Showing 3001 words to 6000 words out of 15803 words
Chapter 2 - SILAR MUTUWA FREE PAGES by Zahra Royal Star .txt
ganinta yadda ta nuna kwata-kwata bata tsoron sa ko shakkar sa dama macen daya ke son samu kenan wadda bata shakkar kallon idonsa tayi magana wadda zata kama kanta wadda take da class shi kansa sai da ya jinjina ma Surayya yadda duk da tana mahaukacin sonsa bata fito ta sanar dashi ba har sai da yazo da kansa ya furta harya nemi auranta..............✍️
*ZAHRA ROYAL STAR CE*
Share fisabilillahi🥰🙏
*💔🧟♀️☠️SILAR MUTUWA🧟♀️☠️*💔
(Horror Story)
ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*
PAGE 3️⃣➡️4️⃣
Wani irin jini kalar ruwan ganye ke zubowa tana lashe baki, nuna sa tayi da hannunta wani farin haske ya fito ya shigi Goga wata irin zabura yayi yana makyarkyata kamar wanda wutar neper ta kama sai da taga ya wahalu sana ta saki wata irin dariya mai k'arar gaske sana ta b'ace b'at sai dariyar da tayi ce ta karad'e lungu da sako na wajan wata irin amsawa kuwwa dariyar ke yi kamar yanzu ne take dariyar.
Su Goga kuwa ganin sun tsira ba wadda ya tsaya d'aukar wanni abu suka arce da mugun gudu yadda kasan ita ce ta biyo su a baya.
Basu sauka a ko ina ba sai a wani rub'ab'b'an gida wadda suke kwana kai daka kalle su kasan sun jiga tu wani daga cikin su ya ce "kai Oga na kasa tuna miye ma ya faru a wajan shin muryar wacece muka ji ne?", Kowa shuru yayi dan kwata-kwata kamar anyi masu yasa a cikin kwanyarsu sun kasa tuna shin muryar wacece ma suka da ainahin miye ya faru abinda baza su manta dashi ba dai shine sunsan sun tare wata budurwa ita kanta sun kasa tuna fuskarta, share abun sukai duk dukan da suka sha suka fara jinya ba k'aramar jinya sukai ba suna suka wartsake suka koma fagen shashancin su.
A wajan su Surayya kuwa tsintar kansu su kai a gidan da suka kama na wajan makarantar a cikin d'aki sai sharar bacci suke koda suka farka basu kowa komai a ransu ba dan kwata-kwata suma ba'a basu damar su tuna wani abun ba.
Zaune Surayya take suna waya da Ammee tana mata fad'an danmi bata Kira su ba data isa ta sanar dasu isarta gashi kinsa mijinki cikin damuwa, dan kuwa Surayya nada aure karatu ne ya kawota an d'aura auran ne a bisa sharad'in saita gama karatu zata tare.
Zunb'uro baki Surayya tayi ta ce "Ammee amma ba sai ya kira ni ba sai yaje ya data miki hankali yana ganin ke kad'ai kika rage min Allah sarki Daddy na Allah ya jik'an sa da rahma ina kewar Daddy", ta idasa maganar wasu hawaye na neman kumce mata ita kanta Ammee cikin raunin murya ta ce "kin ganki ko zaki sa zuciyoyinmu karyewa abinda nake so dake yanzu shi SADEEQ mijinki yasa an samar mai aiki a nan school d'in taku zai rink'a koyarwa har ki gama dan saboda ke yasa a samar masa aikin nan", cike da kid'ima Surayya da d'an kishi-kishi ta ce "amma Ammee miye da sai yazo nan wallahi Ammee karki ga school d'in duk Arna sunfi yawa ga y'an mata wadda kwata-kwata basu da kintsi bare kamun kai d'ai-d'aiku ne zaki ga yarinya ta zauna tayi abinda ya kawo ta in...... Kamin ta idasa maganar Ammee ra tare ta da cewa "kinfa San waye mijinki kinsan yafi k'arfin ya zauna yana koyarwa kinsan waye shi a k'asar nan kema Allah ne ya inganta rayuwarki kuma ya dasa masa soyayyar ki kin manta irin wahalar da kika sha na soyayyar ku aka rasa wazai furta yana san wani cikin ku shi girman kai kema haka duk da ya kasance d'an uwa a gare ki duk sadda yazo gidan nan danke yake zuwa amma saiya wani share yayi kamar badan ke yazo ba, to taya za'ai mai irin wannan hali kike zaton ya kalli wata mace yadda ma yake sonki ke kinsan hakan ma bazai yuwu ba", kunya ce ta kama Surayya yadda Ammee ta fahimci kishi ke damunta Ammee ta k'ara mata fad'a kan cewa "Surayya ki kama kanki karki ga cewa ai gaku waje d'aya ki basa kanki tun kan a kaiki d'akinsa ki kankaro ma kanki daraja again kuma ki kama kanki Kinga ke matar aure ce koda yake tunda Sadeeg na kusa nasan shi shima da d'an banzan kishin tsiya dole nasan zuwansa sai kafa miki doka ni wallahi yayi min dai-dai ma daya biyo kin", ta idasa maganar tana sauraron yadda Surayya ke zuba shagwab'a ita fa za'a takura mata, bayan sunyi sallama da Ammee .
