho da gudu harda taslem duk suka futo a motar wata mika islam tayi taja doguwar hamma ko rufe baki batayi ba,da sauri Aslam yadan bige bakin yace ba'a fada miki in anyi hamma ana rufe baki ba ihu ta kwala a firgice y juyo yace dan Allah kiyi hakuri yakai hannu y rufe mata baki,da yake ba wanda yaga time din daya bige bakin nata.
Shiru tayi taja tsaki ta murguda masa baki,kaka ta kalleta tace ke kuma ihun mene wannan kamar wadda tayi gamo cuna bakinta gaba tayi bata bata amsaba.
Su mommy da aunty amarya ne suka futo sukayiwa kaka sannu da xuwa har part dinta aka shigar da dukkan kayansu dayake an riga an share part din.
Bayan sun gaida kaka,islam kuwa hankalinta yana kan taslem yar 3 year tanata mata wasa,aunty amarya tace islam baki gammu bane ba gaisuwa murmushi tayi tace aunty amarya ina xuwa wasa nakewa taslem duk maganar da takeyi ko dago kanta batayi ba.
Girgixa kai aunty amarya tayi a ranta tace Allah y shirya,futa su mommy sukayi suka kawowa kaka abinci kala kala bayan sunci,islam ta mike ta shiga toilet fanfo takeson kunnawa ta kasa,saboda ba irin na kauyensu bane garin kici kici ta kunna shower kawai sai jin ruwa tayi y xubo mata ihu ta saka tana wayyo Allah na shiga uku.
Da gudu suka tashi sukayi bathroom din ganinta sukayi a tsaye jikinta sai rawa yakeyi ta rufe idonta sai ihu takeyi ruwa duk y jikata,Aslam da Amir dariya suka farayi ganin dalilin kukannata sauran yaranma duk suka dau ihu suna villager girl aunty amarya kuwa tsaki tayi ta koma mommy ce ta shiga bathroom din ta kashe shower din kayanta ta taimaka mata ta cire,sannan tayi mata wanka ta bata towel suka futo,mai ta shafa mata da powder sai kwalli islam tace mommy bakiyi min dige-dige ba,mommy tayi murmushi tace nan birnine ba'ayi ko kinaso a dinga ce miki yar kauye xumbura baki tayi tace niba yar kauye bace mommy tace ai dama bance miki yar kauye ba,islam tace to daxu daga ina ruwa y xubo naga ba a bude saman bandakin yake ba balle nayi xaton ruwan samane jan hannuna mommy tayi suka koma bandakin tace wannan shower sunanta wanka akeyi da ita dariya ta kyalkyale tace yasin birni yayi ta dada kyalkyalewa da dariya a haka suka futo yaran suna ganinta suka fara villager girl kugu ta kama ta joge kafa tana girgixa tace wace bulleja gal din wlh ni ba sa'arku bace sainayi muku tsinannen duka(nikuwa nace kaji turancin manyaππ).
πππ
*daga* *sisin* *mama*
πππ
[11/12, 8:55 PM] βͺ+234 703 443 5155β¬: (8/10/2016 4:30pm)na umma yahya musa
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON* *KAKA*
*14*
Dariya suka dada tuntsirewa da ita faduwa tayi tahau birgima mummy ce ta korasu sannan ta koma lallabar islam.
Amera ce ta dawo part din kaka saboda islam,da daddare bayan sun gama cin abinci islam ta kalli Amira tace Amira wai ku bakwa futa wasan darene,Amira tace eh munan ba'a futa wasan dare amma munayi a sarraunding din wataran,islam ce tayi tsaki tace menene sorondin murmushi Amira tayi dan tasan in tayi dariya yanxu xatasha bala'in islam dan adan xamansu ta gane masifaffiya,tace tsakar gida islam tayi dariya tace auho to tashi muje muyi.
Xaro ido Amira tayi tace wlh yaya aslam dukanmu yakeyi in yaxo y tarar munayi yace wai saimun hadu da aljanu tsaki islam tayi tace wlh ke xabuwa ce kixo muje xan tare miki in xai dakeki,Amira tace wlh badani ba tsaki islam ta kumayi tace to munyi fada karki kara kulani,murmushi Amira tayi daga haka bacci y kwashesu.
Washe gari kaf yaran gidan in banda taslem suka shirya suka tafi makaranta bayan daddy da Abba sunxo sun gaida hajiya,islam ta gaishesu,Abba yace islam ki dauko mayafi xamuje ayi miki interview xaki fara xuwa makaranta,bakinta ta xumbura ta dauko tunda suka tafi take guna guni ita batasan makaranta kuma ko an kaita sai taga dama xata,tunda suka doshi gate din makarantar ta saki baki daga saman gate din makarantar an saka *khadija* *memorial* *nursery* *,* *primary* *&* *secondry* *school*duk daba nisa ne da makarantar ba,dan a bayan gidansu makarantar take,saboda yadda makarantar ta tafi da imaninta da suka shiga kuwa gaba daya tunaninta y tsaya saboda makarantar duk shuke-shuke ne parking Abba yayi yace mamana futo mu tafi hannunta y kama direct office din principal suka wuce,bayan sun gaisa Abba y fadawa principal yarinya y kawo amma yana neman alfarmar a sakata a primary 3 saboda daga kauye y daukota,principal yace ba komai amma ku nemar mata lesson teacher dan in bata kokari xa'a iyayi mata repeating Abba yace ai dama akwai lesson teacher dayakewa yan'uwansu.
