Showing 105001 words to 108000 words out of 132515 words

Chapter 36 - BAKAR WASIKA- Book 1 By Khadeeja Candy .txt

09 Oct 2024

31704

sakeke da zarar rayuwarki ta inganta, ma'ana kin gane yan'uwanki ko kuma kin samu wanda zai aure ki, kuma wannan auren zai kasance ne kawai a tsakaninmu, babu wanda zai san da wannan sirrin har mu rabu”


Dauke kai tai tana jin abun wani iri, an taba aure ba yan'uwa ba kowa? Daga ita sai shi?


“Zamu yi ne saboda tsare mutunci da gudun fushin Allah, kuma na rantse miki da Allah zan sake ki a duk lokacin da dayan biyun nan ya faru! Ko dai kin gane wasu daga danginki ko kuma kin samu wanda ke sonki tsakani da Allah zai aureki, karki damu da tunanin babu yan'uwa ko naki, zamu yi wannan auren ne saboda ke, domin ni ina da wanda zan aura, kuma mu yi wannan abun ne a rubuce kuma akan yarjejeniyar saboda ki samu natsuwa”


Ya fada kamar ya san abun da ke ranta. Da gaske aurenta zai yi saboda abun ya fada ko kuma dai saboda wani dalilin ne na dabam?


“Momy...”


“Karki damu da ita, ba zata taba sani ba na miki alkawari”


“Leila...”


“Taya zan barta ta sani bayan kuma ita zan aura? Ya kike ganin zata kalli abun? Wannan abun zai zama sirrine a tsakaninmu”


Ta girgiza masa kai.


“Ba zan iya ba”


Ya cikama bakinsa iska ya busar kana ya kai hannu ya shafa kansa.


“Daman bana son cilas ta ki, yanzu dole mu nemo wata mafitar ta dabam, zan memo miki wani gurin da zaki zauna tare da wasu mutanen, amman kamin na samu wannan dole ki zauna a nan kamin mu samu wata mafitar”


Sai ta rumtse ido wasu zafafan hawaye na sauko mata.


“Inna ta yi gaskiya, ta fada min zan yi kuka a gaba, sabowa da wata rayuwar ba abu ne mai sauki ba, fuskantar kalubale bayan wani kalubalen abu mai wahalar gaske, ina a tsakankanin rayuwa da mutuwa, farinciki da sabo sun min nesa, samun sukunin na zuciya da ruhi ya min tsada”


Har ya kai hannu ya kama hannunta, sai kuma ya maida hannun a cikin dayan hannunsa ya rike.


“Miyasa ba zaki yarda da kaddara ki karbi duk abun da ya zo miki da hannu biyu? Wata kila idan kika bi rayuwar a yadda ta zo miki sai ki samu sukuni da walwala a gaba?”


Ta bude idanuwanta da suka soma yin ja ta kalleshi.


“Kana ta karfafa guiwa a inda babu karfi, taya kake ganin komai zai zo min da sauki? Na rasa uwa a gaban idona suka kashe mahaifina, aka kashe yan'uwana a dare daya na rasa komai, a tsakanin wadancan ranaku da na yau na rasa wacece ni, ina jin zafin abun a raina ina jin kamar zuciyata zata fasa kirjina ta fito babu abun da yake da sauki a gareni...”


Ta karasa tana ta shesshekar kuka jikinta na rawa, hawaye na sauko mata kamar an yi su ne kawai saboda wannan ranar. Gaba daya jikinsa yayi sanyi sai tausayinta ya kara kama shi, ba tare da ya so ba ya kai hannunsa ya kama hannunta ya jimke sosai, sai kawai ta kara fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya.


“Za ki iya yarda da ni?”


Ta daga masa kai tana kuka.


