Showing 1 words to 3000 words out of 4233 words

Chapter 1 - BACCIN SO FREE PAGES BOOK BY MAMAN SHAKUR.pdf

M.Shakur   

21 Nov 2025

6414

BACCIN SO



✍M SHAKUR


EPISODE 1️⃣

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI!


Cike gidan yake makil da jama’a, kana ganin yanayin tsarin ginin gidan kasan irin gidan masu
dan rufin asiri ne daidai gwargwado, babban compound ne mai dan madaidacin girma dakeda
wata yar kodaddiyan milk gate dayake a bude sabida jama’a dake shiga da fita. Yammata
ansha makeup ansha anko, sun zagaye wata yar budurwa dakana ganinta kasan itace
Amaryan sabida yanayin tufafin jikinta da gwargwaro dakuma lalle datasha a hannaye da
kafafu, rawa suke sosai a tsakar gidan gaban DJ dayake buga kida yana chanza wakoki anama
Amarya liki yan 50, da yan 100naira….


Duk wannan kidan da hayaniyan da ake bugawa bacci take acikin dakin dakeda dan duhu dan
an sauke labulen window, kaman an tsikareta firgigita tabude idanunta tana kallon saman silin
na dakin dawani irin sauri ta tashi zaune gashinta nawani irin zubowa bayanta mai tsawo baki
kirin dayake a tsefe, sanye take da atampa wanda kana gani kasan sabuwa ce anko kuma dan
tayi kama da na mutanen tsakar gidan yan biki, an manta dinkin doguwan riga dayamata wani
irin bala’in kyau a jiki, very simple style mara nauyi kwata kwata, waige waige tashigayi kaman
mai neman abu sai kawai tamike tsaye zumbur tana yarfe hannu karamin lips nata ya furta
“Ammi” wanda muryanta baya fitowa, saita shiga tafiya ahankali ahankali still kalle kalle take
tana shafa fuskanta da kanta tana sosa gashin data shiga hargitsawa yafara komawa wani iri
kawai tabude kofan dakin, jama’a ne birjik afalon ana hayaniya, tana bude kofan kowa yadago
kai yakalleta jikake falon tsit sai kuskus da aka fara, kanta tasauke kasa ahankali, saita cigaba
da tafiya ahankali batare data hada ido da ko mutum daya na falon ba bakinta na furta. “Ammi,
Ammi, Ammi” ba lallai ma kaji metake cewaba idan bakazo kusa da ita ba, sai gyaramata ake
kowa na cire roban abincinsa daga kasa, kawai tawuce tayi kofa tafita jama’an dakin na kuskus.
“Yarinya kyau iya kyau amman kan ba dadi sam, sam”. “Wai ahaka aka haifeta koko jinnu ne
cus kyawawan yara haka daman ance yaran jinnu ne”? “A’a wannan fa haka aka haifota da
tabin hankalin ba jinnu bane, yoh yarinyar da asibitin mahaukata ma ake kaita”………
Jama’a ne cike a compound din ga rawa anayi tana fitowa kawai tafiya tashigayi har lokacin
kuma kanta akasa tana magana ita kadai “Ammi, Ammi” tana tafiya tafiya irin wacce ba direction
dinnan nan da nan jama’a suka fara kallonta.
Amaryan dake filin rawane ta hangota taja tsaki takalli daya daga cikin yammatan wajen tace “je
dan Allah ki kirawa mahaukaciyan chan mamanta kafin ta hargitsamin biki, dan wlh tabatamin
biki sainaci ubanta kafin akaini gidan mijina” dasauri kawarta tace “toh bari naje” fita daga cikin

