Showing 24001 words to 27000 words out of 44640 words

Chapter 9 - Dingishin Kwado Book 1 Complete Hausa Novels By Hadiza D Auta.docx

jinin gidanmu.

Ni da yaya Munirah muke yin komai na hidimar gidan domin mun lura sassafe yake tashi ya hau hidimar shirya yaran nasu tare da rage mata ayyukan gidan, domin iyayen ƴar aikinsu basu yarda ta biyosu kudu ba. Shiyasa yake taya ta aiyukkan da cikinta ya yi nauyi. Ganin haka ya sanya muka daina komawa barcin safe muna gama azkar zamu fice mu hau hidimar gyaran gidan da abun da zai ci tare da yara. Sai sun tafi sai ku koma mu kwanta idan mun tashi sai muyi abin da zamu ci. Ba ƙaramin daɗin zuwanmu suka yi ba. Duk da yadda Abida bata sanya kanta a hidimar da muke yi ba, daga matar gidan har maigidan tattalinta suke yi tamkar ƙanwar momi ce.

Na riga da na gane yadda Baba babba ke son Abida haka yaya Asad ma aka jarrabe shi da sonta. Shiyasa idan tana gabansa take baje dukkan wants ɗinta shi kuma yana yi mata yadda take so.

Bansan me yasa har muka yi kwanaki bata fesa musu na sake haɗuwa da Sahalu ba ta bakin nata.

A wannan zaman na ɗan fara sakewa da yaya Asad har ina iya zama tare da shi mu yi hira gabaɗayanmu.

Wani dare muna zaune a falo ni da Abida muna kallon wani Nigerian fim (The wold apart). Jaruma Ini Edo ta yi matuƙar ba ni tausayin yadda ta faɗa tarkon son ɗan sarki. Domin nasan zafin soyayya. Tausayin da na shiga na yadda iyayen yaro suke ƙyamar haɗa iri da talakawa makaskanta. Tuni barci Mai nauyi ya yi awon gaba da Abida, yayin da yaya Munirah da matar gidan sun jima da shigewa dakunan barci tare da yara.

Ni kaɗaice idona biyu. Daidai lokacin kuma na ji alamun dawowar maigidan.

Ya shigo sanye da kakinsa da suke matukar yi masa kyau. Yana nan cak a tsaye tamkar saurayi. Ga shi sun fara tara yara. Duk da dai babu tazara a tsakanin yaran nasu. A zamana na fahimci shi ɗin mai son ƴaƴane bai ɗauki ɗabiar yin tazara ba, har ita matar ko dan lokacin duniyar bata waye irin yanzu ba ne, ko dan rayuwar cike take da aminci da sauƙin rayuwa?

A kasalance ya shigo jikinsa babu kuzari ya zube a kan kujerar da take maƙwabtaka da wacce Abida take kai.

A hankali na ce "Sannu da dawowa yaya".

Ya amsa da faɗin "sannu Sarauniyar shaibah. Kallo kuke yi ne har barci ya sure wannan?"

Kaina na ƙasa na ce "eh.

Ya taya ni mayar da hankali kan allon talabijin din. Murya babu amo na ce "Na yi maka abinci?"

Da mamaki ya ce "A wannan daren zaki iya yin girki?"

A sanyaye na ce "Ai akwai komai da za'a buƙata indai zaka ci, sai na dafa maka".

Ya ce "idan baki takura ba, dafa yunwa nake ji sosai".

Na miƙe da hanzari, na nufi kicin ina tunanin mai kuma zan dafa ne? Wanne iyayyin ne ya jani yi masa tayin girki?

Ina ma na bar shi ya ɗauko cake ɗin da ya saba ci da shayi ya ci abinsa.

Na fi mintina goma ina tsaye a jikin freezer ina nazarin me zan yi masa mai sauƙin sarrafuwa kuma wanda ba zai dame shi ba tunda kwanciya zai yi.

