Showing 15001 words to 18000 words out of 46393 words
Chapter 6 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NA TAKORI.pdf
suka aura. Ba ruwan su da kowa
nasa including wadanda suka yi silar zuwan shi duniya.
Amma duk da haka yana kula da MACCIDO MALL daga can inda yake, lokacin da Muhsin ya samu gurbin
karatu a Danfodiyo abubuwan za su yi masa yawa, don haka ya nemi Yayan da ya nemo masa mataimaki
amintacce, wanda zai iya handling dukkan ayyukansa na manager.
Akwai wani abokin yaya da suka yi karatun sakandire tare da ya biyo ta hannunsa yana so Yayan ya samar
masa aiki tun da jimawa. A wannan lokacin sai ya nemo shi. Bayan dogon bincike da amincewa juna
dukkanin su, ya yarda zai zama mataimakin Muhsin.
Al-Qasim Ka’oje ke nan, wanda shigowarsa cikin harkar mall ba mall din kadai ya taimakawa ba. A sannu
ya shiga ran Addah sabida hankalin sa da nutsuwar sa. Ga shi da biyayya kamar ita ta haife shi, sai ya
shigo sosai cikin harkokin gidan mu yake taimakawa ta kowanne fanni, sannan ya zama tamkar wakilin
Yaya Maccido wajen harkokin cikin gida, da kula da gidan don Muhsin yanzu ta kansa yake a jami'a. Shi
Al-qasim yana yawan kiran Yaya Maccido su yi magana, ba ya jira sai Yayan ya neme shi, duk abin da ake
ciki a kan harkar kasuwancin da abin da Adda ke bukata yana kokari ya ga ya sanar da shi tunda ganin sa
yanzu ya gagare mu.
Al-qasim shi yake kai Adda asibiti yanzu sakamakon ciwon sugar da hawan jini da ya same ta rana daya.
Yawanci in zai kai ta ganin likita da safe suke zuwa, lokacin ni ina makaranta. Har cefanen wata na gidan
Al-Qasim ke yo wa, wataran a aljihunsa yake sayo abubuwa ya kawo, musamman fruits, mutum ne shi
mai yawan ALHERI sosai, ga shi da ilmi don Muhsin ya ce min masters gare shi, kuma a yanzu haka yana
karatu part-time na PhD dinsa a Open University.
Tun shigowar Al-Qasim al’amuran gidanmu abubuwa da yawa suka gyaru mana, matsaloli da yawa suka
kau. Addah kullum ce min ta ke,
“Na yi dan da ya maye min gurbin Maccido!”.
Ni haka kawai ban cika sakewa ba idan yana gidan. Ya cika kallo, ni kuma bana son kallo. Daga baya na
lura ni kadai yake yawaita kallon. Wannan abu na matukar kular da ni, a kan me zai maida ni dubarudu ba
dama in zauna sai ya debi lunkuma-lunkuman idanun sa ya yi ta lafta mini yana maida ni unease?
Rannan na yi wa Adda korafi.
“Wannan dan naki ya cika kallo wallahi”.
Adda sai cewa ta yi,
“Ke da wane idon ki ka kalle shi, har ki ka san ya cika kallo?”
Yau bayan ya tashi daga mall ya zo gidan kamar yadda ya saba da manyan ledoji a hannun sa, ya yi
sallama ya shigo falon, daga ni sai Adda muna kallon talabijin.
Addah ce ta amsa, ni kam a zuci na amsa. Na kalle shi sau daya na dauke kai, a raina ina fadin,
“Ga fa duba-rudu ya iso”.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
https://www.arewabooks.com/book?id=6329c8029b3e7782f077921d
YIWA KAI HISABI
Har gaban Adda ya karasa ya tsugunna ya gaishe ta, sannan ya aje mata ledojin da ya shigo da su masu
tambarin ‘Maccido mall’, kayan amfanin gida ne da ya kan debo mata a shagon su da toiletries da abincin
gwangwani iri-iri. ‘Yar karamar ledar da ta rage a hannun sa ya iso gare ni ya aza min bisa handle din
kujerar da nake zaune,
“Autar Adda ga tsaraba na yo miki daga mall”.
