Showing 1 words to 3000 words out of 150998 words
COMPILED BY
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE..
Saturday/03/02/2018_
*芦禄芦禄芦禄SAIFUDDEEN芦禄芦禄芦禄*
```By Billy giro馃槉```
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
```Bismillahi rahamanir rahim```.
_Zan fara da sunan Allah ina kuma fatar na kammala da yardar shi_.
_Allah yasa haka amin._
*芦禄Page芦禄 1*
_Kuka yake sosai gurfane a gun wani kabari,wanda yanayin kukan nasa ze tabbatar maka
cewa haqiqa yayi babban rashi,musamman yanda idanuwan sa suka kumbura sukayi wani irin
jajur ta yanda duk wanda ya kalle sa dole se nashi idanun sun ciko da qwallah sbd tausayi_.
_A nn gurfanen da yake ne wani yazo shima se kukan yake ya tada shi ya rungume shi sosai a
jikin sa,se rarrashin sa yake yana bashi magana,amma sam ya kasa daina kukan har se da yaja
shi suka fita daga maqabartar_.
*Baya Kafin faruwar hakan*.
芦芦禄禄禄芦禄禄
Tsaye yake gaban mirror d'aure da farin towel a qugunsa yana taje sumar kanshi,wanda kallo
d'aya zaka mishi kasan cewa hadadden guy ne shi,first class da sam bai aje kanshi kusa ba.
Sosai yake matuqar ji da kanshi sbd Allah yayi shi me tsananin kyau tamkar shi yayi kan shi.
Shiyasa sosai kyawawan en mata ke rubibi akan sa amma sam baya kula su,mace d'aya kawai
yake kulawa wato "Sophie"wata classmate d'isshi da sukayi karatu tare a London wacce yanzu
haka tana nn Nigeria ta biyoshi.
Bayan ya gama taje sumar kanshi ne ya tafi da cumb d'in yana qara kwantar da sajen fuskar
shi dake kwance luf kan farar fatar shi tas wacce tamkar ka kwanta jini ya fito.
Sai da ya feshe jikin sa da body spray snn ya nufi kan bed inda ya ajiye kayan sawar shi da ya
ciro,ya zauna tare da cire towel d'in jikinsa ya cillar gefe,ya janyo guntun wandon sa fari qal ya
saka snn ya saka dogon wandon sa na suit silk fari,rigar ciki baqa yayi stocking da black belt,ya
saka necktie fari,sucks baqaqe da takalmi baqaqe snn ya saka er samar shi fara,ya fesa turare
kana ya d'auki briefcase d'issa ya fito bai zarce koina ba se 6angaren iyayen shi.
Ya sami mahaifiyar tashi ta fito daga kitchen tana jera breakfast kan dinning.
A natse ya gaida ta fuskar sa ba yabo ba fallasa,byn ta amsa yace am going.
Da sauri ta kalle shi tace"breakfast fa gashi har na kammala had'a komai ka d'an tsaya mana
kaci ko kad'an ne"
Yace"No umma ina sauri ne"
Ba tare da ya jira me zata ce ba yasa qafa ya fita abin shi.
Ta bisa da kallo kawai tana mamakin yau ko Abban sa bai je ya gaida ba ko lafiya,nan se ga
Abban na shi ya fito cikin shirin sa tsaf na fita,ta kalle sa tace kaddai kaima fita zakayi hakan nn
baza ka ci komai ba kmr yanda saifuddeen ya fita.
Komai be ce da ita ba se d'an murmushi yayi had'e da girgiza kansa a lokacin da yaji tashin
motar saifuddeen,kana ya qarasa gun dinning yaja kujera ya zauna yana fad'in"Halan me
saifuddeen yace maki da zai fita?
Umma da ta janyo plate zata fara serving nashi tace"ce min yayi sauri yake"
Abba yace"haka dai ya gaya miki amma ba wani sauri da yake da akwai dalilin da yasa baya
so mu had'u"
Umma tace"shi saifuddeen d'in?
