Showing 51001 words to 54000 words out of 62597 words
Chapter 18 - CENTUAR COMPLETE Book by Aisha Sani Abdullahi .pdf
ce,"Wai kai wani irin mutum ne, shin ka zama Mace ne da ba za ka iya daukan
mataki akan wancen wawan ba? Kar ka manta fa tun da cen ba ishasshen wayo gareshi ba
amman yanzu ka barshi har yana iya tada mana hankali? Ba ma wannan ba ga dukkan alamu
fa so yake ya karbi mulkin nan, kana gani? Ka zuba idanu kana gani ba wani matakin da zaka
iya dauka?"
Tsawar da ya yi mata ne yasa ta dawowa cikin hayyacinta.
"Ke kin fini son sarautar nan? Kin san tun ina da shekaru nawa a duniya na fara wannan shirin?
yayin da ake yiwa Ɗan shekara goma kallon yaron da bai san me yake ba,ni a lokacin na jima
da gama fara shirina,kuma ba wanda ya isa ya tarwatsa mun komin tsanani ko da kuwa zan
rasa raina ne sai dai kowa ya rasa,ki fice mun da gani tun kafin ranki ya yi mugun ɓaci." Ya faɗa a fusace yana nuna mata bakin kofa.
Daren ranar gabadaya yan gidan taruwa sukai a falon Hajiya kaka illa Mai Martaba da Kilishi da
suke can suna fama da tasu damuwar.
Sai da dare ya raba kafin kowa ya koma part dinsa.
Janinah kuwa damuwarta kawai hanyar da zata bi ta kaiwa Farouq abinci.
Ta zo zata bashi kenan daya daga cikin masu gadin suka kamata.
Aka sanar da Mai Martaba dukkanin yan gidan kowa ya fito aka yi cirko-cirko.
Cikin fushi Mai martaba ya bada umarnin cewa ita ma a turata ciki tunda har tana tausayinsa ai
sai ta tayashi zama.
Hakan kuwa aka yi.
Maamah da sauran matan sai kuka.
Cikin karfin hali ta kalli Mai Martaba ta ce,"Amman ka cika azzalumi na karshe."
Ta tafi tana kuka.
Ko kallonta bai yi ba ya gyada kai ya juya ya tafi abunsa shi ma.
Kilishi kuwa wani irin kumburi ta fara tana nishi a zuciyarta tana fadin,"Lallai rasa ran yarinyar
nan daidai yake da wasa da rayuwar sarautar Arham,ba zai saɓu ba,ba kuma zan lamunce ba."
Ta kudurta aranta itama tana tafiya.
☆☆Farouq ya ce,"Tausayina ya sa kin jefa kanki cikin matsala, ban ji dadi ba,kuma ban so
faruwar hakan ba,ki yi hakuri ki yafe mun nine sila."
Janinah ta laluba hannun Farouq ta rike,"Zamana cikin duhu da yunwa tare da kai ya fi mun
zamana cikin haske da abinci Ya kai Ɗan Uwana,bana jin tsoro ko fargabar komai indai zan
kasance a tare da kai,ban yi nadama ba,kuma ba zan taɓa nadama ba."
Hira suka dunga yi har barci ya kwashe Janinah.
☆☆Da asubar fari aka fara yekuwar Rasuwar Baba Malam,Yarima Rasheed ya fito da sauri
yana kara maimaitawa,"Baba Malam?"
Ba shakka sunanshi ya jiyo ana sanar da cewa za a sallace shi.
[06/07, 2:52 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-31
Zuwa ya yi shima ya shiga sahu suka sallace shi bayan sun dawo ya gidan Baba Malam ya
koma.
Yana zuwa ya tarar da Iyalansa nata kuka,Yaransa da Matarsa wacce karfi ya gama barin
jikinta.
Yarima Rasheed bayan ya gama yi masu gaisuwa ya ce,"Amman jiya fa ƙalau muka dawo da
shi gida,bai nuna mana wata alamar rashin lafiya ba."