Dauka na yi na bude babu ko an gode, sabida yadda yake ba ni haushi da kallon sa, amma ganin
choculates ‘yan uban-ubansu masu tsada ban san sanda bakina ya bude ya yi godiyar ba. Na fiddo mars
da kit-kat na bude na gutsira kunnena har motsi yake.
Adda ta ce, “Ki dai sha kadan, kin san lokacin watan ki ya kusa, kada ki zo kina min murkususun nan naki”.
Wata kunya ta kama ni, na saci kallon Al-Qasim, sai na ga bai ma gane zancen da Addah ke yi din ba.
Zama ya yi bisa centre carpet daga gefen Addah yana yi mata bayanin ribar da ake ta samu a wannan
shekarar.
Rannan kafin ya shiga mall ya zo gidan da sassafe yana sauri, bayan sun gaisa da Addah ya tambaye ta, ko
na tashi daga barci? Addah ta ce, bari ta dubo ni. Ta same ni tashina ke nan ina shirin shiga wanka, ta ce,
“Ma’u zo mana, Al-Qasim yana nemanki”.
Na zumburo baki, “Duba-Rudu za ki ce Addah!”.
Dakuwa ta yi min, “Ungo naki, bana son raini wa na gaba. Kada in kara ji kin ce masa Dubarudun nan, ke
da wane idanun ki ke dubansa har ki ka san yana duban naki?”
Sake zumburo baki na yi, na daura zani bisa rigar barci na na dora hijabin sallah ta na bi bayan Addah.
Yana tsaye tsakiyar falon rike da kwamfutar kan cinya (laptop) a kunne. Ya yi kwalliyar sa tsaf yadda ya
saba. A perfect gentleman. Ina fitowa ya tako zuwa gare ni da saurin sa muka game a tsakiyar falon.
Ya ce, “Yauwa kanwata, kin fito?”
Na gyada kai.
Ya sake matsowa da laptop din.
“Wani dan taimako za ki yi min, ai kin iya microsoft excel ko?”
Cikin jin kunyar kada in bada kaina in na ce ban iya ba, ban ma san mece ce ita din ba, na gyada masa kai
kawai.
“Yauwa! Please Master ya kira ni Abuja yanzun nan (Yaya Maccido), ga shi ina da muhimman bayanan da
ban shigar cikin kwamfuta ba. Ga su a rubuce bisa sheet din nan don Allah daga yanzu zuwa dare ki
shasshigar min”.
Ya miko min takardun da kwamfutar.
Ban yi kasa a gwiwa ba na karba. Ya yi min murmushi tare da godiya.
Ya ce, “Me zan kawo miki?”
Na ce, “Babu komai, ka gaida min Ihsan kawai”.
“Za ta ji, insha Allah”.
Da haka ya yi mana sallama ya tafi.
Na koma daki na aje (laptop) bisa gado na na zuba mata ido ita da takardun. Kwata-kwata ba abin da na
fahimta. Wannan shi ne karshen tozarci idan Al-Qasim saurayin da ke ji da kansa ya fahimci zero nake a
boko. Duk kidifirin da na ke masa ai dariya zai koma yi min tunda (empty-head) gare ni. Wasu hawaye
suka ciko idanu na, na ce bari in yi wanka in zo in jagwalgwala abin da ya sauwaka, da babu gara ba dadi.
Bayan na yi wanka doguwar riga kawai na saka na zo na dinga danne-danne a kwamfuta, shiga nan fita
can ban san sunan komai ba, ko abin da nake yi daidai ne ko ba daidai ne ba.
Har azahar ina abu daya. Sai da Addah ta turo Hauwa ta gaya min ga Nabeelah a waya, sannan na rufe
kwamfutar ba tare da na yi switching off ba, sai da cajin ta ya kare ta kashe kanta.
Sai da Al-Qasim ya yi kwana biyu a Abuja sannan ya dawo, don shi ne ke kula da sabon ginin wani mall
din ko ko Plaza da Yaya Maccido ke yi a Abuja. Wanda ba shi da maraba da na Sokoto a komai..
