Showing 24001 words to 27000 words out of 30967 words

Chapter 9 - RINTSIN SO Book 2 Hausa Novels by Indo Ce.txt

Indo Ce   

18 Nov 2025

435

gamo da Abba a tsakar gida yayi tsaye da bulala a hannunsa sai faɗa yake, Mama Sayid Shaheed kuwa kuka kawai sukeyi.

kanta Abba yayi yana cewa, "ina kikaje??? nace ina kikaje??"

Cikin kuka tace, "Abba wallahi asibiti mukaje"

Yace, "ni zaki yiwa munafurci?? asibitin ne tin rana sai yanzu bayan magrib?"

Kafin tayi magana ya hau dukanta da iya ƙarfinsa yana tambayarta suwaye da waye wanda take mu'amala dasu, sai da ya gaji da dukanta sannan ya saita mata hanya yace ta fice masa daga gida.

Haƙuri ta shiga bashi tareda roƙon afuwarsa amma yace firr besan da hakan ba, taso gaya masa abunda Jose ya gaya mata sai dai be bata dama ba dole taja jiki ta fice, tana tafiya tana kuka ba tareda sanin ina zata dosa ba.

ji tayi an riƙe hannunta nan fa taƙara firgicewa, ganin Dawood ne yasa yaji zuciyarta ta fara yaji, ƙoƙarin fizge hannunta tafarayi amma takasa.

Yace, "A'isha ki tsaya ki saurare ni mana" a masife tace, "me zaka gaya min?? yanzu ma wani sharrin kazo min dashi?? meyesa kake son ganin bayana ne Dawood me nayi maka??"

Be saurare ta ba sai jan hannunta da yayi ya tura a cikin motar sa yajata ganin yayi ƙofar gidan su da ita yasa ta sake fashewa da kuka tana roƙonsa akan ya barta ta tafi gidan ƙanin Abbanta dan kuwa tana matuƙar tsoron Abba idan ransa ya ɓaci bayaji baya gani.

tsawa ya daka mata hakan yasa tayi saurin kama bakinta sai dai kukan ƙasa ƙasa, huci ya furzar kafin yace, "kiyi haƙuri nayi miki tsawa amma nima ba haka naso ba ki tashi mu shiga ciki"

Girgiza kai tayi alamar "aa" bayan son jiranta ta ɓata masa lokaci dan haka ya saɓa ta a kafaɗa, da sallama ya shiga gidan har lokacin duk suna tsakar gida ya dire ta sannan ya riƙe hannunta tamau.


Abba yace, "mene kuma hakan"

Dawood yace, "Abba Aisha bata da laifi gaba ɗaya kuskuren nawa ne"

Abba yace, "wani salon yaudarar ne kuma akazo min dashi?? kai meye laifinka a ciki??"


Yace, "Abba asali nine na rabata da mutuncin ta kuma Wallahi Abba bayan ni bata san kowane namiji bata yawon banza ba ɗabi'arta bace, Abba nine na aikata kuma na haneta da sanarwa kowa, dan haka bata gaya muku ba, ranar da Saifu ya kore ta daga gidansa a gidana ta kwana ni na ɗauketa, tin tana yarinya nayi mata fyaɗe, kuma a cikin gidan nan lokacin Mama bata da lafiya tana asibiti,...

Tiryan tiryan ya zayyana musu yadda akayi kamar yadda ta sanarwa Nuriya yana maganar yana kuka.

