Showing 51001 words to 54000 words out of 62795 words

Chapter 18 - Auren Huce Haushi Book 3 Complete By arewahausanovels.com.ng.pdf

yanzu ta koma ga

Allah Bata da sauran bakin ciki saboda Allah maji rokon bayinsa ya amsa Mata addu'arta wadda
take yinda babu dare babu Rana, saukar Al'quran ma anyi Mata babu adadi Tunda abin ya faru
tana addu'ar Allah ya tona asirin duk Mai Hannu a cikin Lamarin, sannan ta juya ta dubi Abbie
tana fadin daga yau kwanan gidan Nan ya qare min abinda nake jira kenan Daman gaskiyar tayi
halinta, to Kuma yau Alhamdulillahi gaskiya tayi halinta Dan Haka Nima hanya kasan fita ta. Ta
juya ta fice itama, abinda ya tada hankalin Abbaie din kenan ya bita da sauri ya fice shima, Dan
Tunda yake a zamanzu magana makanciyarta haka Bata tab'a hadasu ba. "To fa kinji dalilin
Daya mayar Ammina niger. Hakan ne ya Kara harzikani saboda anyi min rashin adalci, lokacin
fa Sameer yazo min da bayanin na jinjinawa Batool matuk'a yarinyar tayi min bazata Sosai, Abu
kamar Wasa Duk Wanda sukabi Ammi babu Wanda ta yarda ta biyo da suka Fara rinjar Hajja
ne bayan zuwan Hajiya Inna Ammi ta dawo Damagaram gurin Yayanta kafin ya Yanke Mata
hukunci dawowa sokoto dole, hummm Amma fa Ina biyiye da duk motsin Ammina Dan Yanke
huldar da nayi ta zahiri ce Amma a badini Ina cikin duka lamuranta Dan Ina zuwa Yamai duk
lokacin danaso ganinta sai dai su nemeni su rasa a can garin, ganin nesa ta tazo kusa yasa
nayi zamana a garin ku dankwali yaja hula, sauran bayanai da yawa Kuma sirrina ne. Kinji
kadan daga abinda ya sameni Dan ma na takaita Miki wasu abubuwan da uncle saminu ya
ringa nuna min ke dai abar kaza cikin gashinta kawai, idan ana cin B'aure ba'a tona cikinsa
Kuma idan ana sallah ba'a magana, wani sanin sirrin cikin ciki sai dai hanji kawai, Dan haka ban
Hana ki gaisa da zuri'ar uncle saminu ba Amma na yanke Hulda dasu har abada kamar yanda
mahaifina ya cire Shi a cikin duk sabgoginsa sai dai abinda ba'a rasa ba Dan masu iya magana
na cewa hannunka baya ribewa ka yanke kayar,to kinji summary na abinda ya faru Dani ya
Zama sanadin da yasa na fito a wancan lokacin sai dai ni Alhamdulillahi hakan wata Rahama ce
daga Allah.
Jinjina abin Zahra take a cikin zuciyarta ace duk wannan masifa ta dumfari mutum Daya ai sai
Wanda Allah ya bawa karfin zuciya da imani ace duk girman family Kamar wannan duk sun
maka nak'i Sai mutum biyu kawai lallai anga taskun rayuwa.
A hankali ta sauke numfashi tana kallonsa Banda tasan baya son kuka ba da wallahi saita
matse yanda zuciyarta ke Mata zafi, Dan ji tayi ta tsani safnar da yayarta tsana Mai zafi wadda
ita dai ko Mama da Salma da suka nuna Mata qin jini bataji su kamar wadannan ba.
"Me amorrrr....".
Ta fada a hankali.
Gyara Mata kwanciya yayi a cinyarsa Yana kallonta cikin Ido.
"Umhummm.... Fadi ya akayi?".
"Allah ya Kara maka juriya da hakuri kaga jarabawa ta rayuwa, lallai Ubangiyi yayi gaskiya da
yace shin bazan jarabceku ba?. Amma taka dai Kam sai Mai karfin Imani Dan Mai karamar
kwakwalwa sai kansa ya buga koya fada wata harkar Tunda babu ni'imar da Ubangiji Bai maka
ba, Allah ya hore maka amma ya baka kariya daga fadawa mugunyar rayuwa, ya tsare min
kayana Alhamdulillahi Allah abin godiya".
Dagota yayi daga kwancen ya kafa Mata idanunsa da suke razanata a wancen lokacin Wanda
Kuma suke tsumata a yanzu.
"Kice Kayan naki ne ke kadai, to ya za'ayi da sauran dake kokowar shigowa Kuma?".
Wani warrrr tayi masa da sexy din ta Wanda wani irin Abu yake walainiya a cikinsu.
"Ai dagani babu wata a yanzu dai saina cinye na sude kayana tas sai dai su samu sudin

