Showing 27001 words to 30000 words out of 61953 words

Chapter 10 - MU RAYU A TARE Book Complete Romantic Hausa Novels by Mom Islam .txt

03 Dec 2025

1444

da tozali, ta ajiye Mata, kana ta fito Mata da sabuwar atamfa wacce Aliyu yayi Mata tun sallah ɗinkin ya matseta sosai,

Godiya mahaukaciya tayiwa Ummi, kana ta shafa man tayi kwalliya tasa kayan, duk da batasa bra ba tayi kyau sosai.

Ummi ta kalleta, cike da farinciki tace "ammata na tayi kyau, kin kalli kanki a mudubi kuwa?"

Mahaukaciya ta sunkuyar da kai.

"Na gama aiyuka saura ɗora girki, shikuma sai anjima, so nakeyi ki bani labarinki tun daga lokacin da kikasan kanki har kawo yanzu"

"Mahaukaciya tayi murmishi kafin tace "zan baki labari, amma da farko sunana Tasneem, amma ki kawo aikin girkin mu fara inayi ina baki labari"

Ummi tace "karki damu, taliya zamu dafa, kuma ai akwai ruwan zafi a ajiye"

Mahaukaciya tace "da farko dai asalin sunana Tasneem, ni bahaushiya ce, asalin ƴar garin Kano, iyayena sun rasu, a hatsarin mota, zasuje shiga jirgin tafiya Saudiya basu ma ƙarasa filin jirgin ba sukayi hatsari, lokacin banfi shekara goma sha uku ba, ranar da su Ummana sukayi kwana bakwai da rasuwa, danginta suka tafi dani gurinsu, a gurin ƙanwarta na girma, mahaifina babban ɗan kasuwa ne, Alhaji Sulaiman Bushasha, itama ƙanwar Umman tawa mai suna Karima, sunada kuɗi sosai, sai da nayi primary da secondary amma a jss na tsaya, dama tun ina k'arama aka sani a school, lokacin da na dawo gurin anty Karima naci gaba da secondary da Islamiya, inada shekaru goma sha shida, yaron aunty Karima ya fara neman aure na, mutane sunata cewa nayi ƙarama amma ita anty Karima bata ganin ƙan-ƙanta ta, haka ya dinga zuwa gurina hira yana zuwarmin da kayan ciye-ciye, har da kayan sawa, kwatsam wani mai suna Zahradden ya fito shima wai yana sona,yaron  hamshaƙin mai kuɗi ne, sbda mahaifinsa, yanada shaguna a kasuwa sunkai bakwai, sannan a wani garin ma yana dashi, banda ƙasar waje da sukasan da zamansa, dama anty Karima matar ƙanin Ummana ce, mijinta ne ƙanin Ummana, uwa ɗaya uba ɗaya suke da Ummana, shikuma mahaifin Zahradden abokin ƙanin Ummana ne, ina kiransa da Uncle, wata ranar Lahadi, da safe, ya kirani corridor sbda yana tsoron anty Karima, yacemin, kar in sake in karɓi soyayyar ƙanin Anty Karima, sunansa Haseem,

Nace "Uncle mayasa kace haka?"

Cikin kwantar min da hankali yace "wlhi yana shaye-shaye, nikuma maraicinki nake dubawa, duk da kinada gata ba na wasa ba, amma Allah da kansa yace "ki zaɓawa ƴaƴanki uba nagari, haka shima mijin, to kinga Haseem akwai gyara a lamuransa, tunda har neman mata yakeyi, kema kanki kin sani ba sai na gaya miki ba, zai fi ki auri wanda zai kula dake da ƴa'ƴanki, mahaifinsa mutumin kirki ne, kinga lokacin rasuwar iyayenmu, sai da yayi sati yana zarya wlhi naji daɗi, sannan iyayenki suma suka rasu, duk da bawai mun rasa bane, wlhi shi yake biya miki kuɗin makaranta".