filin rawan tayi tai bayan gida ta nufa inda mata ke girki dagudu tayi wajen mata mata tadan
manyanta akalla zatai 46yrs haka tana sanye da same atampa da kowa yasaka tace “Ammi ga
Amirah chan tsakar gida zata fara haukan” anatse Ammi tajuyo takalleta kafin tai magana
matan dake kusa da Ammi tace “wai ku yaran yanzu maisa baku da tarbiya ne iyye haka ake
magana Zainabu”? Turobaki tayi tace “to karya akayi? Danma nazo nafada mata ai danayi shiru
abina kwashe nemanta anjima…..” Ammi bata tsaya jinsu ba wucewa tayi da dan sauri
tazagayo cikin compound din tanabin ko’ina da kallo tana nemanta da idanu gabanta nadan
faduwa ta tare wata yar yarinya tace “kinga mini Amirah Baby?” Baby tace “tana waje tana
nemanki Ammi” dasauri Ammi tasaketa tai hanyar gate tana zuwa taganta awaje tafiya take still
ba takalmi akafan dasauri Ammi tasa hannu takama hannunta tace “gani nan Amirah” Ammi tai
maganan tana kai dayan hannunta kan kafadarta tajuyo da ita tanadan maida ijiyan zuciya
sabida kalan saurin datayi, ahankali for the first time sai yarinyar tadago kanta Ya Rabbi! Tsarki
ya tabbata ga Allah ubangijin daya hallicci kowani bil adama, dan yarinyar nada kyau, wani irin
kyau da kafin kaga mace mai kyanta sai an tona, sak Amminta tundaga white skin color din,
saidai tafi Maman kyau nesa ba kusa ba, ga gashin idanu dogaye bakake sosai, ga gashin gira
baki acike mai yawa kaman buzuwa, tanada dogon pointed nose, ga karamin baki pink yir
exactly irin na jarirai, gefen fuskanta da goshinta duk akwai gashi kwance kaman buzuwa, chak
ta tsaya tana kallon Ammi kuma babu wani reaction akan idanunta kona damuwa, kona baccin
rai, kona farin ciki, Kona tsoro, kona bakin ciki, kawai fuskanta is straight, dan ijiyan zuciya
Ammi ta sauke tadan sassauta murya tace “jibeki ba kallabi akanki, ba takalmi akafanki,
banasha gayamiki duk sanda kika farka baki ganni ba ki zauna awajen zaki ganni zan dawoba
amman bakijin maganata, wuce mutafi” Ammi takara rikewa gam tashiga tafiya, Ammi na tafiyar
da ita ahankali suka shigo cikin gidan daidai wata mata datasha ado sosai tanada dan jiki kana
ganinta kasan itane Maman Amarya ta tareta tana wani hura hanci tace “idan kinsan ba girkin
zakiyi ba maisa kikace zakiyi tunda hankalinki nakan wannan abun” tanuna Amirah da kanta ke
kasa tana dab da Ammi dake rikeda hannunta, adan natse Ammi tace “yanzu zan koma
nacigaba Maman Baby” Mamababy tana wani huci tace “shidai yafi miki, kibar mahaukaciyan
nan kiji da abincin jama’a” ko kadan Ammi bataso yau ranta yabaci saisa kawai takara kama
hannun Amirah da kyau suka wuce bayan gidan, few matan dake wajen suka bisu da kallo
ganin Ammi tadawo da yarinyar, wani plastic chair Ammi tadauka ta ijiye tadaurata akai tace
“zauna bari nabaki abinci” Ammi tajuya dawani irin sauri kaman gudu Amirah ta tashi, Matan
dake wajen suka bita da kallo Ammi tajuyo ta kalleta ganin taki zama takara biyota sai kawai ta
kyaleta bata cemata komiba tabude katon kulan wajen tadauki plate tazuba mata white rice da
stew tasaka spoon tajuya mata sannan tace “muje” Ammi tai gaba Amirah tabiyo ta abaya,
Ammi takamata tasata a kujera ahankali saita debi rice a spoon tadankai bakinta jin ba zafi
sosai saita debo takawo wajen bakinta dasauri tabude bakinta hakoranta farare passs, Ammi ta
samata shinkafan, karba tayi duk tana kallon idanun Ammi tana taunawa ahankali, sai Ammi
takama hannunta tasaka mata plate din tace “yauwa to maza cinye, bance ki tashi ba gani nan
girki zanyi kinji”? Shiru tayi tana kallon Ammi tana chewing rice din, Ammi tace “kice to” da dan
karamin voice nata da Ammi kadai kejinsa aduniya tace “toh Ammi” wani heart melting smile
Ammi tayi ta tsaya tana kallonta sai kuma ahankali takai hannunta tashafa kumatunta tace
“yauwa yar albarka na, maza cigaba da ci ingani” sauke kai tayi daga kallon Ammi ta debo
abincin a spoon takai bakinta tafara ci Ammi tace “yauwa Masha Allah, kada ki tashi gani nan
anan” Ammi tajuya tayi wajen murhu tana tafiya tana waigowa dantaga kota mike taganta

