Showing 45001 words to 48000 words out of 111817 words
murmushi kawai yayi ya sallami Ummu, ya kwanta abinsa ba damuwan komai a zuciyansa, ransa
wasai, sai addu'an fatan alkairi da yake yi, da kuma Allah haɗa yaransa da mata nagari.
Ya Farooq farinciki yake abinsa bai da damuwan komai, daman budurwansa ta faɗa masa an ce ya turo,
yana niyan yiwa Abbaa magana kenan ya musu wannan magana, shi dai ya Danish cin rai kawai yake yi, shi
yana da budurwan amma gaskiya ya rasa dalili tunda incident ɗin nan ya faru stakaninsa da Banafsha, sai
ya fara jin haushin budurwansa haka kawai, ga shi tunda ya zo weekend ɗin nan, gobe Sunday zai koma
amma ko kallonta bai yi ba balle ya mata wani mugunta, dan shi bai huce ba har yanzu, Ya Farooq na masa
magana ma amma ko kula shi bai yi ba, kuma bai shiga cikin gida ba dan baya son surutun Umma.
Ina kwance na gaji da kwanciya na miƙe nayi ayyukan da ya kamata, wanka na shiga na gama na shirya, ina
zaune shiru ni ɗaya a gida har nayi sallahn Magrib su Mamina ba su dawo ba storo ma ya bi ya cika ni,
kaman nayi kuka haka nake ji, ga shi banda waya balle na ƙira Mamina, da ace ba weekend bane sai na
shiga gidan su Umaima, amma weekend ne bana buƙatan haɗuwa da Ya Danish dan nasan yanzu haka ba
zai wuce ma suna ƙofan gida ba, haka na daure na zauna cikin storo.
Malam Abbo sai da ya shirya zuwa wajan Banafsha abincin ruhinsa, sannan ya bi masallaci yayi sallahn
Magrib, ana idarwa ya tashi ya kamo hanya cike da addu'an Allah bashi ikon furta mata soyayyansa, kuma
Allah ya sa ta amsa, dan sosai take masa kwarjini, Malam Abbo ba ƙaramin kwalliya ya ci ba, ga wani
ƙamshi da yake yi na musamman, Malam Abbo haɗaɗɗen matashin saurayi ne wanda ba macen da sa ta
kallesa bata ji ya burgeta ba, cikin tafiyarsa na nistuwa yake taku har ya iso ƙofan gidan su Banafsha, kuma
ya wuce su ya Danish a ƙofan gidansu, ya Danish kallo ɗaya ya masa ya ganesa, shi ne saurayin da yake
ganinsu tare da Banafsha, tuni wani haushi ya rufesa da ya tuna abubuwan da ta ke masa, ga shi ranan bai
samu ya koya mata hankali ba, ƙwafa yayi ya bi Malam Abbo da harara.
Dai-dai isowan Malam Abbo ƙofan gidan su Banafsha, dai-dai isowan motan Alhaji sun dawo daga anguwa
da Mami, Alhaji da kansa ya sauƙa ya buɗe gate ya shige cikin gidan, Mami da yake ta kalli Malam Abbo,
sai ta faɗawa Alhaji ai malamin su Banafsha ne ya masa iso, ta juya ta shige ciki shi kuma Alhaji ya fice
waje, Malam Abbo yana ganinsa ya fara fara'a, cikin mutuntawa suka yi musabaha suka gaisa, sannan
Alhaji ya masa iso suka shige cikin gidan.
Mami na shiga ta sameni zaune sturu-sturu da idanuwa kaman an tare kule a buta, duk a storace nake,
murmushi tayi ta ce, "Sannu da gida ƴar Mami mai storo."
Ina murmushi na tashi na rungume Mamina na ce, "sannunku da dawowa Mamina."
"Yauwa Faɗiman Mami, ki shige ki sako hijabi dan naga malaminku ya zo" Mami ta faɗa tana nufan
ɗakinta.
Ajiyan zuciya na sauƙe dan storo ya tafi tunda Mami ta dawo, ɗakina na wuce ina murmushi dan sai yanzu
da Mami tayi magana sai na tuna Malam Abbo ya ce zai zo gidanmu, amma mamaki nake da zuwan da yayi
da dare da kuma ko me ya kawo sa Allahu a'a lamun, nidai ya ce akwai maganan da za mu yi, addu'a nake
Allah ya sa alkairi ne, kuma Allah yasa ba wani laifin na aikata ba.
