Showing 9001 words to 12000 words out of 20751 words
Chapter 4 - ZABIN MAHAIFIYATA Book Complete BY ESHAAT.txt
a gaban rigan, ya saka farin hula da farin takalmi se agogo silver colour. Shima yayi kyau sosai a takaice dai sunyi anko ne da salma. Ya hade fuskarnan kanshi yana kasa yana daddana waya be ko nuna alamun yasan da zaman mutane a wajen ba.
Girgiza kai kawai tayi ta rufe motar ta juya ta koma cikin gida. Bayan k'awaye da sauran mutane sun shishshiga mota ne, motoci suka fara tafiya suka nufi hanyar da zata kaisu "ME SANDA GREEN GARDEN" sbd acan zasu gudanar da dinner. Tafiya akeyi amma ba wanda yayima dan uwansa magana. Salma kanta yana k'asa tana wasa da zoben azurfan dake hannunta shikuma ya maida hankali wajen danna waya ko me yake dannawa oho.
Da saleem yaji shirun yayi yawa ne yayi magana"amaryan mu yau ba gaisuwa ne?" murmushi salma tayi ta dago kanta ta kalle shi ta cikin mirro tace ina wuni yaya saleem. Lafiya lau ya amsa mata cike da jindadin girmama shi da tayi. Ya hidiman biki? AlhmdlhοΌ ta amsa. Duk abinda sukeyi A.A be ko d'ago kanshi ba balle ya tanka musu. Ba wanda ya sake magana har aka k'arasa wajen. Bayan motocin sun gama parking mutane suka fiffito suka nufi cikin hall din.
Juyowa salim yayi ya kalli A.A yace Friend dan ALLAh karka fita ku d'an jira ayi arranging din k'awayen,πππ be d'ago ba balle ya amsa masa. Bayan fitan saleem ne ya d'an juyo da kansa ya kalli salma da kanta yake k'asa, zuba mata ido yayi gabansa yana faduwa ya rasa dalilin dayasa idan ya kalli yarinyar se yaji faduwan gaba.
A gaskiya tayi mishi kyau sosai, daman haka take da kyau? duk da mata basa gabansa amma ya tabbatar wa kansa wannan ta dabance. dan tana da wani sirrin kyau wanda mutum bazai saniba d idan yana tare da ita ga wani kwarjini da tayi masa. Besan lokacin daya saki murmushi ba, adai-dai lokacinne salma ta d'ago da kanta dan taji a jikinta kamar ana kallonta. Suna had'a ido ya d'auke kansa ya murtuk'e fuska kamar be tab'a dariya ba.
Kallonsa kawai salma takeyi tana mamakin halinsa mutum se miskilancin tsiya, gashi dai ta kama shi yana kallonta amma ya kauda kai kamar bashi ba. Dani kake zance zakama dawo kan hanya indai nice ta fad'a a zuciyar ta.
muje zuwa
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:35PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
ZAB'IN MAHAIFINA
π³π³π³π³π³
Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)
πHAJOW ππ
ππ©βπ§βπ§π©βπ§βπ§π©βπ§βπ§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS βπΎβπΎβπΎπ
Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI
page 17
Bayan sady ta gama mata make-up din salma ta saka hijab d'inta tayi sallar magriba dan lokacinsa harya kusa fita, tana idarwa aka kira isha'i. Tashi tayi ta yi sallar isha'i. Bayan ta idar tayi addu'o'inta aka shiryata cikin doguwar rigan material fitted gawn, wanda A.A suka kawo mata akan tasa ranar dinner. tasaka mahadin kayan ta fesa turare. Gaskiya salma tayi kyau dan kuwa my namecy taci kudinta, inso samune ayi mata k'ariπ.dan ta'iya shirya amare.
