Showing 3001 words to 6000 words out of 16112 words
baya kanta saboda raɗaɗin da yake yi ma ta sakamakon
kwallar da ya bugu a kai.
Ihun da Uwani Matar Kawu Iliya da ta biyo bayansu ‘Yar Gwal kuma ta kasance ita ce mai
wannan Manja ta kwala shi ne ya dawo da hankulansu kanta har ma da wasu mutanen gari
masu wucewa dama sauran matan gidan domin ihun da Uwani ta kwala sai ka ɗauka mutuwa a
ka yi ma ta, dan hannu ta ɗaura a kai tana ci gaba da zunduma ihu faɗi take.
“Ƴar Gwal kin kasheni, shikenan naja ma kaina dana hanaki bashin manja domin da ban hanaki
bashin manja ba, ba zaki ɗauko gaba ɗaya kwallar manjan ba gashi yanzu kin min asara
shikenan ɗan jarin da nake taƙamar ina sana'a da shi kin yi min sanadi, wayyo Allah ni Uwani
tawa ta sameni!.”
Yadda Uwani ta ɗaura hannu a ka tana ihu tare da wannan sambatu abin zai baka dariya za
kuma ta baka tausayi....
*Kayyasa! to dai kunji da yadda labarin namu ya fara. Ni dai nayi can *
* Happy New Year My Reader's*
_Cheer's to a fresh start, a new chapter, and a year full of dreams coming true_
1/1/2025!
Nainarh KD ✍️
07067953066 Or 08081129487.
♡YAN TIRIRRISHI
_Short Story_
# Nainarh KD
# Perfectly Pen's
https://chat.whatsapp.com/EKGtef2G0MxHyOMMUrN0bX
..02
Iya Sahu dake gefe sai faman salati take tana rarraba ido tama rasa abin faɗa dan kuwa ta san
yau babu zaman lafiya tun da har a ka taɓa Uwani Matar Autanta Iliya bata ankara ba taga
Uwani ta miƙe a fusace ta nufa wurin da 'Yar Gwal take da niyyar kai ma ta duka.
Sai dai kafin ta ƙari sa tuni 'Yar Gwal da ta ankara ta yi gefe tana dariyar ƙeta ta ce.
“kin yi ma kanki Uwani tun farko da na bi ki ta hanyar lallami da kin saurareni da duk haka ba
bata faru ba ai...”
Ƙare maganar 'Yar Gwal ya yi daidai da haɗa ido da suka yi da Rabi'ah da tsaban takaici ya sa
ta kasa magana.
Ai kuwa me 'Yar Gwal zatayi in ba dariya ba musamman ganin yadda fuskar Rabi'ah ta koma
kamar mage ta yi ɓarin manja kasancewarta mai farar fata.
“Iya Sahu wai kuwa kina ganin abin da nake gani dan Allah tayani duba ji fa yadda fuskarta ta
yi....”
Cikin dariya 'Yar Gwal take maganar tana nuna Rabi'ah da takeji kamar ta fasa ihu.
Ita kuwa Iya Sahu da sai lokacin ta lura da baƙin da suka yi idonta kuma ya sauka a kan
Haleema da ta ƙari sa tana bawa Rabi'ah haƙuri ita ma 'Yar Gwal sai lokacin ta lura ta ita ta
kuma gane ta.
“Laaa Auntyn Birni kece, yaushe kika zo ne?”
Cewar 'Yar Gwal cike da zumuɗi.
Ita kam Iya Sahu sai cewa ta yi.
“Haleema Amare saukar yaushe, ah lale marhaban ku shi go ciki, ashe har kin ƙari so”
Ba musu Haleema taja hannun Rabi'ah suka nufa gidan yayin da 'Yar Gwal da sauran 'Yan
Matan suka bi bayansu.
Da shigarsu gidan kallo ya dawo kan su kasancewar gidan gida ne na gandu akwai mutane da
yawa a ciki da zallar surukutan Iya Sahu ne.
“Rabi'ah Please kiyi haƙuri nasan bakiji daɗin abin da ya faru ba amm...”
