Showing 393001 words to 396000 words out of 441529 words

Chapter 132 - Mafari Hargitsin Rayuwa Book Complete by Ummu Muaz.txt

09 Nov 2025

6642

wala kuwata illah billah huwal aliel azim ya fara maimaita masa cikin nutsuwa kafin ya kai hannu ya zare bindigar da yake riƙe da ita a ɗayan hannun sa .

Wani irin kuka ya fashe da shi yana damƙe hannun Maimartaba da yake cikin nasa yace " Baba me na mata ? Meyasa ta min hakka ? Itta ta ɓata min rayuwa ta tayi sanadin da suna na ya ɓaci ƙima ta ta zubbe , iyayena sun ka yi fushi da ni , Baba me na mata ?

" Ka ƙira ta ta dawo ta faɗi inda ta kai Mata ta , Ita tayi enlevé na Fatima

" Me Fatima ta mata zata badda ta ? Ina ta kai Fatima ?

Ya ƙara cewa haka da wata irin buɗaɗɗiyar muryar da tayi amsa kuwwa a baki ɗayan sashin .


Falmata da take tsakiya da yin kuka cikin tsoron ko Hajiya Mama ta turo mata Aljannu ne su kashe ta kamar yadda ta faɗa mata a yanzu? domin da ta shigo ta ji tana karatun Alkur'ani .

Shine ta mammake Mata baki ta ɗora da tsorata ta da cewa zata mata turen ifiritai su zuƙe jinin ta muddin ta sake karatun kur'ani .

Jin tashin muryar Youssouf yana ƙiran sunan ta ya sa ta zabura ta miƙe zafin da ya ratsa ƙafar ta ya sa ta saurin komawa ta zauna wasu sabbin hawaye na sake zubo mata .

Da rarrafe ta ƙarasa bakin ƙofar ɗakin ta soma bubbugawa da ƙarfi tana ƙiran sunan Youssouf .

Da gudu Youssouf ɗin ya fito saboda shirun da wajen ya ɗauka ya bashi damar jin muryar ta a kusa .

Duka ɗaya ya yiwa ƙofar ta karye da ƙiris ya rage bai faɗa mata akai ba .

Yana shiga ɗakin ya zube guiwowin sa a ƙasa ya ɗago ta "Fatima-Zahra Est-ce que ça va? Alhamdulillah , Alhamdulillah '

Wani irin kuka ta fashe da shi tana ƙan-ƙame shi kamar zata koma jikin sa cikin kuka ta fara cewa " Dan Allah ka fitar da ni anan ka mayar da ni gida wajen Mamana, waccan matar ita ce ta kawo ni nan ta kulle ni yau kwana huɗu tace min zata kashe ni ,idan na yarda nayi magana , kai ma ita ta yi ma asiri kai da Yakaka ita tayi , ita tayi muguwa ce bata da kirki ....

Jijjiga ta yayi da sigar rarrashi yace "va bien mon amour Votre protégé en toute sécurité maintenant babu abunda zatta sake iya yi miki kin ji Fatima ki nutsu ki daina kuka ? Tayi miki ciwo ? Ina yake miki ciwo ?

Ya furta hakan yana ɗaga kallon sa zuwa kan Maimartaba da Hajiya Umma waɗan da suke ganin kome kamar a shirin film wai Hajiya Saratu da suke rayuwa da ita shekara da shekaru ita ce ta yiwa ɗan su duk wannan mugun ƙullin ?.

Ko Hajiya Umma bata taɓa zaton sharri da muguntar Hajiya Saratu , bayan irin mummunan asirin da ta yiwa ɗan ta har ya kai da zata iya enlevé surukar ta ?? Wacce irin ƙiyayya ce wannan Hajiya Mama take mata ?

Da hannu Hajiya Umma ta ƙira Ubbo da Siyama waɗan da suma suke tsaye kasaƙe kamar ruwa ya cinye su tace " ku kama ta zouwa sashi na .

Cikin sauri Youssouf ya girgiza kai kafin yace " zan tai da ita da kaina.

Gyaran murya Maimartaba yayi kafin yace

" bar su su tai da ita kai kouma ka biyo ni .

Daga haka ya juya bayu da sauran al'ummar gidan da har kawo yanzu babu wanda ya iya cewa ƙala wasu suka rufa masa baya .

