Showing 21001 words to 24000 words out of 30967 words

Chapter 8 - RINTSIN SO Book 2 Hausa Novels by Indo Ce.txt

Indo Ce   

18 Nov 2025

437

a gurina ke kaɗai zan iya gayawa, amma ki tashi mu zagaya inda babu mutane"

Tashi Nuriya tayi suka zagaya gurin ba kowa duk suna ɗayan sashin suka nemi guri suka zauna, Aisha tace, "lokacin ina yarinya Mama ta taɓa yin wata rashin lafiya me tsananin da sai da aka kwantar da ita a asibiti tayi kwanaki, to a wannan datsin ne wata rana, su Sayid suna makaranta Anti Zulaihart ita aka bar mana a gida domin kulawa damu, a ranar tace min zataje asibiti gurin Mama ni kuma na zauna a gida sai na kulle kar nabar kowa ya shigo, nayi nacin duniya da magiya akan tabarni muje tare amma taƙi, haka tasa ƙafa tabar gidan nan tabarni duk da ƙananun shekaru na, ina zauna zaune sai naji ana ta bugun ƙofa............."







(Littafai na, SIRRIN ƘETA A JINI ƊAYA TAJMAHAAL Paid BOOK IB ƊAN WANKA Tareda RINTSIN SO"








*INDO CE*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 25*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*





"....da nace bazan buɗe ba sai naji ba'a dena bugun ba dan haka nayi tambayar waye, nan yake ce min Dawood ne, nace Mama bata nan ya tafi idan ta dawo sai shima ya dawo, amma sai yaƙi sai ma cewa da yayi aiko shi akai ze ɗauki wani abu, ni kuma jin hakan yasa na buɗe masa da tunanin gaskyar abunda ya faɗa, sai bayan nan nagane ashe labarin ba haka yake ba, to a wannan lokacin ne ya samu dama dan kowa baya nan, da yake inada gardama da na bujire masa ma haka yasamin ƙarfi, bayan nan kuma ya bani kyakkyawan kashedi akan kar na faɗawa kowa yace idan na faɗawa wani to zeyi min abunda yafi wannan, to ni kuma ina tsoron hakan, mutumin da ya iya danne ƙaramar yarinya yayi mata fyaɗe menene baze iya aikawata ba? ko akaina ko akan wani nawa nasan ze iya cutar damu, ga yara nan su Aunty sun haifa banaso ta dalilina ya cutar da wani dan haka yanzu ma bazan faɗa ba zan cigaba da riƙe maganar har zuwa lokacin da Allah ze tona masa asiri"

"Haka nasha wahala a lokacin nan kafin kowa yazo na kwanta ga zazzabi ya tara ni, shi dama Dawood babu wata alama da yabari wadda zata nuna wani abu yafaru sai dai azabar da nakesha kawai koda Anti Zulaihat ta dawo ta tarar ina zazzaɓi sai tace nasha magani bayan nasha taga abun ba sauƙi sai ta tsiri cewa aje asibiti ni kuma ina tsoron su gane wani abun dan haka na daure na dena nuna damuwata kuma na kafe akan bazanje ba, haka sukai ta yimin tambayoyi amma naƙi basu amsa me kyau, Anty Maimuna a lokacin taso gane kamar wani abun yafaru saboda yadda taga ina tafiya da kyar kawai sai nace musu ciwon ƙafa nake kuma na tubure ahakan har sai da nayi abunda ya ɓata musu rai sukai fushi suka ƙyaleni, dama idan Abban mu ya dawo gidan su suke tafiya yana dawowa kuwa sukai gaba shi kuma dama Abba yana ɗakinsa muna namu, ...
Haka nayi ta haƙuri na danne duk wani raɗaɗin da nakeji na kwana cikin wannan baƙin ƙadamin, washe gari ma na ƙoƙarta ina ɗan zagayawa kar su ganni a kwance su kinkime ni sukaiwa likita kowa yayi maganar tafiyata sai nace ciwon ƙafa nake idan ka matsa kuwa duk zafin da nakeji akanka zan juyeshi dan kuwa DA INA YARINYA inada faɗa sosai"
.....

Nuriya ta numfasa kafin tace, "lallai wannan ya cika mara mutunci kuma maci amana in Allah ya yarda sai ya gamu da abunda hankalinsa baze ɗauka ba sai ya gamu da ƙuncin duniya da na lahira baze taba ganin ƙarshe me kyau ba mugu, shine kuma dan rashin kunya har Saif ne za'a kaiki gidan sa ya koro ki saboda wannan dalilin? lallai bashi da ma hankali"

tayi Murmushin takaici tace, "Nuriya Saif be san hakan ce tafaru ba amma ko ya sani ma hakan zeyi min dan kuwa suna da mummunar aƙida ta son zuciya, a koda yaushe neman tsari nake dasu da irin su"

Haka sukaita jajantawa juna sannan suka koma ɗaki.