A lokacin kaina ya kulle, ina tsoron ɓata mu'amalarmu da Anty Karima sannan ina tsoron bijirewa Uncle, wata rana ta kirawoni akan in gaya mata tsakani da Allah nake son Haseem?, wlhi bansan lokacin da bakina ya suɓuta nace "ni Zahradden nakeso ba"

Cikin sauri anty Karima ta kalleni kana tace min "au kina nufin bakyason ɗan uwana kenan?"

"Ba haka bane anty nidai shi nakeso"

Nan fa ta rufeni da masifa, tare da cemin "wlhi bazan ƙara tausaya miki ba, a matsakinki na marainiya, har nawa kike da zaki dinga nunawa mutane isa?, badan Haseem yace yana sonki ba, wlhi baza'ayi miki aure yanzu ba"

Nidai ina jinta uffan ban ceba, taci gaba da cewa "karki sake neman wani abu a gurina, nima na cire hannu a lamuranki, kuma wlhi koda wasa kika sanarwa da yayanki maganar bakyason Haseem sai nayi maganinki"

Ashe Uncle yana laɓe a bakin ƙofa yana jinta,

Washe gari da ta fita anguwa ya kirani yacemin "in kwantar da hankalina anty Karima mutumce da inhar ta ƙwallafa rai a abu sai ta sameshi, shikuma bazai bari na auri Haseem ba, insha Allah gobe iyayen Zahradden zasu zo tambaya tare da dukiyar aure, in nuna bansan komai akai ba zeji da ita"

"Toh" nace masa idanuna na tsiyayar ƙwallah,

"Tasneem bawai kin isa aure bane, kawai ina son kuɓutar dake daga wannan gidanne nasan koda ina lura da wasu abubuwan bayan na dawo, idan na fita bansan abinda zatayi miki ba"

"Daga nan ya miƙe yabarni a parlo inata kuka"

Washe gari, ina ɗakina naji Uncle yana sanar mata da cewar "iyayen saurayina suna hanya tayi musu girki"

Cikin rashin fahimta tace "bata fahimci abinda yake nufi ba, dama zugani yakeyi akan kar inso Haseem, shi kenan ta zuba mana ido, abinci ne bazatayi ba yayi abinda zeyi"

Kasancewarsa mai haƙuri banji yace mata komai ba, sai ma ficewa da yayi,

Can anjima na fito ina wanke-wanke, naga ya shigo da babbar leda, ashe abinci ya siyo a restaurant ya nemi kula ya juye ya Kai ɗakinsa,
Dama yanada fridge ya ɗibo kayan sha ya ajiye musu.

Ina kallonsa ta labule, tunda ba mai duhu bane,

"Allah Sarki iyayena"

Na faɗa lokacin da hawaye ke bin fuskata.

Abinda zai baki mamaki, ta ƙofae baya suka shigo, har sukayi maganganu su suka gama babu wanda ya sani, ashe harda ƙanin kakarmu da abokin ƙanin kakarmu Uncle ya kirawo akayi maganar.

Fitowar Uncle ya tabbatar min da sun tafi,

Tun daga ranar na fara fuskantar matsaloli sosai, saboda wlhi ko abincin kirki bana samu, gashi kakannina duka sun rasu, sai dai ta wajen uwa, itace a raye, mahaifin Ummana ya rasu,

Ranar da Anty Karima ta tafi anguwa na samu Uncle nace "masa, ya mayar dani gurin Hajiya, kakata mahaifiyarsu kenan, yacemin inyi haƙuri lokaci kaɗan ya rage"

Kuka nasa masa, dole ya tausayamin washe gari, yasa na tattara komai nawa na koma can da zama, ranar nayi bacci sosai dan babu masifa, ita farinciki tadingayi da zuwana
Dama Uncle ya sanar mata da maganar saka ranar biki da akayi sati Uku, Hajiya ta dingayi masa masifa akan ya gaji dani ne da ake shirin aurar dani yanzu ba a bari nayi karatu ba?"

Haƙuri ya bata, daga nan bata sake cewa komai ba.

