Showing 36001 words to 39000 words out of 61953 words

Chapter 13 - MU RAYU A TARE Book Complete Romantic Hausa Novels by Mom Islam .txt

03 Dec 2025

1437

tsaye suka wuce gurin boka, wani ƙasurgumin jeji suka dinga tafiya, bakajin kukan komai sai na, tsuntsaye, riƙe da hannun juna suke tafiya har Allah ya kawosu gindin wata ɗirkekeyiyar bishiyar kuka, cikin ƙaraji da murya marar daɗin sauraro sukaji ance "ku koma da baya, sannan kuma bama son sallama"
Jikin Hajiya babba ya ɗauki kyarma, ta riƙe hannun umma gam tana cewa "Umma wlhi mu koma nikam bazan iya jure wari da tsawar nan ba"

Shiru Umman tayi bata kulata ba, har suka  iso gurin bokan suna tafiya da baya, kana Umma taja hannunta suka zube a ƙasa.

"An gaisheka boka an gaishe da madugu an gaishe da hatsabibi"

Cikin jin daɗin kirarin yayi murmishi jajayen haƙoransa suka baiyyana, sai kuma ya turɓune fuska kafin yace "baku da matsala da maganina, duk wanda muka bawa sai ya dawo yayi mana godiya, dan haka ku kwantar da hankalinku, meke tafe daku?"

Umma tace "wlhi kishiyar yarinyata ce ta mallake mijin bayajin maganar kowa sai Tata, sannan akwai wata maiyyar yarinya da aka tsinto, yana mugun sonta"

A gaggauce boka yace "yanzu me kukeson ayi mata?"

Hajiya babba da sai yanzu ta samu bakin magana tace "inaso ya zamo maganata kawai yakeji, sannan ya zamo danginsa suna sona sosai, ita kuma yarinyar inason a sanya ya mance da labarin ta, sannan ya dinga ji dani kamar tsoka ɗaya a miya"

"Duk wannan zancen da kikayi, anyi an gama, ɗan gajere na jinki shine zeyi komai, amma kafin nan munason gashin kan ita kishiyar taki, sai kuma farcen Alhaji shima muna buƙata, sannan munason rigar yarinyar guda ɗaya"

Jikin Hajiya babba na rawa tace "ni yanzu ina zan samu waɗannan abubuwan daka ambata?"

Cikin daka tsawa yace "idan har kinason aiki dole kibi hanyoyin dana faɗa idan kuma bakyaso ku ɓacemin anan"

Umma tayi murmishin yaƙe cikin sigar bada haƙuri da kwantar da muryar,
"Dan Allah boka kayi mana rai, saboda inganci aiki irin naka shiyasa muka taho gurinka domin ka taimakemu"

Boka ya sheƙe da dariya, kana yace "na gama magana idan an samu abubuwan dana ambata ko yanzu kuka kawo, yanzu aiki zai wakana"

Umma ta riƙe hannun Hajiya babba kana ta fiddo kuɗaɗe dubu ashirin ta ajiye a gabansa, kana suka miƙe, suna tafiya da baya-da baya har suka iso gurin mota.

Koda suka shiga mota, Hajiya babba ta rafka uban tagumi kana tace "Umma a ina zan samo waɗannan abubuwan da boka ya ambata?"

Umma tace "haba kekuwa sai kace ba mace ba, idan har ke jinina ce wlhi zaki iya, kidena bani kunya"

Hajiya babba tace "to shikenan Umma zan jaraba in gani"

Sai bayan isha'i sannan ta koma gida,lokacin Hakeem ya daɗe dayin barci, sai da ta leƙashi sannan ta wuce ta kwanta babu batun Sallah, sai ma tunanin "ta yaya zata samo abinda boka ya umarceta?"

Da wannan tunanin barci mai nauyi yayi awon gaba da ita.