Abba ma tini yafara kukan baƙin ciki gami da kunya, Mama kuwa murmushi tayi tace, "to Alhaji dangina sune tsinannu su suka lalata maka ƴa shima wannan inaga dangi na ne, ai Allah ba azzalumin sarki bane gashi tin kafin tafiya tayi nisa ya fitar dani ya wanke dangina daga mugun zargi dama dangin ka sunce Khaalif ne ya hure mata kunne ya lalata, kuma Allah zeyi min sakayya da ni da ita bamu da ƙarfi kuma bamu da ikon da zamu hukuntashi Alhaji amma tabbas Allah ya san yanda zeyi dashi, bamu yafe ba kuma bazamu yafe ba"

Dawood ya share ƙwalla sannan ya kalli Aisha cikin sanyi yace, "tin bayan rabuwarmu a wannan ranar na nemi nutsuwa ta na rasa duk tunani na ya juya ya koma kanki, mafarkin ki da tunanin ki suka hanani bacci, A'isha ni namiji ne kuma nima na kamu da son ki so me tsananin da zan iya fansar da rayuwata akanki"











*INDO CE..*
[7/5, 10:54 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 27*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*






Cikin kuka tace, "Abbana shine kawai zeyi min zaɓi na karɓa bazan ƙara yarda naso wani ba har sai idan Abba na ne ya zaɓar min shi, indai har yace ya amince nima a shirye nake"

Daga haka ta miƙe ta shige ɗaki, kan kujera ta zauna ta share hawayen sannan tafara dariya sai da tayi me isarta kafin tace, "Dawood kenan, yanzu ka shiga hannu"

Mama ce ta katse ta da cewa, "Aisha meyesa zaki ɓoye min wannan abu? ba irinsa ake kira da sirri ba fa meyesa zaki ji tsoron wani bayan ubangijin ki?? da kin sanar tin a lokacin da ansan matakin da ya dace kinga yanzu ya riga ya cuceki yayi miki mugun tabo ya zubar miki da mutunci a idon duniya"

Ƙasa tayi da kai kafin tace, "shima ze ga dai-dai nashi Mama"

Mama tace, "da izinin Allah kuwa sai yayi nadama mafi muni a rayuwarsa, amma duk da haka ya cucemu wani idan ya yarda wani baze yarda ba yanzu duniya ta ɗauka ke ba ƴar arziki bace amma Allah zeyi maganin komai, Addu'a ta ta karɓu Allah ya bayyana mi damuwarki Aisha kuma ya tona asirin wanda ya zalumce ki"

Murmushi tayi tareda cewa, "Mama dan Allah ki dena zubda hawayen ki komai ya wuce"

Tace, "be wuce ba dan indai ina raye bazan bari ki auri wannan macucin ba"

shiru tayi tana wasa da ƴan yatsunta.


washe gari tin safe Abba ya neme ta a gefe ta zauna tana sauraren abunda ze ce, bayan yayi gyaran murya yace, "to Aisha ina neman Afuwarki baya ga haka kuma kince zaɓi na kike so to gaskiya bazan ƙara wannan kuskuren ba idan kinada wanda kike so ki sanar dani idan ma bakida shi ki jira har lokacin da Allah ze kawo"

Shiru tayi takasa cewa komai sai zuciyarta da take bugawa yanzu wasa biyu ya rage mata ABU da Jose cikinsu wa zata zaɓa??? idan tace ABU shi ya warke yanzu bashida matsalar komai, mugun halin da Jose ya faɗa shi yake sawa taji duk duniya bata da burin da ya wuce ta aureshi kuma ta zauna dashi a duk halin da yake ciki, shi kuma yafi son ta auri ABU yanzu me zata cewa Abban????. sanin batada amsoshin wannan tambayoyin yasa tayi shiru kawai da yaƙara tambayarta ma sai ta fashe da kuka sai da ya lallaɓa ta ya rarrashe ta da ƙyar sannan yabar zancen, ya koma kan Dawood tambayarta yayi wane mataki take son a ɗauka akansa, kawai tace a ƙyaleshi karma a ɗaga maganar duniya taji kawai abunda take so Abba yace masa ze aura masa ita, koda ya tambaye ta dalilin hakan bata bashi ƙwaƙƙwarar hujja ba, da yake neman hanyar gyara kuskure yake sai ya amince kawai.

