Showing 3001 words to 4233 words out of 4233 words

Chapter 2 - BACCIN SO FREE PAGES BOOK BY MAMAN SHAKUR.pdf

M.Shakur   

21 Nov 2025

6413

gidan
mijina da Amirah, da mijin zataji koda Amirah? Hmm yaro yarone!.



EPISODE 2️⃣


Wuraren 7 akazo kai Amarya za’akai Amarya wurin Ammi danta samata albarka Maman Baby
tahana tace awuce ita, itama Ammi taso fita amman gudun cin mutunci abainar jama’a yasa tai
zamanta ga Amira da bata isa tai motsi batare data bitaba, ga Miemie data samu ta lallaba
tahakura gwara tazauna cikin yaranta sune farin cikin rayuwanta. Tasss suka gyara falon da
jama’a suka zauna sukai moping ko’ina Miemie tasa turaren wuta sannan sukai isha’i, Ammi ta

kunna mata cartoon a TV a falo sabida ta yarda tazauna taje tai wanka, tace “zauna keda
Miemie bari naje nai wanka, yi kallo abinki kinji diyar albarka, bari naje na watsa ruwa” Ammi
bata jira amsanta ba tawuce tana kyaftama Maryam idanu alamun tariketa, bin Ammi Amirah
tayi da kallo harta shiga bedroom dinta, saita janye kanta tamaida kan tv ahankali Miemie tace
“mayyan Ammi, bazaki iya rayuwa babu Ammi ba Amirah” ringing taji wayanta nayi daga
dakinsu dake kusadana Ammi hakan yasa tamike dasauri tace “Ya Amirah ina zuwa Ya Umar
na kirana” tawuce dakinsu dakin yarage just Amirah ne ciki, kusan 10min tana zaune ita kadai
tana kallon tv aka bude kofan dakin da sallama ciki ciki. “Assalamu Alaykum” wani irin tsalle
Amirah tayi tasauka daga kujeran datake zaune tasauke kanta kasa dasauri, wani dattijo ne
haka ya shigo yana sanye da suit, fuskanshi ahade ba rahama yama Amirah wani kallo mara
dadi kafin cikeda kunci yace “ke ina uwarki”? Kan Amirah na kasa tana wasa da fingers nata
tana goga hannunta awajen cinyanta tasaman riga kaman bada ita akai magana ba, dattijon
yaja wani tsukin takaici. “Mtswww useless girl!” Yawuce yashiga tafiya takalmin kafansa cover
shoe na kos kos kan tiles na parlor, bedroom na Ammi yabude kofan yashiga yamaida kofan
yabugo da karfi yarufe dayasa Amirah tasake firgita saita dago kanta tana kallon kofan saitakai
hannunta tasosa gefen fuskanta takasa komawa tazauna, hannunta sai rawa yake tana sake
goga hannuwan ajikinta sosai sosai.
Karan yanda aka bugo kofan yasa ahargitse Ammi tafito daga bandaki tana kokarin daura zanin
wanka da kyau danta dauka Amirah tafadi ne, taga mutumin hakan yasa ta dakata tadan sauke
ijiyan zuciya tace “sannu da zuwa Daddy, wlh nadauka Amirah ce tafadi bakaga yanda na
tsorata ba” wani bakin kallo yamata tareda daga mata hannu yace “that’s not why I’m here
Madam, ubanme da me kika fadawa Asiya yau?” Ahankali Ammi tace “kaman ya?” Cikin fushi
sosai Daddy yayo kanta kaman zai rufeta da duka yace “ke mesa baki da mutunci, how dare
you disrespect my wife? Ba ke kikace zaki girki bakiyi ba kuma kikahau zaginta agaban jama’a
on her daughter’s wedding day, ke maisa bakida mutunci, you’re a very very useless woman
saisa kika haifi that useless, foolish, dumb headed girl dinchan!” Wlh zagin daya mata ko kadan
baimata zafi ba, amman na Amirah yamata zafi da ciwo arai.
Faduwa gaban Ammi yayi tadan kalli kofa cus tasan the way fada da ihu ke triggering condition
din Amirah gashi daman bawai shiri suke da Babanta ba dan baya gamaciji da ita, cikeda
damuwa da dan sassauta murya Ammi tace “Daddy dan Allah kayakuri kadena daga murya
Amirah na falo kasan ba ishashen lafiya ne da itab….” Tasssss! Yadauke Ammi da mari mai zafi
kafin Ammi ma tadawo hayyacinta yasa duka hannayenshi ya hankadata ga ruwan wanka dake
kafanta jikake tasss Ammi tafadi akasa sosai, Daddy na huci sosai yace “nikike gayama
maganan banza? Sabida mahaukaciyar yar da kika haifo bazanyi magana dake ba? Who do
you think you’re? Are you telling me how I should behave because of that dumb mental girl”?
Dan bude kofan dakin kadan akayi hakan yasa Ammi dataji kaman kafanta ma ya murde tadago
kanta takalli kofan shima Daddy yajuyo jin an bude kofa, Amirah ce tabude kofan dakin amman
kanta akasa sai yakushin hannayenta biyu take cikeda karfin hali Ammi ta kakalo murmushi
tace “Amirah banace idan ina magana da Daddyn ki kidena shigowa ba, go and watch your
cartoo….” Cikeda zafin zuciya Daddy cikin tsawa yace “ubanme kikazo yi anan wuce ki koma
inda kika fito ja’ira dakikiya, mahaukaciya kawai” ko motsi Amirah batayiba saima cigaba da
susan hannunta datakeyi, sosai ran Daddy yabaci azuciye yajuya zaiyi kanta cikin fushi yace
“badake nake magana ba kikeyi kaman badake nake ba, nace kibar wajen nan” dudda Ammi
naji kaman tai targade akafa amman ganin zaiyi kan Amirah wani karfine yazo mata ta yunkuro