azaune amman tanabin Ammi da idanu tanacin abinci ko kyafta idanu batayi, dan ijiyan zuciya
Ammi tasauke ta tsaya kusada Rakiya tace “kuyakuri Rakiya” Rakiya tace “haba bakomi,
dawainiya da yara haka ai ba karamin aiki bane, kuna nema mata maganin islamic kuwa?”
Spoon na girki Ammi tadauka tana juyawa tace “babu wanda ba mayi, ba matsalan jinnu bane
da itaba rashin lafiyane kawai daga Allah” dayan matan tace “gaskiya yakamata kiyi dagaske,
ga sa’onninta duk sai aure, to wannan ma ai kanwartata tayi aure abarta tunda har anzo an
tambayi aurenta, jibidai yau Ramla ce Amarya, gaskiya dai kuyi da gaske inba hakaba babu
wanda zai auri mara lafiya”Ammi bata kara magana awajen ba sai aikin gabanta take bini bini
tana dagokai ta kalli Amirah da har lokacin idanunta nakan Mamanta duk inda Ammi tayi tana
binta da idanu, gama hada komi Ammi tayi tarufe pot tazo tadauki pure water tazo wurin, Ammi
ta bude mata ta karbi plate din ta ijiye sannan tasaka ruwan abakinta hannuwanta tasa ahankali
tadaura akan na Ammi kullum idan Ammi nabata ruwa haka takeyi tashiga sha tana kallon
Ammi, Ammi tamata murmushi tace “saura kimini wasa da ruwa anan agwagwa kawai” dago
kanta tayi alamun ta koshi, murya chan kasa tace “Ammi pee”Allah yasa tagama hada komi na
girkin kawai tsotsewa zaiyi akwashe takalli su Rakiya tace “tunda an gama bari nakaita ciki nasa
mata kallabi” dasauri Rakiya tace “karki damu tunda kingama zamu kwashe kiji da abu daya”
Ammi batace komiba ta karbi plate din ta ijiye takama hannunta tace “muje toh” kankame
hannun Ammi tayi suka wuce Ammi tace “duk sanda kika kara fitowa babu kallabi akanki saina
saba miki mena gayamiki game da budekai ba kallabi”? Batace komiba ahaka suka shiga falon
Ammi ga jama’a awajen Ammi ta gaggaisa dasu Amirah na tsaye wajen dab da Mamanta
tanama wasa da yatsun Ammi ne ita kadai haka Ammi tawuce da ita bedroom duk aka bisu da
kallo, ta maida kofan tarufe sannan tace “cikani kije kiyi fitsari” dan dago kanta tayi batare data
saki Ammi ba sai kawai Ammi tawuce da ita bandakin tabude kofa tace “shiga” ahankali tasaki
hannun Ammi, Ammi tace “yi adduan shiga bandaki” ahankali bakinta ya shiga motsi saita shiga
Ammi tajuya zata wuce dasauri Amirah tace “Ammi” dan dakatawa Ammi tayi kaman zata mata
fada but she knows harda mutanen dasukayi extra yawa yau agidan da hayaniyan biki yasa
she’s being extra clingy today, other days tana dan bata space even though duk inda zaka gan
Ammi zakaga Amirah you must find her awajen, sai kawai Ammi ta tsaya tace “jekiyi to gani
nan, maza kiyi alwala” gyadama Ammi kai tayi tawuce tana daga riganta Ammi na kallonta
batako kyafta idanu kana ganin yanda take komi kasan mahaifiyarta tai kokari dan bata wani
shirme, tashi tayi bayan tayi tsarki tamaida pant dinta sannan tai flushing zata taho Ammi tace
“alwala baki salla ba” alwala tashigayi shima exactly yanda ake alwala sannan tafito Ammi da
kanta ta rufe kofan bayin tadauki hijabi tabata tasaka maroon yamata bala’in kyau ta kabbarta
salla tayi shima perfectly tana idarwa tajuyo takalli Ammi, Ammi dake daukan ribbon da comb
tace “ba kallona nace kiyi ba tashi kizo nan nakama suman nan naki” ahankali ta tashi ta linke
dadduma da hijab ta ijiye inda Ammi ke ijiye saita taho dayake abakin gado Ammi take zaune
tana harhada ribons nata dasuke cikin wata yar karaman jaka daban hawa gadon tayi ta kwanta
tadaura kanta kan cinyan Ammi, Ammi takalleta tace “ai yamiki kyau mage” saita dauko comb
zata fara kifa kanta yayi a cikin Ammi, Ammi tace “zan kwadeki idan baki tsaya ba tunda ke baki
kaunar ataba miki kan nan, kinfiso kiyita tsorata mutane dashi, bani kan nace” ahankali tafito da
kan tasa akan cinyan Ammi, suka fara.
Tun tana yar yarinya batason ataba kanta dambe ake sosai, itama Ammi saida tayi da gaske
hakan yasa ko yanzu ma ahankali take taje mata gashin, gashinta is so silky and very black
kuma bata tabasa relaxer ba, kama gashin tayi agida biyu tsaf tagama hakan yasa tajuyo da kai