“karki damu Haleema ba komai na haƙura”
Rabi'ah ta katse Haleema dake bata haƙuri, da kanta Haleema ta taimaka ma ta ta wanke jikinta
da fuskarta sannan suka tare a Ɗakin Iya Sahu yayin da Haleema ta ware gefe guda ita da Iya
Sahu suna tattaunawa.
Iya Sahu ta ci gaba da faɗin.
“amma Hafsatu ta bani mamaki ban taɓa zaton haka daga gare ta ba yanzu da ta hana kuyi
TIRIRRISHI a gidanta saboda lalacewa shi ne kuma ta iya haɗa ku da ƴarta kuzo nan dan bata
da mutunci”
Iya Sahu ta ƙare maganar cike da takaici dan kuwa bata ji daɗin abin da ƴar nata wato
mahaifiyar Miemie ta yi ba, shi ya sa lokacin da Mahaifiyar Haleema wato Hajiya Larai ta kira ta
tana sanarda ita abin da ƴar uwarta Hafsatu ta yi ma Haleema ya sa Iya Sahu ta ce tun da haka
ne su zo nan ƙauyen suyi, in ya so sai su kwana tun da gobe ne ɗaura aure in ya so bayan
ɗaura auren sai su tafi domin a garin za'a ɗaura Auren kasancewar Mahaifinsu Haleema
Asalinsa ɗan garin ne kafin daga baya suka koma birni shi da Matarsa mahaifiyarsu Haleema
da yaranta.
“karki damu Iya ai ba komai tana gudun kar a lalata ma ta gida ne...”
“wani gida, gidan banza da wofi a kan wani gida zata yi miki haka ta manta uwa ɗaya uba ɗaya
suke da mahaifiyarki...”
Ita dai Haleema shiru ta yi tanaji Iya Sahu ta ci gaba da sababi dan kuwa ranta ya ɓaci sosai
bisa abin da Hafsatu ta yi sai dai ta yi shiru dan kanta sannan Haleema ta bar wurin ta koma
sashen Iya Sahu tana shiga Ɗakin ta hango Miemie ta takure a gefe guda, ajiyar zuciya ta
sauke sannan ta ƙari sa wurin da Miemie take ta zauna kusa da ita tana ɗan murmushi ta ce.
“Miemie wani abun ne ya faru?”
Da sauri Miemie da batasan tazo wurin ba ta kalleta sai kuma ta girgiza kai murya ƙasa-ƙasa ta
ce.
“ba abin da ya faru kawai banji daɗin Abin da Mommy ta yi muku ba ne kuma har ta iya haɗa ni
daku muzo shi ya sa na kasa sakin jikina, Dan Allah Aunty Haleema kiyi haƙuri da halin Mommy
muma kanmu yaranta ba raga mana take ba.”
Miemie ta ƙare maganar murya a raunace.
“karki damu kinji domin ban yi fushi ba na kuma yi ma ta uzuri, kedai ki saki jikinki ki kuma shiga
mutane in ba so kike Rabi'ah ta ci gaba da tonarki ba”
Haleema ta ƙare maganar tana kallon Rabi'ah da shigowarta Ɗakin ke nan daga banɗaki take.
“ai ni bani da abin faɗa Haleema nama ji da abin da ya dameni, Bama wannnan ba gaba ɗaya
tun shigowarmu garin nan na lura sam babu network kuma so nake nayi kira urgency na rasa
yadda zan yi...”
“wuri ɗaya ne ake samun network mai kyau a garin nan in kin yadda zan rakaki amma sai idan
Auntyn Birni ta yadda na shiga cikinku 'YAN TIRIRRISHI nima a yi dani.”
Gaba ɗaya juyawa suka yi suna kallon 'Yar Gwal dake bakin ƙofar ɗakin tana wannan magana.
“lallai kam to kun dai ji Haleema da Rabi'ah shawara ya rage naku mu dai 'yan kallo ne.”
Cewar Zieey tana dariya.
Rabi'ah ta ɗan ja tsaki tana faɗin.
“ai kuwa zaki bushe indai sai kin shigo cikinmu ne zaki kaini inda zan sama network mai
kyau....”
____
Kwana biyu zaku jini shiru ban jin daɗi...
