Showing 48001 words to 51000 words out of 90447 words

Chapter 17 - MISKILI NE COMPLET BOOK BY MOM FAREESA.doc

asirin kurciya tabar gida"sbd karta auri nasir tafi y'ay'ana hutawa.... innalillahi wa inna ilaihir!! shine abinda mommy ta fad'a tana mik'ewa tsaye arikice, tana jin kamar ancire mata abinda yamata takunkumi game da k'in neman salma"daddy kallon zabba'u yakeyi babu ko k'iftawa"yayinda sadeeq da khalifa suka kasa mgn....wlh dama na jima da zargin akwai saka hannunta aciki"ku cikata duk gidan ubanda zataje taje sakaryar allah ce ai"cewar mommy tana kuka"aikuwa su khalifa suka cikata da gudu ta fita"daddy yabiyota saidai tana isowa bakin titi wata mota da zata wuce aguje tayi ball da ita"saida tayi sama da dawo k'asa"me motar bebi takan taba yabar wajen aguje"kasancewar anata kiran sallar magrib wasuma wajejen har an tada sallar"hakan yasa bakin titin bbu mutane sosai"kuma dama ba babban titi bane cikin layin gidajen anguwar titin yake"wasu mutane biyu da daddy suka rufu kanta"gwiwarta da kanta yabugu sunata jini"dakkota daddy yayi yadawo da gida cikin gidan"ya ajiye ta d'akinta "yasanarwa shamsiya dake zaune ta gama sallah cewar"ta kira y'an uwanta su kaita asibiti shi bazai iyaba"sosai abin yabata mamaki suka kama kuka itada sauran y'an uwanta"d'akin mommy yanufa yasameta tana kuka tana sanarwa yayanta alh bello komai ta waya"zama yayi gefenta duk su khalifa na zaune"bayan ta gama wayar yace"kiyi hak'uri bilkisu"sai yanzun na fahimci tabbas asirin da zabba'u tayi hardamu tayimawa"tunda bamu nemi y'armuba"amma alhmdllh zuwa gobe zamu fara bada cigiyarta akafafen sadarwa ko k'ilan allah yasa adace"mommy na kuka tace"dama ai ba yau tafara yimun asiri ba"taje itada allah bazan tab'a yafe mata ba"allah ya isa tsakanina da ita"kaima na gama zama dakai da y'ata tadawo zamu bar maka gidanka"adalci kakemun nan gidan?ko kuwa damuwa kayi danine?kasa mgn yayi bece komai ba"khalifa da sadeeq suka tashi jikinsu asanyaye suka bar d'akin "daddy yace"kiyi hak'uri bilkisu wlh bayin kaina bane"muddin nayi bincike itace tayi haka wlh bazan cigaba da zama da itaba"yanzun haka accident tayi"yalabarta mata komai"tsaki taja tana fad'in matsalarta ce"daga haka ta mik'e tsaye ta wuce bed room d'inta"yayinda su shamsiya suka nufi asibiti da mahaifiyarsu....washe garin ranar duk mutanan gidan cikin damuwa suke"sai wajen k'arfe 9:30 am daddy yafara shirin fita shida samarin gidan da nufin afara nuna pics d'in salma gidajen tv da jaridu"mommy na zaune d'akinta tayi tagumi hawaye nata zuba tana tuna salma wayarta tayi ringing"saida taji gabanta ya yanke yafad'i tadai d'aure ta d'auka tana yin sallama.....zumbur ta mik'e tsaye tana zaro ido waje tace"da gaske salma kece?daga d'ayan bangaren amaan na kuka tace"nice mommy"karki tashi hankalinki ina cikin koshin lafiya"sbd allah ya jefani hannun mutanan k'warai"alhamdulillah allah nagode maka! mommy ta fad'a tana fita daga cikin parlourn tasami daddy dasu hamma yusuf tsaitsaye da alama niyar fita suke"alh ga salma ta kirani"ta fad'a daidai lokacin da amaan ke cewa mommy ga ammi mahaifiyar hamma shariff daya tsintseni zata muku bayani"dato mommy ta amsa"bayan ammi