Showing 18001 words to 21000 words out of 136541 words

Chapter 7 - 2&3 AUREN KWANGILA COMPLET by Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

har bai manta ba shi ne garin da mahaifiyar Suhaana ta gaya masa nan ne
garinsu. Allah mai karfin iko! Buwayi gagara misali.
Shi da Sagir suka yi sallar magriba, ya ja shi dining suka ci abinci, tuwon shinkafa ne miyar
taushe, ta ji tantakwashi da man shanu. Yaushe rabon da ya ci tuwon shinkafa! Sosai ya ji dadin
abincin ya yi musu godiya. Naira dubu biyar ya ba wa yarsu, ya ce ta sha (choculate). Uwar ta yi
godiya suka rako shi har bakin motarsa ya ja ya tafi suna daga masa hannu. Yana tafe a kan titi yana tunani, sanyin A.Cn motarshi na ratsa kasusuwa da bargonsa. Allah ya
dube shi ya kusa yanke masa wahala insha Allahu. Zai cika wa Hafsat alkawurrurukan da ya
daukar mata a kan lokaci, zai ci gaba da manne wa Sagir tare da bincikarsa har ya tabbatar da

zarginsa, amma ba zai hada su da Hafsat ba in har ya zamanto da gaske sune yan uwanta, sai
waadin aurensu ya cika.
Don haka ko da ya shigo ta dade da yin bacci. Bai damu da ya neme ta ba ya wuce dakinsa
don ya san yau ba ta da damuwa tunda ta yi magana da Mammanta, hankalinta ya kwanta.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da
Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan
zunubi ranar gobe kiyama*

Barrister Abdulazeez Dakata ya koma da bayansa ya jingina a jikin kujerar da yake zaune.
Kewar Muazatu ta sauko masa, yau kwana uku ba su yi magana ba, ya san kuma bai isa ya
kira ta a wannan lokacin ba (as a law-school student). Fassara reactions din Suhaana yake so
ya yi, wadanda ta yi yau a gabansa ya gane inda ta sa gaba, ya kasa. Idan haushinsa ta ke ji
me ya yi mata? Da ma can ya yi mata alkawarin samun kulawa irin ta maaurata ne da yanzu ya
saba alkawari ya bata mata rai? Ya yi zaton ya fada mata kowa zai yi zaman kansa ne ba tare
da shiga rayuwar dan uwansa ba?
In ta manta ne zai iya sake zaunar da ita ya sake yi mata rehearsal na rayuwar da za su yi har
zuwa waadin auren. Idan bukata gare ta na wani abu, ko kayan abinci ta bude baki ta ce babu
kaza mana, shi yake hana ayi zalinci balle shi a kan-karan-kansa ya zalunci na kasa da shi. Ya
ci gaba da lalubawa cikin kwakwalwarsa yana nemo ta inda ya kuskure mata. Wata zuciyar ta
ce, Kicin... waya... audugar mata...!!!
Kansa ya sara, wadannan ma bukatu ne masu muhimmanci a wajen mace tunda ya san ba zai
iya bukatar da ta fi kowacce din ba. Mikewa ya yi ya nufi kicin yana dube-dube, abubuwa da
yawa irin su dankali, albasa, doya, kayan miya duk babu. Ya bude freezer da sauri ya mayar ya
rufe. Babu komai! Ya bude firji nan ma babu komai na kayan girki, irinsu (Veggies), babu
lemuka, babu ruwan sha komai na kayan masarufin gida babu a kicin din. Ya so ya fahimci
hakan tun da jimawa abubuwan da ke kansa suka mantar dashi. To don me ba za ta bude baki
ta gaya masa ba? Ko bata da baki ne?
Zuciya mai gaskiya da adalci a tsakiyar kirjinsa ta ce da shi.
A ina ta ganka? In ka dawo ba ka nemanta, in za ka fita ba ka gaya mata. Kowanne irin aure
akwai bincikar lafiyar iyali a cikinsa, banda naka.
