Showing 87001 words to 90000 words out of 132515 words
Chapter 30 - BAKAR WASIKA- Book 1 By Khadeeja Candy .txt
sauki, taya zan manta komai a take? Saboda ta mutanen da basa maraba da kai abu ne mai wahala! Har yanzu na kasa yarda cewar na rasa komai, ina ta marmari kauyena, da mutanen kirki masu karamci dake cikinsa, na yi kewar mahaifiyata da Babana, har abada ba ni da mai maye min gurbinsu”
Ta share hawayenta sannan ta soma wasa da yatsun hannunta wasu hawayen na sauko mata.
“A da, ina rayuwa ne cikin wani karamin gari, mai cike da albarkar manoma, duk da kasancewar ban samu ilmin boko ba, na samu na addini daidai gwargwado, kuma ina zaune da yayyuna cikin jindadi da farincikin rayuwarmu ta yau da kullum, ni kadai ce mace bayan mazaje bakwai da mahaifiyata ta haifa, hakan ya saka na zama yar gata, ina jin kamar babu wanda ya fini more rayuwa, abun da ban sani ba, ashe kaddara tana nan tana min wani tsari, a lokacin da mahaifiyata take cikin rashin lafiya na bakinciki abun da akai ma yayanta kasan me ta fada min?”
Ta kalleshi sai ya girgiza mata kai alamar be sani ba.
“Tace kuka na yana nan gaba, sai na tambaye tana take ganin zan iya rayu idan bata raye? Tace min zaki rayu amman akwai kuka a gaba, a yanzu na gane abun da take nufi, tabbas zan rayu amman wace irin rayuwa zan yi? Ban sani ba, kuka da take fada min cewar zan yi na tabbatar shi ne na fara tun a yanzu, yanzu na fahimta wanda ya rasa uwa ya rasa ta har abada, wand ya rasa yan'uwa ya rasa su har abada, abu ne mai wahala farinciki ko murmushi ya sake kusantar fuskata...”
Ta fashe da kuka sosai, Talba ya ja dogon numfashi a hankali ya sauke.
“Baki taba tunani miyasa Allah ya hada ni da ke ba? Wata kila a yadda nake da rufin asiri idan na tare ki a hanya, ba zaki tsaya ba zaki ji tsoro, wata kila ni kuma ba zan taba jin a kamata na tsayar da ke na tambayi damuwarki ba, amman sai Allah ya kawo silar da zata saka na hadu dake cikin sauki kuma har na dawo dake da zama kusa da ni, idan Allah ya karbe wani abun sai ya maka hanyar wani, ki dauka duka wannan yana cikin jarabawarki, Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wassalam yafi kowa gata a gurin Allah kuma Allah yafi kaunarsa da kowa, amman a haka Annabi ya girma babu mahaifiya babu mahaifi, ni da ke banbancin kaddararmu kadan ne, ni ma na tashi babu uwa ba uba, sai dai na zamu gata, irin gatan da nake kokarin baki a yanzu, ki dauke ni a matsayin yayanki, saboda ina ganinki kamar yar'uwata ne, duk abun da zan yi ma kanwata Amal ko Leila zan miki, ki sake jikinki, zan maida ke yar gata believe me zaki zama Shalele ta ko'ina”
Kanta na kasa tana hawaye har ya gama magana, sannan ta dago ta kalleshi, be yi mata kama da mai karya ba, kamaninsa da cikar kamalarsa be nuna akwai gazawa a tare da shi ba. Sai dai me? Matar daya ambata da sunan cewar matar da zai aura ce zata yarda? Anya ma zata jure zama a gidan tare da ita?
“Ina da tabbacin ba duka aka akashe yan'uwanki ba, Inshallah idan hankali ya kwanta kin samu lafiya zan muje mu nemi inda yan'uwanki suke, yanzu taso muje ki ci abinci”
“Ina son na yi sallah, ban yi sallah ba ana biyana salaloli da yawa, dazun ma na fara tura keken naje na yi sallah sai.... ”
Daga haka ta labarta masa abun da ya faru ciki har da wanda Madina tace idan ya dawo ta fada masa. Be jidadin abun da Leila tai mata ba, sai dai be nuna mata ba.
“Okay amman yanzu bari ki fara cin abinci ki samu kuzari, sannan muje ki yi sallah okay?”
Ta daga masa kai.
“Zulai zata zo ta tura ki bathroom ki wanke bakinki sai ta fito da ke ki ci abincin ki yanzu”
“Aa bana so yanzu wannan zata zo ta fara min masifa, kuma zata hana su yi min komai”
Ta fada kamar zata fasa kuka.
“Kina son na tura ki?”
Ta daga masa kai, sai ya mike tsaye ya dauketa ya dora a wheelchair din. Ya turata da kansa har bathroom din ta wanke bakinta.