ta amshi wayar ta mata sallama kafin su gaisa"mommy tasaka wayar handsfree ammi tafara musu bayani atak'aice"kafin daga k'arshe tace "munaso idan babu damuwa kuzo mu damk'a muku y'arku ga hannu"kuma kuyi mgn da malamin daya bata taimako ta warke"mommy tace"gobe zasuzo" sai godiya mommy ta dinga yiwa ammi da sakama shariff albarka"daga k'arshe daddy ya amshi wayar suka gaisa da ammi da amaan"sannan hamma yusuf ya amsa sukayi mgn da amaan yasanar mata abinda yafaru agidan bayan b'atanta"aciki harda accident d'in da anty zabba'u tayi tana kwance asibiti"damuwar tace allah ya kyauta"anjima idan hamma nah yadawo zan bakushi saiku gaisa"lallai salma kin iya kalar dangi ko?"daga ganin mutum kice yazama yayanki?"k'in mgn tayi yace"ga khalifa da sadeeq ku gaisa .... amaan bata dena wayar dasuba saida katin ammi yak'are duka"sannan ta hak'ura da wayar"ammin tace"ta saka hijab taje bakin titi ta siyo ta dawo taci gaba da wayar"amamakin ammi sai taji tace"ah ah ammi hakanma yayi kar naje na fita hamma be saniba zai mun fad'a"daga haka ta wuce d'aki ta kwanta bbu jumawa bacci yayi awon gaba da ita"sai wajen k'arshe 12 saura ta tashi"kai tsaye toilet ta nufa anan taga bak'on ta yazo"bayan ta fito ta kimtsa ta fito parlourn"ammi na kwance kan 3 seeter "abdallah na zaune yana kallon ball"kin tashi amaan?"eh ammi meye za'a dafa ne?"ah ah ki barsa ki huta ni nayi musu abincin ranar"dan allah kar muyi jayayya ammi indai ina gidan nan bazan bari kiyi aikin komai ba"pls anty amaan kimana me dad'i kamar na d'azun "cewar abdallah yana kallonta"tayi murmushi batace komai ba "ammi tace"to shikenan y'ata duk abinda kikaga yadace ki aza "jummai da laure na kitchen d'in zasu d'an kama miki wani abun dan kuyi sauri ko?"dato ta amsa ta wuce kitchen"suna aikin jefi jefi shariff na fad'o mata arai"sai wajen k'arfe 2 ta gama"su jummai suka jere komai a dining area "ita kuma sbd ba salla takeyiba ta wuce d'aki tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa"lokacin da fito zataci abinci har ukku ta wuce amma shariff shiru be dawo ba......da yamma suna zaune a parlourn"da abdul da sadeeq da abdallah da amaan"mazan nata fira ita kuma tana duniyar tunani"abdul nata satar kallonta "sai yawan sakota cikin firan tasu yakeyi ita kuma tana sharesa"ahaka shariff yashigo cikin parlourn da sallama cikin tattausan muryansa"yana rik'e da wasu fararen ledoji irin na shopping"fuska bbu yabo bbu fallasa yashigo amma yana ganin amaan zaune atare da samarin atake ya had'e rai ya kauda kansa "adak'ile ya amsa sannun da suke masa"ita kuwa saida taji gabanta yafad'i tayi saurin tashi tsaye tana nufosa ahanakali tace "hamma sannu da zuwa"yauwa"ya amsa da k'yar yana juyowa suka had'a ido"ta sunkuyyar dakai "beyi mgn ba yamik'a mata ledojin hannunsa"k'in amsa tayi "hakan yasa yad'ago kansa ya zuba mata manyan idanuwansa.