Take na yanke shawarar na yi masa jollof din patateo. Sai da na kammala yanka albasa na yi jajjaga tattasai da attaruhu sannan na ɗora na tsayar da ruwan sanwa ƙadan tunda dankalin turawa baya karban ruwa da yawa sannan na fara feraye dankalin. Na buɗe firij na ga ragowar papper fish ɗin da muka ci da rana. Na fito da wanda nasan zai cinye na zuba a girkin.

Na rufe, na koma gefe, gabaɗaya ƙamshi ya cika kicin ɗin na tabbatar har gidan gabaɗaya ya karaɗe. Rabon da na ga sinadaran girki masu ƙamshi irin wadanccan sai a shekarun nan bayan ma haihuwar Farha.

Spice ɗin Amreesh spice's Kano duniya ne, domin suna saka armashin girki, suna mayar da ƙamshin gida ya zama na alfarma, haka nan ko baka jin yunwa ƙamshin zaɓaɓɓun spices na sanya ka ci abinci ba tare da ka farga ba.

Tabbas spices ɗin Amreesh ba shi da na biyu a wajena da wajen duk wanda ya taɓa tu'amalli da su. Ku nemi naku kai tsaye ta wannan lambar..09093510131 Tana aika ko ina a ƙasar nan. Ga mutanen jiharmu ta Kano da Katsina kuwa kakarku ta yanke sa'a domin takuce, ku hanzarta tuntubarta.

Dinner bowls ɗin da na san ana zuba masa abinci na dauko na zuba a ciki. Na shirya komai hatta coffee ɗin da yake sha duk dare sai da na shirya, hakan kuma bai hana na saka masa ruwa da lemo masu sanyi ba.

Na kinkima na nufi falon. yana hango ni ya zabura ya miƙe tare da faɗin "standstill! Ta ya ya zaki kinkimo wannan tray haka ba ki san illar da daukar abu mai nauyi yake yi muku ba?".

Ya ƙaraso ya karɓe. Maimakon ya dire a dainin tunda shine kusa da kicin sai kawai ya wuce cikin falon da alamu so yake yana ci muna hira, domin ni dai ban taɓa ganin ya ci abinci ba akan dainin ba, tunda muka zo.

Hakan kuma bai mini daɗi ba domin takura zan yi, so nake kuma na dawo da kallon baya domin an wuce ni da yawa, tunda CD plate ne a lokacin.

Muka zauna ya fara cin abincin cikin nutsuwa. Ya kalli yadda na mayar da hankalina kan kallon. Ya ce "To zo mu ci mana yayar Abida". Na yi murmushi tare da ce wa "Alhamdulillah tuni muka ci abinci bana tare da yunwa".

Ya ce "Jiya Abida ta siyar mini da jaridarta da maƙudan kudaɗe.

Zuciyata ta harba, na tabbatar labarin jaridar ya shafe ni ko da kuwa ba gabaɗaya ba.

*A lame skin & Beauty Zaki samu dukkan nau'in kayan oriflame da dukkan mayukan da suke gyara fata **07036662633*

Ya cigaba da cin abincin ba tare da ya fasa labarin ba.

Ni kuma na cigaba da kallon da ba fahimtar komai nake yi ba, tunda ya zauna. Jira nake ya kammala na kwashe kwanukan na tashi Abida mu yi ɗaki na kalla gobe idan Allah ya kai mu.

Sai da ya kammala ya yi gyatsa tare da hamdala. Ya ce "Sarauniyar shaibah ashe kin iya girki mai ɗanɗano na musamman?"

Bansan ya aka yi ba dariya ta ƙwace mini na ce "Kasan me yasa ka ji daɗinsa?"

Ya girgiza kai da azama ya ce "Faɗa mini sirrin, nasan dai Madam ma ba baya ba wajen shirya girki, amma dai ke da nasan ba shiga kicin kuke yi ba, na yi mamakin yadda kika yi shirya shi cikin nutsuwa, kuma cikin ƙanƙanin lokaci."

Da dariya sosai na ce "Sai dai ka yi hakuri domin ka ci majina haɗi da tasonon Bilki. Hakan ne ya sanya ya maka daɗi da yawa.