“Zaki yi fitsari?”
Ta girgiza masa kai alamar aa. Sai ya turo ta ya fito da ita sai da suka kawo gurin kofar sannan ta kula da kofar a balle take, sai dai bata ce komai ba tana ta kallon hanyar har ya fito da ita falon. Iyakar abun da ta sani Leila ta rika kanta tana ja da karfin tsiya, bayan baka bata san me ya faru ba, sai ganinta tai ta farka daga bachi.
“Waya kwantar da ni kan gado dazun?”
“Ni”
Ya amsa mata a takaice sannan ya tura kujerar har gurin dinning, babu kowa a falon daga shi sai ita sai katon Plasma. Da kansa ya shiga zuba mata abincin, sannan ya mika mata. Sawun takun talkami da taji ne ya saka ta waiga ta kalli Upstairs din sai ta hango Madina da Leila suna saukowa a tare, suna hada ido da Leila tai saurin maida kanta kasa cike da tsoro. Kallo daya Talba yai musu ya dauke idonsa, kusan a tare suka kalli juna, ba Leila kadai ba har Madina ta ji zafin ganin Talba na zubawa Aminatu abincin da kansa, sai dai ta dannewa zuciyarta bata yarda ta nuna ba, duk da kasancewar Leila ta fada mata komai daya faru dazun.
“Amman wannan wulakancin ne, haba Talba? Taya zaka zuba mata abinci a irin plate din da muke cin abinci? Kuma ka kaita har gurin dinning?”
Madina ta yi saurin rike ta.
“Haba Leila miye haka?”
“Ai dole na yi magana, dazu fa har rumgumar ta yai...”
Tana kokarin kai hannu ta taba Aminatu data make guri daya Madina ta yi saurin rike ta da karfi.
“Leila miye haka wai?”
“Wallahi sai ta bar gidan nan, na rantse da Allah ba zata zauna a nan ba”
Ta fada da karfi kamin ta kwalawa Momy kira tana ihu. Uffan Talba be ce mata ba, ko kallonta be yi ba sai aikin zubawa Amina ruwa yake a cup. Kamar da gangan Madina ta saki Leila ta karasa gurin dinning.
“Karki taba yarinyar nan”
Furucin da yai mata ne yasa saka ta tsaya cak, domin bata ji wasa a muryarsa ba kamar yadda fuskarsa ma bata nuna wasan ba. Aminatu ta yi saurin sakin plate din abincin dake hannunta idonta cike da hawaye. Hango Momy na saukowa tare da Amal da Kabir yasa Leila ta dauki ruwan da Talba ya zuba a cup ta watsawa Amina.
“Haba Leila miye haka?”
Madina ta fada tana zaro ido tare da saka hannayenta ta rufe baki.
“You should apologize ki bata hakuri yanzu nan”
Talba ya fada yana nuna mata Aminatu.
“No Leila ta yi kuskure, amman ba zata bata hakuri ba, you're just hurting her”
Kabir ya fada, Momy na karasa kusa da ita ta maida Leila.
“Ya isa haka Talba, ba zan yarda ka wulakanta Leila akan wata banza ba”
“Momy kin san abun da ta yi”
“Be dame ni, amman ta duka ta bawa wannan musakar hakuri ne ba zata tayi ba!”
Nan da nan jikin Aminatu ya fara rawa, Talba ya kalli Momy.
“Wannan ba daidai ba ne Momy”
“Miye daidai tana yar riga kace ta bawa wata banza hakuri? Wai gata ka fi leila ne ko kuma miye?”
“Kuma na rantse da Allah ba zata zauna a gidan nan ba, Wallahi Momy sai dai ku zaba ni ko ita...!”
Leila ta fada tana buga kafa a kasa. Leila ta ji wani irin dadi, komai ya faru kamar yadda take so, duk da kasancewar bata yi zaton da wuri haka komai zai faru ba, daman ta zo gidan nan kawai saboda Leila ta kirata tana kukan rumgumar da yai ma Amina, sai dai a yanzu komai ya yafi kamar yadda take son ya tafi. Da sauri ta nufi Aminatu dake kuka taja kujerarta.
“Madina ki kyale yarinyar nan a gurin nan?”
Sai ta girgiza ma Momy kai.
“Dan Allah Momy ki gafarce ni, be dace ku yi wannan fada a gaban yarinyar nan ba”
Bata jira abun da Momy zata sake cewa ba, ta tura Aminatu zuwa corridor, a azaton Momy Madina ta yi hakan ne saboda bata son su yi fadan a gabanta kasancewar su yan'uwa.
“Abun da kake ba kyautawa ba ne, Talba, be kamata ba, ko a dazun ka rumgume yarinyar nan a gaban Leila kuma kasan dole zata ji ba dadi ba, and now kana kokarim feeding dinta for what”
Talba ya nuna Kabir da yatsa.