Tun bayan tafiyar Huda daga gidan Ummanta, ta koma sarin kayan sawa takalmi da kayan koli hoda janbak da sauransu, sannan ana kawo mata kayan ɗaki irin kamar idan auren mutum ya mutu ta siya, sannan tana siyarda maganin mata sosai, dan yafi ƙarfi ma a sana'ar ta,
Safiyar Asabar, bayan ta kammala gyara gida tayi abin karyawa, ta ɗaga waya ta kirawo ƙawarta, abin mamaki kuɗin da Alhji Auwal ya bata ba ƙaramin bunƙasa sukayi ba,
Bayan ta ɗaga Umma tace "Maryamah ya zakiyi min haka, kawai jiya wani mutumi yazo hira gurina?"

Wacce Umma ta kira da Maryamah ta tuntsure da dariya kana tace "wlhi gani nayi Kun dace shiyasa nayi masa hanya"

Umma tace "to duk ma ba wannan ba, kinsan kuwa yace da wuri yakeson auren, nida nafi shekara goma ban waiwayi dangina ba, to yanzu me zance musu?"

"Hhh Gaskiya ƙawata akwai ki da tsoro, a tunanina zaki fara nemo mana hanyar jin daɗi da huta kawai sai ki dinga wani tunani can, ko ance miki masu ɗaura miki aure babu su ne a garinnan? "

"Gaskiya ne Maryamah Allah yasa mu dace, ya kamata kizo gobe ki rakani siyo kayan ɗaki tunda ya fara maganar bikin bayason ya wuce sati ɗaya"

Maryam tace "ai komai zai tafi dai-dai insha Allah kedai kici gaba da tsuma kanki da magungunan nan naki masu rikita kwanyar mazaje"

Umma tayi dariya kana tace "sai kinzo"

Ta katse kiran.
Jiga-jigan magunguna ta dinga ci gaba dasha, sbda ta gigita sabon ango.

Washe gari, suka shiga kasuwa suka siyo gado da katifa da drowa da madubi, duk da na hannu ne, amma basu wani ji jiki ba, a ranar aka jera komai, da yamma sai ga Mahabob da Huda sun shigo da sallama, baki washe Umma take amsa wa, kana ta shigar dasu ɗakinta, bayan sun gaisa, Huda ta ajiye wa umma sabulai da omo tace Mahabob ne ya siya mata,
Godiya Umman tayi masa kana ta sanya musu albarka, ta tambaye su ya iyayen nasu,

Sukace l"afiya lau"

Mahabob ya miƙe tare da cewa "Huda zan jira ki a waje"

"To" tace masa  kana ta mayar da hankali kan kayan ɗakin da taga an sauya"

"Umma masha Allah ɗaki yayi kyau"

Umma ta washe baki kana tace "wlhi Huda aure zanyi nan da kwana shida, shiyasa naketa gyara gida"

Huda tace "kai  Umma shine ko ki gayamin?"

"Huda ba gashi kin sani ba"
Daga nan suka ɗan taɓa hira, huda tayiwa Umma sallama suka wuce, da niyar sai ana biki saura kwana biyu zata zo ta kwana.

Alhaji Lukman ɗan tijara, sunan wanda Umma zata aura kenan,
Mutum ne mai arziƙin gaske, sai dai yanada wasu ɓoyayyun ɗabi'u, wanda ba kowa zai san da haka ba sai wanda ya zauna dashi,

Zuwa dare har Umma ta kwanta rurin wayarta ya tasheta, murya irin ta mai barci tace "ranka shi daɗe Barka da dare"
"Barka amaryar Lukman ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya"

Umma ta amsa da "lafiya lau Alhmdulilah"
"Dama inaso gobe idan Allah ya kaimu muje ki zaɓi irin gidan da kikeso ki zauna"

Da sauri ta tashi zaune, tare da cewa "ni harna gyara gidana wlhi"

"No ai bazai yiwu ba, dole a low cost zaki zauna G.R.A,"

Cikin farinciki tace "Allah ya kaimu goben"

Ya amsa da "Amin"

Alhaji Lukman ɗan tijara ya kalli abokansa dake zaune kusa dashi, kafin yace "mutuniyar ta faɗa"

Suka sheƙe da dariya mai sauti, ɗaya daga cikin abokansa yace "ya kamata ka sanar mata da larurar dake tare da kai, kar sai Kunyi aure a dinga kai ruwa rana"...!