“Na miki alkawarin zan dawo miki da farinciki a rayuwarki, ban ce zan dawo da iyayenki da yan'uwanki ba, amman da yardar Allah sai na samo miki wadanda za su maye miki gurbinsu? Zan dawo miki da farincikin da kika rasa Amina i promise you this! Kin yarda da ni?”


Ta sake daga masa kai, sai ya sauke numfashi a hankali yana jin kamar ya rikata ya saka ta a kirjinsa ya rarrasheta. A hankali ya zare hannunsa ya mike tsaye yana nuna mata gadon.


“Kwanta”


Ta kalleshi daker tana kokarin tsayar da kukan da take.


“Ta.... Tafiya... Zaka yi....”


Kamar ya ce mata eh sai kuma wata zuciyarta ta hana shi, wata kila idan ya amsa mata da eh zata iya cewa ba zata zauna ba, idan kuma ya ce mata aa ta kwanta ta tashi bata tararda shi ba zata dauke shi makaryaci. Be ce mata komai ba ya nufi inda bargon yake aje gefen gado ya dauka ya rike.


“Kwanta, ki samu bachi”


Ta hau saman gadon gaba daya ta kwanta sai ya dauki filo ya mika mata ta karba ya rumgume, sannan ya lullube ta. Baka jin komai a dakin sai saukar numfashinta da karfi, gefen gadon ya samu ya zauna yana kallonta, zaman da yai sai ta ji natsuwa har ma ta samu damar lumshe idonta, ta kai hannunta a baki tana cizawa a hankali. Kallonta yake for so many reasons, na farko rayuwarta yake hangowa, da kuma tasa ta ina zai sama mata duka abubuwan da take bukata? A dayan bangaren kuma yana tunanin Momy. Lokacin lokaci take sauke ajiyar zuciya da karfi tana shakar numfashin a hankali. Sai da ya tabbatar bachin nata ya nina sosai sannan ya mike tsaye ya karasa inda take ya kai hannunsa ya janye hannunta daga bakinta ya kara jan bargon ya lulluba mata har gurin wuyanta, sai kuma ya tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarta, samun kansa yai da murmushi kamin ya juya ya fara takawa cikin izza ya nufi kofar dakin, hannunsa ya kai ya kunna ac dakin sannan ya juyo ya sake kallonta, kamin ya sa kai ya fice ya ja kofar a hankali ya rufe, this is the first time da yake taba kofa a hankalin saboda gudun katsewa wani bachi, after Daddy. Fita kofar falon ma a hankali ya jata ya rufe saboda kar karar rufe kofar ya tashe ta, sannan ya saka key ya rufe kofar daga waje, sai da ya fara isa ya gurin gate din ya bude sannan ya dawo ya fita da motarsa sai kuma ya dawo ya rufe gate din ya koma cikin motar. Kamin ta fita unguwar aka soma kiran sallah magariba, a kusa da wani masallaci ya faka motarsa ya fita yai alwala ya shiga masallacin yai sallah sannan ya dawo cikin motarsa yai mata key ya dauki hanyar gida.
Kamin ya isa ya kira Daddy a waya, sai dai har wayar tai ringing ta gama be daga ba, hakan ya saka shi rike wayar a hannu ya cigaba da tukin da hannu daya har ya isa gida, yana danna horn sai ya ji babu dadi tunawa da Momy bata cikin gidan, har yake jin kamar ya juya ya koma domin shiga cikin gidan yana masa nauyi a yanzu, ya kasa daina ganin laifin Daddy na yanke irin wannan hukuncin kuma yana ganin shi ne silar komai, tun da yake da Momy ko fushi be tana ganin ta yi ba, balle kuma har saki ya shiga tsakaninta da Daddy, idan ma an taba ta an yi ta sigar da su ba za su gane ba. Har ya isa harabar aje motocin ya faka motarsa be lura da Kabir dake jingine jikin mota yana waya ba, duk da kasancewar ko'ina na gidan haske ne irin hasken nan da ko allurarka ta fadi zaka iya gani, ko da yake hausawa sun ce hankali ke gani ba ido ba.
Sai da ya bude motar ya fito sannan ya kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar Kabir, rufe motar yai ya karasa inda Kabir yake jingine ya tsaya tare da zuba hannayensa aljihu yana kallon harabar gidan kamar bako.


