Showing 249001 words to 252000 words out of 441529 words
Chapter 84 - Mafari Hargitsin Rayuwa Book Complete by Ummu Muaz.txt
Mutum dai baya 茩in ta Mutane wai ance da 蓳arawo ya gudu聽 , Bi Rahima can dai kin tambaye ta Dan Allah .
Garam !
Hajja ta rufo 茩ofar 蓷akin ta .
Sa茩are tayi a tsaye tana son harha蓷a tunanin ta domin ta kai ga fahimtar meyasa ta ga kamar ana gudun ta ? Ashe girman laifin ta har ya kai ya sa ta zama abun gudu a wajen mutane ?聽
Falmata ina Falmata ? Ta san idan kowa zai guje ta a duniya a zare Falmata a cikin su , Falmata baza ta ta蓳a gudun ta ba , ina take ?
Ta juyo da nufin fitowa ta nufi sashin Baba , sai ga Rahima tare da wani mutum wanda bata kai ga sanin sa ba .
Mallam Kabir ga ta nan , ta nuno Yakaka wacce take tsaye 茩i茩am rungume da hoto .
Dan Allah kana ganin ta ?
Ina ganin ta mana Hajiya Rahima , ai wannan Mutum ce , ba Fatalwa ba ,聽 hala an samu akasi ne wajen jin wani labari akan ta ?
Ke baiwar Allah wacece ke ? Daga ina kike聽 ? Me kuma kika zo yi nan?聽
Zuwa lokacin Yakaka ta fara hasaso abunda yake faruwa , dan haka fuskar ta na bayyana sabon alhini ta matso tana cewa .
Rahima ni ce Yakaka , ba Fatalwa ba ce ni , ban mutu ba , waye yace na Mutu ???? Ina Falmata ?
Ba tare da Rahima ta ce 茩ala ba , bata kuma yadda ta 茩arasa kusa da Yakaka ba ta sake juyawa da 蓷an gudu ta nufi sashin Baba , da daman daga can 蓷in take shine ma ya ha蓷o ta da Mallam kabir 蓷in da ta zo ta same su tare suna ganawa ,
Tana cikin yiwa Baba bayanin dawowar Yakaka 拼ar gudun hijira wanda suke da tabbacin mutuwar ta a wajen haihuwa shekaru kusan shidda da suka wuce ,
Sai ga Mallam kabir tare da Yakaka wacce take biye da shi聽 .
Da ido Baba ya bisu bayan ya amsa sallamar su ,聽 har suka 茩araso cikin falon inda Yakaka ta nemi waje daga can gefe guda ta dur茩usa bisa guiwowin ta ,
Mallam kabir bai zauna ba yayi bankwana da prof tare da juyawa kan takun sa ya bar wajen .
Prof bai yiwa kamannin Yakaka sani na sosai ba amma tabbas ya shaida fuskar ta , saboda ya ta蓳a ganin ta a farkon zuwan ta gidan sa , sannan a 蓷an ta茩aitatcen zaman da tayi a gidan tana zuwa gaishe shi lokaci-lokaci .
Babu alamun firgici a tare da shi yake amsa gaisuwar Yakaka , wacce kan ta ke a sunkuye .
Cikin nutsuwa irin ta manyan mutane da suke da tarin ilmi ya soma da tambayar Yakaka daga ina take ? Me kuma ya faru da ita tsawon shekarun da tayi bata nan ? Bai shigo mata da batun labarin mutuwar ta da yake tabbatacen Al'amari ba a wajen su a tsawon shekarun da tayi bata nan .
Tambayoyin sa suka fargar da Yakaka tare da tuno mata da Malama Maryam da ta baro can a layi fiye da mintoci ishirin ,
Wacce ta san zata taya ta fuskantar mutanen ta da tarin laifukan da suke kan ta ,
Tare muke da ba茩uwa Baba , a min iznin na shigo da ita .
Je ki shigo da ita babu kome .
Bata jima ba suka dawo da tare da Malama Maryam wacce聽har ta fara shiga halin damuwa ganin lokaci ya 蓷an jaa batare da ta ga dawowar Yakaka ba .
