Showing 18001 words to 21000 words out of 150998 words
sami
cikin sa ba irin abinda bata yi ba dmn cikin ya zube amma Allah da ikon sa bata yi nasara ba
har ta haife shi,a tunani na renon cikin sa da tayi na tsawon wata tara da yanda tasha wahala a
gurin haifuwar shi zai sa ta so shi amma sam hakan besa ta damu dashi ba,masu aiki kawai ta
barwa suna hidima dashi,nono ma se ta ga dama take bashi,har na gaji da baqin halinta na
sake ta.
Umma tace"amma dai duk da haka haqqi ne akanta a snr da ita"
Yace"maman yusra kinfi kowa sanin bana son Saifuddeen yasan wace ce mahaifiyar sa dmn
baqin ciki ne kawai a gare shi,a gurin hajiya ya tashi tun da yayi wayo ya fahimci cewa hjy kakar
sa ce,ya fara damuna ina mahaifiyar sa,ban ta6a gaya masa ba sai dai kawai nace tayi tafiya da
haka har Allah yasa mukayi aure nida ke,a gabanki na kawo shi nace masa gaki kece
mahaifiyar sa da yake damuna kullum,kina kallon yanda ya rungume ki cikin tsananin farin ciki
da jin dad'i wanda tun daga lokacin ya d'auka kece mahaifiyar sa da ta haifeshi har yau baisan
bake kika haife sa ba and still bana so ya sani dan haka kar ki qara min zancen wnn banzar
matar bana so.
Kayi haquri inshaa Allah hakan bazai sake faruwa ba.
umma ta fad'a tare da tashi ta fita daga d'akin.
kici6us tayi da Nusaiba tsaye a bakin qofar d'akin idonta tap da qwallah da alama ta ji duk
abinda suke fad'i.
Wani irin kallo umma ke mata da kmr mamaki snn taja hannun ta da sauri ta tafi da ita zuwa
d'akin ta,
tace "Nusaiba uban me kikeyi a bakin qofar Abbanku kika la6e kina sauraren abinda muke fad'i
iye!
Da sauri ta girgiza kanta tare da share hawayen da suka zubo mata tace"wlh umma ba la6e
nake maku ba,umman kd ce ta kira a waya ta tace na kai maki wayar tayi ta kiran wayar ki baki
d'aga ba shine naje ban same ki a d'aki ba nazo d'akin Abba da niyyar maku knocking shi ne
se..... Shine se kika ji muna magana kika tsaya kina sauraren mu ko!to bari kiji in gaya miki wlh kar
inji mgnr nn ta fito kinji ko!
Da sauri Nusaiba ta gyad'a kanta alamar taji snn ta fita daga d'akin kmr yanda umma ta
umarce ta.
Taje d'akin su tayi kwance kan bed kmr wata marar lafiya dan gabad'aya se taji tausayin yayan
nata ya kama ta yazai ji idan ya gano umma ba mahaifiyar sa bace bayan yana mata kallon ita
ce ta haifeshi....."Nusaiba lafiya me yake faruwa?
zarah ta tambaya wacce tana zaune kan bed koda Nusaiba tazo ta kwanta.
A kafai ce Nusaiba tasa hannu ta share hawayen da suka sakko kan kumatun ta sbd ta bawa
zarah baya bata iya lura da abinda take ciki,byn ta share hawayen ne snn tace"ba komai kaina
ne naji ya d'an sara min shine na kwanta"
Muryar ta a sanyaye ta mata sannu.
Snn taci gaba da duba littafan ta na islamiyya da take dubawa sbd dama aikinta knn idan bata
yin komai,wacce duk ta d'an fad'a sbd zullumin auren da za'a mata da wanda bata san ya
rayuwar ta zata kasance ba,wanda tun rnr ta ganshi da Sophie suna wnn iskancin wani irin
tsanar sa take ji a ranta ko ganin sa bata son yi asalima bata sake ganin sa ba d'in tun daga rnr
dan kwata kwata ya daina shigowa cin abinci,gidan su jamil yake zuwa can yaci.