Ayi  haƙuri da rashin posting da yawa Please

Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

59-60

Sam baiji daɗin maganganun nasu ba, sannan ya alƙawartawa zuciyarsa bazai baiyyana mata ɓoyayyen sirrin dake lulluɓe a zuciyarsa ba.

Washe gari, breakfast kawai tayi sai ga kiransa ya shigo wayarta, ring ɗaya ta ɗaga cikin salon bariki tace "amincin Allah ya tabbata a gare ka Alhajin Allah"

Sai da ya lumshe ido, kana ya shafa tumbinsa, kasancewar daga shi sai gajeren wando yake zaune, kafin yace "tare dake, idan kin gama shiryawa zanzo mu tafi, kiga gidan da yayi miki"

"Eh na gama"

Ta faɗa tana miƙewa tare da ajiye wayar.

Cikin sauri ta gyara ko'ina kana ta shirya cikin atamfa ɗinkin riga da zani sai mayafi data yafa, kalar adon atamfar wato pink color, kana ta maƙala ɗan kunne ta fito hannunta riƙe da key na gidan, kana ta fito waje, lokacin da take kulle gidan Alhji Lukman ɗan tijara ya iso, horn ya danna kana yayi murmishi, kallon Umma yakeyi kamar ƙaramar yarinya, sbda tashi ɗaya tayi haske tayi kyau, musamman ma da ta shiga shafe-shafe.

Itama murmishin tayi kana ta buɗe gaba ta shiga.

Suna cikin tafiya yace "zasu biya kasuwa domin suyi siyayyar kayan akwati"

Cikin jin kunya tace "Tom"

Kai tsaye suka wuce G.R.A dake ɓukur park, a bakin milk color ɗin get yayi parking kana suka fito, key ya ciro a aljihunsa sannan ya buɗe ƙofar suka kutsa kai ciki,

"Masha Allah gida yayi kyau"

Umma ta faɗa daga shigarsu,

"Sai ma kin shiga ciki"

Koda suka shiga cikin gidan, a kan ɗirkekiyar kujera mai numfashi Umma ta zube, tare da sauke ajiyar zuciya kana tace "Alhji bani da bakin yi maka godiya, sai dai ince Ubangiji ya ƙara arziki da wadatacciyar lafiya"

"Amin ai kin wuce hakan, a gurina"

Sai da ya zagaya da ita lungu da saƙo na gidan, kana ya tambaye ta idan akwai abinda beyi mata ba ta faɗa,

"Yayi komai gunin sha'awa"

Umma ta faɗa jiki na rawa.

Daga nan suka wuce kasuwa, ya kashe mata kuɗi sosai musamman gurin siyan zannuwa da turaruka.

Daga nan suka wuce Shan Rufaida yoghurt, koda sukaje Umma bata wani yi kauyanci ba, saima burgeshi da take dad'ayi,

Daga nan ya dawo da ita gida, kaf kayan da suka siyo harda akwatunan yace ta wuce dasu gida.

Bayan ya ajiyeta ya wuce.

Tana shiga gida ta nemi guri ta zauna tare da ƙarewa kayan kallo.

Jiki na kyarma ta ɗauki waya ta danna number Maryamah, kamar jira take, ring ɗaya ta ɗaga tare da cewa "sai kuma na jiki shiru"

Umma ta kwashe da shewa kana tace "hamm Alhji ya kashemin kuɗi, da kinada halin zuwa da kinzo kin kashe ƙwarƙwatar ido"

Maryamah ta gigice tare da cewa "wlhi ganinan zuwa ko zan sami wani abu"

Lokacin da Maryamah tazo ana kiran sallahar azhar, ta samu umma na sallah, bayan ta idar ta shafa adu'a kana ta kalli Maryamah tayi murmishi kafin  tace."ƙawata kwaso kayan a kan gado"

Jikin Maryamah na rawa ta kwaso kayan, tare da cewa "kai-kai ƙawata Allah ya yanke miki wahala, gaskiya irin waɗannan alhazan abin riritawa ne, gaskiya ki riƙe shi gam ƙawata"

Umma tayi murmishi kafin tace "ya hutar damu maganar kayan ɗaki wlhi gida yayi kyau"

Maryamah tace "haka akeso amma a shawarce ya kamata ki je garinku saboda kinsan aure ba abin wasa bane, dalilin...."