Youssouf bai saki hannun Falmata ba duk da cewa tun da ta ji muryoyin mutane a wajen ta raba jikin ta daga na shi amma ya ƙi sakin hannun ta .

Har Sai da Hajiya Umma ta kama hannun Falmatan ɗaya ta rike sannan tace masa " ka tai ga ƙiran Mahaifin ka , itta tana ƙarƙashin kulawata .

A hankali ya miƙe yana waiwayen Falmata da ta sunkuyar da kan ta ya fita zuciyar sa cike da jin tausayin falmata da ya lura har rama tayi ta fita a kamannin ta duk wai a sanadin sa Hajiya Saratu ta mata haka ?

Ubbo da kan ta ta haɗawa Falmata ruwan wanka kamar yadda Hajiya Umma ta umarce ta ,

Hajja wacce yau ta samu damar shiga har uwar ɗakin Hajiya Umma tana sharar hawaye tace " mu je na gasa miki ƙafar ta ki uwarɗakina ko kya ɗan ji daɗin ta sannu kin ji Allah ya miki sakayya .

Hajiya Umma da take kallon Falmata cike da tausayi cikin ran ta wani irin yanayi take ji zuwa yanzu ta fara yarda da cewa kamar da sakacin ta har Hajiya Mama tayi nasarar kama Falmata yarinyar da zuwa yanzu ta fahimci da ita da danginta baki ɗaya basu da wata alaƙa da halin da rayuwar ɗan ta ya kasance a ciki kamar yadda take zato a baya , ashe Hajiya Mama ita ce mafarin kome ba Falmata da 'yar uwar ta ba .

Fuskar ta bata ɓoye halin da zuciyar ta ke ciki ba tace " kar a taɓa mata ƙafar za'a ƙira mai gyara yazo ya duba idan ma kuma asibiti za'a kai ta sai a tafi .

Ɗan lankwasa kai Hajja tayi tace "to bari a jira , O' ni hauwa'u yau na ga kura da fatar akuya ganin idona , wasu mutanen launin hankaka ne da su gaban su fari bayan su baƙi ai ba ƙaramin marar imani bane zai yi kinnafin ɗin ɗan adam ba , yo ai tazarar da take tsakanin kinnafaa da boko haram kaɗan ce , Allah ya raba mu da miyagun mutane .

A hankali Hajiya Umma ta amsa da "Amin dai , tana mayar da kallon ta kan Hajja.

A can ɗakin ganawa ta musamman Maimartaba tare da manyan mutanen Fada nasiha suka dunga yiwa Biyamuradi Youssouf suna tausar zuciyar sa , sun gwada masa girman haƙuri tare da matsayin da mutanen da Allah ya yiwa baiwa da haƙuri suke shi tare a gurin sa

da kusanci da haƙuri ke kawo wa tsakanin Mutum da Mahalccin sa Sannan suka jawo masa ayoyi da hadisai .

A ƙarshe suka bashi tabbaci kan cewa jarabawar Rayuwa ce Allah ya masa domin ya gwada ƙarfin imanin sa dan haka ya bar kome ga Ubangiji da idanun sa zai ga sakayya .

A hankali ya dunga jin nutsuwa na safko masa da kafin wani lokaci ya ji baki ɗaya zuciyar sa ta sauƙa wani irin nutsuwar da ya jima bai ji irin ta ba tana safko masa .

Liman da yake malami masanin Alkur'ani ya cigaba da cewa

"sannan shi sihiri gaskiya ne da masu aikata shi kaɗai suka yi imani da shi ,

"babu shakka cikin kur'ani duk wani magani da warakar kowacce cuta yake dan haka ga ayoyin Alkur'ani masu warware sihiri zan faɗa maka idan za ka iya kayi da kan ka Yousssouf idan kuma ka gaza ka bayar a yi maka ina mai tabbatar maka da cewa dukkanin wani sihiri da anka maka sai ya karye da iznin Allah sannan kuma Allah zai baka kariya daga dukkanin wani mgunta da za'a sake nufar ka da shi ta hanyar sihiri ba zai yi tasiri akan ka ba, ka samu takarda da alƙalami ka rubuta a yanzu Youssoufa ayoyin sune kamar haka :


1). Ta'awwizi da Basmala.