Da daddare ya zo gidan suka gaisa da Addah. Tunda na ganshi gabana ya fadi don tunda na aje
kwamfutar sa ban kara bi ta kanta ba, ko dan caji ban sa mata ba.
Ya dube ni da murmushi, ya ce, “Ihsan na gaishe ki tayi ba ki masha Allah ga shi tana gudun ta ko’ina”.
Na yi murmushi sosai, na ce,
“Oh my daughter”.
Ya ce, “Maza a dauko min aikin da na sa ki, Master na jira in tura masa yanzu”.
Ba musu na mike kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, na dauko kayan sa na kawo masa. Ya karba yana
shirin kunnawa ya ce, “Ya? Babu caji ne?”
Na ce, “Ban saka ba”. Na fuske abuna, don ma kada ya kara yi min wata tambayar.
Da kansa ya tashi ya je ya jona ya bata lokaci ta kama sannan ya kunna. A hankali yake duba abubuwa da
aikin da ya sa ni Nana Asma’u in yi masa.
Duk wasu muhimman applications masu dauke da bayanai masu muhimmanci na goge masa su. Da ya
shiga excel don ganin aikin da ya sa ni sai ya tarar na cika raws din da sunana Asma’u Adam Bebeji da
kuma ABCDEFG.
Mamaki, takaici, tu’ajjibi suka taru suka lullube Al-Qasim Ka'oje. Me hakan ke nufi? Ba ta iya ba ko
shakiyanci ne ta jaza mai asara haka?
Amma ai ‘yar makaranta ce, ajin karshe a sakandire, makarantar ma mai aji da mukami, ko last week shi
Adda ta tura ya biya (school-fees) dinta kudi na gugar wuri masu yawa. Kada dai a ce asarar kudin tara
ake yi a kan Asma'u?
Amma da yake mai ilmi ne bai nuna komai a fuskar sa ba. Ya dauko murmushin karfin hali ya dora wa
kyakkyawar fuskar sa.
“Ma’un Adda, na ga aiki ya yi kyau fa na gode”.
Na saki baki ina kallonsa, “ABCD fa na rubuta maka. Ni ma su kadai na iya, shi ya sa na rubuta maka su sai
kuma sunana”.
Adda ta rage sautin talabijin ta bada attention dinta ga hirar mu.
“Al-Qasim wai me ye?”
Ya ce, “Adda aiki na bai wa Ma’un ki ta taya ni, sabida Master ya kira ni Abuja da sauri, shi ne aka rubuta
min Asma’u Bebeji maimakon aikin nawa, aka kuma yi min ciko da ABCD aka ba ni alakoro da goge min
duk wasu muhimman bayanai da ke cikin kwamfuta”.
Adda ta juya tana sakin dariya. Dariyar da ta kular da ni na tashi na bar musu falon. Sai da Adda ta yi
dariyar ta ma'ishi sannan ta ce,
“Wa ya aike ka? Kuma ba ka tambaya ta iya ko ba ta iya ba kawai sai ka ba ta?”
Ya langwabar da kai cike da takaici, ya ce, “Sai da na fara tambayar ta fa ta ce ta iya”.
Adda ta sake yin dariya ta ce, “Ma’u da ka ke ganinta kanta babu komai na karatun boko. Tunda aka haife
ta haka take, sunan zuwa makarantar ta "jeka-na-yi-ka". Ina tsammanin daga sakandire ta gama shiga aji
don ba za ta iya karatun jami’a ba”.
Maganar ta doki Al-Qasim sosai, domin kuwa shi so na yake, so na hakika. Wanda yake fatan ya kai mu ga
siradin aure ya samu tsatso daga gare ni. In haka ne to me zan koya wa ‘ya’yan sa idan yayi kasadar aure
na?
Ya dubi Adda fuskar sa dauke da tausayi da soyayyar Asma’u.