Hajiya halimat ce tayi sallama ta shigo dakin. wawοΌ my daughter kinyi kyau sosai,ta kai dubanta ga sady tace gaskiya takwara kin iya tsara kwalliya,ai wannan indai baka santa ba baza ka iya ganeta bama. Lallai kina da kyauta me tsoka tunda kika sa daughter tayi kyau haka.
Ita kuma sady jin an yabeta ne yasa ta fara magana cike da iyayi,ai hajiya inayi fiye da hakama. murmushi Hajiya halimat tayi ta kama hannun salma suka nufi falo. Kawayen amarya na zaune sunyi kwalliyar su cikin lace orange da touch din blue a jiki, se suka saka head blue suma sunyi kyau ba lefi.
Har bakin mota hajiya halimat takai salma, wata had'ad'd'iyar mota naga ta bud'e ta saka salma a ciki, galases din motar tint ne baka iya hango wanda yake ciki.
ta dubi saleem dake zaune a gaban motar tace ga amanar 'yata,kar ku bari wani abu ya tab'a min ita dan kunsan bazan bari ba. Sake juyowa tayi ta kalli A.A wanda ke zaune a bayan motar. yana sanye da shadda purple colour anyi design fari a gaban rigan, ya saka farin hula da farin takalmi se agogo silver colour. Shima yayi kyau sosai a takaice dai sunyi anko ne da salma. Ya hade fuskarnan kanshi yana kasa yana daddana waya be ko nuna alamun yasan da zaman mutane a wajen ba.
Girgiza kai kawai tayi ta rufe motar ta juya ta koma cikin gida. Bayan k'awaye da sauran mutane sun shishshiga mota ne, motoci suka fara tafiya suka nufi hanyar da zata kaisu "ME SANDA GREEN GARDEN" sbd acan zasu gudanar da dinner. Tafiya akeyi amma ba wanda yayima dan uwansa magana. Salma kanta yana k'asa tana wasa da zoben azurfan dake hannunta shikuma ya maida hankali wajen danna waya ko me yake dannawa oho.
Da saleem yaji shirun yayi yawa ne yayi magana"amaryan mu yau ba gaisuwa ne?" murmushi salma tayi ta dago kanta ta kalle shi ta cikin mirro tace ina wuni yaya saleem. Lafiya lau ya amsa mata cike da jindadin girmama shi da tayi. Ya hidiman biki? AlhmdlhοΌ ta amsa. Duk abinda sukeyi A.A be ko d'ago kanshi ba balle ya tanka musu. Ba wanda ya sake magana har aka k'arasa wajen. Bayan motocin sun gama parking mutane suka fiffito suka nufi cikin hall din.
Juyowa salim yayi ya kalli A.A yace Friend dan ALLAh karka fita ku d'an jira ayi arranging din k'awayen,πππ be d'ago ba balle ya amsa masa. Bayan fitan saleem ne ya d'an juyo da kansa ya kalli salma da kanta yake k'asa, zuba mata ido yayi gabansa yana faduwa ya rasa dalilin dayasa idan ya kalli yarinyar se yaji faduwan gaba.
A gaskiya tayi mishi kyau sosai, daman haka take da kyau? duk da mata basa gabansa amma ya tabbatar wa kansa wannan ta dabance. dan tana da wani sirrin kyau wanda mutum bazai saniba d idan yana tare da ita ga wani kwarjini da tayi masa. Besan lokacin daya saki murmushi ba, adai-dai lokacinne salma ta d'ago da kanta dan taji a jikinta kamar ana kallonta. Suna had'a ido ya d'auke kansa ya murtuk'e fuska kamar be tab'a dariya ba.
