Showing 42001 words to 45000 words out of 61349 words
Chapter 15 - Halysaah Book Complete By Khaleesat Haydar -1.pdf
kamawa yake
for 3 days baki san halin da mutumin nan yake ciki ba gashi ke kanki kina testifying kyawawan
halayyarsa, wallahi ki shirya in rakaki mu je ki dubasa da jiki, kuma kafin nan mu fara biyawa ta
shopping mall kiyi masa shopping da zaki kai masa, shi ma sae yaji dadi wallahi" Khaleesat
tace "Kawai sai in kama tafiya har gidan nasu duba shi? Ai bai ma dace ba sai kace wasu
marasa kamun kai Safiyyah, be it in USA still bai dace ba, mu mata ne fa" Safiyyah ta mata
wani kallo, can tace "Ai da naki matsalar ya taso haka ya cire kudadensa sama da miliyan goma
sha biyar ko fin haka if i am not mistaken yayi solving maki matsalar ki, shi kuma bai da lafiya rai
kwakwai mutu kwakwai kince zuwa dubasa rashin kamun kai ne, to rashin dacewa ya wuce
zaman da ku ke yi gida daya? Shi wannan me za ki ce masa? Wani lokacin baki ma nazarin
maganar dake fitowa bakin ki Khaleesat, in zuwa dubasa bai dace ba to zamanku gida daya ma
ai bai dace ba be it in USA" Khaleesat dai sai kallonta take ta kasa cewa komai, can dai tace
"Ban gane ba, Miliyan goma sha biyar for what??" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Ohh for
what ko? da yake business class ticket din da ya siya maki an gaya maki na wasan yara ne ai,
to bari ki ji Business class ticket kusan 5000 dollars ne base on Airline, ki lissafa 5000 ko 4000
dollars kudin Nigeria kiga nawa zai baki" Khaleesat was speechless after realizing Safiyyah is
saying the truth, banda dala dubu dayan da ya bata da zata tafi, sannan ga kuma domestic
flight ticket from lagos to kano, and from kano to Abuja, bata mance irin hotel din da ta zauna na
few hours a garin Lagos ba, sauke idonta kasa tayi bata sake cewa komai ba, Safiyyah ta ja
tsaki tace "Wallahi ki ajiye wnn kauyancin naki ki zama wayayyiya ki dinga yin abun da ya dace,
komai a rayuwar nan kamawa yake Khaleesat, to wai ku ka zauna apartment daya ba ace
rashin kamun kai ba sai don zaki je dubasa bai da lafiya? ni abinda ke daure min kai kenan"
Khaleesat dai taki cewa komai with many thoughts running her mind, a haka dai suka rabu
kowa ya tafi gida... The next day sai da Safiyyah tasan duk yanda tayi convincing din Khaleesat
da dadin baki da masifa da bacin rai, daga karshe Khaleesat ta yarda su je can inda Housemate
dinta yace gidansu ne su dubosa amma fa don babu yanda ta iya da Safiyyah ne don har cikin
ranta tsoron zuwa anguwan take don unguwa ce na masu kudi a kasar, to in ma sun je su ce
me ya kai su? What if iyayensa ko wasu yan uwansa mata na gidan sai su yi yaya kenan? Kasa
hakura tayi har sai da tayi ma Safiyyah wannan tambayar, Safiyyah tace "Dai dai kenan in ma
iyayensa na gidan, ai ba Nigeria bane nan USA ne, kuma tsaf za su amshe mu hannu bibbiyu
su yi farin ciki da zuwan mu don duba ɗan su muka je yi bai da lafiya" Khaleesat ta sauke wani
boyayyen ajiyar zuciya, Safiyya tace "Amma ni har raina ina son sanin dalilinsa na dawowa
