Showing 12001 words to 15000 words out of 15803 words

Chapter 5 - SILAR MUTUWA FREE PAGES by Zahra Royal Star .txt

06 Jul 2024

3842

saina shiga wallahi had'uwa irinta Garkuwa ba abinda bazaka iyayi kan wannan bawan Allan ba kai ai Allah ya zuba halitta ga wanga mutune inji sakwatawa, wai ga kud'i ga kyau komai ya had'a ai dole ayi hauka a kansa ita kuma waccar banzar Surayyar harta isa ta ce ita d'aya keda shi ina tama shirya yanzu aka fara wasan muda ita", da sauri Zuby ta ce "kware kuwa hakane babu abinda bazaka iya ba akan irin su Garkuwa yanzu yaushe zaku raka ni wajan bokan a shirye nake nayi komai na kashe ko nawa ne", da sauri cikin k'awayan nata guda biyu wata ta ce "ai ko yanzu inkin shirya kina da uwar kud'in ki zamu iya zuwa", da sauri suka mik'e Zuby na cewa "ku tashi mu tafi da zafi-zafi ake bugun k'arfe ai ba zama inta kwana a zaune ni a tsaye na kwana tunda ta bari na kyalle ido naga Garkuwa hmm kota halin yaya saina same shi"...........✍️








*ZAHRA ROYAL STAR CE*






Share fisabilillahi🥰🙏
*💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔
(Horror Story)









ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️










*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*














*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*






PAGE 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣




Kamin sunyi wani yink'uri ya kaima d'aya daga cikinsu cafka ya kada shi k'asa yana wani irin gurnani yana niyyar kai mai cizo kokowa suka farayi da sauri Goga ya d'auki wani itace ya kaimai duka a kai.




Sakinsa yayi da sauri yana fad'uwa k'asa ya rik'e kansa yana sakin wata irin k'ara da gurnani.




Da sauri Goga yaja d'ayan suka fara gudu ganin yadda ya tashi kamar ba'a kaimai duka ba ya fara binsu a bayansu yana shin-shine shin-shine gudu suke suna waigen bayansu ganinsa suke kamar walk'iya yana matsowa gare su.




Goga ne ya saki wata irin k'ara yana zubewa k'asa k'afarsa ya kama ganin wata irin k'aya mai tsinin gaske ta cakesa a tafin k'afarsa harta b'illo saman k'afar tasa da sauri sauran mutanan sa suka matso gare sa suna tabbayar lafiya yayi sauri su cigaba da gudu dan gaf yake da isowa gare su.




Da kyar Goga yasa hannunsa ya runtse idonsa yana cire k'ayar da sauri wata irin k'ara ya saki ta azaba wani irin zafi yake ji har tsakiyar kansa.




Ba yadda ya iya haka suka tashi yana d'angyashi suka cigaba da gudu.




Jan birki su kai su dukansu ganin gabansu wani irin ruwa mai shegen yawa ya tare musu hanya ruwan duk ya cinye hanyar ruwan sai yayi girman wani garin waigawa su kai ganin ba kowa dage binsu abin mamaki ma sai suka tsinci muryar wadda ya zama horror ya dawo dai-dai yana cikinsu cike da tsananin tsoro da mamaki suka bisa da kallo kauda mamakin su kai ai babu abinda ba zasu iya gani ba.




Da saui Goga ya ce "ga mai buk'atar shan ruwa yayi maza yasha kamin mubar wajan nan dan ruwan nan yadda yake da yawan nan zai iya anbaliya ya cinye mu gaba d'aya", ai da sauri suka duk'a domin shan ruwan sai dai mi ruwan ne ya zama wani irin jini mai kaurin gaske da kakai hannunka jini ne zaka d'ebo inka cika matsawa jikin ruwan kuwa ji zakayi kamar za'a kawoka ciki, da sauri suka tashi suna zare ido y'an hanjin cikinsu na hautsinawa iyanzu da yawa cikin su sai tsinewa Goga suke suna danasanin kasancewa tare dashi amma tsoro ya hana su nunawa a zahiri sai dai a zuci da yawa cikin sun fidda rai da fita wannan jeji anya ma za'a maida su cikin gari kuwa irin wannan jejin ko a film basu tab'a ganin irinsa ba wasu daga cikinsu zubewa sukai suka fara durzar kuka kamar wasu mata.