& ..da sauri ta kawar dakai ahankali tace"hamma ni bazan amsaba sai d'aure fuska kakeyi ko?"beyi mgn ba yamatso dab da ita yakama hannunta guda yasaka mata ledojin.....yanayin yadda taji taushin hannunsa saida takusan sakin ledojin"tamkar bayaso yace"meye amfanin kije kiyi zaune cikinsu?"to hamma yazanyi?kaifa na zauna jiran dawowarka"bayanma ka fita bansani ba"ta fad'a cikin shagwab'a "ya kauda kansa yana fad'in muje sarkin k'orafi"yayi maganar suna jerawa ahankali suka nufi dining area "taja masa kujerah ya zauna"abinda tasan zai buk'ata ta zuba masa "sannan ta matsa gefen fridge d'in dake wajen ta d'akko ruwa da kwalin lemo tazo ta ajiye masa"thank you! babu godiya tsakaninmu hamma"ta fad'a tana kok'arin tafiya...ina zakije?"zan mayar da ledojin d'aki"zoki zauna kiduba su anan ki bani labarin yadda kukayi da y'an gida"sosai taji dad'in tambayar tasa"gefen sa ta zauna tana duba ledar farko"kwalin waya ce k'irar iphone14 pro max, sai ledar pads...da sauri ta d'ago kanta akunyace tana kallon sa"ashe ita yake kallo sai suka had'a ido"gira guda ya d'age mata yana fad'in yaya dai ?"kauda kanta tayi tana duba gudar ledar"sweets ne da manyan chacoolates"ta turo baki ta kauda kanta"uhmm !sbd dan na siyo miki da pad kike wannan faman turomun bakin"very soon zanyi maganunku keda bakin naki....toni dama nace ka siyo mun itane hamma?"tab'e baki yayi tamkar ba zaiyi mgn ba sai kuma yace"nasan yau ko jiya jinin naki zaizo shiyasa naka miki"kokin manta time d'in da kike tambayata jinin ya d'auke yaya zakiyi?? yak'are maganar ko ajikinsa yana ci gaba da cin abincin sa dayayi masa masifar d'adi"ya tabbatar amaan gwanace wajen iya girki dan yasan itace tayi girkin "sbd yasan kalar girkin ammi da d'and'anonsa.... amaan kuwa....
'?

wannan book d'in na kudine ! idan kina buk'atar siya serious regular grp 300
vip grp 1000
via 2230373842 nabila aliyu uba bank

ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

d'
=?%? *MISKILI NE*d'
=?%?

*41&42*




......... Amaan kuwa tunda yafara maganar ta sunkuyyar dakai k'asa tana jin kamar k'asa ta tsage ta shige ciki sbd kunyar da kalamansa suka bata" Azuciyarta kuma gulmarsa takeyi wai wannan hamman bashida kunya"saidai kuma k'asan ranta farin ciki ne da mamakin kamarta zata rik'e wannan wayar me tsananin tsadar gaske?"tama fahimci irin wayarsa ce yasiya mata...idan kin gama tunanin gulman tawa kije kisaka phone d'in naki chargy"yafad'a cikin cool voice d'insa yana cigaba da cin abincin sa"saidai haka nan yaji kunyarta ta burgesa....ganin ta mik'e tsaye tak'i yadda ta kallesaba yasaka shi cewa"akwai sim card zuwa dare zai hau"bance kisaka contact d'in saurayinki Aciki ba"yafad'a cikin hura hanci yana yatsina fuska"Amaan dai batayi mgn ba "tana kuma mamakin meyasa yatsani yaya nasir wai??"tana wannan tunanin ta wuce daga wajen batare data koma tankashiba"shi kuma yatab'e baki yana fad'in nafiki miskilanci yarinya mu zuba mu gani"daga haka yaci gaba dacin Abincin sa"koda ya idar bebi takan taba ya wuce shashensa yayi wankansa yafice ta k'ofar baya"Amaan kuwa cikin farin ciki ta nunama Ammi wayar sannan tasakata chargy"ta zauna tana duba chacoolates d'in"can kuma ta Ajiye ta d'auki ledar pad d'in ta wuce bath room....wasa wasa tun Amaan na zaman jiran dawowar shariff harta hak'ura ta wuce d'aki wajen k'arfe 9: 30 pm ta d'auki wayar ta bud'e taga sim d'in ya hau"tana duba balance nata taga tanada credit kusan na 10k"shiru tayi tana d'an tunani"can tace"lallai hamma wato shi