2). Fatiha kafa 7.

3). Aya biyar Ta farkon Suratul Bakara sau 7.

4). Ayoyi biyu ta tsakiyan suratul Bakara wato - Wa ilahukum ilahum wahid la'ilaha illa huwa har karshe sau 7.

5). Ayatul kursiyyu Suratul Bakara aya ta 255 sau 7.

6). Ayoyi uku a karshen Suratul Bakara wato daga baikin Amanarrasul Bakara 284-286 sau 7.

7). Shahidallahu a chikin Al Imran aya ta 18 da 19 sau 7.

8). Inna Rabbakumullahi Ladhi khalaqas samawati wal ardh.. acikin Suratul Al'araf aya ta 54 da 56 sau 7.

9). Afa hasibtum Annama khalaqanakum Abasan suratl Mu'minin aya ta 115 da 118 sau 7.

10). Wa Annahu ta'ala Jaddu rabbina mattakhadha..." a cikin Suratul Jinni aya ta 3 zuwa ta 9 shima kafa 7.

11). Aya goma na farkon Suratul Saffat shima sau 7.

12). Aya Uku na karshen Suratul Hashri wato "Lau anzalna hathal Quran.

13). Aya ta 10 na karshen suratul Yasin su ma sau 7.

14). Kulya ayyuhal kafirun sau 7.

15). Qul huwallahu ahad sau 7.

16). Falaqi sau 7.

17). Nasi sau 7.

A rika tofawa a ruwan zamzam ko ruwan sama ko ayi a duka biyun amma dabam dabam a samo ganyen magarya a dandaka guda bakwai-bakwai har gida 7 wato na kwana 7 Safiya da maraice ana sha ana shafe jiki dashi.


Da fatan ka Fahimta Yossoufa ? Sannan a kome kake kada kayi wassa da ibadar ka domin itta ɗin kariya ce mai girma daga dukkanin abun ƙi , ka faɗaɗa ibarda ka yalwata ta , sannan ka yawaita sadakha domin ita ma kariya ce .'

Youssouf da yake gama rubutu ya ɗago kan sa fuskar sa a nutse yace" na fahimta Malam kuma Nagode Allah shi saka da alkhairi .


Daganan ya baro sashin maimartaba bayan ya musu godiya mai tarin yawa , ya bar su suna cigaba da tattunawa .

Sashin sa ya nufa kai tsaye yayi wanka ya ɗaura alwalar sallar la'asar zuciyar sa da take cike da tausayin Falmata da son sanin halin da take ciki ta sa shi dole ya miƙa hanya zuwa sashin Hajiya Umma .

A zaune ya tarar da Hajiya Umma , a falon ta na ciki da Hajja sai kuma Ubbo suna sake jimamin lamarin banda ɓarin nauyayan kalmomi babu abun da Hajja take yi da lokaci-lokaci ubbo kan yi dariyar wasu kalmomin na Hajja .

Zuciyar Hajiya Umma ta sanyaya da ganin Yousouf ya dawo cikin nutsuwar sa har ma ta gagara ɓoye jin dadin ta .

Tayi hamdalah a bayyane .

Bayan sun gaisa ta ɗan dube shi kafin tace " ƙafar Fatima da akwai ciwo domin kouwa da kyar take iya takawa duk da dai na mata tambayoyi cikin amsar da ta bayar tacce bata da wata damuwa sai ta ƙafar da daman akwai tsohon targaɗe a gurin kuma ta sake gurɗewa dan haka nayi magana a ƙira mai gyara a duba ƙafar ko kuwa asibiti za'a ?

Cike da jin daɗin kulawar da ta nuna a karon farko ga Falmata , Youssouf yace "duk wanda kin ka ga yafi dacewa Umma.

"Ka shiga ciki ka gan ta suna ɗaki tare da Siyama.

A bisa ɗaya daga cikin gadajen Hajiya Umma biyu da suke ɗakin ya hango ta a zaune tayi wankan ta fes jikin ta sanye da doguwar riga ta atamfa daga gefe Siyama ce a kusa da ita hannun ta riƙe da wani ɗan kyakkyawan tasa ( Bowl ) da aka zuba ferfesun ƙaza a ciki da chokala biyu a ciki fork da soup spoons,

Ganin shigowar sa bai sa Siyama ta fasa kai soup spoon ɗin da ta cika da ruwan ferfesun bakin Falmata ba sai dai ta amsa sallamar sa da murmushi akan fuskar ta .