Sosai take farin ciki, idan ta tuna Dawood kuwa koda yaushe cikin kiranta da turo saƙonni yake ita Kuwa tai ta karɓa tana fakawa nuna masa take idan ba shi ba sai rijiya, gefe ɗaya kuwa kullum cikin ƙara so da shaƙuwa suke itada ABU abunda yake damunta kawai Jose da batasan halinda yake ciki ba dan yanzu ya zama ɗan kaɗai idan ya furtse sai yafi sati ba'a san inda yake ba.

Yau Mahaifin Jose yayi takakkiya zuwa wajen mahaifin ABU dan ya lura shi ba ta ɗan nasa yake ba har yanzu besan ciwon sa ba dan haka ya yanke shawarar zuwa ya nemeshi akan yaje ayi maganar aure, anyi sa'a beyi gardama ba ya amince suka sa ranar zuwa.


Tana cikin goge tsakar gida Saifu yayi sallama, amsawa tayi tareda binsa da ido cikin mamaki, ƙerere ya tsaya kamar gawar sababi yana kallonta, wani shu'umin murmushi ta sakar masa kafin tace, "barka da warhaka yaya Saifu"

Sai da ya haɗiye wani ƙululu da yayi masa tokarere a maƙoshi kafin ya amsa da kyar yace, "barka dai Abba ya tashi??"

Tayi farrr da ido kafin tace, "inajin ya tashi gaskiya"

a tsaye ya sume saboda wata duniyar da ya faɗa ita ba ta tunami ba ita ba duniyar mutane ba, sai da tace, "ka wuce mana" sannan ya sauke gwauron nishi ya wuce, da sallama ya shiga ɗakin, bayan wani lokaci Abba yayi kiranta, ai kuwa da sauri taje ta durƙusa gami da cewa, "Abba gani"


Abba yace, "to kinji dai abunda Saifu yace yana so ki koma ɗakin ki yana bada haƙuri tareda neman yafiya sannan yace beyi saki uku ba gida kawai yace ki tafi ya sakeki, shin haka ne?? kuma zaki iya amincewa ki koma???"

Girgiza kai tayi tace, "Abba bazan iya ba kuma bama haka bane yanzu zan ɗakko takardar da ya bani da hannun sa"

Abba yace, "to kai Saifu kaji abunda tace kuma koda ta amince ni bazan amince ba baka cancanci zama mijinta ba, da farko ma kawai ka ɗauka ƙaddara ce ta kawo hakan amma yanzu anyi walƙiya bazan ƙara bada ƴata gareku ba ko ba wannan ba, kai kaci mutuncin ta kaci zarafinta yayanka ya keta mata haddi kodan kunji nayi shiru shine zaka ƙara dawowa??? to tabbas idan na ƙara ganin ka a gida na Saifu ranka ze ɓaci fiye da tunanin ka, na rabaka da hanyar ma da Aisha tabi ba kai ba ita ko hanya karka yarda ka ƙara haɗawa da ita"


Cikin mamaki yace, "wane yayan nawa kuma?? me yai mata??"

Aisha ta fashe da kuka tana cewa, "kaje ka tambayi yayanka Dawood shi yasan amsar da ze baka"

Da sauri Abba ya shiga rarrashinta gami da kwantar mata da hankali yana haƙur-ƙurtar da ita.

Saifu kuwa cikin ɓacin rai yabar gidan kamar me shirin dukan iska.

itama ɗakinta ta koma ranta duk a ɓace gefe guda kuwa tayi farin ciki da irin hukuncin da Abba yayanke.

Ranar asabar da wuri Abi da mahaifin ABU suka zo suka sami Abba da maganar auren ABU da Aisha, sai da ya tambayi ra'ayin ta tace ta amince sannan shima ya yarda bayan sun tsaida magana suka koma.

Kiran Khaalif ne ya shigo ta amsa, bakinsa har harɗewa yake wajen cewa, "Ayeesha Yaya na zaki aura?"