apartment dinki ya zauna bayan ga nasu gidan can, nace da wani abu a kasa kince min ba
haka ba, wallahi kilan ya san ki from somewhere Khaleesat" Khaleesat tace "Sai kuma kiyi ai,
nace maki bamu taɓa sanin juna da shi ba" Safiyyah tace "Ma ji ma gani dai" Sai da Safiyyah ta
fara jan Khaleesat zuwa inda za su siya kayan ciye ciye sannan suka yi ordering Uber da zai kai
su unguwan, tun da suka shigo Safiyyah ke kallon manyan Gidaje with fascination, Khaleesat
kuwa gabanta sai faduwa yake sai addu'a take a ranta, ita banda Safiyyah tayi insisting da babu
abinda zai kawota wai duba Housemate dinta, dai dai kusa da gidan Uber din ya tsaya duk suka
sauka, Safiyyah dake zaro ido tana kare ma Glass house din kallo tace "Ke kin tabbata nan ne
kar mu shiga gidan mutane a kira mana 911 mu shiga uku Khaleesat" Khaleesat bata san
sanda tayi dariya ba amma bata tanka ma Safiyyah ba, Khaleesat ta ciro wayarta tayi dialing
number Salem ita kanta zuciyarta bugawa yake gaba daya she is afraid, sai da kiran ya kusa
yankewa ya daga, sai gashi a mota zai fito daga cikin gidan, sauka yayi daga motar ganinsu,
yana kallon Khaleesat da mamaki yace "Ohh you are here, sannu da zuwa...." Gaishesa tayi ta
sauke idonta kasa kamar munafuka, ya amsa da fara'a, Safiyyah ma ta gaishesa sannan tace
"Dama ta zo duba jikin Housemate dinta ne shi ne na rakota" Yana gyada kai yace "Ohh that's
so thoughtful of her, mu je ciki to...." Suna biye da shi suka shiga cikin katon gidan, Safiyyah dai
sai gwale ido take tana bin gidan da kallo ta gefen ido, ita dai Khaleesat gabanta sai faduwa
yake sosai ko daga kai ta kasa, after walking briefly sai gasu sun iso entrance din shiga parlon
gidan, kofar shiga parlon ma kadai sai ka kalla ka sake kalla, Safiyyah ta saci kallon motoci uku
dake compound din kuma masu tsada, suna shiga parlon gidan Khaleesat ta hada ido da Ajay
dake zaune kan kujera ga different fruits daga gefensa yana kallon abu a wayarsa at the same
time yana cin apple dake hannunsa, 3 quarter ne baƙi a jikinsa with gray polo, tuni ta dauke
idonta tsabar yanda ta rikice bata ma san sanda ta bude baki ta gaishesa ba tana makale bakin
kofa, hade rai yayi ya dauke kai ya ci gaba da kallon abinda yake a wayarsa.
07087865788 ✍
[20/05, 11:45 pm] +234 812 308 8480: ✨✨HALYSAAH✨✨
By _Khaleesat Haiydar_✍
14....
Safiyyah ma dake kallonsa kamar munafuka tana in-ina tace "Good... good evening sir" Without
looking at Safiyyah ya amsa yana cin apple dinsa, Salem na kallonsa speaking calmly yace
"Ajay sun zo duba jikin Jay ne" Ajay ya ajiye apple din hannunsa, sai kuma ya kai wayarsa
kunne alamar bashi da lkcn basa amsa, ganin haka Salem ya juya ya kalli su Khaleesat yace
"Bari in masa magana a sama, za ku iya zama ku jira ni, have a sit pls" Daga haka ya nufi
stairs, ko haurawa saman bai yi ba Khaleesat ta zaro ido tace "Innalillahi" da sauri ta koma
bayan Safiyyah ganin wani jibgegen kare ya nufo su yana haushi, Safiyyah ta dinga buga ma
karen jakar hannunta tana koransa ita ma a tsorace, Salem ya dawo parlon da sauri ganin