kud'i ba matsalarsa bace"kodai fushi yakeyi danine?"tafad'a tana mik'ewa tsaye k'irjinta na tsananta bugawa sbd Amon jarumar muryansa dataji"da sauri ta saka hijab ta bud'e k'ofar ta fito.....wlh da gaske nakeyi Abokinah tazo tamun rantsuwar idan har zaka Aureta zata dena komai...wani irin tsinkewa zuciyar Amaan keyi, taji kamar zata faso k'irjinta ta fito"da sauri tayi baya"adaidai lokacin dataji shariff na fad'in look mus'ab! kasan babu Abinda na tsana sama da wata tace tana sona ko?"to pls muma Ajiye wannan zancen sbd na tsaneta bana k'aunarta"Allah yasa ta mutu sbd ni"Abinda take Aikatawa kar Allah yasa ta dena"yafad'a cikin zafin rai yana huci...pls calm down shariff meyayi zafi haka? nifa turoni tayi bayan ta had'ani da girman Allah da monzonsa"shiyasama har na maka mgn"ni kaina nasan fareedah bata dace dakai"pls mus'ab dan Allah kaje mun had'u da safe office "cewar shariff yana mik'ewa tsaye"da sauri Amaan ta koma ciki sbd sautin takun takalminsa sawu ciki dataji"shi kuma tama gaban d'akin ya wuce bebi takan jin Amaan d'in tayi bacci ba ko batayiba"sbd har itama haushinta yaji yanaji.... Amaan kuwa wata wawuyar Ajiyar zuciya tasaki me k'arfi tana rintse ido ta fad'a saman bed"k'asan zuciyarta tana jin sanyi sbd kalaman da shariff yafad'a Akan yarinyar.....tana Ahaka Aka turo k'ofar d'akin"saida k'irjinta yabuga tama d'auka ko shine sai taga Ammi ce"baki kwan taba Amaan?"eh Ammi zan kira mommy ne"dato ta Amsa ta fita"d'aukar wayar Ammi tayi tana dubawa"can ta gano number d'in shariff ta d'auka"bayan ta Ajiye ma Ammi waya ta saka number d'in mommy ta kira....sai wajen k'arfe goma da wasu mintinah ta gama wayar"bayan mommy ta sanar mata gobe insha Allah zasuzo ta turo cikakken ful Address d'in gidan Ammi"yadda dasun iso garin zasu zo nan....koda ta kwanta tunanin shariff ne yamata sallama"wanda zuciyarta ke ganin bala'in kirkinsa da mutuncinsa"ta fahimci yana k'ok'arin kyautata mata fiye da tunanin me tunani"idan Abaya yamata haka yanzun Aita dawo hayyacinta ko?"saima kyautatawar taci gaba"saidai ranta yabata yanada saurin fushi"zatayi k'ok'arin ganin yarage wannan yawan saurin fushin kafin tabar gidan....da wannan tunanin bacci me dad'i yayi Awon gaba da ita..... shariff kuwa sai bayan yayi wanka da shirin bacci zuciyarsa ta bujuro masa da tunanin Amaan"sai jan tsaki yakeyi yana juyi saman bed"ko coffee d'in dayake sha yau be nemaba, sbd mus'ab yabashi haushi daya kamasa zancen fareedah "yarinyar daya san y'ar lesbian ce meye zaiyi da ita ko mata sun k'are a duniya??.......k'arfe 10:38 pm ya sakko k'asan yana sanye da jallabiya fara gogaggiya yanata zabga k'amshi fuskarsa ad'aure tamau"hakan kuma be hanashi yin kyau ba.....wani iri yaji sakamakon hango Ammi da yayi zata shiga d'akinta"Anutse yace "Ammi"juyowa tayi suka had'a ido "ya kauda kai da k'yar yace"dama zansha coffee ne Aturo Amaan ta kamun....dakatar dashi tayi da cewa"y'ata tayi bacci"koma bata yiba bbu inda zataje"dama kana buk'atar coffee d'in kak'iyin mgn tun d'azun??"bece komai ba yana dai tsaye gefen up stars d'in "sanin ba mgn zaiyiba yasaka ta wuce d'aki tana murmushi domin tagama fahimtar shariff yagama mutuwa a soyayyar