Yace"shi d'in yaron da ko kad'an baya so in masa zancen aure amma jiya se gashi na ganshi
da wata baturiya a office d'inshi yanda na gansu abun takaici matsayin sa na musulmi yana biye
mata kan lalaci irin nasu na turawa.
Numfashi umma ta fitar snn ta zauna a hankli tana kallon Abba wacce da alama tasan
saifuddeen na tare da Sophie ba yau ba amma se tace "kana nufin yanzu saifuddeen duk jiji da
kanshi yana kula en mata.
Abba yace"Hm Mamn yusra knn ae duk namijin da kika ga baya kula mace to ba lafiyar sa
qalau ba,amma irin kulawar da ake so shine namiji ya nemi mace da son aure ba irin shirritar da
naga saifuddeen ya d'auko da wacce sam aure bazai ta6a shiga a tsakanin su ba,dan haka wlh
sam bazan yarje masa wnn shashan cin ba,ni aure zan masa ko yana so ko baya so! Yana kaiwa nn ya fara cin abincin da umma ta zuba mishi.
Umma dake kallon sa tayi shiru bata sake cewa komai ba,se abinci ta zubawa kanta ta fara ci
cike da tunanin yanda zata shawo kan saifuddeen ya rabu da Sophie,dan ko kad'an bata son
huld'ar sa da ita shiyasa ma bata so Abba yasan da ita ba.
Se da yamma liqis saifuddeen ya sake dawowa 6angaren su umma,sanye da qananun kaya a
jikin sa,rigar fara ce tas me guntun hannu,rubutun jikinta baqi ne manya da aka rubuta *Being
human*,wandon kuma fari ne tas tree quarter wanda duk da cewa fuskar sa ba annuri amma
yayi matuqar kyau se qamshi ke fita a jikin shi sbd mutum ne shi da sam baya wasa da turare
yana son qamshi sosai a rayuwar shi,shiyasa jinin sa ya had'u da Sophie dan haka take itama
ko yaushe cikin qamshi take. Umma dake zaune kan doguwar kujera hannun ta riqe da littafin addu'o'i ta kafe idon ta a
kansa har ya qaraso ya zauna a kusa da kujerar da take zaune,still fuskar nn tasa ba annuri ya
kalle ta yace"umma i will back to England"
Umma tace"meyasa?
Yace"kmr yanda suke buqata"
Tace"kmr ya u mean zaka kar6i tayin su ka koma can da aiki ka bar asibitin mahaifinka
saifuddeen?
Yace"eh"
Da mamaki tace"why?
Muryar sa a hnkli can ciki yace"Abba yasa min ido umma ni kuma bana so"
Umma ta numfasa tace"saifuddeen knn idan Abban ka bai sa ido akan rayuwar ka ba to wa
kake so ya kula da rayuwar ka ya nuna maka hanyar da ta dace kabi iye"
Shiru yayi kmr beji me tace ba taci gaba da cewa"saifuddeen kaifa musulmi ne bai kamata dan
kayi karatu a qasar turawa ba kazo kana yin irin halayen su marassa kyau snn kuma a maka
magana kaji haushi,ka sani fa ko kad'an Abban ka bai ji dad'in yanda ya same ka office kaida
Sophie ba dan nasan ba makawa ita ce ya ganku tare tunda yace min baturiya. A qufule yayi d'an guntun tsaki yace"umma bafa wani abu ya ganmu munayi ba fa,just ya samu
tana kan laps d'ina muna magana shine kawai se ya balbale ni da fad'a wai kar ya qara gani na
da ita,wat kind of this umma.