haushin da karen ke yi zai yi attacking dinsu, Ajay ya mike ya nufi karen yana kiransa yace
"C'mon Legend" Karen ya juyo da gudu ya dawo gun Ajay da yayi patting din kansa, Salem ya
dawo kusa da su yana murmushi yace "Mu je saman kawai tunda tsoron kare ku ke, ai ba
abinda zai maku kawai yaga baƙin fuskoki ne shi yasa" Khaleesat da jikinta ke rawa ta bi bayan
Salem da sauri Safiyyah na biye da ita, a haka Salem yayi leading dinsu har sama zuwa
Bedroom din Jay, knocking yayi yana tsaye bakin kofar, Khaleesat sai waige waige take tana
ganin kamar karen zai sake biyo su saman, sai da Jay ya amsa ma Salem knocking din da yayi
sannan ya kallesu yace "Bari in sanar masa yana da baƙi" Daga haka ya bude kofar dakin ya
shiga ciki ya kullo, Safiyyah ta rike haɓa ta kalli Khaleesat murya can kasa tace "Ke wani tantirin
ɗan iska ne wannan muka gaida a kasa ya mana walakanci haka?" Khaleesat bata tanka ta ba,
har sannan kuma bata daina waige waigen da take ba don gani take fa karen nan zai iya biyo
su har sama, sai ga Salem ya fito daga dakin yana kallonsu yace "Za ku iya shiga, ni zan ɗan
fita sai na dawo" a hankali Khaleesat tace "Ohk mun gode" Bude kofar dakin tayi still gabanta
na faduwa ta shiga cikin massive room din da sallama Safiyyah dake gwale ido na biye da ita a
baya, wani ɗaddadan kamshi hade da sanyin Ac ne yayi welcoming dinsu a cikin babban dakin,
Housemate din nata na zaune saman makeken gadonsa alamar Salem just woke him up, his
room was just something else wajen tsaruwa da haduwa, Khaleesat taki yarda ta hada ido da
shi zuciyarta na bugawa ta zauna nan ƙasan lallausan carpet din dakin, a hankali yace "C'mon
Halysaah, ga gefen gado ku zauna, ko ku zauna kan kujera" Khaleesat bata dago kanta ba tace
"I am comfortable here" Ya lura kamar she is frightened, ya kalli Safiyyah dake kallonsa bayan
ita ma ta zauna, dan murmushi yayi mata yace "Hello...." Kana jin muryarsa kasan he is still
recovering, Safiyyah ta gaishesa da fara'a tana tambayarsa jikinsa, yace "Alhamdulillah, ya
karatu?" Tace "Alhamdulillah" Ya kalli Khaleesat yace "Ya kwana biyu Housemate? Hope you
are doing good?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa tace "Ya jiki?" Yana murmushi yace "Da
sauki, Alhamdulillah" A hankali tace "To Allah Ubangiji ya sauwake ya kara lafiya" Yace "Ameen
ya Allah" Safiyyah ta ajiye ledan hannunta kusa da gadon dakin tace "She got you this"
Khaleesat ta kalleta, godiya yayi masu gaba daya, sai kuma ya fara kokarin sauka daga saman
gadon yace "Bari in kawo maku ruwa" Edge din gadon ya zauna kamar bazai iya tashi ba,
Khaleesat tace "Aa mun gode, we are okay" Ya kalleta a hankali yace "To ai ba ke kadai nayi
offering ba Housemate" After some seconds ya tashi ya bude portable Fridge din dake dakin ya
dauko masu ruwa da tsadaddun lemuka duk ya ajiye masu sannan ya fita daga dakin walking
slowly, exactly irin kayan jikin Ajay ne a jikinsa shi ma, Safiyyah ta rike haba tana kallon
Khaleesat bayan ya fita, sai kuma tayi kasa da murya tace "Khaleesat kin dai ga arziki ko?