“Don't you dare tell me what is right and wrong, don't you dare judge me, this is my life waye kai da zaka kalubalanci abun da na yi?”
“So baka isa ka kawo wata a gidan nan just to hurt my sister in front of us? And now ba zamu zabi wata akan Leila ba, take her away”
Wani irin kallon kallo suke tsakanin shi da Kabir ko wane zuciyarsa ta kawo kamar ya rufe dan'uwansa da duka yake ji. Daker Talba ya samu hade numfashinsa ya kalli Leila dake tsaye sannan ya nufi corridor da zai sada shi da dakin da Aminatu take ciki. Bakin kofar dakin ya tsaya yana kallon Madina dake rumgume Aminatu tana share mata hawayenta da dankwalinta, ita ma tana kuka.
“Dan Allah ki yi hakuri ki daina kukan nan, ban taba rasa kowa ba, amman na fahimci yadda kike ji, akwai ciwo sosai ki kwantar da hankalinki Inshallah Talba ba zai bari ayi miki komai ba, ni kuma zan kula da ke kamar kanwata Inshallah”
Yadda take hawaye sai ka rantse da Allah kukan gaske take, zaka yi zaton da gasken gaske take tausayin Aminatu. A badini kuma tana yin hakan ne saboda ta ji kamshin turaren Talba ta san yana tsaye bakin kofar dakin ko ma cikin daki.
Aminatu na hada ido da Talba ta saki Amadina tana kuka.
“Dan Allah ka kai ni inda yan gudun hijira, ko wani gurin, bana son fada bana son fada dan Allah karka yi fada da su dan Allah...”
Karasowa yai cikin dakin ya risina gabanta yana kallon fuskarta, magana yake son yi mata amman ya rasa ta ina zai fara.
“Idan zamanta a nan zai kawo matsala, zan iya tafi da ita gidamu, Mamana bata da matsala kuma zan iya kula da ita, kamin Momy da Leila su sauko”
Madina ta fada muryar na rawa, a ranta tana ala ala ya amince, a hankali Talba ya juyo ya kalleta.
“You can trust me. Wallahi ba zan mata komai ba, tare na da Leila ba zai saka na cutar da wani ba, yarinyar nan ta cancanci rayuwa mai kyau...”
A nan ma Talba be ce mata komai, ya juya yana kallon Aminatu.
“Excuse us Madina”
Murmushi ne ya cika fuskarta, saboda ya kiran sunanta, kusan tun da take da Leila ba zata iya tuna rana daya ta taji sunanta a bakinsa ba.
24
Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
“Kar abun da Leila tai ya dame ki, tana da zafi ne, amman a sannu zata fahimta ta daina”
Aminatu ta saka hannu ta share hawayenta, wasu a sauko mata.
“Komai be da sauki a rayuwar duniya, komai ka sara yana da wahala ka samu abun da zai maye maka gurbinsa, rayuwarmu da ta ku akwai banbanci, kuma tana da gaskiya, ni yar kauye ce marar gata wanda bata waye a komai ba, ba kamar ni ba talaka kuma yar kauye, be kamata na zauna a mazauninsu ba, ko kuma na ci abincin a inda suke so, muna da banbanci mai nisa a tsakaninmu”
“Ban taba ganin wannan banbanci ba, ban taba jin cewar Leila ko ni mun fiki ba saboda dukiya, ita ma kuma kurciya ce ke janta”
“Idan ita kurciya ce, Momy fa?”
Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai ce mata.
“Momy tana goya mata baya ne saboda bata son bata kunya a gaban mutane, ko da ni zan yi fada da Leila wani lokacin zata iya shigar min ta yi ma Leila fada”
Ta yi shiru hawaye sai sauko mata suke.
“Kalleni”
Ta dago, sai idonta ta sauka cikin nasa, a karon farko ta ji kwarjininsa ya cika sa, akwai kalama a fuskarsa kamar yadda natsuwarsa take kara fito da siffar zatinsa.
“Zaki iya zama a gurin Madina ko kuma na kai ki wani gurin dabam?”
Ta kawarda fuskarta tana tunani.
“Ban sani ba, wata kila ita ma iyalan gidanta kamar na ka ne, ba lallai ne su karbe ni, amman ka min wani alkawari dan Allah”
Kallonta yake, ita ma kamar tasan ba zai tambayeta minene sai ta fada tana yawo da idonta a dakin.
“Ka min alkawarin, zaka nema min gurin da zan zauna cikin yan gudun hijira yan'uwa, ko kuma ka nema min wasu daga dangina kamar yadda kai alkawari”
Yayi murmushi kadan.