Ya maƙe kafada tare da miƙo mini tafin hannunsa na dama ya ce "Fato mini, ki ga idan ban lashe ba, bare wanda ya ɓace a cikin abinci wuta kuma ta ƙone dukkan bacteriya ɗin da zai yi illa."

Na yi ƙasa da kaina domin wani irin kallo yake yi mini da na kasa gasgatawa. Zuciyata ta harba da tsananin gaske domin gaskiyar magana Sahal kawai ke mini irin wannan kallon, domin ko yaya Faruku ban taɓa ganin ya yi hakan ba, duk da na tabbatar yana sona bilhakki, kawai bansan me ya hana shi zama serious ba.

Hakan da ya yi kuma shine yafi domin ba zan taɓa yarda na auri mai mata ba, bare matarsa azababbiya ta ɗauki karan tsana ta ɗora mini haka siddan matsalakan

Kunya ta rufar mini, jikina ya yi sanyi sosai domin har cikin zuciyata kallon ya taɓa ni ƙwarai da gaske.

Ya haifar mini da wasiwasi da sanyin jiki.

[8/24, 12:53 PM] Surayya Dee: *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*

*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*

*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*

# 08032773332#

# 09069067488#

*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*DINGISHIN KWADO*

*BY*

*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*

*HALIN YAU*

*SABO DA KAZA*

*BAK'AR TA'ADA*.

*9*

*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*

*Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*

*07036662633*

*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*

Ya numfasa bayan ya janye hannunsa. Ya ce "Ashe kun sake hadewa da yaron da autar momi ta ce ƙiris ya rage ya shiga sahun zabiya".

Na kasa amsawa domin nasan babu labarin da yafi wannan tashe a cikin jaridar Abida.

Murya babu amo ya ce "Wai har iyayensu sun zo wajen baba babba?".

Na ɗaga masa kai dan ya gane tabbas zancen da ya ji a wajenta gaskiyar lamari ne.

Murya babu amo ya ce "Anya baki yi rushing ba kuwa Maigado?

Kina kallon kan ki a madubi kuwa? Ke fa gaba ɗaya ba'a miki zubin da ƙananun maza zasu same ki ba. Kin fi dacewa da zaratan maza musamman na jami'an tsaro".

Na kiɗeme ainun domin na kasa gane shima son nawa yake yi ne ko kuwa? Ni kuwa me zan yi da shi? Ban so yaya Usman ba a matsayin saurayi, sai shi? A ture ma yaya Faruku bai zama serious da maganarmu ba, amma kaf ya'yan baba babba shi kaɗai zan iya yin haƙuri na karbe shi a matsayin mijin aure ba dan komai ba sai dan tarin alherinsa da sadaukarwarsa, sannan ina jin zuciyata tana bugawa akansa. Ban da shi kuwa ban ga wanda zan iya yiwa alkunya ba a cikinsu, domin na tsani auren zumunci har zuciyata. Bare yaya Asad kwata kwata bai mini a matsayin mijin aure ba. Ya mini baƙi da yawa, ba shi da kyawu irin wanda nake so, sannan ƙarfinsa ya yi mini yawa, a lokacin sai nake ganin kuskure kaɗan zan yi masa ya targaɗa ni. Bare kuma ga matarsa da ta fini ilimi da gogewar rayuwa dan kuwa da kaɗan ya girme mata shekarar da suka yi aure ta kammala digirinta na farko a jami'ar Maiduguri. Yayin da shi kuma a lokacin shekararsa ɗaya da kammalawa.

*Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.*

*Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa*

*08163761797*

Da suka yi aure ta yi digirinta na biyu a Ɗanfodiyo University Sokoto a lokacin yana aiki a Kebbi. Dan haka ya ajiyeta a Sokoto yake jele tsakanin Kebbi da Sokoto.

Yanzu kuma ƴaƴansu uku tana shirin dire masa na hudu. Waya kai ni cusa kaina a tsakaninsu ta riga da ta fini wayewa da dabara, shi ɗin ma kamar a hannunta yake.