Cikin nutsuwa da kamalar da Allah ya hore mata Malama Maryam ta gaishe da prof , sannan ta gabatar da kan ta a matsayin Malamar Yakaka wacce ta 蓷au darasi a wajen ta tsawon shekaru biyar da 蓷oriyar watanni , a garin Abuja , daga haka ta tsagaita .
A hankali muryar Yakaka ta fara tashi tiryan-tiryan take bada labari tun daga irin Gadar zaren da Samy baby ta ha蓷a mata har kawo ranar barin ta Maiduguri da ta sanyata ta tsallake ta bar Jaririyar ta a ranar da ta haife ta , da zummar zata kai ta Abuja wajen mahaifn 拼ar ta suyi aure ta dawo ta 蓷au yar da 茩anwar ta .
Wacece ita Matar da kika bi ? Menene聽 dangantar ku da ita ?
Tambayar Prof ta katse Yakaka .
Shiru Yakaka tayi na 蓷an wani lokaci , tunowa da tayi da irin rufin asirin da Doctor Hamza ya yi mata a farkon kawo ta gidan ya bayyana ta a matsayin 拼ar gudun hijirar da mijinta ya mutu ya bar ta聽da ciki ,聽
茦aramin tunani irin nata tare da mummunar 茩addara suka sa ta sanya 茩afafu ta ham蓳arar da irin tarin rufin asirin da Allah ya yi mata a tun wancen lokacin da hakan ya jawo a yau ita da kanta zata tona binnannen sirrin nata聽 .
Domin a yanzu ta 蓷au al茩awarin baza ta sake yin 茩arya ba , dan haka idanun ta na tara 茩wallar nadama da irin laifin da ta aikata ta koma baya , kan ha茩i茩anin gaskiya ta 蓷orar da labarin ta tun daga farkon shigowar su birnin Maiduguri zaman su a sansanin su, da zaman da suka yi聽 a gidan Madam saly , shigowar Biyamuradi rayuwar ta wanda ta ambace shi da "sojan wata 茩asa ," har zuwa zaman ta a Abuja tare da dawowar ta a yau bata boye duk wasu gaskiyar da yakamata ta bayyana su ba ga mutumin da shine na farko da suka samu mafaka mai cike da karamci da tarin 茩auna a 茩ar茩ashin sa ,
Shiru ne ya gifta na tsawon wasu mintoci , da hakan ya bada dama ga malama Maryam ta 蓷ora da sake bada kyakkyawar shaida ga Yakaka , yadda ta jajirce wajen neman ilmi ha蓷i da yadda ta cije tare da taimakon Allah ta hayewa fa蓷awa ga rayuwar karuwanci kamar yadda ita samy baby ta so da ta aikata .
Mamakin mazajen guda biyu shi yafi kome yin tasiri a tunanin Prof, da har ta kai shi ga gaza cewa wani abu .
A zahiri yau ta bayyana a gareshi cewa daga 茒an sa Hamza har shi wancen mutumin da ya zo har nan gurin sa ya 茩arbi auren 拼a a wajen sa duk 茩arya suka wanzu tsawon lokaci suna gindaya masa akan rayuwar marayun yaran su biyu .
Wanda a zahiri 茩aryar ta su ta cutar matu茩a gaya , ba su kuma kyauta ba .
茦aryar da Hamza yayi ita ta tokare ta hana shi yayi yun茩urin nemo yarinyar ya dawo da ita ta zauna 茩ar茩ashin kulawar sa kamar yadda a tun ranar da ya kar蓳e su ya al茩awartawa kan sa , wanda hakan ba wani abu ne me wahala ba kasantuwar sa babban Mutum , amma sai hamza yayi masa 茩arya cewa ta mutu har ma yayi jana'izar ta a asibiti , wanda a zahiri tun lokacin聽 shi Hamza yana da masaniyar guduwa tayi , ko me yasa yayi hakan oho !