tama kasa mikewa tsaye takai hannunta takama hannunsa arude tace “Daddy dan Allah karka
tabata dan Allah kayakuri, bawai batajin maganan ka bane, ba cika gane maganan take ba dan
Allah kamata afuwa, don’t beat her please” wani kalan juyowa Daddy yayi sabida bakincikin
yanda Ammi tarikemai kafa baiyi wata wata ba kawai ya fizge kafansa ya tokare Ammi aciki,
Amirah dake yakushin hannunta tawani kalan buga kanta akofa jikinta yafara kyarma, Daddy na
ihu sosai yace “maganan banza maganan wofi dani kike magana zanyi maganin ki toh agaban
diyar naki nagama dake nakoma kanta tunda you’re becoming bold” kawai yashiga dukan Ammi
tun Ammi na daurewa bata ihu tashiga kokawa dashi tanason kwace kanta tafara ihu. Sosai
Amirah tadinga buga kanta akofa cikin yar karaman muryanta tana “Ammi……Ammi…Ammi…”
dukawa Daddy yayi yakaima Ammi naushi a hanci yace “zan miki jina jina yau ba nikike
maidawa karamin mutum ba”wani kalan juyawa kan Amirah yafara, har rotating idanunta suke
in circular motion da kanta kaman lizard, plate na tangaran da Ammi tabata abinci dazu tagani
anan dakin kawai saita taho ta duka tadauka jikinta ko’ina rawa yake ta taho wajensu dukansu
babu wanda ya lura da ita, batai wata wata ba tadaga plate din da duka karfin da Allah yamata
na duniya kawai tabugama Daddy plate na tangaren akansa wani irin mugun mahaukacin bugu
saida tray din ya tarwatse jikake ratsatsaaa!!!! ihu Daddy yayi sosai, sai jini, yashiga juyowa
amman kafin ya idasa juyowa ya zube akasa a sume bayako motsi Ammi tazaro idanunta ta
kankare tsabagen tsorata da mamaki, awani irin haukace Amirah ta duka tadauki a piece of
broken plate din from kasa mai sharp mouth Ammi da muryanta baya fita tace
“Am…..Am….mirah Amirah” Amirah was not her self tai inda Daddy ke kwance a sume zata
chakamai kwalbal Ammi takama hannunta, Amirah tai wani ihu “ahhhhhhhhhhh” ta fizge kanta
zatai kan Daddy Ammi batasan sanda tasa karfi tai kan Daddy ta tare sa tana bude hannuwanta
ba tana goge hancinta dake jini tace “ni zaki kashe ai ba Babanki ba Amirah, maza chakamin
kwalban kinji saimu mutu mubar miki duniya!” Dakatawa Amirah tayi amman har lokacin tana
rike gam da kwalban jikinta na rawa sosai tana huci, taki kallon Ammi tana wani irin nishi kaman
zata shide na zuciya tawani kankame kwalban dayasa jini yafara fita daga hannunta Ammi
tamike da kyar tana dingishi tayi kanta, hannunta takama zata cire kwalban amman tayi tayi
takasa sai numfarfashi take tana kallon Daddy har lokacin, Ammi tafashe da kuka kawai
tarungumeta tana shafa kanta sosai tace “it’s okay, babu abinda yasamen eh Amirah, calm
down please, bagani nan ba eh, Ammin ki lafiyanta kalau!” ko kadan she wasn’t calm Ammi
tadago tasake kai hannunta kan nata tace “bani kwalban kinajin ciwo” amman ina Ammi takasa
karbe kwalban nan daga hannunta tsabagen yanda ta kankame kwalban gam gam.

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login