Cikin daka tsawa, Umma tace "bakisan komai a kaina ba bakisan kowa nawa ba, dan haka bana buƙatar kowa ya sani"

"Haba Umman Huda, ya ina baki muhimmiyar shawara kina kaucewa, bakya tunanin ta dalilin ƙaryar waliyai da zakiyi masa idan ya gano gaskiya abin bazaiyi kyau ba?"

KANO•• Ƙauyen ƴan yakuba

Garine wanda ya kasance ƙauye sosai, yawancin abinda sukeyi  shine noma da kiwo, kowanne magidanci taƙamarsa noma da kiwo,
Gidan malam Ado, gidane mai ɗauke da mata biyu, koda yaushe basu da aiki sai masifa, duk da dukkansu babu wacce ta taɓa aihuwa, amma masifa taƙi ƙarewa a cikin gidan,

Hansa'u itace babba sai  Saratu ita kuma itace amarya, hansa'u ta kasance mace mai haƙuri da kawaici, yayinda Saratu ta zamo gagararriya a cikin gidan, shekararsu biyar da auren Saratu, ya shawarcesu akan zai koma zuwa Jos cirani, dukkan su sunyi na'am, Wase Gari kuwa Saratu taje gidansu ta sanarwa mamanta maganar da malam Ado yayi, cikin rashin amincewa da tafiya da Saratu, tace "wlhi da ke zai tafi, ƙarya ne, tashi muje gurin baba insha a anyi an gama"

Saratu ta miƙe tare da yafa zanin da ta luluɓa kana suka wuce gurin malam wato baban mamanta, suna zuwa maman nata ta isar masa da duk abubuwan da suke so, kana suka kwashe ƙarya da gaskiya suka gaya masa,

Yayi musu alƙawarin kawar da hankalin jama'a akan tafiyarsu, sannan aka sanya masa tsanarta a zuciyarsa. "ammafa tanada juna biyu harna wata uku"

Malam ya faɗa yana kallon Saratu, Saratu ta zaro ido tare da dafe ƙirji kana tace "wlhi sai na kashe abinda ke cikinta ko ta haisheshi"

Daganan suka dawo da ƙulle-ƙullen magunguna, Saratu ta dawo gida, bayan sati ɗaya, abubuwa suka fara faruwa, kama daga kaf danginsa abokan arziƙinta da ƴan uwanta duka suka tsaneta, ko ina Hansa'u ta shiga sai dai a dinga kyararata tare da hantara, hakan yasa ta dena fita ko ina, sai alwalah da wanka ne yafe fito da ita, abinci kuwa sai dai idan almajiri ya shigo ne saratu zata zuba abincin ya miƙa mata,

Sosai Saratu ta zamo tauraruwa mai haska ko ina, duk wannan gwagwarmayar da akeyi, mahaifiyar Hansa'u tayi tafiya garinsu sati Uku kenan bata gida, bayan ta dawo ta samu mummunan labari game da ƴarta Hansa'u, itakam asirin beyi tasiri a kanta ba, sbda tayi kuka kamar me,

Kwanan mahaifiyarta biyu da dawowa su Saratu suka tafi Jos,

Koda ta kawowa Hansa'u ziyara ta sameta tana kuka, ta tambaye ta lafiya ta sanar mata su malam Ado sun tafi sun barta, tana kuka take maganar,

Maman ta dinga rarrashinta tare da  sanar mata, inhar Allah ya sauke ta lafiya, bayan ta yaye zata bashi yaronsa, idan namiji ne, idan kuma mace ce Tom"

Da wannan shawarar suka koma gida, mamanta taci gaba da taimaka mata.