Matarsa ta ce,"Tabbas ya shigo lafiyarsa ƙalau cikin yanayi na farinciki ma irin wanda zan iya
cewa na jima ban ga annashuwa a fuskarsa kamar jiyan ba tamkar wanda aka yiwa albishir da
gidan aljanna kuma har ya kwanta yana cikin ƙoshin lafiya,asuba ta yi,mun saba shi ke
tashinmu sallah yau muka ji shiru har na tashi,hakan yasa na je dakinsa in duba ko ya makara
ne tunda jiki da jini kila gajiya tayi yawa ashe shi ya jima da barin duniyarma akan
shimfiɗarsa,yanzu irin mutuwar da ake kenan zaka rabo da mutum lafiya yanzu anjima ka ji
ance ya bar duniya,Allah Ubangiji ya ji kanka ya gafarta maka Malam."
Ta karasa maganar tana share hawayen da ke zuba a idanunta.
Yarima Rasheed ya amsa da,"Amin amin,Allah ya kara hakuri,bara inje."
Ya masu sallama sannan ya fice zuciyarsa cike fal da sake-sake domin bai gamsu cewa Baba
Malam Mutuwa ya yi kawai ba babu shakka akwai sanadi.
☆☆☆☆
Cikin fushi Kilishi ta kara nufa Bangaren Mai Martaba.
Zaune yake ya yi tagumi yana tunani a bakin gado.
Hankada kofar ta yi kawai ta shige ba tare da ko sallama ba.
"Alkawari dai kayane kuma kasan nima na sha wahala wajen tabbatuwar burinka tare da nufin
nima za ka cika mun nawa,nina rufa ma asiri kuma baka goyon bayan kashe mahaifinmu
sannan ka kore Ɗan uwanmu,ka sheda mini cewa mulki daga kanka zai dawo karkashina ga
duk Ɗa namijin da zan haifa,hakan yasa muka shirya haɗa auren Janinah da Arham domin
tafiyar komai cikin sauki amman yanzu na lura ita kanta yar taka ma so kake ka kasheta,to ni
wallahi Allah na yi rantsuwa babu kaffara ko da ace yarka ta bar duniya batun zama Sarkin
al'adun Arham babu fashi,ni bai dameni ba duk yadda zaka yi ka je ka yi domin tallafar mulkin
nan in ba haka ba kuma ko da allura ta tono garma kai ka sani kuma ina kara tunatar da kai
cewa kamar yadda zaka iya komai akan Sarauta nima zan iya kila ma mafiyin hakan."
Tana gama faɗin hakan ba tare da ya ce mata komai ba ta fice abunta.
Dafe kanshi ya yi yana juyawa tare da bin ficewarta da kallo kawai.
☆☆5stars sunji shirun Farouq ya yi yawa,mussamman Zeeyter ta damu,Zoe kuwa har Khalil ta
kira tana tambaya shin lafiya kuwa domin wayarsa akashe,dake sun karbi wayar sun kashe
kafin suka sa shi a dakin duhun.
Maaah kuwa da ta kira su sanar da ita cewa sukai aikine ya masa yawa amman yana cikin
koshin lafiya suka dai yi mata jawabin da zai kwantar mata da hankali duk da cewa ita dai jikinta
ya bata cewa akwai matsala lallai Farouq na cikin wani hali.
Ganin ba yadda zata yi hakan yasa kawai ta dage ba dare ba rana ta na yi masa adduoi kamar
yadda ta saba.
Number Javed suka nemo cikin record dinsu.
Suka fara bibiyarshi,da farko dai yaki fada masu komai amman daga karshe da ya fahimci su
din su waye kuma Farouq na yawan bashi labarinsu hakan yasa ya laburta masu dukkanin
abun da ke faruwa.
Lokaci guda suka shirya zuwa nigeria,Khalil ne ya kira Zoe domin daukan private jet,Khalil da
kanshi ya je ya dauko Maah kan cewa Farouq ne ya ce a daukota,Deejerh da Xavier,Haiydar da
Zeeyter dukkanin su sun hallara a malaysian daga nan suka nufo nigeria kai tsaye.
Sun sauka a Abuja sun kama hotel sai da suka kwana tukunna washegari suka dauki motoci
biyu suka shiga cikin Niger da ke tun acen Haiydar ya masu ordern mota.