tana kallon Ammi, Ammi tai murmushi tace “iyye Yammata na tayi kyau Masha Allah, yimin
murmushi nagani yayyy”tsayawa Amirah tayi tsuru tana kallon Ammi sosai dake murmushi
kaman zata hadiye Ammi da manya manyan fararen idanunta, ahankali Ammi tajuyo dakatar da
murmushin datakeyi tai shiru sai kuma idanunta suka cicciko da hawaye dasauri tadauke kanta
tadanja hanci irin maison hadiye kukan nan jikinta yayi sanyi looking very sad, kama hannun
Ammi Amirah tayi tashiga wasa dashi tana tattaba hannun tana wasa da fingers din Ammi tana
nannade wannan da wannan, sai Ammi tajuyo da kanta ahankali kawai tazuba mata idanu tai
nisa a tunani, aka bude dakin dasauri Ammi tajuyo wata yar budurwa ce tana sanye da anko
itama kana ganinsu kansu daya kuma kamanninsu kusan daya kawai Amirah zata nuna mata
hasken fata ne ita wannan hasken ta kaman na Ammi ne, ta ijiye jakan makaranta tace
“Wayyoo Allah na Ammi ina wuni nagaji” murmushi Ammi tayi tace “andawo daga school
Miemie, yaya test din” dasauri tataho wajen gadon tace “Ammi nayi kokari sosai” tai maganan
duka idanununta na kan Amirah da kanta ke cinyan Ammi tana kirga yatsun Ammi kaman
batasan da mutane a dakin ba, Ammi takalli Amirah tace “tashi toh ga Miemie tadawo daga
school, Miemie zauna min da ita bari nakoma naduba abinci zan kawo miki shinkafa kema”

Dasauri Miemie tazauna kan gadon tana kallon Amirah tace “yau bazaki kulani ba sabida ban
kawo miki tsaraba bako” Ammi tamusu dariya tace “kunfi kusa” Ammi tasa hannu tadagota
ahankali tace “zauna da yaruwanki bari naje nakawo muku abinci” Ammi ta karbe hannunta
tamike dasauri itama tamike, Ammi cikeda fada tanuna mata gado tace “zauna anan nace ita
Maryam din bakuwan kice, tun safe banda sukuni sabida ke sai bina kike kuma kinki yarda da
kowa, abin naki harda yar uwanki yau, wuce ki zauna nace” tunda Ammi tafara fada tasauke
kanta kasa takai hannayenta tana sosa cinya duk saita bama Ammi da Maryam tausayi,
Maryam da taji duk ba dadi dasauri ta taso takai hannu zata kamata dawani irin sauri ta matsa
kusada Ammi, Ammi tace “kyaleta kawai Miemie kinsanta hayaniya da jama’a duk suna tada
mata da hankali, yau rashin yardan hardake kuwuce muje” Maryam tace “kuma Ammi da bata
ganki ba da nine zata mannemawa hakafa” Ammi tace “ai tunda tamiki halinta yau karki kara
kawomata komi daga school” Ammi tawuce tai gaba dasauri tabi Ammi kaman bindi Allah tasa
kan akwai hula yanzu, Maryam ma tabisu tana kallon yanda simple gown din yama Amirah kyau
na wuce misali, backyard Ammi tayi anan taga Maman Baby awajen da ake kwashe abinci a
kula tahade giran sama da kasa Ammi ta taho wajen zata wuceta Maman Baby tace “ki barshi
kawai bana bukatar ki, Allah yasa inada wasu dazasu tsaya kan abinci jekiji da diyarki mara kai”
dasauri Rakiya tace “mekuma yayi zafi Maman Baby kinsan yanda yara suke especially marasa
lafiya kuma duk ita tahada abincin ai kafin takaita ciki”
Cikeda fada Maman Baby tace “karki gayamin magana Rakiya, bakisan meke faruwa bane
acikin gidan nan, bakin ciki take taga sa’an diyarta yau tana aure ga tata diyar kai duka yaran
nata ma babu manemi, daya ba kan gado kan ba dadi balle ma ayi maganan aure akanta,
dayan kuma sai bakin rashin kunya” Maryam ta tabe baki tana juya idanu, Maman Baby tace
“shine takeso mutane su zageni kar kowa yaci abincin tunda ba yarta ke aure ba” ahankali
Amirah takama bayan rigan Ammi tarike jikinta yadan fara rawa bawai tana kallon mutane bane
but she understands everything that is happening around her, bataso taga ana fada da
mamanta, dazaran an fara zakaga tarike ko hannu ko rigan Mamanta kanta akasa, Maman
Baby tana kallon Ammi cikin idanu tace “to bari kiji wlh sama taima yaro nisa saidai yadaga
fuska ya kalleta nariga namiki fincinkau Zainabu, diyata na biyu kenan danake aurar wa kekuwa