"Allah Sarki Tasneem kice kinga uqubar rayuwa, bari mu ɗora girki naga har ƙarfe ɗaya saura 12:45pm"

Back to story 🤞

Sosai tausayin Huda ya kama Amani, sosai taji zafin abinda Ummanta tayi Mata, amma ta fara tunanin Anya uwarta ce kuwa?
Suna isowa gida, Aseela ta riƙewa Huda hannu suka wuce part ɗinsu, Amani kuma ta ɗauki jakar kayan, Mahabob yaji daɗin kulawar da suke nuna mata.

Su kuma su Abba da Batool suka wuce nasu part ɗin, Inaya tana murnar ganin Huda tace "yau kam bazata kwana a gurinsu Abba ba"

Lokacin da suka dawo ƙarfe 5:30pm tayi, Abba na zaune a parlo ya danna waya ya kira Amani, cikin bada umarni yace "Please ku dafa indomie ko kusha tea, na aiko Mahabob da bredi"

Dayake suna zumuɗi babu wanda yace komai.

Sosai Batool taji daɗin hutar da ita da Abba yayi, ta taho kusa dashi tare da zame ɗankwalin kanta, ƙananun kitsonta suka baiyyana,

A hankali yakai hannu yana shafa su, cikin kasalalliyar murya yace "yau inaso in kasance da matata"

Abinka da mai zumuɗi ko ince yarinta, sai cewa "tayi bakada matsala" ko wayewa ce oho.

Rungume da juna suka wuce bedroom, kafin sai da ta tabbatar da ta kulle ko ina sannan, da sauri-sauri ya rabata da kayan jikinta, shima haka, tare da rage hasken glob ɗin ɗakin, sosai yake murza mata bre hankalinsa kwance, har wani mammatsasu yakeyi tana nishi ita Kuma, a kunne ta raɗa masa magana,

"Inason yin magana dakai"

"Haba hajiyata kome kikeso ƙofa a buɗe take"

Cikin kissa da shagoɓa Batool tace "uhm dama inason in roƙi alfarma ne, naga Mahabob yarone mai biyayya, wlhi nayi masa sha'awar auren ƙanwata da ta gama karatu a Dubai, satinan har ta dawo gida"

Cikin gamsuwa da maganar tata, Abba yace "haba ai kema momynsa ce, baki da matsala indai akan wannan ne an gama, nima ai samunki da nayi Mai tarbiya ga biyayya, wlhi ba k'aramin daɗi naji ba"

Sosai Batool tayi murna saboda koba komai, kamar inda mamynta ta faɗa zasuci gado mai tsoka, inhar suka zamo su biyu a familyn Alhji Auwal.

Naso yi muku sau biyu, wlhi hakan bata samu ba, masu comments Nagode wlhi kuna raina Kunyi yawa bare in lissafoku ɗaya-bayan ɗaya, wannan saƙo ne ga duk wani masoyina meyin comments.

Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

43-44

Kwanansu biyar da zuwa Algeria, anyi aiki cikin sa'a,

A Koda yaushe Hajiya ƙarama takan keɓe kanta ta dinga gayawa Allah halin da Iffat ɗin take ciki, duk da har yanzu bata fara magana ba, amma alamomin sauƙi sunata samuwa, su da kansu likitocin suka gayawa dady ya haɗa mata dana islamic.

Kamar inda saurayin Juwairiyya Abdul-Alee yayi mata alƙawarin zuwa, sai gashi da daddare, zama yayi ƙofar gidansu kan dakali kafin ya kirata yace "ya iso gashi a ƙofar gidansu"

Juwairiyya jiki na rawa ta fito, harda wani karairaya, kallon gefenta dataga mutum tayi kafin tace "malam lafiya kazo ka zauna mana anan kalan ka shafa mana talauci?"