Umma dake kallon sa tace"Hum Saifuddeen yanzu kai a ganinka ba komai bane Abbanka ya
ganka da mace kan qafafuwan ka,saif ae ko matar ka ce dole ka d'anji kunya bare Sophie
wacce.....dafe kansa yayi sbd mgnr ta ishe shi,yace"umma plz a daina zancen nn haka is
enough ni yunwa nake ji tun safe banci komai ba" Ba yanda umma ta iya se ce masa tayi olryt me kake so kaci?
Yace"abu me d'an nauyi da zan iya ci.
Nan umma ta tashi a hnkli taje gun dinning wacce dama ta kammala girkin ta na yamma,ta
d'ebo masa,tuwon semo ne da miyar agusi wacce taji naman rago sosai tayi kyau har ta gaji se
qamshi ke tashi,ta had'o mishi ruwa da lemu ta kawo mishi ya kar6a tare da mata godiya snn ya
fara ci. 禄禄禄
Da dare umma da Abba suna zaune a falo suna kallon labarai,Abba ne saman kujera umma
kuma tana zaune a qasa manne jikin kujerar yayinda wata yarinya da bazata wuce shekara
biyar ba wato wacce ake kira da yusra tana kwance kan qafafuwan ta tana bacci,umma na fmn
shafa jikinta a hankli. Abba yayi gyaran murya yana me kallon umma yace"Maman yusra wata magana nake so muyi"
Umma ta kalle sa tace"tou Allah yasa ba wani abu bane Alhj"
Yace"ba wani abu bane so nake ki amince na had'a auren saifuddeen da zarah.
Umma ta numfasa tace"cabd'i Saifuddeen da zarah fa kace Alhj?
Yace"Eh haka nace ko anyiwa zarah miji ne ban sani ba?
Aa ae kasan baza ma a fara ba baka ji ba amma dai kasan sam saifuddeen bazai ta6a yarda
ya auri zarah ba ko.
Abba yace"Zarah bata da wani aibu da saifuddeen zai ce bazai so ta ba tunda gwargwado dei
tayi karatu har gaba da primary"
To Alhj kasan fa zarah gabad'aya a qauya tayi rayuwar ta zuwan ta birni jefi jefi ne.
Abba yace"ae shiyasa nace ta dawo nn da zama dmn ki wayar mata da kai,na kuma sata a
university taci gaba da karatu sannu sannu har su zo su saba ita da saifuddeen kafin nasa
lokacin auren su.
Umma tace"gaskiya Alhj kawai da ka bashi za6i ya kawo wacce yake so dan bana tunanin
saifuddeen ze ta6a sakarwa zarah fuska har sukai ga sabawa da juna bare har ace aure ya
shigo tsakanin su abun da kmr wuya.
Yace"Maman yusra ba wani za6i da zan bashi Zarah nake so ya aura,dan haka abunda kawai
nake so dake shine gobe ki shirya kije Rimin dako kizo da Zarah in yaso se kiyiwa inna bayanin
komai nasan in taji baza ta qi ba inshaa Allah,ban sani ba ko dai ke ba kya son Zarah ta auri
saifuddeen ne. Umma tace"ba haka bane Alhj ae Zarah in taji nasan ba qaramin farin ciki zatayi ba dan dai
sosai tana son zaman birni,a duk lokacinda naje ji take kmr ta biyoni.
Yace"to ai duk kece tun tana qarama ba yanda banyi ba kan tazo nn tare damu ta zauna kika
qi alhali yarinya naso.
D'an murmushi umma tayi tace"uhm Alhj knn ae de yanzu komai ya wuce Allah ya nuna mana
gobe lafiya se inje inzo da ita d'in"
D'auke da murmushi Abba yace "Amin ko ke fah".
[11:13AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Sunday/04/03/2018_ *芦禄禄芦芦禄
SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 2*
Washe gari tun da safe guraren qarfe 7 na safe umma ta kammala shirin tafiyar ta ita da
yusra,driver yaja su suka tafi garin Rimin dako wato wani kauye dake cikin karamar hukumar
6agwai dake nan cikin jihar kano.