Kallonsa kawai salma takeyi tana mamakin halinsa mutum se miskilancin tsiya, gashi dai ta kama shi yana kallonta amma ya kauda kai kamar bashi ba. Dani kake zance zakama dawo kan hanya indai nice ta fad'a a zuciyar ta.
muje zuwa
π³π³UMMU AFFANπ³π³
[1:36PM, 2/7/2018] βͺ+234 808 677 7945β¬: π³π³π³π³π³
ZAB'IN MAHAIFINA
π³π³π³π³π³
Written by SADIYA ALHASSAN (Ummu Affan)
πHAJOW ππ
ππ©βπ§βπ§π©βπ§βπ§π©βπ§βπ§HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS βπΎβπΎβπΎπ
Dedicated to PRINCESS ESHAT AYSM
AYSHA BICHIKI
Page 18
Wannan shafin nakine ke kadai UMMU LAILA. kiyi yanda kike so dashi, Nagode da k'aunar ki gareni ALLAh ya bar Zumunciπ€
Bude murfin motan akayi ta gefen salma,aunty hadiza ce ta fito da ita. Shima A.A ya bud'e ya fito
K'awayen amarya ne da abokanan ango suna tsatstsaye. Salma da A.A suka shiga tsakiya aka nufi cikin hall din abokai da k'awaye suna watsa musu flower. Tun daga wajen hall din kake jin kid'a yana tashi. D.J ya bada sanarwan shigowan ango da amarya, duk wanda suke cikin hall din suka mimmik'e. Saida sukaje suka zauna sannan mutanen suka zazzauna.
Bayannan D.J ya tashi yayima ango da amarya barka da zuwa. Aka nemi abokin ango da k'awar amarya suzo su bada tarihin ango dana amarya. Saleem ne ya tashi ya bada na ango, wata 'yar uwar salma tazo itama ta bayar. Bayan sun koma sun zauna aka umurci ango yazo ya yanka cake shida amaryar sa.
Ruk'o hannun salma A.A yayi,da sauri ta dube shi ko kallonta beyi ba ya mik'e tsaye,dole tasa itama ta tashi suka je wajen da zasu yanka cake din. kid'a aka sake cikin wak'ar nura m inuwa wanda yayi musu na bikin. Cake d'in me hawa uku ne, an rubuta sunayesu a jiki. hannunta da nashi suka had'a suka yanka, nan hall d'in yad'au tafi. ya d'auka yasa mata a baki cikin jin kunya ta karb'a itama ta yanka ta bashi.
Bawanda zai gansu yayi zaton ba masoya bane se dai idan ka sani, juyawa sukayi suka koma wajen zansu. Nan akaci gaba da gudanar da taron yanda ya kamata, anci ansha an goge wuya. Wajen diban abinci ne na hango 'yan group d'in just hausa novels da 'yan group din princess eyshat Aysm da 'yan group d'in ummun sadiq novels se ture-ture sukeyi kowa yana son ya cika timbinsa.πππππ
Bayan an tashi daga taron aka maida salma gidansu A.A ita da k'awayenta dan acan zata zauna har agama bikin. Washe gari ya kama yini tun safe sady tasa salma tayi wanka dan tanason tayi mata kwalliyar datafi ta jiya. Aikuwa ta tsara mata dan har taso tafi jiya kyau, tayi shigar jan atamfar sufer wax da ratsin green a jiki. ta saka sark'an diamond da abin hannunsa. Anyi wunin biki lafiya sunyi hotuna se fatan ALLAh ya bada zaman lafiya. Da daddare bayan mutane sun watse angwaye sun sallami k'awaye kowa ta tafi.
Salma tana zaune a kan kujera a dakin hajiya halimat, Aunty hadiza ta shigo ta sameta, to salma nizan tafi tunda ance ba yau za'a kaiki ba,in yaso gobe zan dawo ina fatan babu matsala??? girgiza kai salma tayi idonta ya cuko da hawaye tace bakomai aunty ki gaida min da innata. murmushi Aunty hadiza kawai tayi sannan tayi mata sallama ta tafi.
