Showing 60001 words to 63000 words out of 111817 words
Suhail dariya yayi ya ce, "Ni kuma ka yafe ni ne General? Ko da yake ni da nake da yaya CAS Bunayd ko
General ya yafeni normal ne, daman ni yaya ne babana."
General murmushi yayi ya ce, "Za ka dawo ka same ni, daman shi yake ɗaure muku wajan zama."
General haka yake da yaransa maza kaman abokanayensa, musamman CAS Bunayd, kwata-kwata General
ba shi da zafi, kuma haka matar sa Hajiya Huraira.
Momsee da ke zaune a gefe dariya tayi ta ce, "Dear gaskiya yarannan su maida ka kaka."
General kansa ya shafa ya ce, "Alhamdulillahi kawai za mu ce, yara arziƙi ne tunda Allah ya bamu, dole mu
jawo su jiki dan mu ji daɗin nuna musu dai-dai da ba dai-dai ba, yiwa yara zafi bai da wani fa'ida, illa ya
saka yaro ba zai sake da kai ba balle kasan damuwansa, ko yayi shawara da kai, Allah dai ya musu albarka
ya kare su a duk inda suke."
Da, "Ameen" Momsee ta amsa, suka cigaba da hiransu.
Bunayd yau daurewa yayi bai je ko ina ba, ba dan yaso ba sai dan General bai cika son yawan fitansa da
dare sosai ba, idan ba kamawa tayi ba, amma idan ba saboda General ba sam-sam Bunayd baya son zama,
shi zuwa wajan chasu a jininsa yake, ko da ba zai yi komai ba sai dai ya bawa idonsa abinci yayi catching
fun's, sai da ya gama hutawansa sannan ya shigo palourn nasu na ƙasa, su Suhaila suna ganinsa suka fara
washe baki, shi kuma haɗe fiska yayi dan ya san ba zai wuce su ce yawo da daren nan ba, fiska ba Rahama
ya ce, "Ku kawo ƙur'anan ku."
Stuttt! Duk suka miƙe suka je suka ɗauko, General da isowansa palourn kenan murmushi yayi ya ce,
"Kaman haɗa fiskan da gaske ne, ai ina ga yaran nan sun gama lashe maka zuciya, musamman Suhaila da
Nabeela."
Bunayd shafa kiston kansa yayi bai ce komai ba, ya fara sauraran karatun ƙannensa sai ga Nabeel ya shigo,
kallo ɗaya Bunayd ya masa tuni ya gane nufinsa, shi ma ɗauko nasa ƙur'anin yayi da littafin da suke yi na
addini, Bunayd sai da ya duba karatun ƙannensa duka ya musu ƙari, sannan ya kuma suka zauna hira ana
raha, bai cika magana sosai ba amma idan da ƙannensa ne kuma yana mood to duk shirmen su yana biye
musu.
Da dare ya ja sosai sai General ya kora su kowa ya kwanta, da safe a fara shiri sai Kano in Allah ya yarda.
Bunayd yana komawa sashinsa sai ga ƙira, ganin mai ƙiran sai ya taɓe baki, a fili ya ce, "Yoruba people
akwai reni, to nima ba zan yi attending naka ba sai gobe." Yana gama mitansa ya kashe wayansa ya kwanta.
Cikin dare ya tashi yayi nafilfiulunsa yanda ya saba, sannan ya koma ya kwanta.
Washe-gari Suhail da wuri ya iso, lokacin kuma kowa ya gama shiryawa, ba jimawa suka kamo hanyan Kano
amma ta Flight, jirginsu na sauƙa motoci uku suka zo ɗaukansu daga gidan Alhaji.
Shigan su Bunayd gidan yayi dai-dai da shigowan motan Hajiya Sa'adatu da sai yau ta dawo daga inda ta je,
su Suhaila duk da ba wani sake musu Hajiya Sa'adatu ke yi ba amma duk sun yi hugging nata, a yastine ta
amsa, General da Momsee duk sai su suka ɗaga mata gaisuwa, sannan ta amsa a gadarance, da yake
General ma da nasa part ɗin a gidan, sai suka wuce duka can, Majeeder tunda ta ji zuwansu ta fito ta
rungume sister's nata mata, da kuma General da Momsee, tunda ta maƙale wa Bunayd ko mostawa zai yi
tana riƙe da shi, ba ƙarya Bunayd ma yayi mugun kewan ƙanwar tasa dan ya kwana biyu bai zo ba.