Ganin na kiɗima ainun da furucinsa, watakila kuma ya hango ban taɓa tunanin zai iya ƙulla wata alaƙa ta daban da ni ba, sai ya yi maza ya ce "Wani abokinane matarsa ta rasu watanni uku shine ya ganki ya ce yana son ki, mutumin kirki ne yaransu huɗu suma".

Yana rufe baki na ce "Abokinka fa! Tabdi gaskiya he is too big for me. Ka bashi haƙuri kawai!

Na faɗa bayan na tsuke fuskata ainun .

A tausashe ya ce "Ai na bashi haƙuri tunda na samu labarin kin bada damar da aka je gaisuwa wajen baba babba ai magana ta ƙare".

Jin haka na ɗan saki fuska kaɗan.

Sai kuma ya ce "Amma shi kuma ya ce "Tunda ba ƙudin aure aka kai ba, ba kuma auren aka ɗaura miki ba, zai jarraba sa'arsa domin kin shiga zuciyarsa kin yi kane kane".

Yana rufe baki na ce "Wallahi ka ba shi haƙuri dan kuwa ba zan yarda na saurarere shi ba, tsoho da shi zai ce yana sona?"

Jikinsa ya yi sanyi ya ce "Shi ke nan zan ba shi haƙuri tunda na gane da gaske ba zai ci albarkacina ba. Dama gani na yi mutumin kirki ne, kuma zai yi miki adalci.

Wasa ma nake yi miki matarsa da ranta kawai tana Kano tana karatu ne, shi kuma so yake ya samu wacce zata zauna da shi a Kaduna."

Na ce "Ya bincika a wani wajen ka ga nima ai karatu nake yi a Zaria. Ko kuma ga Abida nan ko zasu shirya".

Da sauri ya ce "Ya ga Abidan amma bai nuna ita ba, dama kuma mai irin yanayinki yake so marar hatsaniya, wacce zata ɗauke kai game da sha'anin yara da matarsa."

Na yi kamar na ce "To ba zai samu ba indai sai ni, amma kwarjininsa ya sanya na kame bakina. Amma raina ya ɓaci akan me ba zai ba shi Abida ba sai ni zai liƙawa sa'ansa mai ya'ya da kuma matar da bata iya sarrafuwa. Domin da ya isa da ita ai da ta bar karatun ta zauna da shi, ko ta yi karatun a Kad poly. Ya miƙe tare da sakin ajiyar zuciya ya ce "Na gode Maigado, na gode da girki, yanzu me kike so na baki dan ki san na yaba da karamcinki?"

Na yi murmushi na ce "I need nothing, amma na roƙeka?"

Da sauri ya ce"Ina jin ki?"

"Ka daina ce mini Maigado. Su Baba kaɗai ke faɗa mini, yanzu tunda ka fara faɗa mini Abida da sauran jama'a sun ɗauka".

Ya murmusa ya ce "Ina takaicin sanar miki kin roƙi abun da bazan iya yi miki ba. Domin ina matuƙa jin dad'i idan na ce miki sarauniyar shaibah ko Maigado. Kinsan kuwa duk Bilki ai mai gadon zinari ce."

Na tsuke fuskata na ce "Ni kam bana so, yanzun nan mutanen gidanmu zasu riƙe su bar Bilkin".

"To ki dinga rubuta sunan duk wanda ya ƙira ki da Maigado idan na zo ki faɗa mini, zan yi miki maganinsa ko waye."

Na ce "Ba zaka daina ba ke nan yaya Asad?"

Kai tsaye ya ce "Ina jin daɗin sunan ne, sannan kuma ban iya yaudara ba, tunda bazan iya dainawa ba".

Ya fita waje ya dauko bandir ɗin 500 a motarsa ya ajiye mini akan cinyata, ya ce ki ajiye idan kin koma gida ki siyi abin da kike so, na gode sosai sarauniyar shaibah"

Ya wuce wajensa ba tare da ya sake ce wa uffan ba.