Ƙarasowa bakin gadon Youssouf yayi ya zauna a ɗaya gefen yana bin ƙafar Falmata da kallo wanda ta kumbura daga idon sawun .

Kallon sa ya mayar ga Siyama yana jifatan ta da ɗan kyakkyawan murmushi yace

"Siyama kina gatata ƙamnar ki hakka ? Da har kin ka ciyar da ita ba tare da ni kin tuna da cikina ba ?

Ɗan murmushi Siyama tayi kafin tace " ai itta a yanzu marar lafiya ce kai kouwa ka samu waraka insha Allah .

Murmushi yayi yana mayar da ganin sa kan Falmata yace "Fatima yaya ƙarfin jiki ? Ina ke miki ciwo bayan sawun ki ?

Cikin 'yar ƙaramar murya tace "ba ko'ina sai ƙafar tawa.

Tashi yayi daga bakin gadon ya ɗan yi durƙuso kafin ya kama ƙafar falmata a hankali ya ɗago ta ,

Ganin haka yasa Siyama tayi saurin miƙewa bayan ta ajiye kwanon hannun ta akan ɗan teburin gefen gado (bedside cabinet) .

Ta nufi ficewa daga ɗakin " Maman Yumna ina za ki tai ?

Youssouf ya furta haka yana bin ta da kallo

Lumshe idanun ta tayi ba tare da ta jiyo ba tace " zan tai na kawo ma abinci .

Daga haka ta ƙarasa barin ɗakin tana jin yadda suke kokawa tsakanin ta da zuciyar ta da take son ganin baƙin Youssouf da Falmatan.

A hankali ya mayar da ganin sa kan ƙafar Falmatan ya kai ɗan yatsan sa babba ya shafa gurin da ya ɗan kumbura a hankali da yasa Falmata rufe idanun ta a hankali tana jin yadda tsiƙar jikin ta ke tashi tare da wani yanayi da take ji na tausayi mai girma yana huda zuciyar ta , yana bin duk wani saƙo da lungu da ɓurɓushin jin haushin Youssoufa ya maƙale a ran ta kan laifin da take zaton duk yayi su a bisa son rai cikin sanin sa da yin kan sa .

Ji tayi laifukan sa na gogewa suna shafewa , ƙaunar sa , son sa , tare da tarin tausayin sa masu nawin da bata taɓa jin makamancin su ba saboda ji da tayi kamar zuciyar ta ba zata iya ɗauka ba , kamar sararin dake ran ta yayi kaɗan.

da wani irin tasiri mai girma suke maye gurbin duk wani ɗan taƙi da ta bar wa soyayya mallaki a cikin ran ta .

Tasirin so da take ji a lokacin ya fi ƙarfin rarraunar zuciyar ta da take sabon shiga a fagen soyayya .

Ɗago da kan sa yayi yana kallon ta bayan ya gama tofa mata addu'o'i a ƙafar ta .

Ya ɗan dau lokaci yana kallon ƙaramar fuskar ta da take sake zama 'yar firat yana jin tausayi tare da wannan son nata mai yawa yana masa yawo a zuci .

Jin sa shiru ya sa ta buɗe idanun ta a hankali suka haɗa ido .

"Sannu Fatima insha Allah za ki samu sauƙi kin ji kou ?

Gyaɗa kan ta tayi

A hankali ya miƙe ya ƙarasa ya ɗauki bowl ɗin da Siyama ta ajiye ya dawo ya zauna , ya fara bata ferfesun tana ci a hankali , har sai da ta ɗan ci dayawa kafin tace masa "ta ƙoshi .

Bayan ya ajiye kwanon ya dawo ya zauna tare da riƙo hannun ta ya sarƙe 'yan yatsun su waje ɗaya "Fatima kiyi haƙuri da abunda ya same ki Allah zai miki sakayya cikin gaugawa kuma insha Allah zan zamar miki garkuwar da babu wanda shi issa ya taɓa ki a rayuwa na ƙyale shi , kiyi haƙuri Fatima .