Washe gari kamar yadda Abba yace ta sanar masa hakan yaƙara tambayarta amma ko alu bata ce musu ba haka akaita gumurzu da ita amma taƙi faɗe har dukanta sukai dik ta shanye, hakan ya tabbatar musu da gaskiyar Saif tin daga lokacin suka hau dokin zuciya suka dena saurarar ta ko abunda ya shafeta kowa fushi yake da ita daga kan Abba Mama Anti Zulaihat Anti Maimuna kowa fushi yake da ita gaba ɗaya rayuwar tayi mata ƙunci bata da aboki sai kuka duk mutanen gidan ƴan biki sun tafi Nuriya ma ta tafi sai Sayid ne kawai yake ɗan kulata shima Mama hanashi takeyi.

yau tana zaune Sayid yazo ya miƙo mata wata takarda karɓa tayi ta warware kafin ta tashi da sauri cikin rawar jiki ta yafa mayafinta sannan ta nufi ɗaya sashin yana tsaye ya riƙe ƙugu idonsa yana kan guri ɗaya da alamun wani tunanin yake.

Cikin sauri taƙarasa inda yake cikin fara'a tareda farin cikin ganinsa, ido ya zuba mata da yake itama shi take kallo yanayin kallon da yake mata sai taji ya sare mata guiwa, cikin daurewa tace, "Khaalif Moh.. meke faruwa ne?"

Yace, "ba komai"

Shiru ce ta biyo baya kowa da nasa tunanin tasan dai da kyar ace babu komai ɗinnan dan ko a yanzu taga canji, katse mata tunanin yayi da cewa, "Ayeesha kinsan abun hakane meyesa baki sanar dani tin wuri ba?"

Cikin mamaki tace, "me kenan??"

yace, "au baki gane ba??"

Tace, "Khaalif wata magana kayi min wadda ban fahimta ba"

Hannunta ya kama ya janyota jikinsa yana cewa, "to bari na ganar dake"

Ido taƙara waro masa cikin alamar tsoro dan kuwa ta lura yau babu alamun soyayayya sai dai wani abun.

Sake rungumeta yayi tsam sannan ya jefa idanunsa cikin nata, cikin wata kalar muryar da bata saba ji daga gareshi ba yace, "kinsan haka abun yake da arha amma kika hanani, ko ni ba namiji bane?? faɗa min mana?? da nufinki na aureki a haka?? to maganar gaskiya bazan iyaba na auri budurwa amma babu lasisin budurci kinga ya tashi abanza"

Tsananin mamakin irin kalaman da suke fitowa daga bakinsa yasa ta kasa magana sai kallonsa da takeyi, murmushi ya sakar mata kafin yace, "wannan kallon na meye ne?? ya isa haka mana abunda bakiyi tunani ba kafinki faɗa sona shine yake faruwa baki taɓa tambayar kanki meyesa duk matan duniya ke kaɗai na maƙalewa ba duk da irin rashin mutuncin da kika shuka min a baya?? nifa dama ba komai nake yiwa ba, ba wai zuciyarki nake buƙata ba iya jikinki ma kaɗai ya isheni more rayuwa amma yanzu labarin ya sauya ni nafasa kije ki auri wanda ze iya aurenki a haka, amma fa raina ya ɓaci sosai da sosai nayi takaicin rasa abunda na daɗe ina muradi, Ayeesha ni ba namiji bane da bazaki yarda dani ba??"

A'uzu billahi itace kalmar da take mai-mai-tawa akan leɓen ta jikinta har kakkarwa yake saboda razani da kiɗima,

Yace, "Ayeesha yanzu nasan ai kin gane me nake nufi ko??"

Jin yana neman wuce iyakarsa ta haryar taɓa inda be dace ba yasa ta shammace shi ta zame tayi gefe tana so tayi magana amma takasa saboda zuciyarta da take bugawa cikin sauri, wasu zafafan hawaye ne suka wanke mata fuska da kyar tace, "Khaalif wallahi ni ba mutuniyar banza bace ni ba ƴar iska bace fin ƙarfina akai duk yadda kake zato na ba haka nake ba wallahi ni bantaɓa iskanci da wani ba, kai ma Allah yayi min tsari da kai shaiɗani ashe dama duk soyayyar taka ta ƙarya da yaudara ce Khaalif?? meye ribarka dan ka cutar dani?? amma Allah yana kallon komai kuma ze saka min wallahi Alhakina baze barku ba Khaalif kun cutar dani kun zalumce ni"