Kikkifta ido ya shiga yi, irin na guilty conscience, ya fito daga kicin din. Ya sa a ransa zai dinga
bincikar lafiyarta ko da bayan kwana dai-daya ne.
Dakinsa ya shige ya yi wanka, ya yi sallar laasar ya sanya kananan kaya marassa nauyi ya
dauki makullin motarsa ya fice.
Kasuwa da supermarkets ya shiga, duk abin da ya kamata maigida ya ajiye a gidansa ya sayo,
wanda zai jima bai kare ba. Hatta pad katon guda ya saya. Waya ce dai har yanzu zuciyarsa ta
ki amince masa da ya sai mata a kan dalilai masu dama. Ya juyo kan motarsa ya nufo gida,
booth dinsa da kujerar bayansa shake taf da kaya. Danfulani ya sa ya kwaso kayan ya shiga da su kicin ya tsaya yana nuna masa inda zai adana
kowanne.

******
Sanda Hafsat ta dauki computer din Abdulazeez ta shiga daki tsakiyar gadonta ta ajiye ta, tana
cike da doki ta nemo takardun karatunta cikin lockers din da ta adana wasu muhimman
takardunta da littattafai na makarantarsu ta (St. John Berchamans College). Lokacin da
Mammahta hadasu cikin kayanta don ta san watarana za ta bukace su. A dokance ta ke komai, amma me? Tana kunna system din fuskar wata kyakkyawar mace ne a
home-screen din tana kwance a kan hannayenta tana sakin wani irin tattausan murmushi. An ce
ko ba SO aure daban yake, Allah (Subhanahu wataala) shi kadai ya san iyakacin karfin izzarSa
a cikinsa. Ji ta yi ranta ya wani irin jagule, zuciyarta ta matse, idanunta sun rufe da kansu. Ko
bai gaya mata ba wannan ce Muazatu kenan. Wadda Abdulazeez ya yarda ya saba wa
iyayensa a kanta, ya jefa Mammah cikin dawwamammen bakin ciki da bacin rai a kanta. Ta ji ta
tsani Muazatu, wata irin tsana da ba ta taba yi wa dan-Adam dan uwanta ba. Bacin ran da ya
sanya ta kasa yin abin da ta ke dokance da yi, zuciyarta ta yi duhu matsananci. Kawai sai ta
kashe komai ta ture gefe ta koma ta kwanta, ta lumshe idanunta.
Sai da suka gama kimtsa komai ya sallami Danfulani, ya zuba ruwa a karamar tukunya ya dora
a gass ya kunna. Nan da nan ya yi zafi, ya dauko ledar cous-cous cikin katon dinsa ya farke ya
juye rabi. Ya kashe gass din. Ya kwashe gabadaya a (food-warmer) ya diba a plate. Miyar da
ransa ya biya da ita tun dazu ya diba ya zuba a kai ya sanya mata sauran a firji yadda ya ganta,
ya ja gefe kan karamin dining din cikin kitchen din ya ci ya koshi.
Ya kora da ruwa mai sanyi ya fito ya yi dakinsa.
Karo ya ci da katon din (sanitary pad) da macleans din (beverly hills formula) da ya saya mata a
falo har da shampoo din (pert-plus) a cikin katuwar leda don haka ya dawo da baya ya dauka ya
fasa shiga nasa dakin ya nufi nata. Daga kwanciyar da ta yi barci ya dauke ta, ga ciwon kai. Ya
yi sallama har sau uku bai ji ta amsa ba, ya yi niyyar ajiyewa a nan bakin kofa ya tafi sai ya tuna
da systemdinsa, kuma zai yi amfani da ita yanzun.