_____
Nainarh KD....
________
MARUBUCIYAR;
1. SARAUNIYAR KYAU, 1,2,3. 700₦
2. TSANTSAR SO 400₦
3. ANEESERH 500₦
4. KIN CUCENI 300₦
5. BA TABBAS 500₦
6. CAPTAIN AYUSHERH 500₦
♡‘YAN TIRIRRISHI!♡
(A Zombie story.....❤️)
2025✔️
Free Book
Posting kullum amma ban da asabar da Lahadi!
Lokacin posting, da dare.
https://chat.whatsapp.com/ICXo7IragdJBkz13G5ex9G
....Masu tambayar mene ne ma'anar kalmar ‘YAN TIRIRRISHI? Ma'anar dai shi ne a taƙaice
kamar a ce ƙawayen Amarya!
____
♡♡♡♡
*_Tafiya suka yi mai nisa daga wuraren da suke duk domin taya ƙawarsu murnar aurenta shi ya
sa suka yarda suka yi kasadar biyota wannan wuri da sunan su ɗin ‘YAN TIRIRRISHI ne sai dai
kwatsam ba tare da sanin dalili ko mafara ba sun tsinci kansu cikin wata iriyar duniya mai cike
da abin tsoro yayin da wata mummunar cuta ta yaɗu ba wai cuta ba ce da a ke samu ta
numfashi ko iska ko wani abu makarancin haka wannan daban ne wasu irin halitta ne na
matattun mutane da suke komawa ZOMBIE da sun cije Mutum cikin lokaci ƙanƙani komai nashi
yake sauyawa shima ya koma ZOMBIE. Ta ya kuke tunanin za su iya kuɓuta daga wannan
masifa? Wai ma mene ne mafarar wannan masifar ne?
Ku biyo alƙalamin NainarhKD domin warware zare da a bawa._*
©Nainarh KD
...3&4
Juyawa 'Yar Gwal ta yi zata bar wurin jin abin da Rabi'ah ta faɗa.
Ganin da gaske tafiyar zatayi kuma a uzurce Rabi'ah take da ta yi wayar ya sa ta ce.
“to ina kuma zakije muna magana bamu gama ba?”
Ba tare da 'Yar Gwal ta juyo ba ta ce, “kedai ba kince baki buƙatar taimakona ba...”
“dawo Please ki kaini na yarda zaki shiga cikin mu shikenan?”
Ƴar Gwal tana dariya ta ce.
“Sosai kuwa.”
Mayafi Rabi'ah ta saka yayin da Ƴar Gwal take sanye da Hijjab da bai wuce iya gwiwa ba suna
shirin fita daga Ɗakin ita ma Suhaima ta miƙe tare da furta.
“Nima zani.”
Ba tare da jira amsawarsu ba ta fice.
“Oh da gaske!”
Rabi'ah da bakinta ba ya shiru ta faɗa tana mai bin ta da wani kallo.
A tare suka fito daga gidan bayan Ƴar Gwal ta yi ma Iya Sahu bayanin wurin da za su je.
Tafiya suka yi mai ɗan nisa amma Ƴar Gwal bata ce an iso ba.
“wai kuwa nace ina zaki kaimu naga sai tafiya muke amma baki ce an kusa ba”
Cewar Rabi'ah dariya Ƴar Gwal ta yi.
“Ai sai mun yi tafiya ta aƙalla kilomita 1 sannan zamu isa yanzu kuma nasan mun yi rabi?”
“Kilomita ɗaya fa?”
“Rabi fa kikace?”
Rabi'ah da Suhaima kowacce ta jefa wa Ƴar Gwal nata tambayar tana zaro ido.
“Eh sosai ma”
“Hmmm bani labari mana akan wannan ƙauyen naku”
“Ai ke kike ganinsa Matsayin ƙauye amma ya mafi wasu state ɗin a wurin mu kawai wurin da
muke rayuwa ne za'a kira da ƙauye amma inda zan kaiku yanzu ku kanku shaku sha mamaki.”
Ƴar Gwal ta bawa Rabi'ah da ta yi maganar amsa.