Gyara tsayuwar sa yayi kafin yace, "ban cutar dake ba fa ke kika cuci kanki kinga da kin bari na aureki komai kike so zaki samu amma kin yiwa kanki, gaskiya naji takaicin hakan sosai yanzu ni ba abunda zance miki sai dai nace Allah yabaki wanda ze karɓe ki dan nasan ko ABU ɗin baze iya aurenki a yanzu ba bare kuma Jose iyayen faɗin rai da girman kai, nima yanzu daidai dani zan nema ina nufin budurwa dan kinsan saurayi sai da budurwa"

Kasa magana tayi kawai ta juya ta koma cikin gida kai tsaye ɗakinta ta wuce ta zube a ƙasa ta haɗe kai da guiwa kuka take me tsananin ƙuna, ji take kamar a wuta take saboda tsabar raɗaɗin da takejin zuciyarta tanayi.

Sayid ne ya dafa ta cikin sanyi yace, "Anti Aisha me Ya Khaalif yayi miki??, ki faɗa min"

ɗagowa tayi ta kalleshi sannan tace, "Sayid ko meye Khaalif yayi min nice na jawowa kaina Khaalif Macuci ne na haƙura da soyayyar sa tin farko amma yaƙara hura min ita yanzu kuma ya gujeni ya ƙara dasa min son sa amma yabarni Sayid ya suke so nayi da rayuwa ta?? shin an halicce ni ne saboda su dinga wulaƙanta ni??"

Taƙarasa maganar tana kuka.
Cikin tausayawa yace, " kar kiyi maganar da zakiyi saɓo Allah yasan da zaman kowa a cikin bayinsa kuma kema kina cikinsu dan haka kiyi haƙuri Allah ze kawo miki sauƙi, ki manta dashi tinda har ya iya mantawa da soyayyar ki kema ki manta dashi ki cire shi daga rayuwar ki"

Tace, "wallahi Sayid ina sonsa so me tsanani kafin na manta dashi zan sha baƙar wahala"

Yace, "haka nan zaki jure amma ina ganin da ki zauna kina ɓata lokaci a banza da kin faɗi gaskiyar abunda yafaru da yafi, kinga yanzu kowa fushi yake dake kuma ɗauka suke da gaske ne abunda Saifu ya faɗa meye amfanin ɓoye gaskiya bayan kinsan dole wata rana zata bayyana??"

Murmushin yaro man kaza tayi kafi tace, "Sayid bazan iya ba duk wanda yakeji da taurin kai ni na fishi ko me za'ayi min wallahi bazan faɗi gaskiya ba sai dai a kashe ni ko kuma ƙarewar dena kula ni a rufe ni a jefa mukullin a ruwa"

Jinjina kai kawai yayi domin kuwa ya lura gwagwarmayar yau da kullum tasa zuciyarta tafara ƙeƙashewa be ƙara wata magana ba ya tashi ya bata guri dan yaga kanta yafara wuta zata fara masifa.











*INDO CE..*
[7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 26*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*









yau ma kamar kullum haka ta kwana da zazzaɓi kamar yadda ta saba dama ba ƙaunar magani take ba bare yanzu da babu me tilasta mata akan ta sha, tana zaune tayi tagumi wayarta tafara ƙara, ɗauka tayi ba tareda ta duba ba takara a kunne.

Cikin muryarsa irin ta maye yace, "Ashsha? kina lafiya??"

Numfashi taja tareda zaro ido cikin mamakin abunda batayi zato ba, cigaba yayi da cewa, "Jose ne, Aisha baki cancanci irin wannan rayuwar ba kwata kwata dan samun rangwame daga su Mama idan sun tambayeki waye wanda kike zuwa gurinsa kice nine duk ki ɗora laifin a kaina ni kuma zan ɗauka ki gaya musu ni ne na aikata komai ke baki da laifi, kuma abokina har yanzu yana sonki yace yana son kiranki dan tunatar dake amma ya kasa, dan Allah ki kirashi kar damuwa tayi masa yawa shi tsakani ga Allah yake sonki kuma ze aureki indai har kin amince, dan haka ni ki ɗora min laifin ki auri abokina kawai hakan shine farin cikina ki temaka min Aisha"

Shiru tayi tana sharar ƙwalla saboda tsananin tausayinsa da ya lulluɓe ta, Jose ɗin da kowa yayi masa shedar mutunci wai yau shine ya zama haka kuma adalilin ta, idan ta tuna takanji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan baƙin ciki. da ƙyar ta iya cewa, "Jose bazan iya ba laifin da baka aikata ba na ɗora maka shi aa, Saif mugu ne bansan me zeyi maka ba bayan kuma ba kaine da laifin ba, ka dena wannan tunanin bazan iya ɓata maka rayuwa ba"