Babu tunanin komai a ransa ya murda kofar dakin ya shiga don a tsammaninsa ma ko tana
toilet ne. Barci ta ke yi, ta saki jikinta sosai tana bacci bilhaqqi. Gashin kanta ya wargaje a kan
filo bakikirin da shi mai sulbi da sheki, amma tsayinsa bai wuce dokin wuyanta ba. Abin da bai
taba gani a matan da ya taba sani ba sai na kanti, musamman Muazatu kullum cikin adon
gashin kanti ta ke shi ya sa ya fahimci ba ta da gashin ne, kuma ba ta son a gane. Ga wata irin
tattausar fata mai hasken da babu surki da mayukan kanti (natural), bakinta jazur dan mitsitsi
gwanin ban shaawa. Gashin idonta mai tsayi ya bi fatar idon ya kwanta a kan matsakaitan
idanunta.
Doguwar riga ce a jikinta mara hannu irin ta robar nan ta bi fatar jikinta ta kwanta a koina,
kalarta (orange). Kirjinta bai cika sosai ba, amma cikar kugunta ya nuna Allah ya ajiye mace
nan da wani dan lokaci. Bai san tsayin mintunan da ya kwashe a tsaye yana kare mata kallo ba
har sai da ta motsa ta juya, ta ji kamar inuwar mutum a kanta. Da sauri ta bude idanunta da
suka sauya kala saboda bacci ta sauke su a kan Abdulazeez Dakata, wanda ya yi hanzarin
sunkuyawa zai dauki system dinsa. Nata hannun ta kai ta dafe system din. Wani gefen yake
kallo bai yarda ya juyo ba balle ta ga kwayan idanunsa.
Zan dauki laptop din ne.
Ban yi ba. Ta fada da murya irin ta wanda ya tashi daga barci.

Tuni ya manta da komai, ya juyo ya dube ta da mamaki.
Ba ki yi ba? Amma na gaya miki ki hanzarta ko? Za su rufe kuma ni ma ina amfani da shi.
Tura baki ta yi gaba ta kyabe shi abin dariya.
Na kunna zan yi, hoton yammata ya hana ni ganin icons din.
Ta sakar masa abarsa ta shiga tattare takardunta da suka watse a kan gadon.
Kasa dauka ya yi, mamaki kamar zai kashe shi. Shi yarinyar nan ta ke kyabewa baki? Ya girgiza
kai ya dauki abarsa, bai ga laifin kowa ba sai kanshi, shi ya bada kafa har ta soma raina shi.
Sanda ba ta ganinsa ta isa ta cuno masa baki ne har ta ce ya zuba yammata a computer?
Kwafa ya yi wadda ta zame masa alada in abu ya ba shi haushi. Yanzu haka hoton Muazatu ta
gani shi ne za ta yi masa sharri wai yammata. Kamar irin ya zuba hotunan mata kala-kala din
nan.
Har ya kai bakin kofa ya rasa abin da ya saukar da haushin da ta ba shi, sai ya dakata ya juyo
ya mika mata hannun damansa na hagun na rike da laptop.
Ba ni takardun ni in yi miki.
Ba musu ta tattara ta mika masa, idanunta na kallon taga. Dawowa ya yi ya amsa, ya fice yana
murmushi.
Aladar maza ne jin dadi in matansu na gida sun nuna suna kishinsu ko me? Ita din yarinya ce
karama da ya tabbata ba ta san mene ne so ba, amma ta samu zuciyarta da kishinsa.
Bai san me ya sa hakan ya darsa abin da ya ji a zuciyarsa ba. Bayan ya gama cike mata
takardun cike da mamakin hazakarta a dukkan makarantun da ta yi a Jeddah da Brussels ya yi
submitting sai ya dauko tangamemen hoton Muazatu da ke dakinsa ya dawo da shi falo ya
kafa. Kana shigowa falon da shi za ka fara tozali. Ba ita ta fito daga daki ba, sai da yunwar cikinta ta hana ta jin dadin kwanciyar da ta ke ta yi
tunda ta yi sallar ishai. A hankali ta sauko daga gadon ta nufi kitchen. Nan ta tadda plate da
cokalin da ya ci abinci da warmer a kan dining. Da sauri ta bude inda ta tadda farin cous-cous,
a plate din da ya ci ta zuba, ba tareda ta tsaya wankewa ba saboda yunwa, ta bude firji ta zuba
miya ko dumamawa ba ta tsaya yi ba ta zauna ta hau zubi.