Sai kuma shi wancen mutumin Niger da ya riga ya san irin mummunan ta'asar da ya aikata na lalata tarbiyar yarinyar nan , amma kuma shine ya sake dawowa ya rufe shi a baibai tare da kar蓳e 蓷iyar sa domin sake samun gara蓳asa har aka 茩ara masa da 茩anwar ta a matsayin mata duk a tafarkin 茩arya ??
Wannan wane irin son zuciya ne ? Meyasa ne gaskiya tayi 茩aranci ? Shin 拼an gudun hijara ba 'ya'ya bane ba ? Ba mutane ne masu 拼anci da galihu irin na sauran Al'umma ba ?聽 Da rayuwar su zata zam ba a bakin kome ba ? Za kuma a dunga yin walagigi da su cikin rashin kulawa da tozartawa , a maishe su ba a bakin kome ba , shin za蓳in su ne rabuwa da iyayen su , dangin su , garuruwan su ? Ko kuwa 茩addara makamanciyar wannan bata iya fa蓷awa kan kowa ne ?
Idan har ya tabbatar da duk labaran da suka bayyana a gare shi gaskiya ne , babu shakka zai yi tsayuwar daka cikin rayuwar 拼an gudun hijirar nan guda biyu , zai zama katanga tsakanin su da duk masu shirin tozarta su a sannu kuma zai 蓷au hukuncin da ya dace akan Hamza da 蓷an mutan Niger .
Muryar Malama Maryam ita ta sanya shi nisawa , ya maida ganin sa kan ta .
Baba ayiwa Yakaka hakuri a yafe mata babu shakka tayi laifi tare da zallar wauta amma domin Allah a 蓷au hakan a matsayin kaddara a cigaba da godewa Allah da ya sa har ta dawo gida lafiya ba tare da wani mummunan lamari ya auku gareta ba ,
Babu kome baiwar Allah mun gode 茩warai Allah ya saka miki da Alheri kan yadda kika kula da ita , kema Allah ya duba miki naki iyali , Allah ya 茩ara mana yawaitar irin ku cikin Al'umma masu taimako domin Allah .
Cikin jin da蓷i Malama Maryam ta amsa da Ameen .
瞥ar boyayyar Ajiyar zuciya Yakaka ta sau茩e ganin yadda Alamu ke bayyanuwa yadda take zaton tsanantar lamarin nata duk bai kai haka ba ,
A hankali ta 蓷ora idanun ta kan Rahima wacce ita ma kallon ta take , suka ha蓷a ido kafin Rahimar tayi mata guntun murmushi marar sauti .
A yanzu hankalin ta ya kwanta ta kuma amince Yakaka ce da gaske ba Fatalwa ba聽 .
Ita ma ta mayar mata da martanin Murmushin , 茩aunar junan su tamkar a jinin su take , duk da tarin abubuwan 茩i da Rahima ta san yakaka ta aikata su a yanzu , hakan bai sa ta ji kamar ta tsane ta ba .
Kalaman Prof ya sa Yakaka sake nutsuwa ta mayar da hankalin ta kan shi ,
Bisa ga doron kuskuren da kika riga kika aikata su Abubuwa biyu zuwa uku sun faru ,
Na farko labarin mutuwar ki , a gare mu tuntuni kin mutu tundaga ranar da kika gudu kika bar 'yar ki .
Na biyu shine zuwan da mutumin da ya 茩ira kan sa mijin ki uban abunda kika haifa yayi ,
Na ukun su shine tafiyar sa da yayi da 'yar sa tare da auren 茩anwar ki a lokaci guda da ni da kaina nayi waliccin auren a nan falon nan na bada auren 茩anwar ki Fatima ga mijin ta uban 'yar ki na kuma 蓷anka masa ita suka tafi tare 茩asar su niger tare da rikiyar Hajja me wurya .
Da ace Yakaka ta ta蓳a sanin yadda ciwon Ajali yake da babu shakka zata iya cewa shine ya dirar mata a lokacin saboda wani irin abu me kaifi da ta ji ya taso mata daga 茩asan mara ya zo 茩irjin ta ya tokare ta ,
Muryar ta a shi蓷e ta wufto kalaman da suke kan harshen ta ta watso su ga Prof idanun ta tsaye 茩em a kan fuskar sa
Falmata ce tayi aure da Baban Mama ?