Abdul-Alee ya miƙe tare da cewa "haba Juwairiyya nine da muka haɗu dake ɗazu, dama motar abokina ne, na aro dan Allah karkice nayi miki ƙaryar arziki"

Tunda ya fara magana Juwairiyya ta ke kallonsa cike da raini tace "mtsw asara ance maka ni ajinka ce?, ka tambayi kaf samarin anguwarnan sunana matar manya, kul karka sake zuwa gidannan dama kaso ka yaudareni ne?"

Jiki a sanyaye ya miƙe har tana tofa masa miyau,

Ta shige gida fuuu kamar zata tashi sama.

Cikin takunsa na nutsuwa ya ƙarasa jikin mota tare da kallon Mubashir, suna haɗa ido, Mubashir ya galla masa harara tare da cewa "wlhi kai wawa ne, ina ganin wulaƙancin da yarinyar tayi maka amma bazaka fasa zuwa gurin ta ba?"

Prince Abdul yace "wlhi tallahi Allah ya jarabceni da soyayyar wannan yarinyar, amma daga yau na haƙura insha Allah bazan sake zuwa ba"

"Oho wlhi kaci gaba da zuwa"

Daga nan suka shiga mota suka wuce.

Niko nace Allah sarki kwalli da turare ya kamo miki Prince kin koreshi.

Cikin ɓacin rai taje ta ɗibi gaushi tasa magani tayi hayaƙi, kana ta ɗauki turaren malam tasa tare da tozali, ta sauya kaya ta fice, a cewarta yau za'ayita ta ƙare.

Kai tsaye wata anguwar ta masu kuɗi ta nufa, tana tafiya tana sauya salon tafiya, cikin sa'a wata danƙareriyar mota tayi parking a gefenta, Juwairiyya taci gaba da tafiya, bata saurari taga waye a ciki ba,
Cikin ɗaga murya mutumin yace "ƴan mata dan Allah ki tsaya"

Cike da jan aji ta juyo tare da kallon motar, sbda bata hango mamallakin motar Ba, tunda a gaba take shikuma yana baya.

A hankali ta dawo gurin motar, da sauri ta sake kallonsa, a shekaru zeyi 40yrs amma sai kace ba wani babba ba, fuskarsa ce zata nuna maka yawan shekarunsa, "da farko dai sunana Alhji Al'amin, ina zaune a garin Abuja, bana zama a Nigeria nafi zama a Chad, bayan munyi aure zaki iya zaɓar ƙasar da kikeson ki zauna a cikinta Ni bamai takura bane"

Mamallakin motar ya faɗa yana kashe mata ido,

"Masha Allah ni kuma sunana Juwairiyya"

"Am ina fatan zaki amshi soyayyata dan bada wasa nakeyi miki ba, inhar kin amince nanda sati biyu zamuyi aure"

Cikin jin kunya Juwairiyya tace "babu damuwa Allah ya shige mana gaba"

Tana shirin wucewa, ya ciro waya ƙirar I phone 13pro max ya miƙa mata a kwalinta, mamaki ya kamata hannunta har rawa yake, tace "duk wannan nawane?"

Alhji Al'amin yayi murmishi yace "inhar kika zamo matata sai kin riƙe wacce tafi wannan, wlhi har cikin zuciyata nake sonki"

Har ƙasa ta durƙusa tayi masa godiya,

Yace "akwai sim card a ciki idan kika kunna zakiga kirana"

Tace "toh"

Zuciyarta nata rayo mata abubuwa da dama.

"Yanzu ina sauri zanje airport ne wlhi, ga wannan babu yawa, kuɗi ya miƙo mata bandir na dubu ɗaya guda biyu,

Hankalin Juwairiyya ya tashi, ta dinga yi masa godiya,

Har ya yi mata sallama ya wuce bata dena leƙen motar tasa ba, cikin sauri ta nannaɗe kuɗin a mayafi tare da wayar, ta dinga gudu har ta kawo gida.

Tana shigowa taga takalmin babanta, cikin ɗaga murya take cewa "baba ka fito wlhi abin arziƙi ya samu"

Baba ya fito da sauri, sbda a tsakar gida ta zube ta kasa ƙarasawa gurinsa,  yana fitowa yayi ido biyu da kuɗaɗe, sbda waya kam besan kuɗinta ba, sai ita da ta sani, bakinsa har yana rawa yace "ƴar baba waye ya baki?"