Na kashe kayan kallon na hau tashin Abida.

Abin mamaki ban wani sha wahalar tashinta ba. Mamakin da na yi ita ɗin mai nauyin barci ce, hakanan mai wahalar tashi ce a barci.

Kwanaki biyu Anty Maryam ta haihu still dai mace.

Hidima sosai maigidan ya yi, cikin farin ciki.

Gaba-daya Aysha babbar ɗiyarsu shekarunta takwas, amma an mata ƙanne hudu, shiyasa a jere suke fikon ƙadan kaɗan ne a tsakaninsu. Khadija a ce ta biyu, sai Saudat ta rasu bayan an haifi Hafsat, sai kuma Hafsat da ita aka yaye akan dole.

Duk inda na yi Hafcy nan take yi, hatta da mamanta ta tafi asibiti haihuwa a wajena ta kwana.

Ba kuma ta yi mini rikici ba duk kuwa da yadda take da maƙon uwa.

Kwana da yini kawai ta yi, aka sallamosu bayan an tantance lafiyarta da ta jinjira. Kusan ni ke hidimar gidan, yaya Munirah tana taya ni da shara ne da moping, amma girki da kula da yaran duk ni nake yi, wani zubin ta kan yi wanke wanke. Abida kuwa kullum a naɗe take wai bata da lafiya, sai dai kuma jinyar bata hanata cin abinci da wanka da kuma nazari a mujalloli da littafai daban daban.

Ganin hakan da masu gidan suka yi ya sanya suka raɗawa ɗiyarsu Bilkisu. Ranar da ya faɗa mana sunan diyar kenan Abida wiwi ta rushe masa da kuka hannuwa a ka, tana ce wa "Yaya Asad haka zaka yi mini, lillahi wa Rusulihi ai kowa yasan ba shiri kake yi da ita ba. Ni ce taka ita kuma ta yaya Faruku sai kuma ka tashi kasa sunanta alhalin ni yafi cancanta ka saka. Wanne iri kunyata ni ka yi haka?"

Da rarrashi ya ce "Kwantar da hankalinki autar momi! Ba matar Usman an ce ta kusa haihuwa ba, to ki ji a ranki matuƙar mace ta haifa to sunanta Maryam-Abida."

Ta sassauta kukan ta ce "Ni dai na fi so kai ka yi mini".

Ya ce "zan yi miki matukar ina raye. Sannan zan saka miki ma a gidan Usman a kusa, sai dai idan ba mace aka haifa ba.

Ta sassauta kukan, duk da so ta yi a canjawa yariyar ta amsa Abida. Yayin da Yaya Munirah ta saki gauron numfashi ta ce "Allah ya bani haƙuri!

Ya yi gajeriyar dariya tare da faɗin "Ke ai yayarsu ce Munee".

A kuɗin da ya bani na ƙirgi dubu ashirin na bashi na ce ya siyo ragon suna, sauran ya yi hidimar sunan Bilkisu. A lokacin ragon dubu goma na bada labari ne.

Ya karba da murmushi ya ce "Lallai kin iya karrama takwara sarauniyar shaibah!

Na sake ɗaukan dubu biyar na kaiwa Anti Maryam na ce idan ta fita ta siyowa little Bily ɗankunnen gold.

Murna da godiyar da ta yi ya sanya na gane ta iya mu'amala da mutane. Na sani tafi ƙarfin abin, sannan na tabbatar ɗan kunnen gold za'a siyo a sanya mata, tunda dukkan ya'yan uku ko wacce zagayayyen ɗan kunnen gold ne a kunneta.

Da matuƙar murna ta ce"Ai kuwa gobe zan fita da kudin nan zan siyo mata Bilki".

Tana mini godiya, nima, ina yi mata godiyar, domin na tabbatar da bata yarda ba, ba zai soma saka ma sunan nawa ba.

Cikin dare Abida ta tashe ni. Ta zuba mini ido ta ce "Bilkisu a ina kika samu kudaden da kike ta wadaƙa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login