Da sake tabbatarwa Prof ya amsa mata da
Haka kalamaina ke nufi.
Abunda take jin ne ya watsu a cikin jikinta ya barbazu tamkar an watsa mata wuta kafin ya sake dun茩ulewa a ma茩ogoran ta ya tsaya ,
Yaa Allah , Yaa Allah , Allah na tuba kar laifin da na aikata ya shafi Falmata , Allah ka dawo min da Falmata , Allah ka...
Mul-mulan hawayen da suka fara 茩waranyowa daga idanun ta tare da fashewar 茩ullutun da yake wuyan ta shi ya hana ta cigaba da magana illa kukan da ta fashe da shi marar 茩arfin sauti ,
Kuka ne irin na mutumin da ya ke a halin 蓷imuwa tare da nadama kuka ne irin na ba yadda zan yi , kukan neman taimako ,
Baki 蓷ayan su irin kukan da take ya ta蓳a zukatan su ,
Musamman Malama Maryam da Rahima ,
A bangaren Prof duk da cewa ya ji tausayin ta amma ya bar ta da hakan a matsayin sakamakon laifin da ta aikata .
A hankali Rahima ta 茩arasa inda take ta sanya hannu ta dafa ta ,
Kiyi hakuri Yakaka tashi mu shiga cikin gida , ki bar kuka hakan ,
Mi茩ewa tayi ta fara taku ba tare da ta cewa kowa kome ba ta wuce ,
Malama Maryam ta rissina ta yiwa Prof sallama tare da shaida masa gobe da sassafe zata kama hanyar komawa gida
Godiya ya sake yi mata , suka rabu suna bin juna da kalaman fatan alheri .
Bayan fitar su bai jinkirta ba ya 蓷au wayar sa ya nemo lambobin wayar Doctor Hamza ,
Fitowar sa kenan daga ICU inda ya jonawa marar lafiyar da aka 茩ira shi domin ita wasu na'urai ya kuma sake duba ta sosai kasancewar ya 茩ware sosai wajen gano tare da bada taimako akan cutar da take damun ta na dajin bakin mahaifa ,
Mutanen da suke 拼an uwa ga marar lafiyar suka taso caa su kusan rai shidda suna tambayar sa yanayin jikin nata聽 ,
Nan dai ya kwantar musu da hankali tare da sanar musu da insha Allah zasu yi bakin 茩o茩arin su, su kuma su taya su da addu'a ya ratsa su ya wuce ,
Ya ji lokacin da 蓷aya daga cikin su tace tunda mun ji yanayin da take ciki sai Maman Bulama ta koma gida ta yi girki ta kawo kuma ta ha蓷o wasu kayan da za'a iya bu茩ata ,
Maa ki mata bayani yadda zata gane sosai dan ke ce kika iya maganar su ta kurame ,
Da hannu suka yafito wata mata wacce take zaune a 茩asa daga gefe .
Da sauri ta taso ta 蓷an russuna daga gefe ,
Maa tayi mata bayani da hannu cikin maganar kurame ,
Cikin sauri take gya蓷a kai alamun tana fahimta,
Naira 蓷ari biyu ta zaro daga jaka ta mi茩a mata , ta sanya hanu biyu ta kar蓳a ,
Ta mata alamar cewa ku蓷in mota ne
Ita ma ta gya蓷a kai kan cewa ta gane
Har ta juya ta sake dawowa ,
Tayi musu alamar tambaya tana nuna 蓷akin da marar lafiyar ke ciki . Fuskar ta na bayyana Alhini .
Amsa maa ta bata da hannu .