Alhaji tare da Malam Abbo suka shigo palournmu, waje Malam Abbo ya samu ya zauna, Alhaji ya shige
ɗakin Mamina ya faɗa mata malaminnamu ya shigo, Mami ta amsa shi kuma ya wuce ɗakinsa, Mami cikin
kamala ta fito da hijabinta, Malam Abbo kuwa cikin ladabi ya durƙusa ya gaidata yana ya sunne kai, Mami
amsawa tayi da fara'a bata ce komai ba ta dai ce bari ta ƙira masa faɗima, ya amsa yana mai sunkuyar da
kai cikin kunya.
Ni kuwa ina shiga ɗakina haka kawai na stinci kai na da ɗan gyara fiska na, na shafa humrana sannan na
ɗau hijabina na saka, ba ƙaramin kyau nayi ba ga shi har da man baki da kwalli na saka, Mamina ce ta
shigo ɗakin da sallama, kallona tayi ta girgiza kai ganin har da kwalli na saka, murmushi kawai tayi ta ce,
"Idan kin gama kwalliyan to yana jiranki" tana gama faɗa ta fice tana murmushi dan yanzu ta fara harbo
jirgin abinda ke shirin faruwa, Banafsha har da kwalliya, shi kuma malamin nata sai sunne kai yake kaman
mara gaskiya.
Mamina na fita na tsaya na gama dariyana sannan na tattaro nistuwata na fice palourn ina mai jin wani iri
haka kawai, ina isa da sallama ya amsa mini, waje na samu na zauna a ƙasa, amma yau Malam Abbo ya
dage firr! Sai na zauna a sama, haka ba dan naso ba na zauna a sama ina cusa fiskana a cikin hijabina, da
hijabin a bakina na gaishe sa muryana yayi wani iri, shi kuma ya amsa yana kwaikwayon muryan nawa
yanda yayi, sai abin ya bani dariya kawai na ɗan murmusa nayi shiru tare da yin ƙasa da kai na, ina wasa da
yastuna.
Malam Abbo can da shirun yayi yawa sai yayi gyaran murya ya ce, "Malama Faɗima yau ba ruwan sha ne,
abin rowa aka fara mini."
Kunya na ji na miƙe da sauri, ni gaba-ɗaya na sha'afa ma, wucewa nayi kitchen na haɗa masa abin taɓawa
har da tuwon dare da nayi, na ɗauko cikin nistuwa na zo na ajiye masa agabansa, murmushi Malam Abbo
yayi ya ce, "ina godiya Malama Faɗima Allah ya yi albarka, sannu da ƙoƙari."
Ina sunne kai na amsa da ba komai, sannan na ce, "ka taɓa abincin dai malam, ka ji girkin ɗalibarka."
Malam Abbo cikin fara'an yanda na sake ya ce, "Masha Allah! Ai dole na taɓa Sayyadata" ya faɗa tare da
kurɓan ruwa, sannan ya dube ni, cikin jarumta ya fara mini magana kaman haka, "Sayyada Faɗimah fatan
dai ban takura ki ba da zuwan da nayi na dare?"
Jinjina kai nayi kawai alaman ba komai, murmushi Malam Abbo yayi ya ce, "To! Godiya nake Sayyadata,
Allah ƙara lafiya."
Murmushi nayi kawai, sai da muka gaisa ya tambayi karatu da boko duk na amsa masa, sannan ya ɗago
yana bi na da wani irin kallo mai narkar da zuciyan abinda kakeso, ƙasa nayi da kai na, Malam Abbo ya
numfasa ya ce, "Sayyadata ina mai fatan babu wanda ya rigani ko ya mini shigan sauri ya mini ƙafa?"
Ba tare da na fahimci abinda yake nufi ba kawai na ɗaga kai, murmushi ya kuma yi ya ce, "Masha Allah!
