Showing 21001 words to 22578 words out of 22578 words

Chapter 8 - SALWA BOOK BY HAFSAT UMAR DANGORO .pdf

Dan Kar ta raina shi,
zai zaunane bakinciki ya kasheshi Yana gani ya Abdul ya aureta " wani wawan Mari zubaida ta
tsinka mata hadi da cewa "to uban waya saki ,har da zakizo kina fadamin wai sabi da Yana
sonta ya tafi ,aini gwara da yatafi din yadda zan Fi lakadawa shegiya duka, ko ya kikace
Ameera?" Dariya Ameera tayi tace ,wallahi Nima nasamu dama ,tun da ya Abdul bashi da lafiya
kullum Yana daki a kwance Nima nasamu da mar da zan nakasa shegiya kowa ya huta......


"Uhm a banza tun da haryanzu ihu ake abayan hari,inga aiki da cikawa kawai shine zan
tabbatar da son da kikewa ya Abdul"Zarah ta fada hadi da hurgawa Ameera harara, ",kan uba ni
kike fadawa haka wato har raini ya soma shiga tsakanina dake, Ameera ta Kai mata duka
Afusace, fuzge hannunta tayi daga rukon da Ameera tayi mata tace "karki kara dukana na fada
miki ,karkiga ni kanwarkice kice Zaki dakeni na kyleki wallahi ramawa zanyi" "au yanzu zarah ni
kike cewa idan na dakeki Zaki rama, wato raini har yakai haka, dafarko nace inason ya Abdul
kema kince kina sonsa na hakura na zuba miki ido Naga iya gudun ruwanki, shine yanzu har
dakin rashin kunya to bari ya huzaifa ya dawo wallahi sai kin raina kanki" daga haka Ameera ta
bangajeta tafice daga dakin zuciyarta nayi mata zafi.




Tom bayan fitar Amma daga dakin, abbane ya dauki wayarsa ya Danna wata number bugu
Daya zuwa biyu aka daga hadi da yin sallama "assalamualaikum" "wa alaikumussalam Alhaji
YUNUS kana lafiya?" "A,ah lafiya klau alhamdulillah Alhaji LAMIN Daman ana jinka kanan, Kai
ka manta da mutane haba ,rabona da na ganka tun rasuwar d'an uwanka ABDULHAMEED,
gaskiya baka da kirki wallahi" dariya Abba yayi yace "wallahi inan abubuwane sun mun yawa
Kuma ga busy duk na shiga shiyasa Amma dai yanzu kana lafiya?" "Lafiya kalau alhamdulillah

ya yaran ina uban Muskilanci shugaban kywawa" alhaji yunus ya yayi tambayar Yana dariya,
murmushi Abba yayi yace "Kai kyleni da Sha,anin yarannan Yan bana bkwai ka haifesu baka
haifi halinsu ba, ya yaran gurinka" "sunnan lafiya kwanaki kausar tayi nacin na barta yazo gurin
Ihsan tasamu hutu Kuma Allah bai yiba" "bawani nan Kai ka hanata zakace wani hmm" Abba
yayi shiru, "uhm ba haka bane wallahi ina Kuwa yarinyar Nan 'yar wajen murugayi kuna Kuwa
zuwa dubata?" "Uhm ai nadawo da ita gurina tun ranar da Zamu taho da ita muka taho ,Kai ma
kasan ina da yadda zanyi na rike ta bazan barta acan TA wulakanta ba, yanzu ma magabarta
ce ta sa na kira ,ina son zata zonan kasar karatu shine nace to Dana kama mata daki a waje ai
gwara ta zauna a gidanka sai hankalina yafi kwanciya duk da nasan halin salwa baza ta taba
watsa min kasa a ido ba" washe baki alhaji yunus yayi yace "ah gaskiya kayi dabara mai kyau
,tun da dai muna kasar kawai ta zauna din Babu matsala yaushene zata soma karatun ?" "Eh
dai Nan da sati guda nakeson komai ya kankama insha Allah dakaina zan kawota ,in yaso sai
na dawo" Tom godiya Abba yayiwa alhaji yunus sosai sann sukayi sallama Abba ya kashe
wayar.