Gidansu kenan fa a Amurka ina ga Nigeria kuma?" Khaleesat ta hade rai tace "Pls stop this
Safiyyah" Safiyyah ta rufe baki da sauri, sai kuma tayi kasa sosai da murya tace "Kuma haka fa,
kar ace da Cctv a dakin mu ji kunya" Khaleesat ta wani kalleta tace "Ki ji kunya dai, tun da mun
gaishesa ki tashi mu tafi kawai" a hankali Safiyyah tace "Gaskiya Housemate din nan naki is
more than nice and calm, ni har naji yana burgeni wallahi, look how he welcomed us warmly
duk da bashi da lafiya" Khaleesat ta daga ido ta kalleta sai dai bata ce komai ba, ita dai
Safiyyah sai bin katon dakin take da kallo with fascination, tayi kasa da murya tace "In na samu
irin wannan dakin ai mance me ya kawo ni kasar ma zan yi gaba daya, anya ma kuwa student
ne Housemate din nan naki" Khaleesat ta hade rai tace "Tashi mu tafi tunda mun dubasa
Safiyyah" Safiyyah tace "Amma ai kya jira ya shigo mu yi masa sallama ko, dadina dake a ko
ina sai kin nuna halin ki, kamar ana koranmu daga shigowa gida kice mu tashi mu tafi" Budewar
kofar dakin ya sa duk suka yi shiru, Housemate dinta ya shigo da sallama ya zauna kan kujeran
dakin ya jinginar da kansa da kujeran, sai ga wani chef din gidan ya shigo da wasu tsadaddun
cookies ya ajiye masu kusa da su, sannan ya juya ya fita, Jay na kallon Khaleesat yace "Naga
kina son cookies sosai Housemate, here are some for you and ur frnd" Bata yarda ta kallesa ba
tana wasa da gyalenta tace "I am okay, tafiya ma za mu yi" a hankali yace "So soon? Amma sai
kun ci cookies tukun" Khaleesat ta ɗan kallesa suka hada ido a karo na farko tun shigowarsu
dakin, sosai taji gabanta ya fadi tayi saurin sauke idonta, ya kalli Safiyyah yace "In bazata ci ba
ke ki ci abunki... Amma ban san sunanki ba kawar Housemate" Safiyya tayi murmushi tana
bude cookies din ta dau guda daya tace "Sunana Safiyyah Adam" Yace "Maa sha Allah, it's nice
meeting you Safiyyah, i am Jawwad Ahmad, or you call me Jay" Safiyyah tace "Nice meeting
you too Jay" ita dai Khaleesat wasa da gefen veil dinta kawai take kanta a kasa, Safiyyah ta
bude handbag dinta saboda kiran wayarta da ake yi, tana dubawa taga Cousin brother dinta ne,
ta mike tace "Let me pick a call pls" Jay yace "Alright Safiyyah" Kofa ta nufa ta bude ta fita
sannan ta kullo masu kofar, ledan da suka shigo dakin dashi ya ɗan bude yace "You got me all
this Halysaah" Khaleesat ta ɗan kallesa tace "Um" Yace "Ohk thank you so much i really
appreciate" Tana kallonsa a hankali tace "Ya jikin?" Yace "I am getting better gradually, daxu sai
naji ina sha'awar wannan tuwon da kika yi some days back" Tana kallonsa tace "Na vegetable
soup?" Yace "No, wannan da na kasa ci, the dark soup, I can't remember the name" Bata san
sanda tayi murmushi ba tace "Ok miyan kuka?" Yace "Shi... kawai naji shi nake son ci sincerely"
a hankali tace "Ohk zaka je can gida anytime soon ne?" A hankali yace "Idan na samu lafiya in
sha Allah" Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam idonsa na gun different direction, Ajay
ne ya bude kofar dakin, kai tsaye ya shigo ya nufi Jay yana mika masa wayar hannunsa yana
kallonsa, ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata kalli inda yake ba, Jay ya amshi wayar
yana duba screen din, sauke ƙafafuwansa yayi daga kan kujeran da yake zaune ganin wanda
ke kan layi, ya kai wayar kunne da ladabi yayi sallama hade da gaisuwa, sai kuma yace
"Alhamdulillah Abba da sauki, wayar a silent yake ne shi yasa" Sai kuma ya daga kai ya kalli