Ya ce, “Akwai abin yi akai Adda, ba haka za'a kyale ta ba. Ni na san irin matsalar ta. Tana da Learning
Disability, tana bukatar koyarwa ta musamman (Special Education). Insha Allahu Ma’u za ta yi karatu
kamar kowa har matsayin da ya fi degree sai ta taka”.
Ba karamin jin dadin kalaman sa kan Ma’un ta Adda ta yi ba. Rana ta farko da wani ya taba ba ta ‘hope’
kan karatun Ma’u. malamanta cewa suke, jaka ce, wasa ne kawai a kanta.
A daren ya kira Master dinsa (Yaya Maccido). Rana ta farko da ya taba yi masa magana a kan kanwar sa
Ma’u. Maccido ya tuna Adda ta taba yi masa magana kwatankwacin wannan a kan Asma’un. Ya bada
shawarwarin da yake ganin in an bi za'a taimaka mata ta rubuta WAEC wannan shekarar ta shiga jami’a.
Yaya Maccido ya dora alhakin komai a wuyan sa ya ce, a ciri kudi ko nawa ne a dauki nauyin karatun nata.
Zuwa wannan lokacin Addah ta dangana a kan Maccido, ta yarda ta haifi Maccido ne, amma Lubabatu ta
haifamawa. Tsakanin ta da shi sai aiken kudi wanda ita ba ta bukata sam. Abinda ta ke samu a kason ta na
mall har ya fi karfin bukatun ta. Nabeelah dai ta ce, ta dage da addu’a akwai abin da ya juyar da
kwakwalwar Maccido daga kansu.
Al-Qasim ya sanar da Addah shawarar da suka yi da Maccido na daukarwa Ma’u malami na musamman
wanda ya yi specializing a kan learning disability zai fara karantar da ita watanni shidda kafin su zana
waec. Ba karamin dadi Adda ta ji ba da wannan gudunmuwa ta Al-Qasim ga Ma’u.
Ta yanar gizo Al-Qasim ya sa cigiyar Malamin Ma’u. Cikin watanni biyu aka samu, amma daga jami’ar
Danfodiyo zai je kullum wajen Ma’un. Sai da suka gama komai Maccido ya dunkule albashin sa na duka
watanni shiddan da zai yi yana koyar da Ma’u ya ba wa Al-Qasim ya ba shi. A ka sa ranar da zai fara zuwa.
A harabar gidan nan ma’adanar motoci akwai rumfa a nan za mu dinga zama. Al-Qasim ya sayo
blackboard, duster da marker wa malamin.
Sai da aka gama komai Addah ta zaunar da ni ta yi min bayani yadda zan fahimta. Ina wuta in jefa
Al-Qasim?!
Lallai ya cika Duba-Rudu, wato har kwakwalwar tawa sai da ya sa madubin Duba-Rudunsa ya hango
maganin ta. Ni ina ruwana da shi? Me ya yi ruwansa da harkata? Da haka kawai zai zo ya sa a takura min?
Zama na yi gaban Adda ina share hawayen abin nan da Al-Qasim yayi min, Addah tana lallashi na tare da
fadin Al-Qasim alheri yake nufi na da shi.
Rana ta farko da Malamin ya zo an kai ruwa rana kafin in yarda in fita. Amma a rana ta biyu, ni da kaina
na fita babu bacin rai. Wannan ya samo asali ne sabida hanyar da Malamin ke bi wajen koyar da ni (so
much persuasive, caring with endurance). Cikin sati daya sai ga ni ina bai wa Addah da Muhsin labarin
Malam Sa’ad ba a taba malami mashahuri irin shi a duniya ba.
Muhsin ya yi dariya ya ce, “Ai daga yau mun daina Hausa a gidannan, turancewa kawai za mu rika yi ni da
Ma’una”.
Da taimakon Malam Sa’ad, da bada karfin gwiwar dan uwana Muhsin, tare da jajircewar Al-Qasim Ka’oje,
na fara fahimtar ilmin boko tare da ganewa ashe shi din abu ne mai sauki, kallon tsoro nake masa. Ko
wata daya ba a cika ba turanci mai kyau ya soma zama a bakina.