Suna shiga cikin Mokwan ma Hotel suka kama sannan suka kira Jeved suka sheda masa inda
suke.
Javed ya sanar da Yarima Rasheed komai hakan yasa suka tafi tare.
Dukkaninsu suna zaune a falon hotel din,suna shiga Yarima Rasheed na hada ido da Maah ya
kame kam bakinsa na rawa ya ce,"Ma....ri...am."
Ita ma ta ce,"Rasheed."
Dukkanin su suka yi shiru suna kallon juna,Zeeyter da Zahra ne suka tashi suka rike Maaah
suka zaunar da ita sannan Khalil ya je ya rungume Yarima Rasheed yana fadin,"Welcome Dad."
Murmushin karfin hali ya yi kafin ya ce,"Thank you."
Shi ma ya zaunar da shi,Khalil ya ce,"Duk da cewa ku ne gaba damu kuma Iyayenmu amman
muna neman alfarmar komai ya wuce please,mun san komai,kuma kowa cikinku ba ya da laifi
akan barin kowa babu shakka wannan tsarin ubangijine,babbar damuwarmu a yanzu shi ne mu
maida hankali kan fito da Farouq tare da taimaka masa kan tabbatar da kudirinsa na alkairi. "
Cikin zaƙuwa Maah ta ce,"Ina yake? Me ya faru da Umar? Me ya sameshi? Don Allah ku faɗa
mun."
Zahra ta rike hannun Maah kafin ta ce,"Maah In sha Allah Farouq na cikin koshin lafiya, Sarki
Abdul-Raheem ne ya sa aka kulleshi a dakin duhu na tsawon kwanaki amman In sha Allah zai
fito kuma cikin aminci da ingatacciyar lafiya. "
Ajiyar Zuciya Maah ta yi kafin ta daga hannunta sama tana fadin,"Ya Ubangiji na ya Allah kafi
kowa sanin gwagwarmaya da kalubalen da wannan bawa naka ya fuskanta tun kafin zuwansa
duniya da zuwansa yarintarsa,girman sa da yanzu,Ina Roƙanka da bashi ikon ganin haske
saɓanin duhun da aka sanya shi,ka haneshi da jin yunwa,kishir ruwa da duk wata azaba dake
tattare da inda yake,Allah ka kare mun shi ka ƙara masa kwarin gwiwa da karfin zuciya."
Ta karasa faɗan hakan tana goge hawayen da ke zuba daga idanunsa.
Rungumeta Zahra ta yi tana shafa mata baya.
Yarima Rasheed ya ce,"In sha Allah babu abun da zai same shi,sannan abun da yasa ba za ku
je gudan yanzu za a iya samun matsala,a tsakanin daren jiya da asubar yau aka kashe Baba
Malam wanda muke samun bayanai agunsa,shi kadai ne ya san komai,don haka ko da na ji
mutuwarsa ban aminta da mutuwar ba a gaskiya nafi gasgata cewa kasheshi aka yi kuma
domin taimaka mana da yake ne amman kuma abun da ba a sani ba shine akwai wanda yafi
Baba Malam din don haka komai zai tafi daidai kuma sai an daukanawa Baba Malam fansa da
ikon Allah,zaku ci gaba da zama anan tukunna in bukatar ku ta tashi zan sanar da Javed ya
faɗa maku ku zo domin aikine ja a gabanmu babba ba karami ba."
Khalil ya ce,"Babu matsala muna nan kuma zamu bada goyon baya ɗari bisa ɗari sai mun
tabbatar da kasancewar komai daidai kafin mu bar kasar nan da ikon Allah sannan muna tare
Jami'in farin kaya na ɓoye." Ya nuna Xavier kafin ya ci gaba da fadin,"Zai fara yin binciken
dukkanin abubuwan da ke tafiya ta ƙasa tare da tsaurara tsaro gudun samun kowacce irin
matsala."
Yarima Rasheed ya ce,"Ma sha Allah na ji dadin hakan kuma nima zan haɗashi da wa inda
zasu iya tallafa masa,Allah ya bamu sa'a. "
Bayan sun gama tattaunawa tafiya suka yi suka bar Maaah da Yarima Rasheed a falon domin
su tattauna.