“Ya akai?”


Kabir ya bukata ganin ya tsaya a inda yake da alama jiran yake ya kare wayar, kallonsa Talba yai jin wata bakuwar kalma da be saba furta masa ba ga fuskarsa a gade kamar bakin hadari.


“Come on.. Karka ce min ka zo nan ne saboda ka yi magana akan abun da ya faru? Kai da baka san zafin uwa ba? Taya za ayi ka ji wani abu?”


Talba ya kalleshi da mamaki.


“Kabir magana fa kake fada min kai tsaye”


“Yes ko ni ma zaka saka Daddy ya kore ni ne? But I'm grown up now ba yaro ba ne ni”


“Kabir me ke damunka?”


Talba ya tambaya da mugun mamaki.


“Babu abun da yake damuna, kawai ina fadar gaskiya ne da ace ka san wacece uwa da baka bari komai ya faru ba? And you won't be here standing in front of me, Momy ta raine ka for so many years amman a yau ka nunawa duniya cewar kai ba danta ba ne, and Thank you....”


Yana fadar hakan ya bar gurin ya nufi hanyar falo, Talba binsa yai da kallon yana mamakin kalaman da Kabir ya fada masa kai tsaye! Ta dayan bangaren kuma sai ya ji kamar an caka masa wuka a kirji, how could someone like Kabir zai ce masa be san zafin uwa ba? For the second time after wacan karon da Daddy ya ba shi labarin komai ya samu kansa da jin wani yanayi irin na Aminatu.






BATURIYA POV.


“Na kira ne kawai na yi miki barka da safiya”


Ta yi murmushi tana kara gyara kwanciyarta kan gadon Umma.


“Na yi fushi baka kira ni da wuri ba har rana ya fito sosai”


Ta fada tana ta zuba masa shagwaba kamar yana gabanta. Sai ya marairaice murya daga can cikin wayar yana bata hakuri.


“Haba Babyna kin san bana son bacin ranki fa, amin afuwa ba zan sake ba, kuma ina tafe da wani katon albishir”


“Na me?”


“Sai kin ba ni goro zan fada”


“Me kake so?”


“Komai ma kika ban ina so, ai ni komai ni so nake”


“To na baka kaina”


“Wow na gode ko da yake ke ma din ai tawa ce”


“To yanzu fada min”


“Abbana ya amince, zai fada min lokacin da yake free sai na fada miki ki duba idan na ki Abbah yana free sai su hadu su ga juna”


Ta dafe kirjinta gabanta na faduwa, ga wani irin tsoro da fargaba da suka rabeta a lokaci daya.


“Da gaske?”


“Haba ana wasa da irin wannan maganar ne?”


“Wow Alhamdulillah, amman ka san me? Ni fa a gidan mu ba a san da maganar ka ba”


“Yeah ai na fadawa Abbana, shiyasa ma nake son aje nema min aurenki so that na samu izinin magana da ke”


“Kana ta maganar Daddy ban ji ka tabo Momy ba?”


“Kin san Momy tana son na auri wata a familynsu ne, amman ita ma ta yi na'am saboda tana son abun da nake so, kuma Abbah ya bi bayana yace matukar suka yi bincike suka tabbatar babu wata matsala za su nema min aurenki”


“Alhamdulillah Allah ya amince mana”


“Amin kin san fa ni na gaji da wannan boye boyen da kike min kin hanani zance da ke, da na yi magana sai ki ce ana fada a gida, kuma ya kamata ace muna haduwa saboda mu kara fahimtar juna da kyau”


“Haka ne, ni kaina ina son haduwa da kai, idan na samu free time zan kiraka sai mu haduwa akwai abubuwa da yawa da ya kamata ka sani akaina ni ma kuma na sani akanka”


“Haka ne, idan kin samu sa'ar fita sai ki fada min inda zamu hadu”


“Inshallah, i love you so much”


Ta fada da muryar dake nuna farinciki take, sai dai a zahiri ba farincikin take ba, tsoron abun da zai je ya dawo ne a ranta.