Saura kwana d'aya asa lalle suka tafi Rimin dako ita da Nusaiba da kuma Nadiya wato 'ya ga
umman kd wacce shekarun su d'aya da Nusaiba sune suka zama en matan amarya tare da dije
dake can.```
```A washe gari aka sa lalle snn suka dawo kano akayi sauran bukukuwa rnr juma'a aka
d'aura aure and by 10pm aka kai Amarya ba kad'an ba zarah tayi kuka har ta gode Allah shike
nn da gaske dai an d'aura auren nn har gata a d'akin ta an kawo ta,tana zaune kan bed kanta
qasa fuskar ta a rufe da gyale kmr dai kowace amarya,su Nusaiba,nadiya da dije se sheri suke
ta mata kmr yanda en matan amarya keyi tana jinsu bata tanka su ba dan ita kad'ai tasan irin
baqin cikin da take ji a ranta an had'a ta da miji d'an iska dako qaunar ganin sa bata yi su har
sunga gurin barkwanci.
Bayan kowa ya watse tana nn zaune kan bed ita kad'ai still fuskar ta a rufe se ci gaba take da
kukan ta dan se kukan ma ya dawo mata sabo.
Qofar d'akin taji an bud'e da qarfi har sai da ta tsorata ba shiri ta miqe ta sauka daga kan
gadon tana kallon Saifuddeen da shine ya banki qofar d'akin ya shigo yana mata wani irin
mugun kallon da yasa ta soma ja baya,shi kuma se matsowa yake inda take har ya had'e ta da
jikin gina,yana kallon ta fuskar nn tashi kmr wani zaki ba annuri ko kad'an,zarah kuwa
gabad'aya ta kame jikin gina tana kallon sa a tsorace,wacce ba shiri ta saki qara sbd yanda
yasa qafar sa ya daki qafar ta da qarfin tsiya se mutsustsuka qafar yake d'auke da takalmin sa
masu masifar ciwo snn yakai hannun sa a bayan wuyan ta ya lotsa akaifun sa ciki sosai ya riqe
mata jijiyoyin wuya gam tamkar ze 6alla mata wuya.
Ae kuwa take idanuwan zarah suka yi jajur se faman qoqarin qwatar kanta take amma ta kasa.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Wednesday 14/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄
SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 12*
Saifuddeen kuwa se qara matse mata wuya yake yana mai ci gaba da mutsustsuka qafar
ta,Zarah dake ta qoqarin qwatar kanta ta saki qara cike da jin zafi cikin kuka tace"wae kai wane
irin mugu ne me na maka!
A qufule yasa hannun sa da yatsun sa biyu ya mugun matse mata baki snn cikin kakkausar
murya yace"ke! dan ubanki har tambaya kike,to bari kiji ba'a ta6a babbar jakar da ta shigo
rayuwa ta ba ta lallata min duk wani tsarin na rayuwa ta ba irin ki,wacce ko d'aura min ke akayi
a qafa bazan ta6a janki ba wlh se dai na tsinke na yar,dan haka tun wuri kiyi gaggawar cire
cewa kin zo gidan nn ne dmn aure never!
Kisa a ranki cewa kinzo fursun ne inda zan azabtar dake na miki hukuncin laifin da kika aika ta
a gare ni,dmn bazan ta6a barin ki ba wlh se na hukunta ki hukunci mafi tsanani da se kinyi
nadamar zowar ki duniya!
Supid!!
Ya fad'a tare da jefar da ita gefe ta fad'i da qarfi har sai da goshin ta ya daki gefen bed da sauri
ta dafe goshin nata tare da fashewa da wani irin kuka yayinda d'ayan hannun ta ke riqe da qafar
ta da ya mutsustsuke duk tayi wani irin jajur,wuyan ta kuma ji take kmr still bai janye hannun sa
ba sbd zafin bala'in da take ji,wacce tana jin yanda jini ke d'an silalowa a hankli daga bayan
wuyan nata,ga bakin ta dake mata sululi sbd matsar da ya masa.