Alhamdulillahi ala kulli halin! Ni ɗin mai sa'a ne Insha Allah, Sayyadata abin da nake faɗa da gaske nake
faɗansa tun daga ƙasan zuciyata, soyayyanki da ƙaunanki sun jima da yi mini mugun kamu, kuma ƙauna ce
wacce aure za ta zama ribarta Insha Allah, ina fatan za'a amsheni hannu bibbiyu tunda an ce babu wanda
ya rigani."
Wani irin kunya ne ya rufe ni lokaci guda, kawai rufe fiskana nayi da hijabi ina ta murmushi, ba wannan
bane karo na farko da namiji ke faɗa mini yana ƙaunata, amma wannan sai na ji sa daban, Malam Abbo ya
kai maƙura duk inda ake buƙatar mijin aure ya kai, alhamdulillahi indai wannan ya zamo uba ga yarana to
ina da tabbacin sun yi dacen uba, amma sai dai kashh! Ba wannan bane a gabana, ban da asali ban da
kowa sai Mamina kawai, aure ba zai yiwu ba a gare ni, ba zan iya yaudaran bawan Allah ba na sa masa rai
ba, ni na riga da na sani a ƙaddaran rayuwata babu aure, kowa na zagina da hantara ta akan ƙaddaran
mahaifiyata, a yanzu zan iya jurewa amma ba zan iya jure hakan a gidan aure na ba, ko ga dangin miji ko
kuma aje-aje har shi mijin da kansa, dole na haƙura da batun soyayya balle a kai ga aure, cikin sanyin jiki na
ɗago shanyayyun idanuwana da ke neman zubar da ƙwalla na kalli Malam Abbo cikin ido, da duk sauran
juriyata da jarumtata na ce, "ka yi haƙuri Malam, amma ni ba zan yi aure yanzu ba kada na bata maka
lokaci."
Daga yanayin Banafsha Malam Abbo ya fahimci ya samu karɓuwa, ko abinda take furtawa ma kokawa take
da zuciyanta wajan faɗan hakan, cikin damuwa ya ce, "Sayyadata ko nan da shekara nawa ne na miki
alƙawarin zan jira ki, nasan ba zai wuce kina son kammala karatunki ba, wallahi banda mastala da bokonki
ni da kai na idan ina da hali sai iya inda rai ya stayar da ni akan iliminki, ina ƙaunanki Sayyadata, na jima ina
dakon soyayyanki amma na kasa furta miki, wannan karo da na samu ƙwarin guiwan faɗa miki dan Allah
kada ki juya mini ƙoƙon barana ba tare da kin cika mini shi ba."
Zuwa yanzu hawayena ƙiris suke jira su kwalalo, a hankali na ce, "ka yi haƙuri Malam Abbo ba zan iya
aurenka ba."
Cikin damuwa yake kallona yanda nake kallonsa ya ce, "Saboda menene Malama Faɗima? Halinane bai
miki ba? Ko nasaba na? Ko kuma menene ba dai-dai ba ki faɗa mini, na miki alƙawarin gyarawa yanda kike
so in Allah ya yarda."
Wannan karon muryana na rawa har hawaye sun fara bin kuncina na ce, "Malam nasan kasan gaskiya akan
komai a rayuwata, nasan kasan duk abinda jama'a ke faɗa a kai na da mahaifiyata, Malam ba ta inda ka
kasa, don babu macen da za ka nuna kana sonta ta ce baka mata ba, Malam ni kwata-kwata auren ne ba
zan yi ba a rayuwata."
Malam Abbo kallon Banafsha yake ba kifta ido ya ce, "Zan aureki a haka Faɗima, zan aureki a duk yanda
kike, ni ke nake so ba komai da ya shafe ki ba, ko wanni bawa da irin ƙaddaransa da kuma jarabawansa, ina
ƙaunanki a duk halin da kike ciki Sayyadata."
Fashewa kawai nayi da kuka na ce, "Malam ko kana so na danginka ba za su aminta da ni ba na sani, dan
Allah ka yi haƙuri Malam, Allah ya baka mace tagari wacce ta dace da kai", ina gama faɗan haka na miƙe
ina kukana na nufi tafiya ɗakina.