Da ɗan mamaki tace, "Khaalif? mene ruwanka to a ciki?? shi zan aura shine wanda na yarda dashi"

Yace, "Aisha idan kin Auri ABU ni kuma fa??"

tace, "wannan kuma ruwanka ne idan kaso ma zaka iya dauwama ba aure ni kam yanzu babu wasu ƴan barikin kalamai da zaka faɗa min su ratsa zuciya ta, kasan wani abu ma kuwa Khaalif?? na tsaneka na tsani duk namijin da besan mutuncin ƴa mace besan darajar so da ƙauna ba, yanzu hankalin Abba rabi yana gareni kayi ƙoƙarin fita shirgi na tin kafin nasashi ya shata maka layi, ai yanzu ko maza sun ƙare Khaalif ba abinda zanyi da irinka ma balle kai na wuce tsararka wallahi"

Daga haka ta katse kiran gami da kashe wayar dan tasan shi da naci idan yafara kira kamar baze dena ba.

wayar yabi da kallo cikin ƙunar rai yana mamakin ma ta yadda akai ya fallasa kansa ya kwafsa gashi yanzu a memakon yaji ya dena ta ta-ta to sai ma abunda yayi gaba.

sati shida akasa lokacin bikin ABU da Aisha, har zuwa lokacin Saifu da Dawood duk basu san halinda ake ciki ba.
Yanzu dukansu gwarama suke a tsakanin su biyun kowa ya zuba musu ido baban su ma Allah ya isa yayi musu dukansu yace be yafe ba.

yau auren ya rage saura Sati ɗaya su kaɗai suke shirye shiryen su ba tareda kowa ba dan kuwa kowa kallon bazawara yake mata shiyasa ba'a wani damu kai ba, Abba kuwa duk motsin da zatayi hankalinsa yana kai kafkaff suke da ita, har tayi ƙiba tayi mul saboda kulawar da take samu.

Wayar Mama ce tayi ƙara ta ɗauka tareda yin sallama a ɗaya gefen Umma tana kuka tace, "Hajiya Rabi Jose ya zama mahaukacin gaske yace ze zo nan gidan ki dan Allah ko me ze faɗa karki saurare shi ya haukace"

Da mamaki Mama tace, "garin ya Yaya??"

Tace, "ba wannan ne abun damuwar ba banaso yazo yayi muku hauka a gida dan Allah Karku saurare shi"

Tace, "to shikenan Allah ya bashi lafiya"

Aisha tace, "waye mara lafiya Mama??"

Mama tace, "wai Jose ya haukace"

Zumbur tayi ta miƙe da sauri ta shige ɗaki sai kuka, Mama ta saki baki tana kallonta kafin ta jinjina kai, Anti Maimuna tace, "nifa ina tunanin akwai wata alaƙa a tsakaninsu ta soyayya"

Mama tace, "ai naga alamun hakan yanzu kuma lokaci ya ƙure mata"

Sayid yace, "ai dama ya haƙura sanadin son nata ne ma ai ya zama haka"

Cikin kaɗuwa Mama tace, "da gaske??"

Yace, "wallahi kuwa"

Sosai jikinsu yayi sanyi ƙalau.
Tin Mama tana sa ran ganinsa har ta dena da alamu ƴar matsutsiyar ta kaɗa shi wani gurin.

Dawood dawowarsa kenan gida yayi tuntuɓe da ƴarsa ƴar kimanin shekaru uku kwance shaƙe shaƙe babu alamun numfashi a tattareda ita, da sauri ya ɗauketa yayi cikin gidan da ita yana ƙwalawa mamanta kira ta fito suka shiga dubata jikinta yayi faca faca da jini, wata muguwar razana yayi saboda karo da yayi da mummunan gani yayi baya taga taga yana shirin faɗuwa.

Da sauri matar tashi ta shiga tambayarsa lafiya, da kyar ya iya cewa, "fyaɗe sukai mata"

Yaraff ta zube a wajen tareda fashewa da kuka ta shiga jera masa Allah ya isa bata yafe ba a cewarta shine ya ja mata komai.