Jinjina kai Rabi'ah ta yi tana kuma ɗan taɓe baki alamar dai bata gamsu ba sai kuma ta ce.
“koma mene ne zamu gani”
“Sosai kuwa. Wai Amma mana na tambayeku me ya sa naga kunzo a wancan dagargajajjiyar
motar bayan kuma daga birni kuke?”
Rabi'ah ta ɗan keɓe baki tana faɗin.
“Ke dai bari ai lalacewa motocin namu suka yi kamar haɗin baki shi ya sa muka hau wannan
domin suma sun ce nan ƙauyen za su ƙari so shi ne suka rage mana hanya.”
Ƴar Gwal ta jinjina kai cike da gamsuwa dan Akwai taɗi kuma da alama an haɗu ne da an dace
ita ma Rabi'ah ba baya ba.
Ƴar Gwal ta sake faɗin.
“To nifa har yanzu Ban san sunanku ba? Koda yake ke zan iya kiranki da Auntyn Manja dan
kuwa bakiga yadda kikayi kyau ba ɗazu da manja ya zube miki.”
Ƴar Gwal ta ƙare maganar tana gimtse dariya.
“hmm ai kiyi dariya da kyau ƴar nan lokacin ki ne, ni dai Rabi'ah nake wannan kuma gata nan ki
tambaye ta.”
Ta ƙare tana yi ma ta nuni da Suhaima da tana jin duk firar da suke amma bata saka musu baki
ba.
Tun kafin Ƴar Gwal ta ce wani abu Suhaima ta ce.
“Suhaima!”
“Suna mai daɗi.”
Ci gaba da tafiyar suka yi suna ɗan taɓa fira har suka ƙara tafiya mai ɗan nisa sannan suka isa
wurin da Ƴar Gwal take faɗa musu haƙiƙa ganin wurin ma ya fi jin labarin sa domin idan ka
shiga ciki kamar a ce wani Garden ne ko wurin shaƙa tawa na musamman da yake ɗauke da
mutane mabanbanta da zallarsu masu yawon buɗe ido ne ƙaton girma na ban mamaki wurin
yake da shi, ga ɓangarori da dama har da gidan zoo shopping mall ne babu dai abin da babu
Rabi'ah da Suhaima sai sakin baki suka yi suna kallon kyau girma da ƙayatuwar wurin.
“Woww amma fa wurin nan ya yi amma da wani suna a ke kiran Wurin dan nasan ba zai rasa
wani suna da a ka saka masa ba”
Cewar Rabi'ah ita kuwa Suhaima sai cewa ta yi.
“Ma sha Allah amma wurin ya tafi dani I love it, can kuma ina ne nake hangowa kamar Lab na
bincike?”
Ƴar Gwal tana dariya cike da murnar yabon da suke yi ma wurin ta ce.
“Ai wannan ma kaɗan kuka gani sunan wurin yana da yawa wasu na kiransa da Kasuwar
Zamani wasu kuma su ce New World sai dai an fi saninsa da New World ɗin musamman masu
zuwa yawon buɗe ido wancan kuma Lab ne da yake mallakin wani Bature ko mene ne ma
sunan Lab ɗin....”
“Scientific Research Lab!”
Rabi'ah da Suhaima suka karanta sunan dake jikin ƙaton allon dake kafe saman dogon ginin na
Lab ɗin.
“Eh tabbas haka ne kuwa. Yawwa tohm anan zaku sama network mai kyau da ƙarfi sai kuyi
wayar da zakuyi.”
Cewar Ƴar Gwal.
Gyara Tsayuwarta Rabi'ah ta yi tana fuskantar Ƴar Gwal ta ce.
“Har yanzu yana biye damu ko?”
Tambayar da ta yi ya sa Suhaima da ta ciro wayarta tana ɗan latsawa ta dubeta da mamaki.
Ita kuwa Ƴar Gwal da dabara ta ɗan leƙa ta bayan Rabi'ah hakan ya sa Suhaima kallon wurin
da take duba.
“Eh amma ya juya baya, wai dama mu yake bi tun ɗazu fa na lura da shi.”
Ƴar Gwal ta faɗa tana dariya.
Ta ƙara da faɗin.