Dukkaninsu sunyi shiru kowa da abun da yake saƙawa a zuciya,lokaci guda kuma duka suka
haɗa baki da fadin,"Shine....
Sai kuma suka yi shiru.
Murmushi Yarima Rasheed ya yi ya ce,"Ki ƙarasa ki faɗa."
Girgiza kai ta yi ta ce,"Aa ka yi maganar ka tukunna."
Ya ja numfashi kafin ya ce,"Shin kin san da cewa na koma ƙasarku ban sameki ba? Me yasa
baki nemi ni ba? Me yasa baki zauna a gunda kika san zan iya ganin ki ba?"
Maah ta ce,"Ban yi tunanin zaka nemeni ba ganin yadda aka rabamu hakan yasa ko da dana
koma gida Iyayena suka ƙi karbana da Addinin musulunci na gwammace da na bar ƙasar
dukanta domin in samawa kaina da Ɗana sabuwar rayuwa."
Yarima Rasheed ya durkusa gabanta yana fadin,"Ki yafeni Mariam, duk nine sila,ni ne silar
faruwar komai, Don Allah ki yafe mun na san na yi kuskure babba a rayuwata ki yafemun. "
Murmushi ta yi kafin ta ce,"Kuskure kam dukkaninmu munyi domin da ace ban yi sanadiyar da
zaka sha giya ba,da duk komai bai faru ba,amman kuma Bawa baya taɓa wuce kaddararsa sai
dai ya ķasa karbanta yadda ta dace,sannan kasancewata da kai ko ba komai ya zame mun
alkairi domin kuwa gani ina rayuwa mafi dadi da yaƙini wato rayuwar musulunci sannan Farouq
duk da cewa ba ta hanyar aure aka sameshi ba amman kuma ya zam alkairi gareni da ma
dumbin al'umma masu yawa tabbacin shi Ubangiji mai rahama ne kuma mai jinƙai sannan mai
ƙarban tuba,don haka ka tashi ka zauna jima da yafe ma kamar yadda nake sa ran cewa
Ubangiji ya yafe muna muma."
Tashi ya yi ya zauna yana fadin,"Ba shakka hakane amman na ji dadin dauwamarki cikin
addinin musulunci sosai da ace wasu ne duk abubuwan nan ya faru da su tuni zasu fice."
"Rashin karfin Imani da karban kaddara ke kawo hakan kuma ai aduk inda zaka kasance dole
akwai kalubale muddin kana rayuwa cikin duniya."
Maaah ta fada.
Yarima Rasheed ya ce,"Hakane kam, abu mafi dadi shine da baki yarda zoben alkawarinmu ba
kamar yadda nawa yake nan."
Kallon zoben suka yi duka suna Murmushi,ya ci gaba da fadin,"Sannan kuma na ga Farouq ya
taso da sanin Computer yana abubuwa tamkar ni."
Maah ta ce,"Ai ance kyan Ɗa ya gaji ubansa hakan yasa tun yana jariri nake kwaɗaita masa so
da kaunar na'ura hakan yasa ya ginu cikinta tun daga yarinta har girma karshe ma sai ya nuna
mun ya fini sonta."
Kallon agogon hannunsa ya yi ya ce,"Oh lokaci ya kure,bara inje zakuji duk abun da ke tafiya. "
Sallama suka yi fita ya samu Javed da Manager suka tafi.
Suna shiga cikin gidan.....
[10/07, 3:23 pm] Xayyeesherthul-humaerath: *CENTURE*
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Labari/Rubutawa
Aisha Sani Abdullahi
Xayyeesherthul-humaerath
The End Of A 5-Stars Chronicle
# Yel#Freeya#Vixeen#Centure.
*We're offering affordable advertising opportunities for your business. Contact me at
08103080717*
PAID ADVERT
*Saudahtu Collections&Data Services*
Your one-stop shop for all your fashion needs!
*What We Offer:*
- Abayas
- Hijabs
- Shoes
- Shadda lace
- Normal lace
- Fabrics
- Bed sheets
- Materials
- Kitchen essentials
- Home decor
- s dresses
- English wear
- And many more!