Be tsaya saurarenta ba ya nufi asibiti da ita,, bayan likitoci sun shawo kanta da kyar suka sanar masa ta kamu da ciwon ɓarin jiki rabin jikinta duk ya dena aiki, tashin hankali da masifa babu wanda be shiga ya zama kamar zautacce yace wancan yace wancan ya kasa zaune yakasa tsaye.









*INDO CE..*
[7/5, 10:54 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 28*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*








Dawood yana zaune ya haɗa kai da guiwa matarsa tazo ta tsaya akansa cikin masifa tace, "ban takardar sallama ta, nagaji da zama da kai da bala'in da yake tareda kai nan gaba ba iya ƴarka ba ni kaina shafa ta zeyi dan haka sakeni kaje ka riƙe ƴarka kayi jinyarta bana buƙatarku dukan ku"

Cikin kame kame yace, "haba Wasila Ƴarki ce fa ba tawa ni kaɗai ba ki tausaya mata mana karki tafi ki barta"

Saurin katse shi tayi da cewa, "yanzu ƴa taka ce duniya da lahira ka sakeni ko kuma kaga bala'i wallahi"

Yace, "bazan sake ki ba duk matakin da zaki ɗauka ki ɗauka"

Sufa tayi ta cikume shi da kokawa kicici kicici har ta samu ta cafki inda take hari, ihu ya zuba cikin ruɗu da tashin hankali yafara meman ɗauki, kafin mutane su ƙwaceshi tini ya sume a gurin, ita kuwa ta koma gefe sai huci take bayarwa.

kai tsaye gurin likita akayi dashi da yake a asibitin ne abokin sa ne yayi duk cuku cukun da za'a dubashi lokacin.
Bayan wani lokaci suka sanar da cewar yana lafiya sai dai jijiyar shaukinsa ta samu matsala.

sosai Wasila tayi murna da hakan dan dama abunda take so kenan kuma tayi ƙudurin ko yana tafiya kansa yana fesar da wuta sai ya sake ta.

Haka akayi Ƴa kwance uba kwance kowa yana fama da tashi larurar, mahaifiyarsa ce kawai take ƙoƙarin komai akansa sauran ƴan uwansa da mahaifinsa kuwa cewa sukayi abunda ya shuka shi yake girba dan haka ba abunda zasu tsinana masa"

Ana kwana ana tashi har ranar asabar ta zamo saura kwana biyu, amarya Aisha a yanzu ne zaka tabbatar amaryar ce tayi kyau sosai tasha ado ko ta ina.

Sayid ne ya shigo da gudu yace, "Mama wallahi ga Saifu can a ƙofar gida sai zazzaga masifa yake"

Kafin ya rufe baki Nuriya tayi hanyar fita tana cewa, "da abamu labari gara mu bayar dan da alama ya haukace"

Ita ma Aisha Mayafi taja tayi waje, kafin wani lokaci duk sun fito ganin ikon Allah, shi kuwa be fasa tijara ba, "anci amana ta an yaudare ni, to wallahi nafi ƙarfinki ko kin auri wani bazaki zauna lafiya ba sai na hanaki farin ciki a rayuwarki azzaluma, kuma nafi ƙarfin kowa duk wanda yace yana sonki ma nafi ƙarfinsa nine na makantar da ABU ɗin kuma kowaye ya shiga hanya ta sai na illata shi"

maganganu yake kamar na marasa lafiya da iya ƙarfinsa kuma da son nuna gaskiyar abunda yake faɗa.

Ƙamewa tayi a wajen jin yace shine ya makanta ABU, bama ita kaɗai ba duk wanda yake gurin ma sai da maganar ta girgiza shi musamman waƴanda basa zaton hakan daga gareshi wanda basu san halinsa ba.

rasa abunyi tayi dan haka kawai ta fashe da kuka tashige cikin gida. Mama tafara tambayarta abunda yafaru, wanda suke biye da itane suka rattaba mata aikuwa ta shiga salati da sanarwa ubangiji gaba ɗaya jikinta yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login