“Kina tunanin yan gudun hijirar suna shan dadi ne? Suna wata irin rayuwa ne mai ban tausayi da tada hankali, abun da za su ci ma wahala yake musu, ba su da muhalli, wasu na fakewa a kangon makaranta ko tsohon gida, wasu kuma suna zaunawa inda yan'uwa ne, amman su suke ciyar da kansu, wasu bara suke su ciyar da kansu, wasu kuma surfe suke su yi wankakau ko wani aikin karfi sannan su samu ciyarda kansu, idan sun shiga wani gurin za a nuna musu kyara ana kiransu da mayu, sadakar ma sai wanda ya ga Allah ya ga Annabi yake ba su, ba rayuwa suke mai dadi ba, ya kamata ki daina wannan tunanin”
“Ba jindadi nake so ba a yanzu, jindadi abu ne mai wahala a gareni, so nake na samu sakewa ina sonnna zauna da irin mutanen dake rayuwa kamar yadda nake, mutanen da basa kyamata, ina ma kasance tare da mutane masu irin rayuwata, wadanda suka san zafin rashi...”
“Ina daya daga cikinsu ai”
Ya fada yana mikewa tsaye. Sannan ya nufi kofar fita wa kusa da kofar ya samu Madina ta jingina tana jiran fitowarsa.
“You should go and talk to your parents first, idan sun amince sai ki sanar da ni”
Ta dago a hankali ta kalleshi.
“Iyayena basa da matsala, amman zan je na sanar da su, sai dai ban san inda zan same ka ba”
Tsayawa yai kallonta sannan ya mika mata hannunsa, tana ganin haka ta fahimci wayarta yake nufi sai tai saurin cire password din wayar ta mika masa. Yana saka number ya mika mata wayar sai ta karba da hannu biyu tana godiya.
“Na gode”
Be kula ta ya juya ya koma cikin dakin, sai ta yi tsalle ta dire a hankali ta kai wayar a hancinta tana shinshinar kamshin turaren Talba kamin ta kai wayar a kirjinta. Sannan ya fito corridor tana boye jindadinta, Kabir ta samu tsaye yana fada Leila.
“Kishi ba hauka ba ne, kowa ya san akwai zafi amman ya kamata ki rika controlling kanki, idan ma wani abu ne ai shi yai miki ba ita ba”
Madina dai bata ce komai ba har Talba ya turo Aminatu kam wheelchair ya fito da ita falon, kanta a kasa tana tsoron kallon mutane, shi ma kuma kofar fita daga falon kawai yake kallo. Momy da Leila har ma da Kabir na tsaye ban kallonsa babu abun da suke har ya fita da ita.
“Aikin banza mtsssss”
Leila ta fada tana jan tsaki. Sai da Madina ta leka windows ta hango ya tashi motar yana kokarin yin ribas sannan ta kalli Momy ta ce.
“Momy zan tafi da yarinyar nan saboda anan zata haifar da fitana ne kawai, kuma idan tana tare da ni zata nisanta da shi ba kamar yanzu ba”
Momy ta kalli Leila sannan ta kalli Madina.
“Ke iyayenki za su yarda ta zauna ne?”
“Eh zan musu bayani kuma ai kin ga ba dadewa za ta yi ba, na dan lokaci ne”
“Shi zai yarda ki tafi da ita?”
“Eh na masa magana, amman yace min na fara zuwa na yi magana da iyeyena”
“Okay ba matsala”
Momy ta amsa ta tana kallon yanayinta, sai ta yi ma Leila sallama tana fadin sai sun yi waya. Momy ta bita da kallo har sai da ta fice sannan ta kalli Leila ta ce.
“Ki yi hankali da yarinyar nan, hankalina be kwanta da ita ba, idan b munafurci ba ta ya za ayi fada akan yarinya kuma ke ki ce zaki dauketa ki kaita gidanku?”
“Momy da sani na tai, sai da tai shawara da ni, plan ne muke hadawa, Madina bata da matsala, ba yau na santa ba fa Momy”
“Ki dai yi hankali, kuma ki san irin sirrin da kike fada mata”
Kabir ya mike tsaye yana kallon Leila.
“I hope plan din da kike hadawa ba cutar da yarinyar nan zaki yi ba, ba na goyi bayanki ba ne saboda ki samu damar wulakantata, no na yi hakan ne saboda na san kina jin kishin abun da Talba yake yi ma yarinyar nan”
“Ba wanda za a cutar kawai zan nisanta ta da shi ne”
“Dauketa za ki yi?”
“Haba Kabir? Idan ma na dauke ta zan yi ai shi ya ja mata...”
Uffan Kabir be sake ce mata ba ya fice falon. Ita ma tashi tau ta nufi upstairs aka bar Momy zaune tana kallon Leila har ta haye.
TALBA POV.
A entrance din ya bar ta, sai da ya fara isa ya bude motarsa sannan ya dawo ya saka hannunsa ya dauke ta ta saka a motar ya dawo ya dauki