Yace, "Aisha ni nace miki haka fa dan Allah ki amince bana so ki cigaba da irin wannan rayuwar kuma ki sani ba wai fasa bibiyar ki zeyi ba mafi sauƙi shine kiyi aure kibar gidan nan"

Numfashi taja ta sauke kafin tace, "shikenan na amince zanyi hakan"

Da sauri yace, "nagode Aisha"

Murmushin dole kawai ta iya yi,
tagumi taƙara zabgawa ta cigaba da tunani a yanzu babu abunda yake damunta kamar Khaalif idan ta tuno da abunda yafaru sai taji zucyarta kamar ta tsage, da ace ta yiwa sauran masoyanta rashin mutunci saboda shi da taga baƙin yanayi Allah ya temake ta batayi hakan ba sai ta bi su a sannu amma da ta ɗauki wasu shawarwarin da tini ya rage daga ita sai ita babu wani masoyinta da ze saurare ta"

Waya ta ɗauka ta kira Nuriya bayan sun gaisa tace, "meke faruwa??"

Tace, "Nuriya Khaalif"

Tace, "me yayi kuma?"

Zayyana mata abunda yafaru tayi Nuriya tafara salati da sallallami dan kuwa abun yayi mata girma bata taɓa kawo wannan tunanin ba. Aisha ce ta katse ta da cewa, "Nuriya dole abun ya baki mamaki, fiye da kowa na yarda da Khaalif na fifitashi akan kowa na yarda dashi fiye da ko wane namiji a duniya ashe shi ba abun yarda bane, idan na tuna dan dole nakeyin kuka"

Nuriya tace, "Allah ya iya mana Aisha da yardar Allah ƙarshen wahalarki yazo in Allah ya yarda hakan shine silar daidaituwar rayuwarki, ki kwantar da hankalin ki ki dena damuwa kina zaune Allah ze kawo miki ɗauki"

Murmushi tayi cikin jin daɗin maganar tata, cigaba tayi da bata labarin yadda sukayi da Jose har zuwa wani lokaci sannan sukai sallama.

Yawan damuwa da larure larure sunsa Jikin Aisha ya rikice yau tin safe bata fito ba tayi bulum cikin bargo sai rawar sanyi take saboda zazzaɓi, Sayid ne ya shigo cikin tausayawa yace, "Anti Aisha kitashi na raka ki asibiti"

Girgiza kai tayi tace, "aa kar ace naje wani gurin" yace, "Anti baza a ce ba fa gaskiya bazaki zauna da ciwo ba"

Badan ta so ba ta tashi ta shirya sannan tace yaje ya sanarwa Mama, koda ya faɗa mata cewa tayi bazasu iya zuwa su kaɗai ba dan haka a nemo Khaalif ya kaisu ta haɗa shi da mukullin mota da kuɗi, haka ya koma ɗakin cikin ƙunar rai ya sanarwa Aisha abinda tace bata da zaɓin da ya wuce hakan shiyasa tace yaje ya sanar masa.

Bayan wani ɗan lokaci ya dawo yace, "yace kizo"

Miƙewa tayi cikin rashin ƙwarin jiki tabi bayan sa, tinda suka fara tafiya bata cewa kowa ƙala ba har suka isa bayan ta ga likita ya sanar mata ta kamu da ciwon zuciya hakan ba ƙaramin kashe mata jiki yaƙara yi ba.

Suna cikin tafiya Khaalif yace, "ina son biyawa wani guri ko zan iya zuwa??"

Shiru tayi masa dan haka ya canja tafiyar, da kyar tace, "Khaalif ka bar Sayid a asibiti fa"

Yace, "na sani ai amma kinsan dai yasan hanya ko??"

Tace, "to dan yasan hanya ba tare muka tawo dashi ba, ina tsoron Mama tayi min faɗa fa"

Murmushi kawai yayi ba tareda yace komai ba.
A bakin wani layi ya ajiye motar sannan ya fita yayi wani gurin tin tana sa ran ganinsa a lokacin har ta dena sai da tayi kuka me isarta kafin bacci yayi gaba da ita, a cikin baccin kamar a mafarki taji ana taɓata ana sumbatar ta, ta farka a tsorace gami da fashewa da kuka jikinta na rawa take kallonsa, murmushi yayi kafin yace, "Ayeeshan Khaalif kin gaji da jirana ko??"

Ita dai baya tayi ta tsakure acan gefe sai kuka take cikin matuƙar firgici, fita yayi ya zagaya mazaunin sa sannan ya cigaba da tafiya, har suka dawo kuka take, tana shiga gidan tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login