Sai da ta yi kat! Ta yi gyatsa ta yi hamdala ta sha ruwa sosai, ta wanke kayan da suka bata,
sannan ta bar kicin din.
Ba ta yi tozali da hoton Muazatu ba sai washegari. Sai da ta gwammace da ta sani ba ta yi
magana a kai ba. Dauke kai ta yi daga kan hoton ta ci gaba da sabgoginta kamar yadda ta
saba. Amma abin ya yi mata ciwo sosai, da ma an ce mutum shi yake bada dama a gane abin
da ba ya so. Za kuwa ta ba shi mamaki, ko a fuska ba zai kuma gane ba ta son Muazatu ba. A daki ta tadda wata katuwar leda da ta lura tun jiya ya ajiye ta, zama ta yi a gefen gado ta jawo
ta ta bude. Kunya ce sosai ta kama ta ganin abin da ya sayo mata, sai dai ta ji dadin macleans
din sosai, kuma wanda ta ke so ko a Brussels tunda suka dawo ba ta same shi ba (beverlyhills
formula). Da kuma Harpic da parazones na wanke toilet sannan air wicks har kala uku. Ta ji
dadi sosai a ranta, wannan ya nuna yana daga cikin mutane masu gano laifukansu da kansu su
gyara, ba zalunci da rashin adalci ba ne da ta yi inkari da su. Musamman da ta shiga kitchen ta
bude firij da freezer sosai ta yi istigfari na kuskuren fahimtar da ta yi masa a farko.
Shi kadai ya san yadda daren jiya ya kasance masa a tarihin rayuwarsa. Wani sabon alamari da
ya bakunci gangar jikinsa don ba zai ce da zuciya ba. Ita zuciya so ne a cikinta, gangar jiki
kuma ba ka iya katange shi daga abin da ya ga dama. A shekarunsa a duniya talatin kuma

cikakken musulmi, mai tsantseni wanda bai taba yin zina ba, yake rokon Allah kullum ya tserar
da shi daga aikatata, Ubangiji subhana ya amshi duainsa bai taba aikatawar ba har zuwa yau
da aka dauko wata mace da bai so aka mallaka masa da igiyoyin aure.
A tunaninsa yadda ta shigo, haka za ta koma inda ta fito, saboda bai yi tanadin hada rayuwa da
ita ba ta kowacce fuska. Sannan a perception dinsa ba ka shaawar mace sai kana sonta. Ya
yarda ya amince har zuciyarsa ba ya son Suhaana, babu soyayyarta ko rabin cokali a
zuciyarsa, amma ganin da ya yi mata jiya tana bacci ya tunatar da shi cewa shi ma namiji ne,
yana bukatar mace for now. Ba sai ana son mace kadai ake shaawarta ba. A cire duk wata
maganar gangar jikinsa, so ko rashinsa, (he need a wife). Gane hakan da ya yi bai hana
(criticsms) iri-iri zuwa cikin kansa ba... Wannan alamari da gangar jikinsa ke bukata a yanzu baa
farawa don a daina... what of idan ta yi ciki? Ya ya rabuwar za ta kasance mai sauki idan da Da
a tsakani? Wane uzuri zai kawowa Mammah idan ya mayar mata yarinya da ciki?
Runtse idanunsa ya yi da karfi ya ci gaba da juyi a makeken gadonsa cikin wani hali na
kaka-ni-kayi! Wata zuciyarsa ta kawo shawarar ya kai ta asibiti a yi mata (family planning), da
gaggawa wata zuciyarta hana ta ce, hakan zalunci ne, babban zalunci!!! Ba ta taba haihuwa ba,
idan ka lalata mata mahaifa sannan ka sake ta, Allah ba zai barka ba. Cikin halin da ya kwana kenan, ya rasa inda zai sa kansa. Duk shawarar da ya kama in ya
zurfafa tunani, sai ya ga ba mafita ba ce. Mafita guda biyu ce, ya sa mata ido ta koma a yadda
ta zo. Ya auro Muazatu su shimfida rayuwa mai maana da soyayya mara yankewa. Ko kuma ya
maida Hafsat cikakkiyar matarsa, amma babu rabuwa, kuma babu Muazatu... sosai yake girgiza
kai inresentment..... zan iya jure komi in dai zan same ki Muazatu!!! Ya fada a fili cikin rashin
sanin abin yi, da ciwon mara mai tsanani ya kwana.