*Visit Us:*
Aliyu Mustapha, Yola and Kano Dorayi
*Get in Touch:*
Call/Text: 08036600240
*Nationwide Delivery Available! *
You can join our group
https://chat.whatsapp.com/EKg8iYM65EcCLY6KZIQhlT
*Stay Stylish with Saudahtu Collections!*
PAID ADVERT
INA MATA MASU NEMAN MAGANIN INGANTA NISHAƊINSU DA MAI GIDA, INA MASU SON
ZAMA TAURARI AGIDANSU ?MAZA GARZAYO GUN YAR SOKOTO DA IZNIN ALLAH
KAYANKI SUN TSINKE A GINDIN KABA
INA MASU FAMA DA INFECTION KUZO GA MAGANI DA YARDAR ALLAH
AMAREN GOBE, KU MA BAN MANTA DA KU BA .
MUNA DA GARIN MAGANI KALA-KALA GUMBA KALA-KALA KAZA, DANBUN KAZA TSIMI
SA TABAJE DA DAI SAURAN SU. DOMIN KANKARO MIKI MUTUNCI A WURIN YALLAƁAI
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI KUMA SIYAN NA GARI MAI DA KUDI GIDA.
DOMIN ƘARIN BAYANI KU KIRA WANNAN NUMBER 08159450159 KO TA WHATSAPP
PAGE-32
Suka ga anyi cirko-cirko an fito da Janinah tana numfashi sama-sama.
Masu maganine kewaye da ita sunata faman kokarin ganin sun ceto rayuwarta.
Da sauri Yarima Rasheed ya karasa yana fadin,"Subhanallah me ya faru?"
Abba Malik ya ce,"Wallahi Janinah ce ba lafiya yanzu masu gadin dakin suka sanar da mu kan
cewa Farouq na ta kwala kira,da kyar take numfashi gabadaya yanayinta ya sauya jikinta kuwa
duk ya gama sakewa."
Karasawa inda take Yarima Rasheed ya yi ya dauketa yana ,"Wannan ina ga akwai bukatar aje
asibiti."
Yana fada sai suka fara kallon kallo.
Mammah kuwa ban da ruwan hawaye babu abun da take ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Kallon Abba Malik Yarima Rasheed ya yi ya ce,"Ku dauko mota muje asibiti mana ko baku ji
bane?"
"Ai Mai Martaba ya haramta zuwa asibiti a cikin gidan nan sai dai masu maganin gargajiya su
duba mutum kawai." Abba Malik ya fada.
Tsaki Yarima Rasheed ya yi cikin ɓacin rai Ya ce,"Yarinya sai suma take tana farkawa da wani
irin numfashi ku tsaya wasa ai sunyi iya yinsu tunda abun ya gagara dole ne akaita asibiti akan
wata dokarshi sai a bari yarinya ta rasa ranta?" Ya karasa maganar yana daukan Janinah a
hannunsa.
Muryar Mai Martaba ya jiyo yana faɗin,"Ka da ka yi gigin fita da wannan yarinyar daga cikin
masarautar nan in dai masu magani ba za su iya ba sai dai amaidata cikin dakin da take ta
mutu acen domin ni duk wanda ya shiga gonata babu ragi tsakanina da shi ko da kuwa ɗan
cikina ne."
Kallonshi Mammah ta yi tana hawaye kafin ta ce,"Ban taɓa tunanin rashin imani da tausayinka
ya kai har haka ba,to wallahi ko da ace hakan shi zai zam sanadiyar mutuwar aurena sai dai ka
sakeni amman ina goyon bayan a fidda 'Yata akaita asibiti. "
Ta karasa maganar tana tsayawa gaban Yarima Rasheed.
Yarima Rasheed ya ce,"Ba ruwana da wata dokarka domin bata shafeni ba, sannan a yau zan
fita da Janinah asibiti ne a matsayin Mahaifi gareta kuma Yaya ga wanda ya haifeta." Yana
fadan hakan ya bude mota yasa Janinah ciki Mammah ma ta shiga ciki sannan Abba Malik ma
ya shiga suka fice daga Masarautar.
Bin kowa da wani kaskantaccen kallo Mai Martaba ya yi