“Na'am Umma gani zuwa”


Ta yi amsawar karya kamin ta ce.


“Ina zuwa Umma tana kirana”


“Okay i love you”


Tun kamin ya aje ya yanke wayar ta tashi zaune tana dudu da hannayenta.


“Kam uban nan, zubar da cikin nan ya zame min dole, amma...”


Bata karasa ba Umma ta daga labulen dakin ta shigo tana fadin.


“Rafi'a, ta so ga yayanki can yana nemanki”


“Toh”


Ta amsa sannan ta sauko saman gadon a ta dayan bangaren tana ala ala idan ba Faruk ya fada masa tsabanin abun da ta fada musu ba. Kamin ta karasa falo har ta fara tunanin irin karyar da zata yi ta kare kanta. Gabanta na faduwa ta zo ta zauna a kasa kanta a kasa Umma dake bayanta ta zauna kan kujera.


“Yaya ina wuni?”


Ta gaishe shi tana dan kallon yanayinsa, sai ya amsa mata fuska ba yabo ba fallasa.


“Umma ta fada min abubuwan da suka faru, na kira Faruq har gida domin ji daga bangarensa, sai dai be fada min komai ba, kawai dai ya ce min ya gaji ne, yayi iya hakurin da zai iya da ke, yanzu kuma Allah ya kare abun, sai dai yayi ta jaddada min cewar ke yar'uwarsa ce kuma uwar dansa, ba zai fadi mummunna abu akanki ba, amman mu zamu fahimci komai da sannu, ina fatar babu abun da kike boyewa”


Ta dago kai ta kalli Yayanta idonta cike da hawaye.


“Haba yaya! A hannunka fa na tashi idan akwai abun da ba halina ba ai kai zaka fara sani”


Umma ta tabe baki


“Ai ni ba haka na so ba Wallahi, da ka biye ta tawa da police station zaka kai shi a lakada masa shegen duka kamar yadda shi ma yayi mata”


“Ai an daga kafa wani gangaren ko dan zumunci, shiyasa na kira shi a gida na yi magana da shi”


“Shi ai be duba zumuncin ba a lokacin da zai wulakantata haba”


“Yanzu dai ayi hakuri komai ya wuce, Allah shi zai saka mata ai”


“Aiko ya saurari abun da zai same shi domin hakkinta sai ya kama shi, kuma gobe gobe zan aika a kwashe mata kayanta duka da yardar Allah, daga ma ta huta da talauci da rashin abincin, kuma ba zamu rika masa dansa ba”


“Yace ma zai rika aiko mata abinci duk wata saboda cikin da take da shi, Allah ya sauwake”


“Ameen”


Ta amsa a tare da Umma sannan ta taso ta baro musu falon da dawo dakin Umma ta zauna tana ta tunanin maganar da Fahat yai mata! Da sauri ta kai hannu ta dauki wayarta ta kira Ramlee ringing daya ta dauka cike da far'arta.


“Yar gari yanzu fa nake son kiranki”


“Lafiya?”


“Lafiya sai alheri, Wallahi Alhajin nan ne ya fara damuna da maganar ki jiya, har yana ce min yana son ya leka chine da ke, bayan shi ma na samo miki wani Alhajin”


“Uhmm ai yanzu fita ma sai ta min wahala Ramlee, Faruq ya sake ni”


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya sake ki fa kika ce Fee'ah”


“Wallahi kuwa yau kwana biyu....”