******
BAYAN WATANNI SHIDDA
Bayan watanni shidda na zana waec, neco da jamb da taimakon Malam Sa’ad ta karkashin kasa. To sai dai
ko da sakamako ya fito ban ci jamb din ba, ita ma waec din credit hudu na samu. Duka gidan babu wanda
bai jinjina min ba tare da tabbatar min da cewa, na yi abin kirki, na yi kokari kada in bari gwiwa ta ta sage.
In bari shekara mai zuwa in sake maimaitawa.
Al-Qasim kuma ya ce, kafin zagayowar shekarar za mu ci gaba da karatu da Malam Sa’ad, kuma zai dinga
koyar da ni ilmin na’ura mai kwakwalwa. Ya sayo dankareriyar kwamfutar kan cinya laptop ya kawo min
matsayin gudunmuwar sa.
Zuwa wannan lokacin kowa ya gama fahimtar inda Al-Qasim ya sa gaba a kaina. Ni din ce dai ban taba
sanya wa raina komai ba, na dauka yana hidima da ni ne kawai a matsayin aikin sa da yake karbar albashi
a kai kamar yadda ya ke kula da komai na gidan.
Domin zuwa yanzu ya zama personal assistant din Yaya Maccido, wanda duniya ta gama bude wa kofofin
arziki ko ta ina. Ya zama babban director a Julius Berger, ya dade da barin gidan sa na Gwarimpa ya gina
wani a Apo. Sun koma shi da gimbiyar tasa da ‘yar su wadda aka ce ta kusan haihuwar cikinta na biyu.
Duniya ta yi mata yadda ta ke so, komai ya yi acan-acan.
Maccido ya zama nata ita kadai, daga ita sai ‘ya’yan da ta ke zubo masa.
Na san a rayuwa in Adda na da damuwa, to ta Maccido ce, wanda ya cire ta daga kan hanyarsa. Tsakanin
ta da shi gaisuwa a waya sai kuma in ya bushi iska ya leko bayan watanni masu yawa. Ita kuwa Lubabatun
ma tun zuwansu haihuwar Ihsan ba ta kara zuwa Sokoto ba. Ta zama Abuja -Woman, daidai da burin ta.
Ranar wata asabar Yaya Maccido ya bugo wa Adda waya ya sanar da ita haihuwar Lubabatu, an samu da
namiji. Yanzu haka suna can gidansu Lubabatun ita da yaran a garin Birnin Kebbi a can za ta yi wanka.
Yaya ko tunanin ya dauko su ita da jaririyar ya kawo wa Addah ta ga jikan ta bai yi ba, sai a hoto ya turo
mana hoton sa.
Aunty Nabeelah rannan da suka yi waya da Adda bata san ina toilet din ta ina jin su ba, ina ji tana share
hawaye tana labarta mata irin banzatar da itan da Maccido ya yi, tsakanin ta da shi sai waya, ba ta isa ya
tako ta ganshi ba balle ‘ya’yan sa.
Aunty Nabeelah ta ce, “Addah ke ma kina da laifi, tunda na ga take-taken yarinyar nan Lubabatu tun farko
na nusar da ke kan ki dauki mataki, ki kuma sa a taya ki da addu’a a kan Maccido, amma ki ka ce ke ba za
ki yi kutse cikin rayuwar sa da iyalin sa ba. Sannan ba za ki sa wani ya yi miki addu’a a kan dan da ki ka
haifa ba.
To Addah zamani ya canza... Kina barci ana yi miki minshari, dan hakin da ki ka raina sai ya tsole miki ido.
Sai yanzu da abubuwa suka fi karfin control za ki koka? Ai kawai ki ci gaba da hakurin ki kuma dage da
addu’a, amma Maccido ya yi mana nisa”.
Aunty Nabeelah ta fada tana share hawaye ita ma. Tana tuna kuruciyar su mai dadi da kanin ta Maccido.
Tun daga ranar damuwa ta ci gaba da taba lafiyar Addah a hankali-a-hankali. Ta soma ciwuka a tsaitsaye
tana danne shi