*Dubai*

Kausar da ke kusa da mahaifinta CE ta kalli Abba ta wan da ya gama waya yanzu, Daman tun
da taji cewar da abban TARABA yake waya tashiga murna tadawo kusa dashi domin taji mai za
ace, Yana katse wayar tace "Abba wai Ihsan ce zata zo karatu Nan?" Tayi maganar taba dariya
alamar murna, domin kausar su biyu Allah ya bawa alhaji yunus,daga ita sai yayanta namiji
Shima baya kasar shekara 3 da suka huce, shiyasa ta damu taje TARABA kodan ta samu
kawar hira, tun da agidan su ba fita take ba, sai dai ta zauna a gida tayi shiru ,ko Kuma ta
zauna da Momynta ita kuma batason hira da mahaifiyar ta sabi da ba komai ne zakace zakana
hura da mahaifiyar ka akai ba, alhaji yunus ne ya kalli yar tashi yace "Uhm mamana ummiterh
ne zata zo 'yar wajen murugayi ba Ihsan ba" baki kausar ta washe hadi da cewa " lahhh Abba
wannan yarinyar kekkewa ita?" "Eh eta mana " ya bata amsa a takaice, "WALLAHI Abba inason
yarinyar Nan Tana burgeni Abba kaga dai 'yar kauyece Amma kwata kwata batayi kala da
kauyawa ba, kamar ba a kauye ta taso ba, wai yanzu Abba ya kake ganin yarinyar Nan idan
akace ta dawo burni AI sai tasa Maza suna rigima akanta" dariya alhaji yunus yayi hadi dacewa
"kin ganki ko sai wani zuzuta mace 'yar uwarki kike, to shikkenan ki kwantar da hankalinki Indai
salwa ce sai kin gaji da ganinta " wani tsalle kausar Tayi ta fada jikin abbanta Tana murna ,"a,ah
karfa ki karyani mamana ke bikisan kin girma ba ne to saina kira nace bamanan ta fasa zuwa
ma" saurin daga abban nata tayi tace "Dan Allah Abba kayi hakuri kada ta fasa zuwa" tayi
maganar kamar zatayi kuka, "a,ah to yaukuma anji kanku keda abban naki kenan " kausar taji
maganar ,dasauri ta daga kanta, hango Momynta tayi tana kokarin zama , da gudu ta fada
jikinta Tana dariya tace "Momy albishirinki?" "Goro " "fari ko ja?" "Fari fata shalelena" "to Nan da
sati daya ummiterh zata zo Nan karatu" "kai Dan Allah dagaske kike ?" "Allah dagaske nake
Momy yanzu Abba yagama waya da abban TARABA " dariya Momy tayi hadi da cewa "oh kace
su kausar an samu abokiyar zama sai Kuma abin da ya karu ko " Dan tsuke fuska kausar tayi
tace "uhm uhm Kai Momy Maine zai faruto?" "A,ah rashin jinki zai karu mana , hakama ya
lafiyar kura ballantana Kuma kin samu kawa, Dan ma ita yarinyar Nan akwai nutsuwa duk da

ban zauna da ita ba" "uhuhm uhm Momy mai kike nufi kina nufin dai ni bani da nutsuwa
kenan?" Tayi maganar hadi da mikewa zuciyata cike da bacin Rai wai ita a lallai taji haushi ta
shige dakin ta .


Bayan shigar ta Momy ce ta kalli alhaji yunus tace "Abban najib wai dagaske ne salwa zata zo
Nan karatu ,banaji ance an daura aurenta da suhail ba ko karyane?" "Uhm kinjiki Daman ana
wasa da aurene da gaskene anyi auren ummiterh da suhail watanni uku dasu ka huce" "to
Amma Kuma zata zo Nan karatu mai zaisa bazata zabi us ba tun da shi big bro acan yake da
zama, Anya kuwa auren yanan" "kinga zainab bana son shashan ci ina ruwanki da aurensu ita
Nan ta zaba idan Kuma gidan kine bakison TA zauna sai ki fada naji" "a,ah ni fa bance ba ,ni
Kuwa nakeson ummiterh ,haka kurum yarinyar take burgeni ,Daman abin da yasa nake
tambaya wai da ita auren ne ya mutu sai mu hadata da najib Naga yarinyar akwai nutsuwa"
"uhm Abba yayi kwafa yace "to idan auren bai mutu ba saiki kasheshi " yayi tsaki ya mike ya
shige daki ya bar Momy a gurin a zaune . "Uhm kwama gama boye boyen ku Indai nice saina
gano komai a to " itama daga haka ta mike tashiga nata dakin.



*U.S*


Tun da jirgin su big bro suka tashi basu sauka ba sai misalin karfe' 2:30 na washegari ranar da
suka tafi, Kai tsaye babban gurin saukar jirgi na kasar us jirginsu ya sauka, tunkan su isa ilahirin
yaran sa dama manyan sojoji masu fada aji suka tsaye domin tarbar sa, sosai filin jirgin ya cika
da sojoji in da kasan wani babban Dan soyasane yazo ko shugaban katsa, ni abin har mamaki
ya soma bani yadda Naga Dan karamin yaro Yana bawa mutane umarnin da mulkarsu, ban
gushe daga tunanin da nake ba, na hango wani kekkewan saurayi sanye da riga da wando
wadan da suka karbeshi suka haskashi yayi kyau sosai abin sau wan da yagani , glas din sake
idonsa na kalla baki wulik baka iya ganin yanayin idonsa sai dai shi ya ganka, a sannu yake
takowa daga cikin jirgin Yana taka mattatakalar cikin nutsuwa da takama, gefe guda Kuma
samir ne tsaye Yana sakar masa murmushi, da matarsa da Kuma kannen sa guda biyu mata,
Daya daga cikin 'yan matan ne ta kalli dayar tace "ke Salma wai bakiga yadda yaya ya kara
kauba wow Amma fa wannan gayen ya hadu" "hade rai wadda aka kira da Salma tayi tace
"aikin banza abin da mun rasashi kina dai ji yaya samir tace aure akayi masa, dalilin komawar
sa guda kenan, ai wallahi tsofaffin Nan nasa basu kyau ta mana ba, haba Shima kamar wani ba
wayeyyeba Yana da class Amma bazai tsaya ta zabi mai aji ba" "uhm ni dai ban hakura ba
wallahi idan ma ke kin hakura ato Dan wallahi saina aureshi, cewar halima "to taya kenan"
"hmm Salma kenan ai Allah ya halatta nasa ya auri mata Daya Daya Daya Daya har hudu
,Kuma dai kinsan waccan matar cushe ce nikuwa zuciyarsa zan sace, ke baki samu labarin
bakwauyiya ya aura ba? "Au wai Dan Allah dagaske 'yar kauye ce"... "Hmm muje gida Kisha
labari ai naji lokacin da shi suhail din yake fadawa yaya samir cewar baya sonta mai zaiyi da
'yar kauye

End book 1

09166764540 HAFSAT UMAR DANGORO
Paid book #500 KACAL

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login