Su Nawwara dake yankan kayan miya sun d'ora abinci Bilki ta ce "ai wallahi Ammee gaskiya take fad'a miki ni Sadeeg yamin dai-dai daya biyo bayanki ni dama nasan Allah tsawon shekaru bazai iya hakurin rashinki ba bare baya ganinki", Surayya ta d'an gyara zama akan katifar da take ta ce "ni ba wannan ba kawai dai school d'in nan akwai k'ura dan na rantse duk wacce ta shiga harkar miji na kunsan Allah zan iya mata koma miye indai akan Sadeeg ne dan haka za'a sha kallo wallahi", ta idasa maganar tana tab'e baki Nawwara ce ta ce "hmm shi kansa saiya miki shamaki da kowanne d'a namiji ko gaisawa kuwa wadda shi yama fiki kishi GARKUWA kai zafa asha kallo wani ma tab'a zaton zaiga Garkuwa da idonsa ba amma ta dalilinki zai gansa duk Najeria fa ansan mijinki Garkuwa ai wallahi Surayya ki k'ara godema Allah, ai kawai dai Allah ya kyauta ni ban tab'a ganin soyayya irin taku ba".
Washe gari tun wajan k'arfe 8:00am dai-dai suka fita lecture da yake duk abu d'aya suke karanta suna cikin class kowa na harkar gabansa ana jiran Malamin da zai shigo na gaba wasu na wajen class ba zato ba tsammani wani arnan k'amshi yayima gaba d'aya class d'in sallama duka mutanan dake ajin har rige-rigen waigawa suke suka wannan wane sabon Malami ne aka kawo musu, ita kuwa Surayya da tun isowar k'amshin a hancinta tasan waye zuciyarta sai bugawa take jinin jikinta na gudu lumshe idonta tayi tana da tabbacin kenan shi ne wadda zai d'auke su English tab ta tab'e baki tana bin y'an matan ajin da kallo yadda ko wacce har suna rige-rigen furta "WOW", kai bama mata ba hatta maza sai da suka sarama Sadeeg.
Tafiya yake cikin k'asaita harya isa gaban allo tsaya yayi yana juyowa gaba d'ayan sa gaba d'aya y'an matan dake ajin sai da sukai MUTUWAR zaune d'an kuwa kyan sa da kwarjininsa ba k'ara min tafiya yayi da imaninsu ba sanye yake da wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya da hular zanna bukar dake zaune a kansa dogo ne ba irin sosai d'in nan ba yana k'irar k'arfi daka kalli damtsin hannunsa kasan cewar yana motsa jiki gaba d'aya jikinsa a murd'e yake yana da yawan gashin gira girarsa har had'ewa take idonunsa kuwa hmmm wai wai wai Allah yayi halitta tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan halitta mai tsananin kyau da kwarji idonsa daga cikinsa kalar ruwan k'asa ne sosai har wani shek'i suke fari kal dasu in aka zo fagen hanci kuwa ba'a magana dan hancinsa dogo ne daga k'asansa ya d'an bud'e kad'an saiya k'ara ma fuskar sa cikar zati idan aka zo wajan bakinsa kuwa kai ya Allah ba'a cewa komai bakinsa mai zanan love ne d'an k'ara mi dashi daga saman lab'b'ansa sai ka rantse yasa janbaki ne amma ainahin kalar su ce jawur dasu.