Alhaji da kansa ya saka masu aiki suka kai wa su General abinci, sannan da waɗanda za su musu aiki har su
koma.
Hajiya Sa'adatu tunda ta shige ko leƙowa bata kuma yi ba, sai kawai cin magani take yi kaman ba ɗan uwan
mijinta da yaransa ba ne suka zo, kaman wasu bare daban.
SU WAYE WANNAN AHALI?
MENENE FARKON LABARINSU?
waiwaye adon tafiya, Inshà Allah a next page za mu ji taƙaitaccen tarihin wannan ahali.
Not edited again, ayi haƙuri da typing errors, Uwar batoorl jikin sai a hankali.
Masu Sharhi ina matuƙar Godiya í ½í±� Uwar batoorl taku.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# í µí¹š
# í µí¹‡í µí¹ í µí¹š &
# í µí¹–í µí¹š
í ½í±„'YAR KARUWAí ½í±„í ½í²…
Officially
í µí¹®
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma ɗaukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
Hafsat Umar
Ɓingel kabi
Masoyiya bealkysou
Habiba muhammad Yusuf
Ameera
مهللا ىلص و ملس ىلع ديس ان هللوسر SAW í ½í¶¤í ¾í´�
í ¼íµ¿️ 61 _ 65
ALHAJI SULAIMAN ILYASU KWALLI!
Shi ne kakan Bunayd, Sulaiman kwalli wanda aka fi ƙira da Sule kwalli shi asalin ɗan jihar Sokoto ne, a
ƙaramar hukumar Binji, su biyu iyayensu suka haifa shi da ƙanwarsa mai suna Rahama, Sule da Rahama
sun taso cikin gata da soyayyar iyayensu, saboda iyayensu na da rufin asiri Masha Allah, su Hausa-Fulani
ne, bayan kiwon dabbobi da mahaifinsu Ilyasu ke yi har da sana'ar hannu yana yi wacce ta danganci nau'in
su kwalli, Sule da Rahama duk iyayensu sun saka su a makaranta ta muhammadiya da kuma ta ilimin
zamani(boko), lokacin da Sule yayi nisa a karatu sai shi ma ya ɗau sawun babansu Ilyasu kwalli ya fara
sana'a irin tasa, cikin ƙanƙanin lokaci da ikon Allah shi ma ya staya da ƙafansa, a lokacin ne kuma ya samu
mata mai suna Hauwa'u ƴar gidan wani babban mutum ɗan siyasa a cikin birnin Sokoto.
Bayan neman da suka yi na ɗan lokaci sai aka yi auransu, bayan biki ba jimawa Sule kwalli ya samu
haɗaɗɗen gidansa a cikin birnin Sokoto, nan ya nemi da su koma duka da iyayensa amma sai iyayensa suka
ƙi su sun fi son zaman Binji, haka Sule ya tattara da Amaryarsa Hauwa'u suka koma cikin birnin Sokoto da
zama, sai dai sa'i zuwa lokaci su dinga kai wa iyayensa ziyara, Hauwa'u matar Sule bafulatana ce gaba da
baya, kuma kyakkyawa ce ta ƙarshe ma, dan haka suna zaune lafiya da mijinta, a sanda auransu ya cika
shekara a lokacin ne kuma ta haihu ɗan ta namiji santale mai matuƙar kama da mahaifinsa Sule, ranar da
ya cika kwana bakwai yaro ya ci sunansa Mukhtar, kuma a wannan lokacin Rahama ƙanwar Sule ta dawo
gaban Sule da zama tana kan karatunta, saboda akwai ratan shekaru sosai stakaninta da yayan nata.
Mukhtar na da shekaru biyar a duniya sai Hauwa'u ta kuma haihuwan yaronta kyakkyawan gaske namiji
mai matuƙar kama da ita, kaman kakinsa ta yi, ranan bakwai yaro ya ci sunansa Sufyan, zuwa wannan
lokaci Ilyasu ya manyanta sosai kuma matarsa Salamatu na fama da cutan ajali, shi kuwa Sule ya zama mai
kuɗin gaske, kullum sintirin asibitin neman magani suke da mahaifiyarsa amma kwana ya riga da ya ƙare
babu dabara, haka saƙon mutuwanta ya riske su, a ranan suka tattara suka tafi Binji, bayan an yi bakwai
suka tattaro suka dawo, sai da aka yi arba'in sannan Ilyasu ya yarda ya dawo gidan Sule da zama.