Bai taba ganin dare mai tsayin na yau ba a kafatanin rayuwarsa. Idan haka sauran watannin da
suka rage musu za su kare, ashe ba zai kai su da sauran numfashi ba.
Mataki biyu Abdulazeez ya dauka don kare auren kwangilarsa lafiya ba tare da ya kara fadawa
halin da ya samu kansa jiya ba. Na farko ya daina shiga dakin Hafsat, in ganin lafiyar tata ya
zama dole, zai dinga jiranta a falo. Mataki na biyu, zai sai mata waya ya dinga kiranta yana jin
lafiyar tata don rage kusanci a tsakaninsu. Zai ci gaba da kin dawowa gida sai ta kure. Rashin
Muazatu ma ya taimaka wajen samun sararinsa da har wata mace za ta yi kokarin kutsowa cikin
rayuwarsa. Muazatu ba ta barinsa haka nan ba sa tare, sai in yana bakin aiki, in tana gari suna
tare, in ba sa gari daya koyaushe suna manne a waya.
Don haka washegari Hafsat ba ta sanya Abdulazeez a idanunta ba ya fice ofis da sassafe. Da
ya tashi office gidansu ya wuce, a can ya ci abinci. Sai da Mammah ta ga karfe tara ta yi ba shi
da niyyar komawa gida ta ce ya tashi ya tafi. A nan yake gaya wa Mammah zai saya wa Hafsat
waya tunda ta ki zuwa gidansu, kuma ta hana shi kawo ta. Ta yi murmushi cikin ranta ta ce, Mu je zuwa... wai mahaukaci ya hau Kura.
A (Bannex) da ke Wuse 2 ya tsaya ya yi cinikin wata karamar (Iphone) ya saya da sunan
Hafsat. Har jikin (receipt) Hafsat Dakata aka rubuta.
Sanda ya iso gida ta dade da kulewa a daki. Ya so ya tadda ita a falon ya ba ta wayar, hakan
bai yiwu ba. Ga shi kuma ya sa wa kansa takunkumin daina shiga dakinta.
Sai washegari zai fita ita kuma ta fito daga kicin suka hada ido, rabon da ta ganshi tun
shekaranjiya. Shi ya fara dauke idonsa, zuciyarsa na harbawa. Akwai wani maganadisu mai
kama da magnet a cikin kwayar idanunta, wanda duk lokacin da ya yi kuskuren hada ido da ita

sai ya ji shi a jikinsa. Neman kujera ya yi ya zauna, ya dafe kansa ya kasa ce mata komai. A
sanyaye ta zagaye kujerar bayansa, ta tsugunna a gabansa, ta ce.
Good morning.
Da ka ya amsa ta hanyar daga kansa da ke cikin hannayensa, amma ba ta yi nasarar samun
kallo daga gare shi ba. Inda sabo ya ci a ce ta saba, don haka ba ta wani damu ba ta mike za ta
wuce. A sanyaye ya cira kai daga cikin hannayensa ya ce, Hafsah?
Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo ba. Cikin mamakin wai ashe ya san sunanta?
Dauki wayar nan taki ce.
Dawowa ta yi ta dauki wayar ta duba, sai kuma ta mayar ta ajiye ta a inda ta dauke ta tana
girgiza kai.
Ba abin da zan yi da ita Yaya Azeez.
Cikin mamaki ya ce, Ba za ki dinga kiran Mamanki ba? Ni ma zan dinga kiranki in ina office.
Ga mamakinsa, sai hawaye suka balle mata. Ta ya ya za ta gaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login