Babu abinda y'an matan ke furtawa sai Masha Allah ko wacce tana addu'ar inama ace wannan bawan Allah ya zamo miji a gare ta ai basu k'ara shiga wani shauk'in ba sai da suka tsinkayi muryarsa mai matuk'ar zak'in gaske da dad'in sauraro turanci yake yadda kasan na k'asashen k'etare suman zaune sukai jin irin turancin dake fitowa daga bakin sa da k'arin mamakin wai shi zai d'auke su English basu k'ara shiga tsananin mamaki sai dai sukaji sunan sa Ahmed Sadeeg Garkuwa, waye bai san Garkuwa a Najeria ba Garkuwar tallakawa tun sunan Mahaifinsa ne tun asali Mahaifinsa mai tsananin taimakon na k'asa dashi ne shi yasa mutane suka sa mai Garkuwar talaka Mahaifinsa mai kud'in gaske ne shi kad'ai Allah ya basa tun yana k'ara mi iyayansa suka rasu baki d'aya y'an uwa sukayi ma dukiyar sa caaa kowa yana buk'atar ace shi zai gaje ta yasha wahalar rayuwa wajan dangi dan sai da suka ga dukiyar ta tafi k'arewa suka guje shi sai dai Allah mai iko ne sadda Sadeeg zai taso ya samu sukula ship aka d'au nauyinsa zuwa k'asar India a Indiar ma yasha wahalar karatu dan kuwa akwai wani d'an k'asar daya fahimci Sadeeg Garkuwa nada mugun k'ok'ari ya sako shi gaba tunda Sadeeg yana yo first class a school d'in kamin zuwan Sadeeg Garkuwa shike yo first class hakan yasa hassada ta shiga tsakanin su ya hassala har mahaifinshi zuwa yayi mai gargad'i mai zafi wadda yasa ba k'aramar rigima suka sha ba har Sadeeg nada zafin zuciya Allah yayosa da shegen k'arfi hakan yasa yayi ma y'an baradan sa mugun duka.
Suna gaf da gama karatu aka kira Sadeeg kan cewa za'a basa aiki yana gama karatun sa kasancewar shi ke yo first class a inda ya ce shi bazai amshi aikinsu ba sai ma shine zai basu aiki dan shi ya taso da hazak'ar k'irk'irar abu su kansu turawan sunyi mamakin jin furicinsa yana bak'ar fata sai girman kai ya ce musu shi ba girman kai yake nuna musu ba sai gaba tar masu da wani Application daya k'irk'ira da kansa sunyi mamaki d'an Najeria ne zai iya k'irk'irar wani application, ai basu k'ara tsure da tsananin mamaki ba sai da ranar da zasu kammala school d'in aka tara duban jama'a a yadda ya gabatar masu da irin app d'in daya k'irk'ira sunyi mamaki wadda har yasa suka kasa cewa komai ba k'ananan kud'i ya samu ba wani ma kyauta zai bashi inda wadda suke takun saka dashi shi kansa sai da ya jinjina masa shi da Mahaifinsa ko ina basa girma ake cikin k'asar India bai baro k'asar India ba sai da ya bud'e kanfani har uku wadda yake mallakin sa sana a dawo Najeria to a k'asar sa ma bai zauna nan ba sai da ya tabbatar ya bud'e kanfani har hud'u wadda suka fi na Indiar ma ya d'auki talakawa wadda suke neman aiki inda sunan Garkuwa ya k'ara binsa duk inda ya zaga Garkuwar talaka hatta lambar motarsa Ahmad Sadeeg Garkuwa talaka ba inda ba'a sansa ba a k'asa Najeria harma da k'asashen k'etare y'an mata kuwa suna mahaukacin son sa sai dai akwai shi da kwarji bare wata ta kawo mai wargi a sadda ya fara ganin Surayya yaje kaima Ammee ziyara dan ya kasance d'an uwa ne a gare su ta b'an garan Uban Surayya ba abinda ya fara had'a su sai rashin jituwa shi kuma tunda ya fara ganinta yadda ta nuna kwata-kwata bata tsoron sa ko shakkar sa dama macen daya ke son samu kenan wadda bata shakkar kallon idonsa tayi magana wadda zata kama kanta wadda take da class shi kansa sai da ya jinjina ma Surayya yadda duk da tana mahaukacin sonsa bata fito ta sanar dashi ba har sai da yazo da kansa ya furta harya nemi auranta..............✍️
*ZAHRA ROYAL STAR CE*
Share fisabilillahi🥰🙏
*💔🧟♀️☠️SILAR MUTUWA🧟♀️☠️*💔
(Horror Story)
ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*
PAGE 5️⃣➡️6️⃣
Dalla-dallah ya fara masu lasin cikin turancin sa mai dad'in sauraro harda hausa yake had'awa domin afi ganewa.