A ranta se Allah ya isa take ta mishi tana ci gaba da kuka a nn har bacci ya kwashe ta a gurin
bata sani ba.
Washe gari da qyar ta iya jan qafar ta taje ta d'auro arwala tayi sallah.
Bayan ta idar ta koma kwanciya,byn wuyan ta da qafar ta duk sun kumbura tana jin kanta kmr
wata mara lafiya haka dai ta samu bacci ya d'auke ta.
Se guraren 9 ta tashi tayi wanka ta shirya,zuwa qarfe 10 da rabi se ga su Nusaiba sun zo mata
da breakfast d'inda umma ta basu su kawo.
Dama yunwa take ji tayi zaune taci se da ta qoshi,nan fa sukayi ta fira abinsu
Se bayan mutane sun fara zowa ne snn suka tashi zasu sauka downstairs zuwa falo a nn
Nusaiba taga yanda zarah ke taka qafar ta da qyar tana d'ingishi,nadiya da dije sam basu
lura ba sbd suna gaba su suka fara fita.
Nusaiba da ta gani ta jata baya kad'an tana kallon qafar snn tace"6ter what's wrong,me ya sami
qafar ki haka tayi jajur?
Zarah ta ta6e baki tace"yayanki mana mugu shine duk ya mutsustsuke qafar"
Me kika mishi?
Nusaiba ta tambaya
Zarah tace"hm meko mugunta kawai"
Snn ta yaye gyalenta dake yafe tun daga saman kanta tace"duba bayan wuyana ma ki ga duk
ya kumbura sbd matsar da ya min"
Nan Nusaiba takai hannun ta a hankli ta ta6a gurin tana dubawa tace"kai oh my God!
lallai yaya saif Allah tun wuri kar ki barshi yaci gaba da miki haka"
Zarah tace"hm basshi Allah ya isa ne zai kama shi dan bazan ta6a yafe masa ba wlh"
Nan ta maida gyalen ta ta yafa har zuwa goshin ta da ya d'an yi ja duk ta rufe bata so mutane
su gani,haka ma da suna saukowa daga staircase se taka qafar ta take a hnkli dan kar mutane
su fahimta,amma duk da haka se da nadiya da dije suka fahimta har ma suka tambaye ta me ya
sami qafar ta tace musu abune ya fad'o min a qafa shine naji ciwo.
Komai basu ce ba se sannu da suka mata snn suka qarasa gurin mutane dake zazzaune a
falo duk mafi yawan su en rimin dako ne wato maman dije da sauran en uwa,wa enda a nn
garin suka kwana gurin umma.
Take gida ya cika tamkal se yinin biki ake Saifuddeen kam tun da safe ya fita gidan be sake
dawowa ba har yamma tayi kowa ya watse se su Nusaiba kad'ai wa enda suma tafe suke sun
fito zarah ta rakosu bakin gate,odar da akeyi ne yasa suka tsaya mai gadi ya bud'e gate d'in,se
ga jamil ya kunna motar sa a cikin gidan shida saifuddeen wanda motar shi ce ta sami matsala
shine jamil ya kawo shi ba dan yaso ba sbd yarinyar da Saifuddeen yake tare da ita tana nn
zaune a seat d'in baya se k'as k'as take tana cin chewing gum ta wani ci uban ture kaga
tsiya,qafar ta kan d'aya tana faman danne danne a waya wacce tana d'aya daga cikin en matan
da ke matuqar son Saifuddeen da se yanzu ne ya fara lokacin su,jamil kam abun har mamaki
ya basa.