Amaan"Amma zata k'yalesa taga zai Ajiye miskilancinsa yasanar mata ko kuwa??"dukda Amaan d'in tasan An kawo kud'in gaisuwarta kuma bata son yaron"hakan bazai saka su fidda rai ba"zata cigaba da addu'ar zab'in Alkhairi"koda bataga iyayen Amaan ba ta fahimci yarinya ce ita me tarbiya da sanin yaka mata"kuma tanaso bayan iyayen sunzo zata saka Acan Adamawar Amata bincike sbd Akwai k'aninta Acan"har cikin zuciyarta tana yiwa shariff kwad'ayin ya mallaki Amaan Amatsayin matar Aurensa"dukda tasan nema cikin nema haramunne Amma Addua itace maganin komai"da wannan tunanin itama Ammin ta kwanta bacci"shi kuwa shariff ya k'ule sosai da hanashi ganin Amaan da Ammi tayi"dama kuma babu wani coffee d'in dazai sha , kawai ita yakeson gani"da k'yar yasamu yayi bacci....washe gari yana dawowa daga masjeed ya wuce d'akin Ammi sbd yaga Amaan"saidai koda yashiga suka gaisa bbu ita"gadai teddy d'in ta da wayarta saman bed yana gani"duk Ammi na lura dashi"ya mik'e tsaye ya rasa ta ina zaice tana ina?"sai kawai yafita ransa na bashi tana kitchen" tunda ga Ammi nan zaune tana Azkhar yasan kuma bata barin Ammi tayi Aiki da kanta"tunanin hakan yasaka yanufi kitchen kai tsaye"koda yatashi shiga cikin sand'a ya shigo Amaan na tsaye gaban gas cooker tana fera dankali"tana sanye da doguwar riga fara k'al y'ar kanti irin ta y'an k'asar turkish"tayi Acuci da gashin kanta data saka red d'in veil ta yane"sosai ta masa kyau yabi bayan ta da kallo"ya kawar da kansa yana d'an sakin jikinsa ta yadda zataji motsin mutum"da sauri kuwa ta juyo"had'a ido sukayi"gabansu yafad'i Atare"Amaan tafara kauda kanta tana cigaba da Aikinta...wai yarinyar nan tana nufin tafi k'arfin tamun mgn ne kome? yafad'a Acikin zuciyarsa yana nufar gaban fridge yabud'e ya d'auki goran ruwa"sai wani d'aure fuska had'e da shan k'amshi yakeyi"yasha Alwashin bazai tanka taba"harya kai k'ofa yaji siririyar sanyayyar muryarta tace"hamma ina kwana?"bana so! nace bana so Amaan!! ki rik'e gaisuwarki"sbd kinga kin samu lafiya zaki bar hannuna shine zaki tsiro da haka?to yayi kyau na gode.... yafad'a cikin kakkausar murya yana fita daga cikin kitchen d'in batare daya kalletaba... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! fassarani zaiyi ni salma?ta girgiza kanta idanuwanta na cikowa da k'wallah sbd ta tsani Arayuwarta Atuhumeta da laifin da bata san ta Aikataba"sosai tasha kukanta cikin kitchen d'in tana Aikinta harta gama"Abinka da farar mace duk fuskarta tayi ja"hakama idanuwanta"tana gab da kammalawa Ammi ta shigo cikin kitchen d'in tana fad'in sannu da Aiki Amaan"su mommy d'in sun kai kusan la'asar kafin su iso ko?"k'ilanma har biyar sai sunkai kinsan da nisa...kallonta Ammi tayi sosai dukda ta juya fuska gefe"gabanta yafad'i tace"Amaan lafiya naga kamar kinyi kuka?"babu komai Ammi kawai ina kukan zanyi kewarku ne"kinga idan sunzo yau gobe zamu juya mu tafi shine fa"batare da Ammin ta yardaba tace"karki koma kuka ga waya Amaan"bayan ita kuma nima Ai zanzo ko shariff yaje ya d'akko mun ke ko?"hakane kuma"to karki koma yin kuka "idan kin idar kizo kiyi wanka ki huta"dato ta Amsa Ammi ta fita daga cikin kitchen d'in "kai tsaye sashen shariff ta