A wajan su Nawwara kuwa sun kasa zaune bare tsaye gashi sun kasa gayama Garkuwa dan mugun shakkar gaya mai suke to su cemai mi ma matarsa ta b'ace kai abinma ba tsari kamar an datse musu baki sai zarya suke cikin dare har gari ya waye da kyar suka shiga exam d'in k'arshe suna jimamin Surayya kar ta rasa wannan damar sai dai abinda ya basu mamaki suna shiga class d'in suka ganta zaune har Teemah ta girgiza da ganin ta a cikin class d'in a inda ta sab'a zama a nan suka hangeta suna fitowa exams d'in kuma kamar an yashe musu duk wata tabbaya duke dank'are cikin ransu murna ma suka kamayi da murnar zuwa gida.




Basu b'ata lokaci ba sukayi sallama da Teema inda Surayya ta ce "karki damu Teemah damun dawo hutu zakiji an yankewa su Goga hukunci Insha Allah", su duka mamaki sukai sun kuma kasa tabbayar tayaya hakan zai faru a cikin zuciyar Surayya kuwa cewa take a sadda zamu dawo su Goga sun d'and'ana kud'arsu sun kai k'arshen wahaluwa a dajin k'are kukanka, wata dariya ta saki a cikin zuciyarta dan yanzu ita kanta tasan akwai wani abu dake shiga jikinta kuma har magana sunyi kuma ta d'au mata alk'awarin ta cigaba da zama jikinta har sai an yanke ma su Goga hukunci.






Garkuwa ne ya aiko da mota y'ar ubansu wadda zata kai su Surayya Katsina dan duk a nan suke shi kuma ya riga su tafiya yahau jirgi zuwa Abuja a nan komai nasa yake kuma a nan yake zaune.




Surayya sai hushi take danmi zai tafi baisuyi sallama ba shima kansa yasan yayi laifi jira yake ta d'an huce tukun ya hau aikin lallashi, a sadda suka isa Kt sai da aka sauk'e su Nawwara sana aka wuce da Surayya unguwar sabon titin kwad'o unguwa ce sabuwar unguwa masu kud'i suka fara gini a cikinta ta zama unguwa ta masu dashi a nan aka sauk'e Surayya dai-dai wani gida mai shegen kyau da tsari da gudu ta shiga cikin gidan tana kiran Ammee ita kanta Ammee da sauri ta fito tana rungume d'iyar tata suna murnar ganin juna.






A wajan su Zuby kuwa wani irin dokar daji ne cikin wani mugun k'auye gidaje jefi-jefi har saida suka daina ganin tsilli-tsillin gidajen rugar sana suka aje motarsu gefan titin garin daba wani titi bane birji ne kawai, suka fara kutsa kansu cikin dokar dajin ko tsoro babu a ransu sai da sukayi tafiya mai nisa harsun jigata ba'a saba da wahala ba, sana suka hango wata bukka daga gefe wata wuta ce ke ci sai wata kwarya dake gefe tana fitar da hayaki.




Daga nesa aka buga musu wata irin tsawa aka ce "ku dakata daga nan la'anannun Allah nasan abinda yake tafe daku kina su ki mallaki Ahmed Sadeeg Garkuwa ko ba haka bane?", Da sauri bakinta har kyarma yake ta ce "hakane boka ina so a mantar dashi Surayya ya manta da ita kwata-kwata a rayuwarsa a tusa mai soyayyata cikin ransa sai abinda nake so zaiyi", boka ya fara dube-dube da sauri ya daka masu wata irin tsawa har suna zabura ya ce "dakata wannan abinda kike so ayi ba mai yiwuwa bane ban tab'a ganin aiki mai hatsari irin naki ba karki k'ara kiran sunan Surayya a nan shi kansa Garkuwar yana da kariya a jikinsa alwala bata sub'oce mai daga jikinsa kuma yana yawan azzakar dan haka ba abinda zamu iyayi a kansu", "amma boka itafa Surayyar" cewar Zuby zuciyarta cike da k'unci wata irin dariya ya saki har dajin na girgiza sun tsorota da dariyar har suna rungume juna sai zare ido suke tsawar da ya buga musu ce yasa suka k'ara had'ewa waje d'aya ya ce "ba na ce karki k'ara kiran sunanta a nan ba inba so kike dagani har ku mu shiga cikin wahala ba ku tashi ku fice min a nan kona sa aljanu su fitar min daku kuma ku sani duk inda zakuje duk wani boka wadda yake ji da tsafi magana d'aya ce zai sanar daku shi ne wannan amsar dana baku sai dai in kud'inku zaici ku tashi in daina ganinku daga nan", ya idasa maganar a tsawace.