A gurguje
mahaifiyar A.A ce ta shigo ta sami salma a zaune tayi tagumi. zama tayi kusa da ita ta janye hannun tace, ki dena damuwa daughter ki daukeni kamar mahaifiyar ki, duk abinda yake damunki ki sanar dani karkiji kunyata kinji? gyada mata kai salma tayi, yanzu ki tashi kije ki kwanta kinga dare yayi. Ta ruk'o hannun salma ta kaita bakin gado tace ta kwanta, ta lullub'a mata bargo kasancewar lokacin sanyi ne, ta kashe mata wuta ta fita ta nufi d'akin me gidanta.
ASUBA TA GARI SAL-AZEEZ.
Washe gari bayan sunyi breakfast, salma tayi wanka sady tayi mata make-up kasancewar itama a ranar zata koma garinsu sokoto dan aikinta ya k'are. Salma ta shirya cikin shadda light brown d'inkin doguwar riga yasha aiki, ta yapa gyale dark brown tasa takalminta flat shima dark brown.
k'arfe 11:00am Aunty hadiza ta iso ita da wata k'anwar inna saude Aunty Asma'u. Bayan an gaggaisa hajiya halimat takai salma falon Alh. Abdul-razak me dala domin su gaisa dan tunda tazo basu had'u ba saboda sha'anin biki. Kanta a k'asa ta durk'usa a gefe cikin jin kunya ta gaida shi, fuskar sa d'auke da murmushi ya amsa mata, sannan ya d'anyi mata nasiha. Ya mik'a ma hajiya halimata emvelop ki bata wannan ATM ne dana bud'e mata account saboda idan tana buk'atar kud'i ba saita tambaya ba, yanzu haka akwai kudin dana zuba a ciki 1million naira, zan dunga tura mata 500k duk wata insha ALLAhu. Godiya sosai salma tayi mishi tana jinjina karamci irin nasu.
Hajia halimat ta ruk'o hannun salma suka fito daga falon, suka iske su Aunty hadiza suna jiransu, gyalenta ta d'auko dan tace harda ita za'a raka salma gidanta 'ya'yanta mata se tsokananta sukeyi, kowacce tana rataye da jakanta kowa zata koma gidan mijinta tunda an gama bikin. Motoci suka shishshiga Aunty hadiza da Aunty asma'u suna cikin mota d'aya, se hajiya halimat da salma suma suna 1 dukkansu driver ne yake jansu.
Wanr had'ad'd'en gida naga sun nufa dake cikin G.R.A(sir kashim) bud'e musu get me gadi yayi saboda besan amarya bane, dan tun jiya matar gidan tayi masa warning akan karya yadda ya barsu su shiga.
Bayan motocin sunyi parking a haraban gidan, suka fiffito salma bakinta d'auke da addu'an neman tsari ta fito da k'afar dama, gabanta se calugude yakeyi. da gudu me gadi ya k'araso daya fahimci su wanene su.
dan Allah hajia kuyi hakuri wallahi tace min karna barku ku shigo,in kuma na barku to a bakin aikina ya fad'a yana durk'usawa.
kallonsa hajia halimat tayi tace ka kwantar da hankalinka mallam musa ba wanda ya isa ya rabaka da aikinka, Nan take ya fara murmushi dan yaga kamanninta da me gidan ya tabbatar mahaifiyasa ce, godiya yayi mata sannan ya koma bakin aikinsa.
Ita kuwa hajiya halimat dama dalilin zuwanta gidan kenan, dan ta tabbatar za'ayi hakan.
Cikin gidan suka shiga, gidan flat ne baida girma sosai amma ya tsaru. idan ka shiga zaka tarar da babban falo wanda yasha had'ad'd'un kujeru seti 2, brown da milk, se labulaye da chanise carpe da t.v plasma babba. a can gefe kuma dining room ne an k'awata shi da dining table da kujeru.
Akwai k'ofofi guda 2 a cikin falon left and right. kowani kofa yana d'auke falo madaidaici da 2 bedroom da toilet, se kuma kitchen wanda yake d'auke da store aciki. Akwai babban kitchen ta baya wanda yake kusa da BQ da alama a ciki masu aiki suke girki.