Bayan wasu shekaru biyar Hauwa'u ta kuma haifan yaranta ƴan biyu mata, aka sakawa ɗaya sunan kakansu
da ta rasu, Salma ɗayan kuma Salima, bayan haihuwansu ba jimawa Rahama ta samu mijinta dan ita kam
auren ya ɗan mata jinkiri ma, shekaranta biyu da aure ta haihu ƴar ta mace ranan suna ta ci sunanta
Huraira, kuma a lokacin Hauwa'u ta ƙara haihuwan ɗa namiji mai suna muhammad, amma ita rahama tun
da ta haihu ciwon ciki ke damunta, a ranan da suka yi kwana ishirin da haihuwa a ranan ta cika.
Rasuwan Rahama sosai ya taɓa ahalinta, musamman da ta bar jaririyan da ko wata bata yi ba a duniya,
mijin Rahama ya bar Huraira a hannun kawunta Sule saboda kara, Hauwa'u ta nemi ta haɗa su ta shayar
tare da muhammad amma Ilyasu ya hana, dan haka madara ake bata, tun su Huraira ba su shekara ba
muhammad yaron Hauwa'u ya koma, a wannan lokaci kuwa Mukhtar da ƙaninsa Sufyan sun zama Samari
dan Mukhtar yana da shekaru kusan goma sha bakwai, shi kuma Sufyan shekaru sha biyu garesa, twin's
kuma shekarunsu bakwai kuma duk suna nan lafiya-lafiya, Mukhtar ma yana karatu kuma yana kula da
harkoki irin na mahaifinsa Sule kwalli, yayinda Sufyan ya dage shi Soja zai yi, kuma da yake ba rayuwan yau
ba ne sai ya samu cikin ikon Allah.
Lokacin da Huraira ta yi shekaru biyar a duniya, lokacin Ilyasu ya buƙaci da su kai ziyara a Binji wa sauran
ƴan uwa, Mukhtar da Sufyan duk suna makaranta ba sa gida, dan haka sai duk suka shirya da Sule da
matarsa Hauwa'u da Ilyasu babansa da yaransa ƴan biyu, Salma da Salima da kuma Huraira, sun shirya sun
kama hanya, lafiya-lafiya haka suka isa, suka zaga dangi suka musu alheri, kwanansu biyu suka tattaro dan
su dawo gida, a hanya kuma suka haɗu da ƴan fashi, duk da sun samu abinda suke nema amma ba su bar
kowa da rai ba haka suka kashe su suka yi gaba, labari na iske Mukhtar da Sufyan kaman za su yi hauka
haka suka zo, sai dai wajan yi wa gawa sutura aka samu Huraira da ranta, storita da lamarin da ya faru ne
ta yi dogon suma ba wai kasheta aka yi ba ita.
Wannan rashi kaman zai haukata Mukhtar da Sufyan, sannan Sufyan ya ɗau alwashin kama masu laifin sai
ya ɗau fansan iyayensa da ƙannensa, Mukhtar kuwa sai dai ido kawai, Huraira haka ta zama shiru-shiru ita
ma kaman mara ishashshen lafiyan ƙwaƙwalwa.
Malam Zahraddin mahaifin Huraira shi ya riƙe su Mukhtar tunda da girmansu ba buƙatan sai ya riƙe musu
dukiya, kawai ya riƙe su ya zama kaman mahaifinsu ne dan saka halaccin iyayensu a garesa na riƙe masa ta
shi yarinyar da kuma basa mata.