“Kin san shi ne Aunty Rabi'ah?”
Rabi'ah bata amsa ma ta ba sai juyawa da ta yi tare da furta.
“ina zuwa”
Sannan ta ƙari sa wurin Matashin da ya ɗan juya baya ai kuwa juyowar da zai yi sai ganin ta ya
yi a gabansa. Huci ya fitar domin bai yi tazo ba dan ma namijin gaske ne shi ya sa bai nuna
alamun tsoro ba.
“Wato nan ɗin ma sai da ta saka ka biyoni ko?”
“Hmmm ai kya bari na ja iska da kyau so kike zuciyata ta buga to da na firgita fa?”
Ya faɗa yana ƙoƙarin ba garar da maganarta.
“Hey Uncle!”
Ta faɗa da ƙarfi da ƙoƙarin danne ɓacin ranta.
“What!?”
Shima ya faɗa yana dubanta da fusatattun idanunsa.
Ajiyar zuciya ta ɗan sauke tana sassauta murya ta ce.
“Uncle Habib Please kar muyi haka da kai Fisabilillah a ce nan ɗin ma ba za'a barni na sha iska
ba sai da ta saka ka biyoni?”
“Ki nutsu Rabi'ah ba nazo nan domin takura miki ba ne i will patiently wait until zuwa gobe da
zaku yi kuma ku gama abin da ya kawo ku sannan mu juya zuwa Lagos amma idan kika bini a
yadda naso ke nan a ka sin haka kuma ko kin so ko kin ƙi ta ƙarfin tsiya kuma yanzu zan koma
dake Lagos kije ki zana jarabawar da kika gudo domin ta”
Shiru Rabi'ah ta yi tana ɗan cizon Lips ɗin ta. Sai kuma ta juya tana duban su Ƴar Gwal da
hankalinsu yake kanta sai ta sake mayar da dubanta kansa ta ce.
“Yanzu ya kake so a yi?”
Ta faɗa rai a ɓace.
“Ko ke fa Good Girl yanzu kika dawo kan hanya. Yanzu dai kije ga ƴan uwan tafiyarki suna jiran
ki kuma wannan tafiyar da kuka yi a ƙasa ta yi nisa su zo na mayar da ku a mota.”
Bata ce masa komai ba ta juya zuwa wurinsu Ƴar Gwal.
_______
Da Dare!
“Aunty Rabi'ah wai wanene mutumin ɗazu ne kin san kuwa har yanzu yana nan cikin Anguwan
ya Parker Motarsa yana ciki amma fa kyakkyawa ne hala saurayinki ne?”
Ƴar Gwal ta ƙare maganar cikin raɗa raɗa tana duban Rabi'ah da ta yi nisa da danna waya.
Shiru Rabi'ah ta ɗan yi tana tuna yadda suka kwashe ɗazu shi ne ya dawo da su ba tare da ta yi
wayar da ta yi niyya ba dama taso ta kira Mahafiyarta ne ta sanar da ita da kar ma ta damu in
taga bata nan kuma tana a Safe Place sai dai ganinsa da ta yi ya sa ta fasa dan tasan za'ayi
haka.
“Kyaleshi kinji idan ya gaji zai tafi”
Ta faɗa ba tare da ta dubi Ƴar Gwal ɗin ba.
Ya mutsa fuska Ƴar Gwal ta yi dan ba haka taso ji ba sai ta ƙara faɗin.
“To baki ce saurayinki ba ne hala dai saurayin naki ne?”
Wannan karon dubanta Rabi'ah ta yi tana sauke numfashi ta ce.
“Ƴar Gwal right? What's your Intention hmmph? to ba saurayina ba ne Uncle ɗina ne”
Bata rufe baki ba taga Ƴar Gwal ta yi wani zaman daɓas tana ɗaura tafin hannunta saman
fuskarta irin maganar ba ƙaramin daɗi ya yi ma ta ba.
“And kar ma ki yi wani tunani daban.”
“Saboda me Aunty Rabi'a's?”
Ƴar Gwal ta tambaya tana wani zaro ido. Har da wani lauya ma ta suna zuwa Rabi'a's.
“Saboda shi