D'aki 1 na uwargida humaira ce, d'ayan kuma na A.A ne wanda yanzu ya barma salma shikuma ya koma d'akin gimbiya humaira. Gidan dai-dai zaman mata d'ayane ita da mijinta, dan basu dad'e da komawa gidan ba. Basu samu kowa a falon ba da alama masu gidan har lokacin basu tashi ba.
Aunty hadiza ce ta ska key ta bud'e dakin dake mazaunin na salma suka shiga. Gaskiya d'akin ya tsaru readers na barku ku wassafo yanda d'akin yake basai nayi muku bayani ba.
Dad'a gyara ko ina sukayi sannan Aunty hadiza taja hannun salma d'aki suka d'anyi maganganunsu ta bata shawaran yanda zata zauna da kishiyarta, karta yarda taji tsoronta, ta fiddo da hisnul muslim a jakarta ta bata, tace ta dage da addu'a. ta kuma yi k'ok'arin juyo da hankalin mijinta gareta.
suka fito sukayi musu sallama dan ita hajia halimat tace ba yanzu zata tafiba se tayima matarsa warning akan salma.
to kunji pa readers koya zata kasance ko biyo ni.
Bayan su Aunty hadiza sun tafine suma suka fito babban falo suka zaunag
Hajiya ta dubi salma tace daughter ki dage da addu'a pa da kuma azumin litinin da alhamis, kin riga kinsan komai ba sena fad'a miki ba.
K'arar bud'e k'ofa sukaji A.A ne ya fara fitowa bayansa humaira ce tasha riga da skirt na lace golden sun matseta kanta ba d'ankwali se kitson attach da ya zubo mata har baya, ba lefi tana da kyau amma bata kama k'afar salma ba.
Ido hud'u sukayi da mahaifiyar sa da sauri ya k'araso cikin falon yana murmushi. Zama yayi akan kujera sannan yace "Gud morning cwt Mom ai bansan kinzo ba" itama murmushin tayi dan taji dad'in ganin d'an nata dan rabonta dashi tun ranar dinner.
Gud mornin son da fatan na same ku lafiya?? ko kad'an bata nuna masa b'acin ranta ba dan tasan bayin kansa bane. lafiya lau ya amsa mata.
Se alokacin humaira ta k'arasa shigowa falon dan mutuwar tsaye tayi da ta gansu, batayi tsammanin ganin hajiyar ba saboda bata tab'a zuwa gidan su ba, bayan hakama ai tayi wa get man warning,wato bejiba seda ya bud'e musu aikuwa yayima aikinsa. ta fad'a a cikin zuciyarta.
Akan kujera ta zauna 1 seater ta gaida hajiyar ta amsa mata ba yabo ba fallasa.
idonta ta kai kan salma wanda ko kallo basu isheta ba balle ta gaishe su.
Gabantane yayi mugun fad'uwa ganin tsantsar kyau irin na salma tunda ake mata kishiya ba'a tab'a mata me kyau da kwarjini kamar salma ba.
Hajia halimat tayi musu nasiha sannan tace "Abdul ga salma nida kaina na kawo maka ita inaso kayi adalci ban yarda ko bayan raina ka rabu da ita ba, kasani duk randa kasake ta to wallahi seka saki wannan matar taka" kuma ina so yanzu ka raba musu kwana. idan ka gama 7days dinka a dakin salma se su fara raba kwanakin.
Ba tare daya kalli humaira ba yace ya raba kwana bibbiyu. Iyakan b'acin rai humaira takai, lallai wannan matar wato tanan ta b'ullo ai kuwa intasan wata batasan wata ba. Matsalan da take samu 1 ne duk yanda takai ga son ta raba Abdul da iyayensa ta kasa. danta kasa cire masa sonsu a zuciyar sa, ta waje d'aya ta samu nasara data hanashi zuwa gidan