"Wlhi baba ina fita na haɗu dashi, yace baya zama a Nigeria a ƙasar waje yake zama, kuma yace idan na amince nanda sati biyu zamuyi aure"

Jikin baba na rawa ya tattaro kuɗin yana rungume wa, tare da cewa "kice kin amince harda  waya ya baki?"

"Eh wlhi baba bakasan tsadar wayar bane shiyasa baka ɗagata ba"

Baba yayi tsaki yana cewa "yanzu dai tunda hidima yanzu ya fara, mu tafi hotal (Hotel) muci abinci, wlhi ƴan dirama (Drama) suna birgeni idan naga sunacin abinci acan"

"Tabbas baya ka kawo shawara amma dole kasa kayanka na sallah saboda karsu rainamu"

LIBYA
Kamar inda babban likitan ya faɗa yau za'a sallami Mona, yau ɗin aka sallameta, kowa danginsa na zuwa, banda ita da maƙiyinta take gani koda wane lokaci, taji sauƙi sosai sbda tana tafiya amma tana ɗan ɗingishi, shima a hankali zata dena, cewar likitan.

Maƙudan kuɗaɗe Shahazad ya cika sbda ayi masa aiki Urgent.

Da yamma suka dawo gida, lokacin Hajara tana barci a ɗakinta, dan batayi zaton yau zasu dawo ba.

Sai da yaje ɗakin Mona ya kwantar da ita, kafin ya dawo parlo ya nufi ɗakin Hajara "Hajarrr!!!"

Ya faɗa da kakkausar murya, wacce ko a mafarki ta jita sai ta firgita.

Da sauri ta miƙe zaune, tare da ware idanuwanta tana cewa "ya jikin Madam?"

Kallon banza ya watsa mata kafin yace "ki ɗora abinci yanzu, Zarbiyan nake da buƙata akwai time table a sama ki duba da inda ake dafawa"

Zata kuma magana ya fice.

A hankali ta dafe kanta, tare da cewa "gobe insha Allah zan nemi alfarmar dena aiki a wannan gidan, wlhi bazan iya ba, gara in koma gurin Inna ko dusa zamu dingaci muci"

Kafin ta share hawayen da suka kwaranyo mata ta miƙe zuwa kitchen.

Allah ma ya taimaketa ta iya turanci duk da ba sosai bane, amma idan ta karanta tana gane wasu abubuwan.

Yau da wuri, Lulu ta tafi, dan ko ƙarfe 8:am batayi ba, sam taƙi yin brakfast a gida, sbda tace "sauri takeyi,

Gidan ya rage daga jami'an tsaro da ma'aikata sai Ala-Uddin da Hassana, tunda ta gaishe shi ya sanar mata da Black tea zatayi bata sake ganinsa ba,

Bayan ta tafasa shayin ta juye a cup guda biyu, da nasa da nata, already yasan cup ɗinsa, tunda yafi nata kyau, sai da ya tabbatar da ta shiga ɗakinta sannan ya fito cikin sanɗa yaje kitchen tana kallonsa ta window, magani ya jefa a nata kana ya dawo ɗakinsa da gudu,

Yanayin action ɗin da yayi yasa ta zargi akwai abinda yayi, tafito kamar batasan ya shiga ba...!

Insha Allah zanyi muku wani 9:30 insha Allah

Yau ansha hira naji daɗi sosai

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

45-46

Tana ganin ya koma ɗaki taje ta juye nata a gurin wanke-wanke, ta kunna pampo kana ta ɗauraye cup ɗin ta juyo ragowar na Kettle ɗin kana ta fito da cup biyu nata da nashi, shima ta window yake leƙenta har yana taka rawa, burinsa tasha shikuma ya iso gareta, a kan table na parlo ta ajiye coffe ɗin, kafin ta wuce da nashi ɗakinsa.