kije kifara ji da mahaukaciyar nan ita kadai tazamema rayuwarki azaba da ukuba” tai maganan
tana nuna Amirah, tunda ake hayaniyan nan babu abinda yabatama Ammi rai sai kalman
karshe data fadi, takalli Maman Baby sosai kaman tabata amsa amman saita fasa sai kawai
tasa hannu takama hannu takama Amirah dake jikinta, takalli Maryam dake huci tacika fam tace
“kuwuce muje” ganin Maryam batai motsi ba Ammi tace “Maryam nace muje” zuciyanta ba dadi
tajuya fuuuu, Maman Baby tadaga murya tace “dakin barta ai tarama miki yanda tasaba, ahaka
zaki kare keda uwarki, Zainabu kekuma nagaya miki aniyanki akanki zai kare gadai daya nan
agabanki kina gani, ke kikasan uban me kikayi Allah yabaki ita mai juyayyen kwakwalwa”
mutanen wajen ne suka dinga bawa Maman Baby hakuri cus zagin yayi yawa sannna tai shiru.
Kofan flat nasu Ammi tabude takalli Miemie dake huci strictly tace “wuce ciki” batai musuba
tawuce ciki, Ammi tashigo da Amirah, duk an fita daga dakin, Ammi tawuce ta ita tazaunar da
ita akan gado takalli Maryam dake tsaye tace “zauna kema Miemie” kaman jira take dasauri
Maryam tace “Ammi wai Matarchan who did she think s…..” “kul!” Ammi tafadi ahankali hakan
yasa Maryam tai shiru, idanunta na ciko da hawaye jikin Ammi yayi sanyi, ahankali tace “idan
baki fahimceni ba Miemie wanake dashi kuma eh? Ina zan sa raina? Ke koda zanyi fada ba
abinda zaki hanani bane Maryama? Kalli yar uwanki ba lafiya, anzo neman aurenki, Babanki
yace nan da wata uku, da shirya aurenki zanji koda ciwon yayarki eh Maryam? Do you think
tsayawa nayi fada is wise?” Ahankali tace “Ammi ni bazanyi auren nabarku anan ba wlh” wani
kallo Ammi tamata tace “ke bakida hankali ko” kawai saita fashe da kuka sosai, ahankali for the
first time tunda tadawo sai Amirah tadago kanta ta kalleta, ahankali Ammi ta taho wajen Amirah
na binta abaya, Ammi taduka tana kamota tace “Miemie mehaka? Meyayi zafi? Why are you
crying like this? Miemie na menene”? Ammi tarungumeta cus Maryam hardly cries, cikin kuka
da tsantsan zuciya tace “sai ayita kiran yaruwata mahaukaciya, Ya Amirah ba mahaukaciya
bace, yar uwata ba mahaukaciya bane, she doesn’t hurt me, bata cutar da kowa, Ya Amirah is
kind, Ammi she takes care of me, kullum idan zani school she cleans my shoe, da farko ma da
rigan jikinta take gogemin saida na nunamata da tsumma akeyi, bantaba fada mata ta gogemin
takalmi ba, idan ina assignment tana zama kusadani taita kallona idan nai bacci awajen zata
kwashe all books din tasamin ajakan school, she watches me and studied kome nakeyi even
though she hardly talks to me, Ammi yar uwana ba mahaukaciya bane kawai Allah ya hallice ta
daban ne, Amirah ba bala’i akanmu bane, my sister is special, and she’s Allah’s gift, I love my
sister ni wlh da ita zan tafi gidan mijina idan Umar bazai yarda ba nafasa aurenshi” ganin yanda
take kuka yasa Ammi kawai tadinga lallashinta ta share shirmen datake fadi na zataje

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login