Ta juya ta kama hanyar barin asibitin ,
Doctor hamza wanda ya gama amsa wayar prof da yake sanar da shi kan lalle ya zo yana son ganin sa daga zarar ya kammala abunda yake a asibitin ,
Ya mayar da wayar sa aljihu tare da juyawa da zummar komawa cikin ofishin abokin aikin sa da shi yayi 茩iran sa domin suyi sallama ya kuma gama yi masa bayani akan irin matakin da yakamata a 蓷aura marar lafiya akai zuwa gwaje-gwajen da ya dace ayi mata聽
茦iris ya rage ya ci karo da matar da ta taho tana ta sauri ,
sannu Hajiya ,
Yace yana kaucewa yin karon su , a fisge ya dubi fuskar ta lokacin da take gota shi ba tare da ta amsa ban hakurin da yayi mata ba
Cak !聽 Ya tsaya , lokacin da kamannin ta suka yi masa yanayi da na wata da ya sani waye ?
khaalty Rahima .
Juyowa yayi da sauri da son sake ganin fuskar ta sosai , sai dai ta riga tayi nisa sai tashin hijabin ta ya ke iya gani wanda ya cika da iska saboda saurin da take zabgawa .
*****
Daga bakin 茩ofar falon Yakaka ta zame ta zauna , tana wani irin kuka ciki-ciki , a halin da take jin zuciyar ta a ciki babu abunda take fata irin kome da ta ji ace a mafarki ne , bacci take yi ta yi wannan mummunan mafarkin , ta gwammaci ace ta bu蓷i ido ta ga kan ta a gidan samy baby , kai ta amince kome ya faru da ita , da dai dawowar ta Maiduguri ta tarar da wannan mummunan labarin da ya kassara duk wani guntun 蓷oki da mararin sake ganin wani nata a duniya ,
Aure , wai Aure da Falmata da mutumin da ya yaudare ta ya cutar da ita , ya lalata mata rayuwa tare da bar mata ta蓳on da har abada ba zai gogu ba , ?
To wai ma ina ya tafi mata da 茩anwar ta ? Kamar ta ji prof yace ya tafi da ita聽 Ina ya kai ta ? Mutumin da ya saba yin manyan 茩arya da yaudara irin haka kome ma zai iya yi , ina suke ? Kai zata iya barin kome ya wuce ya zama ba kome ba amma banda zaman Falmata tare da wannan mayaudarin domin shi 蓷in ai guba ne, dafin sa kuma ya fi na maja-ciki in yai sara .
茒aga sautin kukan ta tayi tunowa da ta yi da miskinancin 茩anwar ta , Wanne irin hali ta kasance a ciki lokacin da labarin mutuwar da aka ce tayi ya riske ta ? Wata茩ila tundaga lokacin bata sake farin-ciki ba , yaya rayuwa ta kasance mata bayan bata nan ? Wanne irin zama take da wannan macucin mayaudarin ?
茩warai ta gaza a wajen聽bada kariya ga Falmata maimakon haka ma ta zama sila na fa蓷awar ta a hatsari , 茩warai hatsari mana aure da mutumin da ba'a kai ga sanin asalin sa na ha茩i茩a ba ,
A hankali Hajja ta mur蓷a makulli ta fito daga 蓷akin da ta shige " jin tashin muryoyin su Rahima da Malama Maryam da suke faman rarrashin Yakaka , da sautin kukan ta ya kara蓷e falon
Oh ni Hauwa'u naga ta kaina ! yanzu ke 'yar nan me ya miki zafi haka a duniyar nan da zaki zo ki fa蓷i a nan shakwa蓳 , kina rusa ihu ya Amaryar da Angon ta ya mutu daren bu蓷an kai ?聽
Ganin babu wanda ya kula ta ya sa ta samu waje ta zauna kan 蓷aya daga cikin kujerun falon , ta cigaba da cewa ,
Rahimatu , ince ko dai an fitar da Fatalwar ? Kar sai mutum yana 茩ailula ya farka ya gan ta daf da kan sa .
Hajja dagaske Yayar Falmata ce ta dawo , Mamar Mama ashe bata mutu ba Hajja ki taya mu Murna ,
A kaikace ta dube su tana daga inda take zaune , ta gya蓷a kai .
Toh , ah lalle kun kaima Barka , 'Yar nan sannu da bayyana , kuma tsawon lokacin nan da kika shafe bakya nan dandi kike ko kuwa Da'awa ?聽 oh