Da sallama ta shiga, ta sameshi yana sanye da ƙananun kaya, ba kamar inda Lulu ta barshi ba, tare da hannunta ya haɗo cup ɗin da take miƙa masa, kana yace "Haseeaina"

Cikin sanyin murya ta amsa da "na'am"

Makirin murmishi yayi, kafin yace "kin amince da buƙata ta?"

Jikinta na karkarwa tace "nidai kayi haƙuri ka barni in koma garinmu dan Allah na yafe maka duk abinda kayimin"

"Never!!!"

Yana saurin ajiye coffe ɗin,

"Wlhi bazaki koma ƙasarku ba har sai kin amince da ƙudurina, nima inaso burina ya cika akan masarautar mu"

Sam ta gaza fahimtar abinda yake nufi, dole ta zube a gurin tana roƙonsa, ganin yaƙi saurararta yasata cewa "shugabata tanada zafin kishi zata iya kasheni idan ta ganmu tare"

"Sai me? ƙarya ne, ni bazan bari ta gano komai ba, sosai nake samun nutsuwa dake, tun kafin a bani umarnin kusantarki, dan haka ko kinaso ko bakyaso sai na dinga sex dake koda wane lokaci"

A firgice Hassana ta miƙe tare da juyawa zata fice, da sauri ya fincikota ta faɗo jikinsa, cikin sauri ta kauce tare da sunkuyar dakai, hawaye na ambaliya a fuskarta, sam ta gaza haɗa ido dashi, sbda iya idanuwansa faɗar mata da gaba yakeyi,

Yayi kisa a gaya mata zai sauya mata gida wanda yafi wannan, sai ga Lulu nan, ashe tanata sallama basuji ba, ganin Hassana a durƙushe gaban Ala-Uddin Samir yasata wurga jakar kan gado, tana gyara sumar kanta da ta rufe mata ido, tare da riƙe ƙugu tace "Hub lafiya?"

"Mu Lulu wai dole sai ta tafi gida, naga kina buƙatar zamanta yasa nace "babu inda zata shine taketa kuka"

"Kai Haseeaina, wannan karon bakizo da niyar yin aiki ba, wancan karon ai kinkai shekara ɗaya da rabi, meyafaru kikeson zuwa gida, idan kuɗi ne baki dashi ki bani number account zansa miki"

Har Lulu tayi maganganunta ta gama Hassana ta kasa magana,

Sai ma miƙewa da tayi ta fice da gudu, tayi kuka sosai da ta koma ɗakinta, sbda ta kasa ɗaukar coffe ɗinma ta sha.

Hajara na kammala abincin tasa a faranti mai faɗi fari na tangaras, tare da saka cokula biyu, sbda haka Shahazad ya umarceta  tun farkon zuwanta,
Tana haurawa steps gabanta na tsananta faɗuwa,
Batasan takamaiman ɗakin da suke ba, dole ta fara nocking na Mona, cikin sa'a, yace "Yes"

"Na kawo abinci ne"

Hajara ta faɗa tana jiran abinda zece mata,

"Okay"
Ta shigo bakinta ɗauke da sallama, karfa idanunsu ya sarƙe ana juna,

Hajara tai saurin sauke idanuwanta ƙasa, ashe Shahazad yana kallonsu,

Bata jira an bata umarni ba, ta fice.

Shahazad yayi wani irin makirin murmishi,

Jikin Hajara na karkarwa ta ƙarasa ɗakinta, itakam gida take buƙatar zuwa, amma bataga fuskar magana ba, "gashi sai ya dinga yi mata mugun kallo ko meye dalili oho?"

Mona na kwance, duk irin kallon da Shahazad yake yiwa Hajara tana kallonsa,  murya wata iri tace "shin Hajar tayi maka wani abunne?"

"Ehhh, tana shiga gonar da ba Tata ba"

Shahazad ya faɗa cikin kakkausar murya.

"Dan Allah ka sassauta mata, tabani labarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login