Su Nusaiba kam fita kawai sukayi sbd driver na waje yana jiran su ba tare da sun tsaya kula da
wa enda ke cikin motar ba kawai dai sunga Saifuddeen da jamil basu kula da wacce ke baya ba
sbd duhun glass d'in motar bazai barsu su iya ganinta kai tsaye ba se idan sun kula.
Zarah na tsaye har sai da suka shiga mota suka wuce snn ta koma daga ciki,idon Jamil qyar a
kanta ganin yanda take d'ingishi ya kalli Saifuddeen dake qoqarin bud'e qofa ze fita yace
masa"halan me ya sami zarah a qafar ta har take yin d'ingishi?
Wani banzan kallo Saifuddeen ya mishi snn yace"oho mata in ma kayi wani banzan tunani ne
to ka ma watsar dan kasan wnn abar ko duniyar nn kaf za'a ban bazan neme ta ba wlh"
Ya buga tsaki tare da bud'e ganbun motar ya fita Jamil ya bisa da kallo d'auke da murmushi
shi sam bai ma kawo wani tunani ba dan yasan halin abokin nasa bazai ma ta6a kula ta ba.
Yana kallon sa har suka shige shida yarinyar sa,ya girgiza kansa kawai
snn yaja motar sa ya bar gidan.
Saifuddeen kuwa koda suka shiga sun sami zarah tana kashe kayan kallo sau d'aya ta kalle su
ta kauda kai taci gaba da aikinda take,Saifuddeen ya riqe waist d'insa yana kallon ta yace"ke
dan ubanki gidan ku ba'a koya maki tarbiya bane da baza kizo ki durqusa ki gaida mutane ba!
Kafin zarah tace komai wacce yake tare da ita ta wani ya tsine fuska tana kallon zarah tare da
fad'in"No dear ka barta kawai ni bana ma son gaisuwar ta,zo mu tafi"
Taja hannun sa suka haura sama zuwa d'akin shi,
zarah ta bisu da kallo ta6e da baki tace"an dai yi asara ga kyau amma ba kyan hali,Allah sa ma
kaf karuwan duniyar nn zaka kawo a cikin gidan nn ni ina ruwana"
Nan ta ida kashe kayan kallon ta haura sama zuwa d'akin ta.
Washe gari da safe tana kwance kan dardumar sallah tana bacci se ga Saifuddeen ya shigo
d'akin riqe da qaramin bokiti a hannun sa cike da ruwa,a tsiyace ya kwara mata su gabad'aya
kan fuskarta,ba shiri ta farka tare da sakin ihu cikin mugun tsorata ta miqe a rud'e tana waige
waige a tunanin ta ko tayi gamo da aljanu ne suka jefo ta rafi. Saifuddeen dake kallon ta ya kwad'a mata gigitaccen mari yace"kalle ni nn nine kije ki bud'e
qofa se faman danna doorbell ake duk an hana min bacci.
Zarah dake dafe da kuncen ta tana kuka tace"amma wlh se Allah ya isa min bazan ta6a yafe
maka ba....wani lafiyayyen marin ya koma kife ta dashi ya nuna ta yace"mind ur tongue ban
tashe ki dan ki gaya min mgnr banza ba,maza kije ki bud'e qofa nace ko yanzun nn nayi
gunduwa gunduwa dake,kinzo se sharara bacci kike tunda an gaya miki nn gidan ubanki ne da
zaki kwanta ki huta.
Da har zata ce bazata ba tayi shiru tana kallon farar kyanwar da ta shigo a tsorace taja baya
dan mugun tsoron kyanwa take.
Saifuddeen da ya fahimta ya d'auki kyanwar yace"zaki je ko sai na cillo miki ita"
Da sauri ta girgiza kanta muryar ta na rawa tace a'a zanje wlh.
Nan ta fita da sauri sauri se fmn d'ingishi take har ta iso bakin qofa ta bud'e.