Daga can cikin wayar Ramlee ta sauke ajiyar zuciya bayan Baturiya ta gama labarta mata komai.


“Wato sai yanzu na gane kin ci ubana da iya makirci Fee'at”


“Uhmmm ni ma ai ba ta wasa ba ce, ni yanzu kin san ma miyasa na kira ki?”


“Sai kin fada”


“Cikin nan nake son zubawar kin ga ina zubar da shi na gama iddata”


“Haka ne, amman kar ki yi gaggawa Fee'at, saboda zai taba lokacinki a yanzu, maganar ba zai yi a waya ba, ina son mu hadu if possible”


“Karki zo gida, zan kira ki idan na samu sararin fita”


“Okay ”


Ya sauke wayar tare da sauke ajiyar zuciya.
29


*_MATAYEN ƘWARAI SARAKAN ADO DA ƘAWATA JIKI DA KWALLIYA KUNA INA NE?._*


_Maza ku garzayo da gudunku ga mutunuyar taku maida tsohuwa yarinya ta sake dawo muku da sabon salo, sabon sunfarin kayan gyaran jiki na mayika da sabulai ƴan gaske💃🏻._


*Kayan kwalliya na mg's skin care zasu maidaki shalele ƴar ƙwalisa tamkar wata ɗan daren sha biyar koda kina da kishiya ƴar Morocco bata girgizaki ba, balle saurayi ɗan son ƙyale-ƙyale da ƙawa ga burwallensa😂💃🏻*.


_Kayan mg's skin care nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai.


*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*👌🏻


Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?
Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki
Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai😘
Soap:3k
Beauty kit:11k
Chat:08062991549
07046881166
07067210195
Call :07046881166
08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra'ayi🥰
Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin😪🤠aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu🥲
Yar shawarmannan duk nasaba😤 hilis kugarzayo arabani da kaya🤝
Nd guest what🤩
Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift😃
Pamper your skin🧖‍♀️
Shine like a bride👰🏻
Glow



*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


Slowly ya shiga bangarensa ya zauna kan kujera, yana maida numfashi a hankali. Kokari yake ya gano laifinsa amman ya kasa, sai kokarin ganin ya hade maganar da Kabir ya fada masa nan ma ya kasa, abun is so painful. Sai da ya hade yawu sannan ya mike tsaye ya nufi windows dinsa. Ya jingina da windows din ya kai hannunsa ya bude curtains din kofar yana kallon harabar gidan, for the first time ya ji yana marmarin ganin kakarsa, rabonsa da ita tun shekara biyu da suka wuce ita bata zuwa shi ma kuma baya zuwa, sai dai ya san duk wata Daddy yana aika musu da kayan abinci, idan lokacin sallah tai kuma sai ya aika musu da abun layya da dinkuna, amman ko kiranta a waya sai ya kwashe watanin be yi ba, abun da ya damu ne da shi kawai rayuwarsa ta nan, sai kuma Daddy da Momy, ya manta cewar yana da wasu familyn na mahaifiya bayan na mahaifi, amman a yau ya tuna saboda Kabir ya fada masa maganar data hana numfashinsa tafiya daidai. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya shiga ma'adanar lambobi ya nemo number kakarsa, ya aika mata kira yana kallon wayar sai da ta dauka sannan ya kara wayar a kunnensa.


“Ashe ko yau za ayi ruwa, Mu'azu ya kira ni da kansa”


Yayi murmushi tare da kai hannu ya shafa kansa.


“Kaka kina lafiya?”


“Ina nan lafiya kalau, sai ciwon kafa ya matsa min har yanzu”


“Subhanallahi zan zo na kai ki asibiti Inshallah”


“Kuna can birni kuna ta kula da wasu kun bar mu a daji, kamar ba mu da kowa, sunayen ku ma sai a radio muke ji, idan ba mu dauki waya mun kira ba kiran ayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login