Ai da gudu suka fito daga dokar dajin suna sauk'e numfashi da sauri k'anwar Zuby mai suna Shahida ta ce "amma wallahi wannan bokan baisan aikinsa ba haba ai wallahi sai mun k'ara zuwa wani wajan Aunty ya kika ce", d'auketa tayi da mari ji kake tassss tassss tana kallonta da jajayen idonta dan saura kad'an ta fashe da kuka ta ce "ashe baki da hankali Shahida ku duba irin wannan bokan har akwai wadda yafi shi ko bakiji miya ce bane ai tunda bokan nan ya kasa na hakura da shiga gidan Garkuwa nima zanje na nemi wadda ya dace dani ai Allah ma yana sona daya fahimtar dani tun wuri wahala kawai zansha tunda Garkuwa bazai tab'a sona dan Allah ba...........✍️














*ZAHRA ROYAL STAR CE*












Share fisabilillahi🥰🙏
*💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔
(Horror Story)









ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️










*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*












*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*






*END END END END*
PAGE 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣




Zaune take a d'akinta tana waya da Garkuwa sai shagwab'a take zuba mai yana aikin lallashi daga can cikin wayar naji ya ce "kinsan Allah Noor zanzo ayi komai a bani ke dan gaskiya a matse nake yanzu haka duk kin susuta ni ina zan iya d'aukar rigimarki baki kusa dani", Surayya kuwa duk kunya ta cikata ta kasa cewa k'ala ji tayi ya hura mata iska ta cikin wayar da sauri ta sauk'e ajiyar zuciya ta fara dire-diren kafafu na tsananin shagwab'ar da ita kanta bata san ta iya ba sai a gaban Sadeeg da sauri ya dafe kansa ya ce "ya salam dan Allah nidai ki bari zaki fara ko kinsan halin da nake shiga kuwa Surayya", ya idasa maganar da kiran sunanta lumshe idonta tayi jin yadda ya kira sunan nata yayi mata mugun dad'i a bakinsa kamar kar ya daina kiran sunan nata ita kanta wani irin yanayi take ciki tana buk'atar mijinta amma tana bala'in tsoron Sadeeg dan ita shaida ce idan ya kamata bafa zai sarara mata ba sauk'e numfashi sukai a tare ji yake kamar ya janyota cikin wayar ta fito ya rungumeta ko zai samu sukuni zaune yake cikin Office d'insa dake Abuja aiki ne a gabansa amma kwata-kwata ya kasa komai duk ta dagulamai lissafi "yarinyar nan k'arshe ce wallahi", ya furta can k'asan mak'oshin sa, tasan komai na lagon Sadeeg tasan komai da zata susutashi nan take shi yasa kullum sonta k'arowa yake a zuciyarsa da gaggar jikinsa, cike da tsananin kewar juna sukai sallama dan saura kwana biyu su koma school.