Mai gadi ne tsaye a bakin qofar wanda har ze juya yaji an bud'e qofar ya tsaya,se da ya gaida
ta snn yace"dama ruwan gidan ne suka d'auke gashi ina so zan bawa flowers ruwa"
"to an gaya ma ni wani abu na sani na gidan nn ne"
Zarah ta fad'a ranta a 6ace tana kallon sa kmr shine Saifuddeen.
Mai gadin bai ce komai ba se haquri da ya bata ze juya se ga Saifuddeen,da saurin ta ta bar
gurin dan still yana riqe da kyanwar a hannu sa.
Tambayar mai gadi yayi mene ne,mai gadi ya gaya mishi.
Nan ya fita yaje ya duba ruwan suka kawo.
Da ya dawo kai tsaye d'akin zarah ya nufa da niyyar gindaya mata sharuddan gidan,but yana
6ird'a qofar d'akin ya jita a rufe.
Zarah na jin sa tayi banza dashi se jiqaqqin tufafin jikin ta ta cire wato kayan bacci riga da
wando da kuma qaton hijabin sallah da ke jikinta,se ta zamo daga ita se inner wears,half vest
ce baqa da pant baqi mai kmr bomb short dan ya rufe mata d'uwawu sosai har zuwa gurin
cinyoyin ta kad'an. Sanyi take ji sosai har tana kakarwa amma bata nemi wani abu ta rufa jikinta ba,dan jin inner
wears d'in jikinta take kmr suma sun d'an jiqe,tayi gurfane kan guiwoyin ta tasa tufafin da ta cire
tana tsane ruwan da sauri tana matsewa a cikin bokiti.
Saifuddeen da yaje d'akin sa yana kallonta ta jikin laptop d'in shi se kallon ta yake kmr da
mamaki,sbd gashin da ya gani da ita sosai mai sul6in gaske baqi wulik dashi ya zubo har
saman gadon bayanta ga black half vest da black bomb short d'in jikinta sun qara fito da hasken
fatar ta sosai se tayi kyaun duba kmr wata wayayya. Ta6e bakin sa yayi snn ya rufe laptop d'in tare da cillar da ita gefe.
[11:14AM, 3/6/2018] 鈥�+234 806 858 0203鈥�: _Thursday 15/02/2018_ *芦禄禄芦芦禄
SAIFUDDEEN芦禄禄芦芦禄*
By
*Billy giro馃槉*
*Dedicated to禄禄禄Zarah gwandu*
*芦禄Page芦禄 13*
Snn ya maida duban sa gun wacce yazo da ita jiya a nn ta kwana tana kwance rufe da blanket
se fmn sharara bacci take,hannu yasa ya yaye blanket d'in,ba wata sutura a jikin ta bai damu ba
se tashin ta ya shiga yi.
A hnkli ta bud'e idon ta tare da jan blanket ta rufe jikinta snn ta tashi zaune tana kallon sa
tace"ya akayi ne dear?
Yace"wanka zakiyi kiyi ki bar gidan nn kafin mutane su fara shigowa bana son qananun
maganganu"
Tace"to da akwai abinda zanci idan na fito dan ni yunwa nake ji sosai"
Fuskar sa a d'aure yace"kin girka ne da zaki ci"
Ta marere ce fuska tace"haba dear ina wnn yarinyar da zan shiga kitchen da kaina"
Wnn qazamiyar ce zaki iya cin girkin ta.
Ta yatsine fuska tace"kuma fa hakane bazan iya cin girkin ta ba gaskiya,bari naje nayi wanka
idan na fito ko tea ne se nasha ko kanada buqatar na girka mana wani abu?
"Bana buqata"
Ya fad'a a taqaice,bata sake ce masa komai ba se sauka tayi daga kan gadon taje ta fad'a
bathroom.
Zarah kuwa bayan ta gama gogen gogen ta,kae tsaye bathroom ta shiga tayi wanka se bayan
ta fito ta shirya snn ta gyara d'akin.
Kana ta kalli agogon bangon d'akin taga har sha d'aya tayi amma ba alamar zuwan su