Yana gamawa ya jefo wata tabbaya shuru ajin yayi baka jin ko tari tsit kallon y'an ajin yake da idonsa masu matuk'ar shek'i da hannunsa yayi manuniya ya ce "you", ya nuna Surayya wani irin rass taji gabanta yayi wata irin bugawa dama tasan za'a rina nunawa zaiyi kamar bai tab'a ganinta ba da harshan turancin ya ce ta fito gaban allo jikinta ne ya fara rawa da kyar ta fito idon mutane yayi mata caaa hararara kawai take aika mai baima san tana yi ba abunda ya k'ara bata mamaki data tsinkayi muryarsa wai minene sunanta wani miyau ta had'iye a hankali ta basa amsa wata tabbaya ya jefo mata ya ce ta juya taba y'an class amsa.
Kowa ita yake sauraro jikinta inba kyarma dan yawan idonun mutane yayi mata yawa wasu ma haushinta suke ji har sun fara kishi a kanta ko wacce tasu ita aka tabbaya koda bata sani ba ai ko sunan ta ya sani tayi sa'a.
Wasu basuyi tsammani ba suka fara jin wani daddad'an turanci har yana so yafi nasa zaki, kunsa muryar mace sosai take bayani wadda tasa gaba d'aya mutane suman zaune harda shi kansa Ogan shi dama yana so yaga shin tana maida hankali tunda a secondary kokuwa.
Tana idasawa aka fara tafi da yawan mazan ajin ta birgesu tana kallonsa da idanuwata ita masu girman gaske wani murmushi ta jefa mai wadda ya kusa sashi zuzucewa da sauri kuma ya maze kamar bashi ba ta koma ta zauna tana sauke wata irin ajiyar zuciya yana gamawa ya fice yadda kasan ya tafi da zuciyar y'an matan ajin wasu yana fita kamar jira suke suka fara zancan sa.
Cike da jin d'an haushi Surayya taja su Nawwara suka fice daga ajin domin zuwa masallaci yin sallah domin k'arfe d'aya har tayi ta gaji dajin yadda ko wacce banza ke zuzuta mijinta zuciyarta har wani motsawa take.