kwano".
Rike Baki Yayi Yana wata dariya kasa-kasa.
"Kai yarinyar nan yaushe kikayi Baki haka? "Wato kin Fara gane garin ko?".
Dariyarta Mai shagaltar dashi ta Fara tana nuna shi da hannu.
"Ni Kuma wane garin na Fara ganewa?".
Ba zato yayi Mata daukar jarirai yana fad'in Bari na nuna Miki garin".


*****Tunda su Ammah suka shiga garin Miya kukan Salma ya tsananta tamkar zata shide,
Banda aikin lallashi babu Abinda su Ammah keyi daga karshe ne Aunty Hassana ta rufeta da
fada ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shi dai malam Bala ko tari Bai kubce Masa ba Dan
yasan sakayyar Allah ce kawai ta sauka akan Mama da 'ya'yan ta Dan dashi wani Maci Amana
ne da Allah kadai yasan abinda suka shuka shida ita to tun tayin farko ta taka Mata birki da
barazanar sanar da Alhajin shine abinda ya kawo basa ga maciji a tsakaninsu.
Ba laifi gidansu Anas din da nasu rufin asirin sai dai da alama rayuwa ake ta babu kwaba a
gidan Dan yanda kannensa Mata suka ringa yatsina fuska ga babu tarbiyya Kota sisin kwabo a
gidan saboda da kyar kanwarsa Haulatu ta bayar da key din dakinta a sauki Baki cewa tayi ita
da kayanta kada a Bata mata, sai wani kanin Anas din yayi Mata Jan Ido sannan ta bada, aka
bude suka shiga inda aka kawo musu Abinci ba laifi ta Nan sun yaba, amma dai uwar tasa
basuga fuska a gurinta ba, sun dai gaisa shima ganinsu Ammah da tayi ba karya sun jiku da
naira gayu ya zauna dole ta mayar da makaman yakinta ta Bari idan sun wuce ta baje kolin
abinda ta tanadarwa daga salmar har Anas din tunda 'yar kanwarta yake aure Bai Kuma fada
Mata ze auro Salma ba saida iyayensa maza zasu tafi daurin auren suka shigo suka fada Mata
Tunda Babansu ya rasu.
A dofane suka wayi gari inda tun karfe bakwai motar Kayan ta sauka a Miya Dan tun dare Abba
yasa akayi lodin Kayan abinda babu yasa su sahura da makotansu suka shiga stores suka
sawo, Kayan toye-toye ma gidan masu yin na sayarwa akaje aka sawo saboda Basu da
matsalarsu a unguwar da Kuma can bakin kasuwa. Kafin azzuhur gida ya kankama na amarya, Ammah ta saka Salma tayi wanka wadda har
lokacin kuka takeyi ga azababban Zazzabi Daya rufeta, a irin kayan da aka dinka na Zahra
Wanda magaji ze tafi dasu Ammah ta debo Mata kala kusan goma ta taho Mata dasu Tunda
babu Abinda aka tanada bagatatan abun yazo. Su Ammah sun Kara Kai Salma gurin surikarta sun bada Amanarta sannan suka mikata dakinta
tare da yayar Baban Ana's din, tana gunjin kuka suka barota Dan abinda Bata tab'a kawowa
bane ko cikin mafarki akayi Mata taci burin auren miji na kece raini ta shiryawa kanta rayuwar
Jin Dadi da walwala Amma sai gashi ta Kare a auren yaron kamfanin nefa Zama a inda ko cikin
hasashe Bata tab'a kawowa ba, haka su Aunty Hassana suka wuce.
Saukinta Daya gidan da abunda aka zuba Mata ze kankaro Mata mutunci ko banza ta Nan
fannin dai babu raini.