Ajay jin abinda Abban ke ce masa, a hankali yace "A'a ba haka bane Abba, i do eat... but not
much, ba gaskiya ya fada ba" Daga haka yayi shiru bai sake cewa komai ba, after a minute
yace "To in sha Allah Abba, Allah ya kara girma" Sai da ya jira Abba ya katse wayar sannan yayi
wurgi da wayar saman gadonsa yana kallon Ajay, wani kallo Ajay yayi masa ta gefen ido ya juya
ya tafi ya dau wayarsa a kan gadon sannan ya fice daga dakin, Khaleesat ta gama tura ma
Safiyyah text din da take na cewa tayi masu ordering Lyft su tafi gida, sai kuma ta daga kai ta
kalli Jay, ganin mood dinsa ya canza, a hankali tace "Baka cin abincin ne ko?" Yace "Ki kyalesa
mana, i took cereal daxu da safe kuma a gabansa, shi in bai bata min rai ba baya jin dadi a
rayuwarsa" Khaleesat tayi shiru kamar bazata ce komai ba, can dai tace "To ai Cereal ba abinci
bane, ka dai dinga ci ko kadan ne" Ɗan murmushi kawai yayi bai ce komai ba, tace "Shikenan,
za mu koma, Allah Ubangiji ya baka lafiya" Yace "Baza ki bari Salem ya dawo yayi dropping din
ku ba?" Tace "Aa, Safiyyah nasan brother dinta ne ke kiranta a waya, kaga tun daxu muka
gama lectures bata koma gida ba" Yace "Ohk ni bari in ajiye ku" Khaleesat ta zaro ido tace "Aa
kai da baka da lafiya, za mu yi ordering Uber do not worry about us pls" Khaleesat ta mike, yana
ganin haka shi ma ya tashi, amma sai da ya dafa kujera for sometime saboda juya masa da
kansa ya fara yi, A hankali Khaleesat tace "Pls kar kayi stressing kanka, just lie down and rest"
Ya dago kansa yace "No, let me see you downstairs" Juyawa tayi ta nufi kofa, ya bi bayanta, ga
mamakinta sai ta ga Safiyyah tsabar samun waje tana zaune parlon dake upstairs tana kallo
tana cin cookies ga lemo a gabanta, to a ina ta samo lemun da cookies, Safiyyah ta washe baki
ganin Khaleesat sannan ta mike tace "Shikenan mu tafi?" Jay da ta hango ne yasa tayi tsit,
Khaleesat ta nufeta suka fara sauka downstairs a tare amma gabanta faduwa yake kar su kara
ganin karen daxu, hakan yasa ta bari Safiyyah ta shiga gaba, Jay na biye da su a baya har suka
sauko downstairs, ai ko karen na ganinsu ya nufo su da gudu yana haushi, Khaleesat ta juya a
tsorace zata koma sama ta ci karo da Housemate dinta dake bayanta, ya rikota da sauri yace
"C'mon, are you afraid of dog Halysaah?" Bayansa ta koma zuciyarta na bugawa, Safiyyah
kuwa sai kora karen take da jakar hannunta fuska daure, shi dai Ajay na zaune parlor tun da ya
kallesu sau daya ya dauke kai ya ci gaba da kallon Football da yake, sai da Jay ya kori karen
sannan ya juya da gudu ya koma gun Ajay ya zauna saman kujeran kusa da shi, Jay ya juya ya
kalli Khaleesat da ta marairaice ita ma tana kallonsa, ya ɗan yi murmushi yace "Ba abinda zai
maku ai, bai san ku bane shi yasa...." ita dai bata ce komai ba, Jay ya jufi Ajay yace "Ajay ina
makullin motana?" Ajay yace "Me zaka yi da makullin mota?" Khaleesat dai tuni ta nufi kofar fita
parlon da sauri don ko kallon Ajay bata son yi, Safiyyah kam tana kallon Ajay tace "To sai
anjima, Nagode sosai" Yace "Allah ya tsare" sallama tayi ma Jay shima sannan ta bi bayan
Khaleesat, Jay yasan bazai basa makullin ba, hakan yasa ya duba aljihun Ajayn ya zaro few
dollars sannan ya juya ya bi bayan Safiyyah, duk yanda yayi da Safiyyah ta amshi kudin taki
amsa, Khaleesat tuni ta kusa fita daga gidan gaba daya, a haka Safiyyah ta bi bayanta.
Safiyyah na kallon Khaleesat bayan sun shiga Lyft har sun fara tafiya ta