Awar su biyu kan hanya snn suka isa garin.
Gida ne d'an qarami suka paka motar su a gun,umma ta shiga daga ciki janye da yusra a
hannunta ta sami wata yarinya da bazata wuce 17 yrs ba tana duqe a gaban murhu tana hura
wuta da iskan bakinta,wacce tana ganin umma tazo aguje ta rungume ta cike da murna tana
fad'in"oyoyo innan bunni shannun ki da zuwa" Kasancewar su Fulani ne Hausar su bata bi dede ba.
Umma dake kallonta d'auke da murmushi tace"Yauwa Zarah ina mutan gidan suke ne naji
shiru kmr ba kowa?
Zarah da ta kama hannun yusra washe da baki tace"eh kawu baya nn yaje gurin kiwo,dije
kuma taje d'ibar ruwa(cewa da er kawunta wacce suke tsara)
Taci gaba da cewa mama asabe (wato mahaifiyar dije) yanzu ta siga bayi,inna kuma cewa da
kakarta tana daga shiki kindirmo take damawa.
Murmushi umma tayi zasu qarasa daga ciki Zarah ke tambayar ta"Nusaiba fa naga yusra kawai
aka zo da ita"
umma tace"eh Nusaiba bata nn tana Kaduna ta kai musu hutu.
Ta qarashe mgnr ne dai dai sun shigo d'akin inna,wanda d'an d'akine da aka yishi kmr bukka
se mutum ya duqa yake iya shiga.
Wacce ake kira da inna tana zaune a tsakar d'akin qwarya a gabanta tana dama kindirmo kmr
yanda zarah tace.
"A'ah Maraba maraba da mutan birni yau kune a garin?
cewar inna wacce tayi maganar ne washe da baki tana kallon umma.
Yayinda umma ta zauna kan d'an qaramin gadon karan da ke cikin d'akin tana fad'in mune inna
ya muka same ku.
Tace"lafiya lau ya mutan birni kowa lafiya?
Duk suna lafiya Alhj ma yace a gaida ki da jiki da kuma lafiyar qafafu.
Inna tace"wlh Alhmdlh jiki yayi sauqi qafafu kuma se sauqi suke tunda na fara shafa wnn
maganin da kika kawo min kwanaki.
Tace"to Allah ya qara sauqi inna"
Inna tace"Amin yayinda take kallon yusra wacce tazo gurinta d'auke da murmushi ta zauna
kusa da ita tana kallon yanda inna ke dama kindirmo,inna dake kallonta tace"ko kin iya in baki ki
qarasa damawa"
Da sauri yusra ta gyad'a mata kai alamar eh,inna ta lakaci hancinta cikin yanayin wasar jika da
kaka tace"to naqi d'in salon ki mana dagwalgwale mu kasa sha.
A shagwa6e yusra ta kama ludayin ita se inna ta bata ta dama.
Umma dake kallon su tayi murmushi bata ce komai ba se kallon d'akin take sam bata son ganin
d'akin nn haka,so take taga komai na zamani a ciki,wacce tuni ba yanda bata yi ba kan inna ta
bari a gyara musu gida a sauya musu komai na zamani amma tace a'a ita bata son rabuwa da
abubuwan gado. Inna ce ta katse mata shirun da cewa"ni kuwa ina Nusaiba?
Umma ace"ae Nusaiba tana Kaduna ta kai musu hutu"
Inna tace"Ayyo wnn karon bamu keda hutun ba knn,to fad'ima je kawowa innar ki ruwa mana
tasha.
Umma tace"Aa inna ni bana jin qishi kindirmo de zan sha snn tare nike da audu driver yana
waje a qofar gida Zarah d'auko kwanon shan ruwa a zuba masa snn ki d'auki tabarma da ruwa
a kofi ki kai masa kafin a gama abinci naga yanzu aka d'aura.