***

A cikin sati daya Zahra da Mahmud sunyi wata irin shak'uwa ta ban mamaki,Dan Daya ji yake
baze iya rayuwa ba Saida dayan Zahra ta Zama 'yar gari sai tsula shagwaba take Masa shi
Kuma duk ya susuce a kanta, ga wani irin fresh da sukayi dan dole idan ka kallesu ka kara,
Saida hankalinsa ya nutsu sannan ya zauna dasu Salis da Bashir ya nemi shawararsu akan
idan suna ra'ayin aiki dashi to suyi Shawara da gida akan Nan gida suke son Zama suyi aikin ko
a waje sannan ya bawa kowa gida a acan Azaren Saida ya fada musu inda gidajen suke Salis
yayi murmushi Shima Mahmud din yayi wani Abu suka tuna, lokacin da Mahmud yaja Salis din
sukaje ana yiwa gidajen pop Salis ke tambayar ko gidan waye haka sai Mahmud din ke fadin na
wani abokin Sameer ne yasa shi ya dube Masa har yake cewa Salis din ko gidan ya burgeka ne
Naga kamar kana sonsa? Dariya lokacin Salis din yayi Yana fadin wa zeba Dan rogo rumfa? ai
irin wannan gidajen sai wadanda sukaci suka tada Kai. Dariya kawai lokacin Mahmud yayi baice
komai ba kawai dai yace Masa ya Taya shi a duba abinda baiyi ba Mai gidan ne yace ayi hakan
Nan Salis din ya zage Yana ta fadin Nan kaza ya kamata ayi nan ayi kaza haka suka zagaye
gidan har suka Gama bada gyaran, haka suka shiga dayan ma aka rubuta komai, to sai yanzu
da yake fadar inda gidajen suka Salis ta tuna da abun, sunyi godiya kamar su Ari Baki Dan Dadi
Bashir baisan lokacin da hawaye ya zubo masa sai gani sukayi Yana share hawaye, saboda
Tunda ya Gama Karatu Bai Sami aiki ba gashi Dan Mai karamin karfi kullum Yana yawo neman
aiki sauda yawa Mahmud Kan fada Masa yayi hakuri da lokaci, in dai aiki ne Saiya zab'a, a
lokacin jinsa kawai yake Ashe da gaske yakeyi saiya zaba din tunda gashi ya Basu options na
zabar Ina suke da muradin yin aikin.
Dariya sosai Mahmud ya ringa yiwa Bashir ganin yanda yake shafe Ido kamar Mace.
"Haba bash meye haka be strong mana Dan Allah, kuka kuma? To in banyi muku ba suwaye
Zan yiwa kun riqeni Amana lokacin da bakusan daga wace duniyar nake ba, kun ciyar Dani kun
dinka mun suturar sakawa, kun bani kudin da kuka nema da karfin jikinku, kun tsaya a gurin
jinyata lokacin dasu Habib ke yinta ga abin Hawa an sakar min babu shamaki duk inda zani, an
bani Mata kunyi uwa kunyi makarbiya gurin hidima da jikinku da aljihunku to ni kuwa ai bani da
abinda Zan biyaku dashi sai dai nace Ubangiji ya biyaku da madaukaliyar Aljanna wallahi tuni
na cireku daga abokai kun zamar min 'yan uwa yanzu ga wannan" ya mikawa Bashir Daya fi
kusanci dashi E.passport ne yace su saurari visa Sameer ze kawo musu ta umarar Azumin nan
Mai kusantowa, yace Kuma kowa ya duba akwai sako a wayarsa, sunyi tsaraba ya Kuma fada
musu tickets dinsu na zuwa Bauchi Yana hannun Sameer, bakin godiyar ma rasawa sukayi Dan
wata kyautar tafi gaban godiya, Dan ya gigita musu lissafi ba Dan kadan ba.
Sameer ne ya shigo da sallama lokacin kwanansa biyu da dawowa daga Egypt gurinsu Mama
Dan Saida akayi Mata aiki sannan ya juyo ya barosu a can, Mama tayi kuka tayi kuka akan
wautar datayi a baya na nuna hassada da ganin kyashin yarinya marainiyar Allah wadda aka
mutu aka Bari ko kanta Bata sani ba Amma shedan yayi Mata katutu a zuciya ta dunga
kulle-kullen mugun Abu Tunda masu dubanta suka barbasa Mata yarinyar tana tare da wata irin
sa'ar rayuwa duk sai ta rude tana ganin ta Yaya hakan ze faru gata Mai kyau na ban mamaki
sannan ace sa'arma tatace tun daga lokacin zuciyarta Bata huta ba, to gashi Alkawarin Allah ya
tabbata gata a gadon asibiti a wata k'asar tare da ciwon zuciya Wanda bakin ciki da hassada
sukayi sanadinsa, ga Kuma wadda take abun a kanta taje inda Ubangiji ya nufa taje din,tunda
Alkawarin Allah baya tashi ga shi Kuma mijin da taketa kangewa kada yazo gurinta shine ya
Zama silar samun waraka ga ciwonta, ga mijinta Tunda sukazo bai Kira ba ya bawa banza