Sun sauka lafiya a Anguwar Dogon agogo, dama ya riga da ya kama gida, kai tsaye shiga sukayi tunda mukulin gidan yana hannunsa, sukaci gaba da rayuwa cikin so da ƙauna, baya ganin lefinta sam ko me tayi masa, sannan ko aiki yaje ya dawo zai zazzage mata aljihu su raba kuɗin dai-dai...!

Dan Allah ayi haƙuri zafa mu shiga typing da yawa🤣insha Allah amman yau anguwa naje, sannan ina jiran shar'i..

Ayi haƙuri da typing error

Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam


Book1

61-62

Acan ƙauye Hansa'u na aihuwa aka raɗawa yarinya suna Huda, wato sunan mahaifiyar malam Ado, shekarar Huda ɗaya a duniya Hansa'u ta rasu, sakamakon ciwon nono wanda ya zame mata cutar ajali,

Sai da akayi kwana bakwai sannan malam Ado yazo gaisuwar rasuwa, mahaifiyar Hansa'u ta damƙa masa huda a hannunsa, yayi magiya akan su barta zai dinga aiko da kuɗi, ai mahaifiyar Hansa'u taƙi yarda, washe gari dole ya dawo da Huda Jos.

Saratu na murna mijinta ya dawo, kawai ta hango yarinya a jikinsa, cikin yamutsa fuska tace "mezan gani ƴar wa ka kwaso mana?"

A tunaninsa murna zatayi tunda bata taɓa aihuwa ba, sai yaga akasin hakan, ta murtuke fuska tana tuhumarsa,
"Yarinyar Hansa'u ce da ta mutu ta bari"

"Toni ina ruwana da mutuwarta wannan kai ta shafa, nidai kasan ba ƴar raino bace ko?"

Cikin lallashi ya siye zuciyarta tare dayi mata alƙawarin siya mata kayan ɗaki,

Haka huda ta taso cikin rayuwa marar daɗi ga tsangwama  da kyara da duka, har Allah yasa ta girm, tun tana da shekaru goma Saratu take ɗora mata tallah, Huda nada shekara goma sha daya malam Ado ya rasu, yafuta gurin aiki sai dawowa akayi da gawarsa,

Saratu tayi kuka sosai, duk da bawai yana nunawa Huda kulawa bane, amma hakan bai hanata yin kuka ba.

Bayan rasuwarsa, Saratu taci gaba da ɗorawa huda tallar shinkafa da miya, a haka har ta ƙara shekaru biyu, shine har kawo yanzu da Allah ya haɗata da Mahabob.

Back to story

Bayan kwana uku da yin maganar sistern Batool, Abba ya kira Mahabob a waya, kasancewar lokacin 12:pm yana barci bai ga kiran Abba, wayar sai ringing take, kasancewar a silent take.

Sai 12:20pm ya farka, ya kunna haske wayarsa, ganin miss call ɗin Abba hankalinsa ya tashi, ɗaurayo baki kawai yayi ya fito zuwa part ɗin Batool.

Da sallama ya shiga, suna parlo Abban na breakfast, Batool ta amsa fuska a sake, kana ya nemi guri ya zauna, cikin girmamawa yace "Abba kayi haƙuri lokacin da ka kirani ina barci"

Sannan ya gaishe da Batool ya gaishe da Abban,

"Babu damuwa, dama inason in sanar maka nayi maka mata ne, duba da yabawa da hankalinta da nayi sbda yarinyar nitsatsiyace, kuma nasan bazaka bani kunya ba"

Sam zancen beyiwa Mahabob daɗi ba, kasancewarsa mai biyayya yasa ya kawar da damuwar da takeson lulluɓe masa fuska, yai ƙoƙarin aro murmishi kana yace "Abba godiya nake"

Abba yace "wato Mahabob nidai babu abinda zance dakai sai godiya, sbda biyayya kam kanayi min, hakan yasa na baka kyautar Company ɗina na cikin gari"
Batool ta zaro ido ba tare da kowa ya sani ba, sannan tace "godiya yake Alhaji"

Abba ya ƙara da cewa "yarinyar ƙanwar Batool ce, sannan yau zatazo gidannan sai ku gana"

"Toh Abba"

Mahabob yace.