Suna fitowa daga masallaci bayan sunyi sallar taji wayar ta na k'ara d'akkowa tayi ganin sunan Hubby yasa ta murgud'a ma wayar baki kamar yana gabanta su Nawwara kuwa sai dariya suke mata kamar baza ta d'au wayar ba tana gaf da tsinkewa ta d'auka ta k'ara a kunne daga sallamar da tayi bata k'ara cewa komai ba tana sauraron muryarsa mai sata shiga wani shauk'in k'aunarsa taji ya ce "ina office kizo ki same ni", turo baki tayi cike da shagwab'a ta ce "amma lecture zamu shiga fa", cikin harshan turancin ya ce mata "bana son gaddama fa kin sani zan iya zuwa har class d'in naku na d'auke ki Allah kinsan zan iya ko in......kamin yama idasa maganar da yake son fad'a ta yanke wayar tana nufar office d'in nashi a zuciya kuwa cewa take kad'an daga aikin Sadeeg Garkuwa tsaf zai iya barinta da jin kunyar jama'a, sai da tayi tabbaya taje ga office d'in dan iyanzu ba wadda bai sheda wanzuwarshu a school d'in ba yadda aka basa babban matsayi shi kansa Office d'in nasa abin kallo ne dan sauran Malamai ba k'ara min ji suke dashi ba har cewa suke su ai gaba ta kai su ko banza makarantar su ta kafa tarihi na zuwan Garkuwa cikinta, ba yadda ba taiba su Nawwara su rakata sukak'iya suka ce "ina zamu shiga tsakanin mata da miji yana buk'atar ganinki ne shi yasa sai kin dawo", cike da jin haushi tabarsu kamar ta d'ora hannu akai ta zunduma ihu haka take ji.
Shigarta Office d'in abinda tagani ne yasa taja turus ta tsaya ganin wata mace tasha wasu shegun kaya daga gani ma wannan ba dai d'aliba ba sai dai ko Mlm ce wani irin kishi ne ya rufe Surayya duk da tasan halin mijinta kuma taga shi Sadeeg bata ita yake ba nunwa ma yayi kamar ba kowa a gabansa, aikin gabansa kawai yake ganin shigowar ta yasa ya tashi kad'an ya saki fuskarsa cikin harshan turanci ya ce "Dr Zuby zaki d'an iya bamu waje nida halali na", wani irin dammm dumm taji gabanta ya fad'i juyowa tayi tana kallon Surayya, mi yake nufi ne ba dai matarsa yake nufin wannan y'ar abar ita ce ba kenan duk burin data ci ya rushe kenan.
Tashi tayi jiki ba kwari ta fice daga Office d'in zuciyarta na zafi.
Tana fita Surayya ta juya cike da fushi zata fice tana turo baki da sauri ya sha gabanta yana turata jikin bango kallonta yake da rikitattun idonsa k'asa tayi da kanta dan kwata-kwata yau d'in wani irin kwarjini yayi mata zata bud'e baki tayi magana tana faman turo baki bata zata ko tsammani ba ya had'e bakinsu waje d'aya jikinta ne ya kama kyarma kamar wacce aka jonama lantarki kwata-kwata ta kasa d'aukar abun saboda bata tab'a yi ba ganin yadda jikinta ke kyarma yasa a hankali ya zare bakinsa cikin tana ya juyawa ya koma kan kujerar dake office d'in yana cewa "hukuncin ki kenan idan kika k'ara min kaddama ban sallame ki zaki fita", ya idasa maganar yana shar mur, irin baya son raini yadda kasan bashi ya gama kiss d'in ta ba.
Cikin sanyin jiki take binsa da kallo ganin yana nuna mata kujera yasa dole ta zauna a hankali kamar wadda aka cirema lakka k'asa tayi da kanta can ta tsinkaye muryarsa yana cewa "ki tabbatar gobe ki sanyo hijab inda hali ma kisa abun rufe fuska bana son kina sa gyalan nan kin sani, dan haka daga yau bana son in k'ara ganin wani wai shi gyale a jikinki kinji?", Da sauri da d'ago tana kallonsa cike da mamaki tasan za'a rina ita wallahi takura mata zaiyi zuwanshi school d'in nan haba ta idasa maganar a zuci can taji muryarsa ya ce "zan takura miki kike cewa ko?", Da sauri ta k'ara dubansa cike da mamakinsa wai shi kamar wani aljani.
Ganin kallon da take mai yasa yashi yin wani shegen murmushi na gefen baki wadda ya k'ara ma fuskarsa tsananin kyau ya ce "zaki iya tafiya ba abinda kuke buk'ata na anfani keda k'awayan naki?", Tashi tayi dan dama a k'agare take tana cewa "a'a babu abinda muke buk'ata akwai komai idan ma akwai wani abun zan sanar da kai", tana maganar tana niyar barin Office d'in tana gaf da ficewa ya ce "daka