ajiyarta Bata Kara Jin ko duriyarsa ba tun lokacin da yaje sokoto tana barcin Allura batasan yaje
ba,yau ga dan 'yar uwarta Mai ingizata tayi komai Dan Hana Allah ikonsa itace Dan cikinta ya
yiwa yarinyar ta cikin shege.
Da kukanta share-share ta ringa fadawa Sameer ya nemar Mata yafiyar Zahra akan abubuwan
data yi Mata.
Kusa da Salis sameer ya zauna ya gaishe da Mahmud sannan suka gaisa dasu Salis din,
sannan ya dauko musu tickets dinsu na jirgin Sha biyu da rabi na Rana, godiyar dai suka Kara
yi musu har Mahmud na fadin "wallahi idan ya Kara Jin godiyar na zasu bata.

**

Ranar da suka cika kwana goma sha biyu Mahmud tun dare ya fadawa Zahra ta shirya da safe
ze kaita gidan Ammi shi kuma zeje Lagos wani aiki, Bai barta tayi barcin kirki ba a Daren,dan
daga baya ma cewa yayi ta shirya ta raka shi suje su wuni su dawo, da kyar ta samu ta
lallabashi da kalamai sannan ya hakura Amma Saida ya Kara rage tafi. Tun asuba zahra ta Kira Aunty zilai suka Fara aikin dabun kaji dasu cake sai da sauran
tarkacen snacks Tunda su duka gwanayene kafin takwas da rabi sun Gama hada har breakfast,
sama Zahra ta koma lokacin Mahmud ma ya farka Dan nine thirty flight dinsu ze tashi daga
sokoto zuwa Lagos. Tare suka fito sukayi break sannan yace ta dauko gyalenta su tafi ya ajeta
ya wuce, fada Masa tayi tare zasu tafi dasu Aunty zilai, waya ya yiwa zayyan ya saka wani ya
kaisu Aunty zilai can family house nasu, lokacin da akace su fito sai gani yayi ana ta fitowa da
manyan warmers ana sakawa a boot din mota, Bai nemi Jin abasin menene ba itama Bata fada
masa ba.
Su suka Fara yin gaba sannan suma suka fice daga gidan, sunzo wucewa ta kofar gidansu Dr
Haseenah ya Dan shafo cinyarta, tsuke fuska tayi tasan abinda yake nufi.
"Komu shiga ku gaisa tana garin har yanzu Tunda Nima Ina garin kinsan lokacin da Ina Nan ai a
Nan take aiki Saida nabar garin ta koma Kano da aiki Tunda daman a kanon aka riketa kuma
masu fada aji ne, jiya da har zatazo ku gaisa sai tace sauri takeyi gurina kawai tazo wani
lokacin ida ta dawo ta shigo ku gaisa". Hade Rai tayi ta hade gabas da yamma tayi kicin-kicin duk yanda yaso ta kulashi tayi banza
dashi har sukaje gidan.
Abbie baya k'asar yaje Benin republic akan wasu Kaya nasa da aka rike a can.
Direct part din Ammi suka nufa duk yanda yaso ta saki ranta abun ya faskara Dan da gaske ya
Bata Mata rai ita fa ta tsani matar Nan ba kadan ba shi Kuma ya kasa ganewa.
Yana tsayawa tayi wuf ta fice Bata tsaya ya fito ba ta wuce Abinta tana ayyana itama ai
Amminta ce bazata tsaya shi ba,Amma kafin takai ga kofar parlourn ya cimmata.
"Ke meya faru Wai kike ta hade min Rai haka?".kauda Kai tayi tana jin zuciyar na Mata zafi.
Janyota yayi ya rungumeta a Nan da sauri ta dago tana rarraba idanu.
"Dan Allah ka sakeni kada wani yazo ya ganmu a haka wallahi ba komai,Dan Allah ka Bari kada
ace bamu da kunya plssss...."
"Baki San anyi min tambarinta ba a gidan Nan wannan ai ba wani Abu bane,nida kace nayi
abun a gidan Nan ko kin manta?".
"Ai sharri ne wancen, wannan Kuma gamu in reality ne".