Malam Abbo ma miƙewa yayi ya fara magana wanda shi ya stayar da ni, "Malama Faɗima kaman yanda na
faɗa miki ina sonki a duk yanda kike, to ina son ki sani ke ce dai-dai ni, kuma ni zan zauna da ke ba kowa
nawa ba, ina sonki ina ƙaunanki ki saka wannan a ranki, in Allah ya yarda in har da rabo kuma da alkairi to
Allah da kansa zai yi Allahnsa ki zama mallakina, amma ina roƙon ba za ki ɗau fushi da ni ba akan wannan
magana."
Ina gama sauraran Malam Abbo na wuce ɗakina da sauri ina kukana, ga samu ga kuma ráshi lokaci guda,
Malam Abbo mijine da ko wacce mace tagari za ta yi addu'an samu, amma ni ga daman hakan ya sameni
har gida sai dai babu hali, ƙaddaran mahaifiyata ya riga ya rusa mini komai nawa, ƙaddaran mahaifiyata ya
sa na tashi banda kowa sai ita dan ina da tabbacin ƙaddaran rayuwanta ne ya rabata da kowa nata,
ƙaddaran amsa sunan ƴar Karuwa da zamtowa ƴar Karuwa shi ne babban ƙalubale na a rayuwa, ɗaga
hannayena sama nayi na ce, "Allah ga ni gare ka, Allah ka iya mini a lamurana, a yanda nake ina matuƙar
son na ga nima na raya sunnan ma'aiki, amma mahaifiyata ta zama katanga a gareni tsakanina da aure, wa
zai auri ƴar mace mara asali kuma ƴar karuwa? Banda Uba banda ƴan uwa banda kowa sai mahaifiya, ai ko
a jikin bishiya na fito albarka, nasan babu ubanda zai amince ɗan sa ya auri ƴar mace mai zaman kanta,
macen da maza daban-daban ke sintiri a wajanta" rushewa nayi da kuka mai ƙarfi saboda ciwon marana da
ya ƙaru ya dawo mini sabo fill dan damuwan da nake ciki.
Malam Abbo kuwa Banafsha na shigewa kaman zai yi kuka ya koma ya zauna, sai da ya ƙara kurɓan ruwa
ya dinga jera ajiyan zuciya sannan ya miƙe, ya juya zai fice sai ga Alhaji ya fito a ɗakinsa, Malam Abbo
daurewa yayi ya shanye damuwarsa da murmushin yaƙe suka ƙara musabaha da Alhaji ya masa sai da safe,
sai da ya rakasa har ƙofa sannan suka yi sallama ya tafi, Alhaji kuma ya rufe ƙofa ya dawo cikin gidan cike
da tausayin wannan matashin, dan kusan maganansu na ƙarshe da Banafsha ya ɗan stinci saura, wannan
jarabawa ce ga uwa da kuma ƴar ta, kuma Alhaji sam-sam bai ga laifin Banafsha ba saboda gaskiyanta ne,
wasu iyayen sai a hankali ba lallai su amince ɗan su ya auri mara asali ba kuma ƴar mace, amma kuma
yana tausayin saurayin dan ji yayi kaman yaronsa ne ya je neman aure aka masa haka, addu'an alkairi
kawai yayi ya tura ƙofan Mami ya shiga, ganin tana bacci sai ya fice ya koma nasa ɗakin ya kwanta.
Malam Abbo yana fitowa ya samu har lokacin su Ya Danish na zaune a ƙofan gida, duk da duhun dare
amma Ya Danish yana ƙoƙarin hango wani abu daga yanayin Malam Abbo, kaman zai ji daɗi kuma sai ya
taɓe baki irin me damuwansa da kashin su, shi kuwa Malam Abbo haka ya koma gida cikin damuwa da
niyan zai bawa Banafsha lokaci ko da sati guda ne ya ji ko ta sauya shawara, idan kuma abun ya ƙi to
gaskiya zai samu Ummanta da maganan, shi ba zai iya jure rashin Banafsha ba, Allah ya gani soyayyanta ya
jima da masa mugun kamu.
Ya Danish har suka gama hiransu suka shige gida zuciyansa cike da son ganin giftawan mara kunyar, ya
samu ya mata wani rashin kirkin ko zai ji daɗi, haka washegari da sassafe ya fito tun su Umaima ba su tafi
makaranta ba ya zauna a ƙofan gida yana son kallon giftawanta dan ya yaɓa mata magana.