nufa sbd ranta yabata shine dalilin kukan Amaan"kawai dai ta b'oye mata ne"hakan kuma yatabbatar mata da cewar Amaan nada hankali da sanin yaka mata.... shariff kuwa ya d'auka zata biyosa ta tayita masa shagwab'a da bashi hak'uri sai yaga Akasin hakan"har cikin main parlour ya zauna yana danna wayar k'arya kodan k'ilan ta fito" Amma sai yaga Amaan shiru"daga bisani ya wuce samansa"sai haushin kansa yakeji wai Akan me zai damu da ita wai?"yana wanka yana jan tsaki "harya fito ya shirya zuciyarsa Acunkushe take....yana zaune a parlourn sa ya Aza k'afa d'aya kan d'aya yana waya da mus'ab"Ahaka Ammi ta shigo"saidai yadda yaga fuskarta yasaka yaji fad'uwar gaba"yada dai dake sbd namijin duniya ne shi"sallama yayima mus'ab kafin yasaci kallon Ammin.....sannu ishashshe me walkin sa! wai yaushe zaka dena wannan zafin zuciyar taka ne shariff?"me kuma nayi Ammi?"tsaki taja tace"me kayiwa y'ar mutane take kuka?"k'arata ta kawo?"ko d'aya"Amaan nada hankali koda na tambayeta b'oyemun tayi"saidai tace mun......ta masa bayani"kafin ta d'ora da cewa"hakan yatabbatar mun wani abu kamata"yau iyayenta zasu zo kuma gobe nake tunanin zasu juya da y'arsu "me makon ka sakata farin ciki shine zaka sakata kuka ko?"shiru yayi yak'iyin mgn "ta juya ta fita daga cikin parlourn"gaba d'aya sai yaga be kyautaba"yasan kawai rashin fahimta suka samu Amma ya lura Amaan nada sauk'in kai"jikinsa Asanyaye ya fito daga cikin parlourn yanufo down stairs "hangota yayi tana jera warmers Asaman dining table"kallon cikin parlourn yayi yaga babu kowa"cikin sand'a ya iso gab da ita yasaki ihu daidai kunnanta.....ta saki k'ara Atsorace ta juyo suka had'a ido"saura kiris ta fad'a saman k'irjinsa"kusancinsu yayi yawa har hannunta na shafo nasa"saita turo baki tad'an ja da baya tana neman barin wajen....dama ke matsoraciya ce bansani ba?"yafad'a yanata kallonta sbd shima ya lura da tayi kuka d'azun....kabani hanya na wuce! shine Abinda ta fad'a kanta Ak'asa"idan nak'i fa?"yafad'a cikin taushin muryansa yana koma fake wajen ta yadda bazata iya wucewa ba"Allah koka matsa kona had'aka da Ammi?? Amaan! yakirata cikin wata iriyar murya har saida taji gabanta yafad'i"uhmm! meyasa jiya muna zaune inata mgn kika mun shiru?"kunyafa nakeji hamma shiyasa"Amma kai kana ganin laifina kana fushi dani damun zaton Abinda ba haka nake nufi ba ko?"tayaya sbd na warke zan maka Abinda be kamata ba hamma??sai kuma ta saki kuka"kinga ya Isa zoki zauna muyi mgn "yafad'a yana matsowa yaja mata kujerah murya can k'asa yace"zoki zauna ki dena kukan"batayi mgn ba ta zauna kan kujerah "shima zama yayi gefen tata kujerar ya ciri tissue dake Ajiye gefe ya matso dab da ita har tana jin hucin numfashinsa "bazaki dena hawayen ba?"saida ta kwab'e baki kafin tace"toka hak'ura?"kina kallon wani wajen bani ba shine zan hak'ura"to Ai basai ka kalleniba zan kalleka ka yarda?"ah ah "yafad'a yana saka dogon hannunsa dake rik'e da tissue d'in ya share mata hawayenta"ya yar da tissue d'in yana fad'in yanzun zakiyi break fast d'in?"uhmm uhmm! ta fad'a Ad'arare sbd jin Alamar idanuwansa na yawo a Akanta"gaba d'aya kunyarsa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login