"To shine me? Ai ba haram bane ko.....,"
Bai karasa ba yaji alamun za'a bude kofar da sauri ya saketa Dan bazeso kannensa ko Ammi
su gansu a haka ba,ko maid din Ammin sai girma ya Fadi.
Sahalatu ce 'yar Babban yayansu Abdallah da Afnan da hannunta suka fito, ai yarinyar na ganin
Zahra ta Fara zillo tana dariya, itama zahrar dariya tayi Mata ta nufesu da sauri ta karbeta daga
hannun sahalatun tayi wuf ta shige tana amsa gaisawar yarinyar.
Ammi ce dasu Aunty Aishat a parlourn farkon sai Aunty zilai daga gefe a zaune bintar dai Bata
gurin Zahra batayi mamaki ba Tunda ita 'yar gida ce, gaba Daya suka amsa sallamarta cikin
nutsuwa Zahra ta karasa kusa da Ammin ta tsuguna har kasa tace "Ammy Ina kwana?".
Ammi wadda bakinta yaki rufuwa saboda farin ciki ta amsa Mata "Lafiya kalau Zahra ya gidan
naku?".
A kunyace ta amsa "lafiya kalau Ammy".
Ammin sai hamdala take yiwa Allah Daya azurta danta da irin wannan matar, a Nan Kan carpet
ta zauna duk yanda Ammi tayi akan ta tashi ta zauna kiyawa tayi sai hakuri Ammin tayi.
Zahra tayi mamakin Ina Kuma ya tsaya Bai shigo ba? Saida ta Jima da Zama sannan ya shigo
ta baya Yana amsa waya taji Yana fadin "ka sayi ticket din online yanzu" Tunda ya shigo
Ammin taga ya wani Kara girma da haske ga cikar Kamala da taga yayi da gani ya samu
kwanciyar hankali. Kusa da Ammin ya zauna Yana gaisheta suka gaisa da Aishat wannan su batool suka gaishe
shi, tashi su batool sukayi suka koma wani falon Aunty zilai ma kitchen ta nufa Tunda ta Saba
tana Taya masu aikin aiki a Dan zaman da tayi kafin ta koma gidan Zahra.
Parlourn ya rage daga Ammi da Yan biyunta sai Zahra da Afnan hira suka Fara a junan su
Zahra na Zaune tana yiwa Afnan wasa, hira Mahmud yakeyi Amma 100% hankalinsa na Kan
Zahra har dai Aishat ta gaji ta jefa masa tambayar data bashi mamaki.
"Waini bros ko dai laifi kayiwa madam ne Naga ka kasa nutsuwa sai kafeta da Ido kakeyi irin na
neman sulhu din Nan".
Dan murmushi yayi Yana Dan shafa gefen sajen fuskarsa.
"Ko Daya kawai burguni sukayi ita da Afnan yanda suke kaunar juna tamkar sun shekara da
sanin juna, ki karbeta ma tafiya zamuyi".
A tare Zahra da Aunty Aishat suka kalleshi Bai kalli zahrar ba Aishat ya bawa attention dinsa ..
"Zuwa Ina kuma mobile?".
"Lagos zamu".
Ai Zahra Bata San lokacin da bakinta ya subuce ba tace.
"Kaiiii..meu amor bafa haka mukayi da kaiba, kace fa wuni zamuyi a Nan Kuma yanzu zaka ce
wai tare zamu Dan Allah ka barni na zauna a Nan din plssss...."
Saida ta Kai Aya ta Farga da inda suke sauri tayi ya rufe fuska da gyalen dake jikinta.
Yau taga ta kanta ita wace iriya ce.
Dan murmushi Ammi tayi kawai tasan da wata a kasa saita basar Aishat ce ta shiga maganar
"a'a kuyi tafiyarku kawai ba wani wunin da zakiyi Tunda kukazo kafa ya kafa ai nasan tafiyarku
Daya idan yayi niyyar ki wunin ai ke kadai zakizo amma fa su binta suka Fara zuwa".
Sai lokacin Ammi ta tuna an kawo musu abubuwa ganinsu ya shagaltar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login