Bayan kwana biyu




Surayya ce tsaye ta rungume Ammee sai hawaye take a ranar da aka koma ta shirya domin bazata k'ara ko kwana d'aya ba tana son isa da wuri domin kai su Goga ga shari'a inko sukayi mata hauka taci Ubansu, so take kamin su Teemah su dawo sai dai suji an yankewa su Goga hukunci, sauk'e ajiyar zuciya Ammee tayi ta ce "ni duk kin rikita min lissafi kiji yarinya kina son sani kuka nima kefa kikace ke da wuri zaki koma ko kwana d'aya bazaki k'ara ba to kuma miye na kukan?", Ammee ta idasa maganar tana kallonta da sauri Surayya ta ce "a'a Ammee kewarki harta fara damuna", Ammee kallonta tayi sai kuma ta ce "anya Surayya baza ai daga dake ba wajan kaiki gidan miji ga abu sai matsowa yake", dan da nan hawaye suka k'ara b'allewa Surayya data tuno da wannan rana kwata-kwata bata son wannan rana tazo tana ji tana gani za'a rabata da Ammee ta.






Da kyar suka rabo cike da kewar juna




Suna isa school d'in da yawa duk ba'a dawo sai y'an nesa wadda wasu ma ba hutun suka yafi ba dan wani inya zo irin y'an kudun nan wani ma saiya gama karantunsa baki d'aya tukun zai koma gida school d'in shuru duk sai taji babu dad'i daga shigowarta garin ta fara tsintar maganar wai su Goga sun b'ata sama da k'asa ba'a gansu ba mutane kuwa murna ma suke da b'atan su Goga dan ba cikin makaranta ba har cikin gari sun addabi bayin Allah.






A wajan su Goga kuwa iya azaba sun azaftu so suke kawai tazo ta fidda su sukam a yanke masu hukuncin nan sunfi buk'atar hukuncin koto akan hukuncin nan da take musu idan suka k'ara kwana ko d'aya ne a wannan dajin mai sark'ak'iyar gaske to ba shakka mutu zasuyi tsawon kwanakin nan basu cin komai sai ganyen dake cikin dajin tun suna ci suna amai har fara zama a cikin su in suna so su shi ruwa kuwa sai dai wani tafashashshan ruwa da suke ganin an aje musu kan hanya dole su dauka su sha bakin da harshan su kamar zasu cire dan azaba haka suke rayuwa tsawon kwanakin nan.




Kwance suke suna wani irin numfashi sama-sama kamar ransu zai fita Inka kalli fuskokinsu hawaye ne ke zuba ta idanuwansu iya nadama sunyi nadama.


Basu sammanin zuwanta dan yanzu ba kawai sukaji wata irin mahaukaciyar dariya ta kauraye ilahirin dajin cike da k'arfin hali suka mimmik'e suna tangali kamar zasu kifa a k'asa ganinta sukai cikin wata mummunar kama wadda yasa hantar cikinsu kad'awa ba shiri suka cure waje d'aya jikinsu na mazari sai kace ba maza ba wata dariyar ta k'ara kecewa da ita dajin har wani rugugi yake kamar aradu zata fad'u, ta buka masu wata irin tsawa ta ce "kun shirya amsar hukunci a koto ko kowa an barku kud'an k'ara kwanaki a cikin jejin k'are kukanka", cikin zuciyar su kuwa cewa suke a lallai yaci sunansa dajin k'are kukanka to komai zakai ba ubanda zai jika bare yasan da kai ya kawo ma d'auki, da sauri har suna rige-rigen cewa "dan girman Allah mukam ki fidda mu daga wannan dokar dajin munji mun yarda mudai a yanke mana hukuncin koto yafi wallahi da irin wannan azabar", wata irin guguwa ce ta turnik'e wajan da sauri suka rufe idanunsu gabansu na tsananta fad'uwa wata irin dariya suke ji a rarrabe kashi-kashi da wasu irin surutai jin shuru yayi yawa sai k'ara ababan hawa da suke jiyowa da sauri suka bud'e idonsu idonsune yayi musu tozali da koto ta ciki tayi fam kamar dama jiran su ake jinransun kuwa ake dan kuwa babu abinda Surayya bata yi ba ko nace abinda ke jikinta tuni an shigar da k'ara lauyan da yake tsayama mata shi kansa ba mutum bane inda koto ta nemi shaidar zargin da sukema su Goga koto ta bada damar a nemo su Goga duk inda suke sai gashi kamar kyaftawa da bismillah aka tsinci su Goga a cikin koto mutane da yawa sun girgiza jin abinda su Goga suka aikta da yawa kuwa basuyi wani mamaki ba inda aka tabbaye su dasu amsa laifinsu nan take bada wata gargada ba suka amsa laifinsu basu ba koto wahala ba al'k'ali ya yanke musu hukuncin rai da rai a gidan yari da aiki mai tsanani nan take koto ta buga gudumarta ta tashi.