Shekaru sun ja, Mukhtar ya zama Alhaji kuma cikin ikon Allah tunda al'amuransa suka yawaita a Kano sai
ya tattara su suka koma can, a Kano kuma ya samu matan aure Sa'adatu ƴar gidan wani kansila, tun da
Alhaji Mukhtar yayi aure aka tura Sufyan aiki a Abuja, ita kuwa Sa'adatu wulaƙanci ne da ita ba kaɗan ba,
haka ta ke yi wa Huraira da mahaifinta, Alhaji ya stawatar sosai, amma sai mahaifin Huraira ya ce za su je
Sokoto ganin gida, duk saboda kada yana babba ya haddasa rashin zaman lafiya stakaninsa yaransa, haka
ya tattara Huraira suka koma Sokoto a can kuma ta cigaba da karatu cikin kewan yayunta dan sosai Huraira
ta saba da su Mukhtar.
Sufyan daga Abuja aka kuma shillasa Lagos, kuma tunda ya je Lagos ta masa daɗi ya zauna daram abinsa,
ba batun aure a lissafinsa, sai dai ya kawo wa yayansa ziyara kwana ɗaya biyu ya koma, ya je Sokoto shi ma
kwana ɗaya biyu ya koma Lagos, yana aikin Soja kuma yana da business wanda ya ɗaura masu kula masa
da business ɗin, kuma a ɓangaren aikinsa ko da yaushe cikin ƙarin girma yake, inda yanzu yake mastayin
General, kuma cikin ikon Allah da taimakon bincike, ya samu ya kama waɗanda suka kashe masa iyaye,
hukuma ta yanke musu hukunci, saboda sun ishi al'umma daman.
Hajiya Sa'adatu ta haihu ɗan ta namiji mai shegen kyau mai kama da Sufyan kaman shi yayi kakinsa, idan
ka ga yaron za ka ɗauka ɗan larabawa ne, yaro ya ci sunansa muhammad Bunayd, Sa'adatu ta ce ta daina
haihuwa ita ba za ta iya ba ta stofe da wuri, ita ba son haihuwa take ba, kuma ko shayar da Bunayd bata yi
sai Alhaji ya stawatar mata, amma duk da haka sam-sam Alhaji bai rageta da komai ba, domin da
mahaifinta ya rasu aka raba gado aka bata nata, sai ya ƙara mata jari a kai ta fara business, wanda cikin
ƙankanin lokaci kasuwancinta ya bunƙasa ta zama Hajiya ita ma, sai dai wulaƙanci ya ƙaru, kwata-kwata
Hajiya Sa'adatu bata son kowa ya raɓe ta ko mijinta, hatta Sufyan da yake ƙanin Alhaji Mukhtar to ba ta
ƙaunarsa, komai ita ɗaya haka take so, ko Alhaji zai yi yaya da ita yanzu bata yarda ta je Sokoto, sai dai ta
kawo masa uzurin ƙarya.
Sufyan ya fi Alhaji Mukhtar ziyara sosai ba kaɗan ba, dan sai Sufyan ya je Sokoto sau biyar Alhaji Mukhtar
bai wuce ya je sau biyu ko ɗaya ba, tunda Hajiya Sa'adatu ta haihu shikkenan kuma sintiri ya samu Sufyan
Kano to Lagos, Allah ya ɗaurawa Sufyan stanstar ƙaunar Bunayd, dan ko da Bunayd yayi shekara biyu sai
Sufyan ya ɗauke sa suka tafi Lagos, duk da ba shi da aure amma ya samu wata musulmar Yoruba tana kula
masa da shi, kuma shi ma da kansa yana kula da Bunayd kaman shi ne mahaifiyarsa, kashinsa fistarinsa
komai akan Bunayd ba abinda General Sufyan bai iya ba, kuma karatunsa Arabic da boko yana kula da shi,
musamman abinda ya shafi Addini da kansa yake zama ya koya masa, baya taɓa yarda aiki ya sha kansa bai
duba karatun Bunayd ba, gata kam iya gata Bunayd na samu a wajan General Sufyan, gatan da ko ɗan
cikinsa ba lallai ya samu ba.
Alhaji Mukhtar kuwa ba abinda ya ce dan General Sufyan ya ɗau Bunayd, saboda shi hakan ma hankalinsa
ya fi kwanciya, akan hali irin na matarsa, ita Hajiya Sa'adatu kuwa gaba-ɗaya hankalinta na kan business
nata ko a jikinta, sai hamdala ma da tayi an rage mata aiki, dan ita ko haihuwan bata so ba balle yaro ya
takura mata, kwata-kwata Bunayd bai san wani daɗin mahaifiyarsa ba, shiyasa shi ma a duniyansa komai
nasa General ne, dan da shi yayi mugun sabo.