Matsa hannun sa da yake cikin nata tayi kafin ta ɗago kan ta tana saka idanun ta cikin nashi tace " Meyasa bata son ka haka ?

"Nima ban sani ba Fatima cikin rayuwata ban taɓa yi mata laifi ba amma ta zuba min ƙiyayya mai zafi da har da taimakon ta anka nemi raba ni da raina bayan ita ta gurgunta rayuwata ta rarraba ƙiyayyar da take min tsakanina da ɗiyan ta da suke 'yan ouwana .

Kan ta ta mayar ta kwantar a ƙafaɗar sa tana kaucewa kallon cikin idanun sa da suka fara sauya launi tace

"Kayi haƙuri ƙiyayyar ta ba za ta sa ko ta hana kome ba sai fa abunda Allah ya rataya alhakin faruwar sa akan ta .

"Idan ita bata son ka Allah da Manzon Allah su na son ka , Maimartaba yana son ka , Umma tana son ka sauran 'yan uwanka suna son ka , Siyama tana son ka , yaran ka ma zasu so ka .

Ɗan jim tayi kafin ta ɗago kan ta tana kallon cikin idanun sa tace " kuma ni ma ina son ka , Ina son ka , ina son ka dayawa .

A bazata ya tsinkayi kalmomin da bata taɓa furta masa ba , zuciyar sa tayi wani ɗan ƙaramin zillo da yasa shi sake ɗago fuskar ta da sauri ya riƙe ta yana kallon ƙwarar idanun ta , muryar sa a tsakani maƙoshin sa yace "me kika faɗi Fatima sake faɗi naji ? Maimaita min ?

"Ina son ka dayawa dayawa ba adadi
Ta sake furta hakan tana kallon fuskar sa cikin ranta " godiya take yiwa Ubangiji da idan ba shi ba da ƙarfin ikon sa wa ya isa mallaka mata wannan mutumin ma'abocin kyau da cikar zati tare da kyaun nasaba ?

Muryar sa tana sake nitsewa saboda ƙasa da yayi da ita yace "dagaske Fatima ?

Hannuwan ta tasa akan nasa kafin tace "da duk gaskiyar zuciyata ina son ka dayawa ,

Wani irin sanyi yake ji tun daga ƙasan ran sa yana taso masa yana nitsar da idanun sa cikin nata yace " son da nake miki yafi wanda kike min yawa Fatima , son da nake miki ba shi da iyaka , ni ban san iyakar sa ba, kin yarda na gwada miki ɗigo dagga cikin sa ?

Kan ta ta gyaɗa masa tana murmushin da yake bayyana haƙoranta ,

Tazarar dake tsakanin su ya haɗe yana manne fuskar sa da ta ta , tare da shauƙin son da suke yiwa junan su suka himmantu wajen gwadawa junan su tatatciyar soyayyar da suke yiwa juna .

Ƙwanƙwasa ƙofar da Aka yi yasa su sa rabuwa da jikin juna ,

Ba'a jinkirta ba aka murɗo ƙofar a hankali ta shigo bakin ta ɗauke da Sallama .

Siyama ce ta shaida musu zuwan mai gyaran ƙafa .

Yousaouf ya masa iznin shigowa bayan ya gyara mata mayafi.

Ba ƙaramar azaba Falmata ta sha ba kafin ƙashin da ya fita ya koma saboda tsamin da ƙafar tayi kwana huɗu da targaɗe .

Siyama da Youssouf su suka dunga rige-rigen share mata hawaye da gumin da ta haɗa sharkaf duk kuwa da sanyin ɗakin .

Bayan ta dawo cikin nutsuwar ta lokacin Youssouf ya bar ɗakin daga ita sai Hajja da ƙaramar murya ta cewa Hajja " Hajja ki bani wayar ki zan ƙira Mamana da Yakaka .

Ɗan jim Hajja tayi kafin da sigar rarrashi tace "Uwarɗakina Amma fa kar ki shaida musu abunda ya faru da ke domin ba'a sanar da su ba tun da Allah yasa kin fita lafiya kar ki faɗa musu kuma zuciyar su ta kasa nutsuwa da zaman ki anan .

"Ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login