A ɓangaren Banafsha kuma da wani irin mugun zazzaɓi ta kwana da ciwon mara, kamun gari ya waye tuni
ta fice a hayyacinta, daman ita idan ciwon maranta ya tashi ba ya mata ta sauƙi, duk wata na Allah sai ta ji
a jikinta, balle kuma ga shi jiya abin ya haɗu mata biyu, ga damuwa ga ciwo, kwata-kwata ko sallahn asuba
ta kasa tashi ta yi, ta galabaita sosai-sosai kuma har lokacin ba wai jinin ya zo ba ne.
Ko da safiya tayi, Mami jin shirun tayi yawa, sai ta ɗauka ko yau Banafsha rigimanta ne ya mosta, da kanta
tayi ayyukanta ta yi wanka chass abinta, Alhaji kam ya koma bacci daman baisan me ake ciki ba, Mami
ganin dai har lokacin ba mostin Banafsha kuma lokacin makaranta ya wuce, sai ta nufi ɗakinta tana surutu,
tana tura ƙofan ɗakin ta shiga ta samu Banafsha yashe a stakar ɗakin a sume, salati Mami ta rafka dan sai
yanzu ta tuno lokacin al'adan Banafsha ya yi, month nata ya zagayo, cikin damuwa ta fice ta ɗauko ruwan
zafi, shafa mata a fiska Mami tayi, sannan ta sa mata a baki, ruwan na kai wa maƙoshinta ta sauƙe wani
wawan ajiyan zuciya, a hankali ta buɗe idonta da suka rine saboda azaban ciwo, ruwan zafin Mami ta bata
ta sha sosai kaman ba mai zafi ba ko cire baki bata yi ba sai da ta shanye tass, sannan ba jimawa ta dinga
kwarara amai, sai lokacin ta samu salama dama-dama ta koma ta kwanta, Mami sai aikin jera mata sannu
kawai take yi, a haka ta tashi ta gyara wajan aman da ta yi, ta cire mata kayanta suka shige toilet ta gyara
mata jikinta, sanin ba lallai in tayi sallahn asuba ba, sai ta mata alwala, suna fitowa ta shiryata staff ta saka
mata hijabinta, a haka a zaune ta ce tayi sallahn kamun taje ta taso Alhaji su tafi asibiti, Banafsha amsawa
tayi da kai, Mami ta fice.
Ya Danish na zaune a ƙofan gida har su Umaima suka fito, yana tunanin ko za su biyawa Banafsha amma
sai suka wuce abinsu, Ya Danish bai san idan yana ƙofa Umaima bata biyawa Banafsha ba, haka suka yi
tafiyansu da Nana, sun je makaranta ana ta karatu Umaima ta zuba ido ta inda Banafsha za ta ɓullo amma
shiru, haka malamai suka shigo har Malam Abbo ma aka musu darrusa har aka tashi ba Banafsha ba
alamanta, Umaima duk ta bi ta damu dan tasan idan ba wani abun bane ya faru to Banafsha ba za ta ƙi
zuwa makaranta ba.
Ɓangaren Malam Abbo ma bai ji daɗi ba dan gani yake shi ya ja mata rashin zuwa makaranta, sai duk abin
ya bi ya damesa, ko da aka tashi ya daure dai bai tambayi Umaima ba yana tunanin zuwa yamma Banafsha
za ta zo, dan Maminta ba za ta barta ta zauna a gida ba.
Ya Danish har ya gaji da zama ya shige gida, har su Umaima suka dawo, shiru ba giftawanta, Umaima ma ko
da suka dawo ba ta shiga gidan su Banafsha ba, ta bari sai zuwa yamma dan tana tunanin ko wani abun ne
ya kuma faruwa tsakanin Banafsha da mutanen Mami ya sanyata fushi taƙi zuwa, bata son taje dubo
Banafshan kuma ta kalleta cikin damuwa, sai tayi zamanta cike da kewan ƙawarta aminiyarta.
Mami ɗakin Alhaji ta shiga da damuwa ta tashesa a baccin, faɗa masa abinda ke faruwa ta yi, Alhaji da
yake shi ma yasan da ciwon Banafsha, cikin