General Sufyan ko ina zai je ƙafansa ƙafan yaronsa Bunayd da ya zama kamar abokinsa, har Sokoto suke
zuwa tare har wajan wani abokinsa Soja ɗan gidan wazirin Sarkin Sokoto, kuma Bunayd ya shaƙu da
Huraira sosai, haka mahaifin Huraira ma sosai yake ƙaunar Bunayd, dan Bunayd yaro ne da duk wanda ya
kallesa to sai ya shiga ransa, ba shi da ƙiriniya irin na sauran yara, kana ganinsa kaga zubin sadauki, yana da
raha idan yayi niya musamman idan yana tare da General Sufyan ko Alhaji Mukhtar.
Bunayd na da shekaru sha uku mugun soyayya ya ƙullu stakanin General Sufyan da yarinyar Sultan na
Sokoto, ta sanadin abokin General Sufyan, Major Ahmad wanda yake yaro a wajan wazirin Sarkin Sokoto,
soyayyan General Sufyan sosai yayi nisa shi da Gimbiya Ramlat, ta san yana da yaya kuma tasan yana da
yaro, wani stautsayi ne ya faru stakaninsu wanda yayi sanadin raba soyayyansu, damuwan da General
Sufyan ya shiga shi ya sanya mahaifin Huraira ya basa auren Huraira tunda ba ta haramta a gare sa ba، duk
kuma abinda ke faruwa Alhaji Mukhtar bai da labari dan yayi tafiya ƙasar waje.
Ba jimawa aka yi auren Huraira da General Sufyan, Bunayd sosai ya ji daɗin da Huraira ta dawo gidansu,
kuma Huraira stakani da Allah take riƙe Bunayd da soyayya kaman ɗan cikinta, duk da ba wai ya cika zama
bane, sakamakon makarantan sojojin sama da General ya saka shi, da farko Sojan ƙasa yayi niyan turasa
amma sai Bunayd ya ce Air Force yake so, shi jirgi yake so.
Alhaji Mukhtar ya dawo ya samu labarin abinda ya faru nan ya bi su da addu'an Allah ya kyauta, a wannan
lokacin ne kuma ciki ya bayyana jikin Hajiya Sa'adatu ba shiri ba sanarwa, duk ta gama sakankancewa ta
daina haihuwa tunda ta yi planning, amma ikon Allah sai ga ciki, baƙin ciki kaman ta yi yaya, ta yi iya yinta
amma ta kasa ɓarar da cikin, haka ta haƙura ba dan ta so ba sai dan ba yanda ta iya da nufin Allah, ciki na
kai wata tara ta haifa yarinyarta santaleliya kyakkyawa mai sunan mahaifiyar su Alhaji Mukhtar, Hauwa'u
amma suna ƙiranta Majeeder.
Huraira na cika shekara a gidan General Sufyan ta haifo yarinyarta mace kyakkyawa mai kama da Alhaji
Mukhtar, yarinya ta ci suna Ramla, bayan shekara biyu ta kuma haihuwan ƴan biyu mace da namiji, Suhail
da Suhaila, bayan wasu shekaru biyun ta kuma haihuwan ƴan biyu, Nabeel da Nabeela, bayan shekaru biyu
ta haifi yaronta namiji amma ya koma, saboda wahalan da ta sha da cikin yaron sai General ya buƙaci da a
stayar da haihuwan, Allah ya yiwa waɗanda suka haifa albarka.
Hajiya Sa'adatu tun da ta haifi Majeeder sai ta je asibiti a ɓoye aka cire mata mahaifa ba tare da sanin
Alhaji Mukhtar ba, kuma har yau bai sani ba.
Yaran gidan General Sufyan sun taso cikin gata da soyayya na iyaye da kuma yayansu Bunayd, kaman yanda
General ya kula da karatun Bunayd, haka shi ma yake kula da karatun ƙannensa, sosai yake ƙaunar
ƙannensa, amma sam-sam ba ya shiri da Mom tasu Hajiya Sa'adatu.
Bunayd ya fara abota da Abeed ne tun san da ya shiga makarantar sojojin ƙasa da farko, sai ya zamana duk
da ya koma air force school to ba su bar abota ba, shi ma Abeed ɗan