Sai barka akema wadda ya tsayama shari'ar anata sa mai albarka.




Bayan kwana biyu su Nawwara da Teemah suka diro cikin school d'in tun kamin su isa gidan da suke suka ji wannan labari mai dad'i ai da sauri suna isa gidan suka rungume Surayya Teemah harda kuka, iyayan Khairat kuwa harda su akayi zaman koto da dangin Anwar ba k'aramin kuka suka sha ba suna tsine ma su Goga suna ta ma duk wadda ya binciko abinda Goga yayima yaran nasu addu'a ba k'ak'k'autawa zuciyarsu sai yanzu ta samu sukuni .






A wajan Surayya kuwa sunyi magana da Aljanin dake jikin Khairat tun tana da rai tana da aljanu jikinta ashe shine ya dawo domin d'aukar ma wa'innan masoya FANSAAA ya ce ma Surayya "Insha Allah zai saka mata itama zai kasance tare da ita duk wani abu na cutarwa inya tunkarota zaiyi iya bakin k'ok'arinsa dan ganin abin cutarwar nan bai iso gareta ba" amma Surayya ta nuna mai ai Allah na tare da ita sai aljanin ya ce ai Allah shine ya turo sa domin taimakon bayin Allah dan haka bazai rabo da ita ba dan har abada ba zai bari a cutar da ita ba, a haka suka rabo da Surayya.




Rayuwa taja yanzu babu abinda ke gaban su Surayya sai shirye-shiryen gama makarantar su sosai Garkuwa shima ya d'auki nauyin wasu abubuwan domin kuwa shi yad'au nauyin kyatuttukan da za'a ba hazak'an d'alibai, sosai aka gudanar da bikin graduation mai k'ayatarwa wadda aka ba kyatuttuka harda su Surayya dasu Nawwara sosai Sadeeg yayi alfahari da matar tasa inda ya gayyaci da yawa cikin Malamai zuwa bikin da za'a gudanar domin tarewar Surayya za'a had'a dinner guda d'aya daga can za'a wuce da Surayya gidanta dake garin Abuja a jirgi za'a d'au amarya Mlm sunji dad'in karmawar da yayi musu na gayyatarsu bikinsa da yayi ai wannan abun al'faharin su ne.




Rana bata k'arya sosai akai taro na gani na fad'a harda su Teemah wajan zuwa a Abuja a jirgi duk mai buk'atar zuwa su Bilki kuwa sune iyayan biki ranar sun kasa zaune sun kasa tsaye inda Surayya da kyar aka rabata daga jikin Ammee kuka tayi shi kamar ba gobe ita kanta Ammee sai da aka wuce da Surayya sana ta kama share hawaye a b'oye.




A Abujar ma saida aka had'a dinner wadda taba mutune mamaki irin su Zuby da muk'arabanta sosai ta girgiza lallai sun shaida Surayya tayi sa'a ita kam Zuby tasan na gaba yayi gaba na baya sai labari domin ganin kwaf har saida sukaje akayi komai dasu waketa tasu ma.




Gidan Surayya kuwa tofa nanne kallo ya koma sama kai yadda zan fasallata gidanma kansa sai a b'ata shafi guda babuce kawai babu a gidan nan kai gidan nan kona shugan k'asa iya abinda za'ayi kenan gida fa ya amsa sunansa gidan Ahmed Sadeeg Garkuwa duk wadda zaiga wannan gida bazai mamaki ba domin kuwa indai Garkuwa ne zaiyi hin mahiyinsa ma.






Kowa sai da ya tabbatar ya an maida shi inda yake cike da abun arzik'i duk wadda yazo bikin nan sai da ya shaida yazo bikin Ahmed Sadeeg Garkuwa wasu ma haka nan ba'a San dasu ba zasuzo kowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login