Kafin Abba ya idda magana Batool ta haɗowa Mahabob shayi mai kauri da bredi da wainar kawai kana ta ajiye masa cokali mai yatsu,

Ruwan shayin kawai ya iya kurɓa kana ya ajiye cup ɗin bai shanye duka ba, sannan ya miƙe yana cewa "Abba godiya nake"

Cike da so da ƙaunarsa Abba yace "Nine da godiya Mahabob"

Bayan fitar Mahabob Abba yace "idan har za'a dinga samun ƴa'ƴa irinki to wlhi kaf zuri'arku abin a aura ne"

Batool tayi dariya tare da rufe fuska,
Daga nan Abba ya miƙe, tare da kulle ƙofar part ɗin su ya dawo gurin Batool,

Wani irin mayataccen kallo yake mata wanda yasa ta gane buƙatarsa, cikin sigar soyayya ta taho gurinsa tare da ɗaga rigarsa ta tura hannunta kan nipple ɗinsa ɗaya tana murzawa da hannu ɗaya kuma yana bakinta tana jujuyashi a hankali, ajiyar zuciya ya dinga saukewa mai cike da sha'awarta, daga ƙarshe dai ta cire masa rigar gaba ɗaya, shikuma ya rungumota ya tura hannu ƙasan mararta, nidai nace bari mu barsu su shaƙata muje gurinsu Amani muji ya ake ciki.

Jiki a sanyaye Mahabob ya ƙarasa part ɗin su Amani, yana shiga ko sallama babu,
Cikin yanayin damuwa ya zube akan kujera tare da dafe kansa, yana mai runtse idanuwansa.

Babu kowa a parlon hakan ya bashi damar yin tunani.

Yayi zurfi a cikin tunani sai ga Amani ta fito, Aseela ta fito Huda tabiyo bayansu, cikin yanayin damuwa Amani ta taho da sauri tare da cewa "bro lafiya kuwa?"

"Babu lafiya sis"

Hankali a tashe suka zube kan carpet tare da cewa "waye bro meke faruwa?"

Aseela da Amani suka tambaye shi.

"Abba ne yakeson yimin aure, wai harya zaɓamin mata ƴar uwar Momy"

Amani ta zaro ido kafin tace "aure kuma? sannan ƴar uwar matarsa?"

"Never wlhi karka amince"

Huda da sai yanzu tayi magana tace "haba Aunty Amani duk wanda ya saɓawa iyayensa wuta zai shiga, ya kamata yayiwa Abba biyayya"

Jiki a sanyaye Aseela tace "hakane bro kayi haƙuri kabi umarnin Abba"

Kamar da wasa, sai ga wasu siraran hawaye sun kwaranyo ta fuskar Mahabob, ya share su da tafin hannunsa kana ya miƙa tsaye, yana ajiyar zuciya.

Dukkansu jikinsu yayi sanyi matuƙa, idan ka cire Huda da take ganin gata Abban yayi masa,

Sai da Abba ya samu nutsuwa kana ya je toilet yayi wanka, ya fito ɗaure da towel, kana ya goge jikinsa ya shafa mai, sannan ya zauna akan bed, gefensa ya kalla yayi murmishi, ya ɗauki kayan da Batool ta ciro masa ya ɗora kan cinya, tare da ajiye hular a gefe.

Bayan ya gama shirinsa, lokacin har Batool ta fito daga wanka itama ta shirya cikin abaya dark blue tayi mata kyau sosai, ya ɗaura agogon hannu kana ya miƙe tare da rungumarta, a tare suka taho bakin ƙofa hannunta riƙe da hular Abba, tasa masa tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login