Nan Zarah ta d'auko kwanon shan ruwa me kyau me marfi da kuma silver cup shima me
marfi,taje waje ta d'auraye ta kawo ma inna kwanon shan ruwan ta ajiye snn ta nufi lungun
ganbu riqe da kofin silver da akwai randa a lungun gambu nn cikin d'akin,dake d'auke da tsafta
taccin ruwan dad'i da aka killace dan ruwan sha kawai,ta d'ibar mishi ruwan snn ta d'auki
kindirmo da inna ta zuba mishi ta d'aura kwanon aka,ta fita riqe da sabuwar tabarmar da ta
d'aukar mishi da kuma ruwan da ta d'ibar mishi a cup.
Nan umma ke snr da inna dalilin zuwanta.
Sosai inna taji dad'i wacce ba musu ta amince da zancen dan ita farin cikinta ne jikarta tayi
aure birni.
Koda zarah ta dawo aka snr da ita har tsallen murna ta dinga yi zata koma birni da zama,se
dai ba'a gaya mata cewa aure za'a mata ba idan an kwan biyu.
Bayan sllr la'asar
tuni Zarah ta kammala had'a komai nata na tafiya har ban kwana taje tayi da en uwa da abokan
arziki.
Da zasu tafi har kuka dije tayi zainab zata tafi ta barta.
Koda suka isa kano se kiraye kirayen sllr magrib ake,kae tsaye umma ta kaita d'akin da zata
zauna wato d'akin Nusaiba.
Byn sunyi sllh umma ta kaita gurin Abba suka gaisa.
Washe gari da safe umma da kanta taje ta kira zarah suzo suyi breakfast,suna tafe kafin su
qarasa gun dinning ta nuna mata saifuddeen dake zaune shi kad'ai kan dining yana cin
breakfast d'insa.
(dan shi haka yake idan yana jin yunwa baya iya jiran kowa)
Tace yayanki ne in munje ki gaida shi amma fa baya son surutu dan karki jashi da srt yaji
haushin ki.
Zarah tace"to,amma waye si da baya son srt inna,ko sine wannan da keyin karatu a waje?
Tayi mgnr ne tana mae kallon umma"
Umma tace mata"eh shine"
Tace"inna ya ma shunan si ni mantawa nake?
Shiru umma tayi bata bata amsa ba sbd sun qaraso gun dining se jawo mata kujerar da ke
dubin saifuddeen tayi,ba musu Zarah ta zauna kmr yanda umma ta mata nuni,wacce tana zama
ta karkatadda kanta tana leqen fuskar saifuddeen da kansa ke duqe gabad'aya hankalin sa na
gun cin abinci bai ko ji motsin isowar su gurin ba,se jin mgnr ta yayi kmr daga sama tace"hai
shannun ka ka tasi lafiya,fad'ima shuna na kaifa ya shunan ka"
Da saurin sa ya d'ago sexy eyes d'insa yana kallon ta fuskar sa a yatsine,a ransa yana
mamakin wnn abar fa daga ina!
Zarah da ta saki baki still kanta a karkace se kallon sa take tayi,a ranta tace"Aradu sina da
kyau wnn"
Se gashi mgnr ta fito a fili
Saifuddeen dake kallon ta cike da tsana yace"of course!but to hell wit u mayya!mtsw!yayi tsaki
tare da kallon umma yace"umma where did u get this abar,wata iri da ita haka tazo ta zaunawa
mutane kan dining kuma kin barta baki koreta ba.
Kallon sa kawai umma tayi bata ce mishi komai ba,haushi duk ya cika shi yana kallon Zarah se
duk yaji abincin ma ya fita ranshi nn ya ture plate d'in abinci gefe ya d'auki ruwa a cup yakai
bakin sa,nn se ga Abba ya qaraso shida yusra janye a hannun shi wanda kai tsaye ya nuna
Zarah yace da saifuddeen ka sani wnn da kake