Principal yace yauwa anan Abba yayi mata registration y siya mata duk wasu school items da xata bukata aka bata unifoam sannan yayi godiya suka futo.
πππ
*daga* *sisin* *mama*
πππ
(9/10/2016 12:00pm)na umma yahya musa
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON* *KAKA*
*15*
Direct kasuwa y wuce da ita y siya mata takalman makaranta masu kyau guda uku da socks,da school bag da launching box surutu take tayi masa akan yadda makarantar ta burgeta Abba kuwa sai murmushi yakeyi.
Suna xuwa gda Abba tun kafin y daidaita packing ta fice a guje direct part din kaka ta sheka a guje ko sallama babu sai ganin islam tayi ta shigo kamar an korota xinbur kaka ta mike tana ke lfy meya faru waya biyoki,ko takan kaka batabi ba ta shige bandaki saboda fitsari ne y korota dama islam tana da wannan dabi'ar bata taba shiga bandaki lokacin da taji bukata sai abin da xatayi yaxo daf sannan xata taho da gudu ta shiga.
Kaka tananan tsaye kekam kamar soja tana jira taga wa xai shigo,Abba ne yayi sallama y shigo dauke da kayan islam a hannu kaka tace au ashe tare kuke yace eh wlh y samu guri y xauna juye kayan yayi yace hajiya ga kayan islam na makaranta nan anjima aslam xai kaita islamiyya kaka tace to angode Allah yayi albarka Abba yace ameen y fice.
Islam ce ta futo ta xauna tace kaka kinga makarantar da aka sakani aradun Allah dole na maida hankali kada su koroni,baki ganta bafa tun daga waje fulawoyi da fanti cikinta kuwa harda kwalta da fulawoyi ai wlh jarababben tanimu ma yakemin masifa inna tsinko mangwaronsa to makarantar harda mangwaro da goba kai kaka ga lilina kai komai dai dodar ta tuntsire da dariya,kaka ma dariyar ta tayata tace kwashi kayannaki kikai cikin daki islam tace toh takai daki ta dawo.
Kaka tace yauwa alhj karami yace anjima aslam xai kaiki islamiyya xumburo baki islam tayi tace gaskiya inshi xai kaini banaso saboda nasan dukana xaiyi tayi a hanya,kaka tace haba ta wajena karki damu xanyi masa magana kafin ku tafi baxai dakeki ba islam tace toh ta tashi,kaka tace ina kuma xaki islam tace xanje nadauko taslem muyi wasa kaka tace toh sai kin dawo,tafe take tana kada yar sandarta tana tana waka part ta gani guda uku rike haba tayi tace ohni yasu to wanne gdan aunty amarya aciki tunani ta tsayayi kawai ta shige wani wanda xuciyarta ta amince mata ta shiga ko sallama babu ta shiga dakunan ta shiga turawa taji duk a rufe har xata juya tace au bari natura wancan ko acikinsa take sadaf-sadaf take tafiya kamar mara gaskiya tana tura kofar kuwa taji ta budu xura kanta da xatayi idonta yayi arba da mugun gani ihu ta kwala.
πππ
*daga* *sisin* *mama*
πππ
[11/12, 8:55 PM] βͺ+234 703 443 5155β¬: (9/10/2016 1:00pm)na umma yahya musa
ππππππ
ππππ
ππ
π
*GOYON* *KAKA*
*16*
A firgice Aslam da yake goge jikinsa dan fitowarsa daga wanka kenan yakai idonsa kanta da sauri taja kofar ta sheka a guje.
Tsaki aslam yayi yace oh god meyasa nake sake yarinyar nan take ganina ba kaya sai ta rainani tsaki yayi yace ai tana rainani ubanta xataci a gdannan.
Islam kuwa sai data futa daga part din sannan ta tsaya tana maida numfashi dariya tahauyi tace lallai yaya aslam dinnan dan iskane in banda iskanci y futo daga bandaki ba kaya bakinta ta kama au kar a jini ace nima naxama yar iskar tunda naganshi ba kaya dariya ta dada kyalkyalewa da ita.
Aunty amarya ce ta futo dauke da taslem xata je part din mommy islam ta gani tanata babaka dariya aunty amarya ce ta kirata tace ke islam dariyar me kikeyi tsagaita dariyar tayi tace ba komai aunty amarya tace toh me kikeyi anan tace gidanki xani dauko taslem aunty amarya tace toh yar kauye ai kin shigo gda part xakice in kuma da hausar xaki fada sai kice bangare xumbura baki islam tayi tace wlh aunty amarya niba yar kauye bace kosu hanne cemin sukeyi yar birni,aunty amarya tace ke kika sani ni karbeta xuwa tayi xata karbi taslem