Showing 12001 words to 13395 words out of 13395 words

Chapter 5 - JASEENA COMPLETE Book by Jeeddah jao.txt

29 Jan 2025

1993

yi dadi ba ! In kin isa yadda na saka tsaro dinnan ki karaso kiga me zai faru! Amma ko da yake ina so inyi magana da ke ,kuma ke kadai don haka ke kadai nake so ki zo ki sameni babu makami kuma !!! Ya sake burgewa da wata muguwar dariyar. Jaseena da idanuwan ta sun kad’a sun yi jajir ta kau da kanta daga duban da take masa tace KAI !!!! MATSORACI!!! KAI NE KAKE TUNANIN TAKOBI KO BAKA SHINE ASALIN MAKAMI ,AMMA ASALIN MAKAMI A ZUCIYA YAKE!!!!” Ta zubar da makaman zata tafi su Jauda suka sha gabanta Aisha tace ” Jaseena ba zamu barki ki shiga ke kadai gurin wad’annan azzaluman ba gaskiya” Jaseena tayi murmushi tace Haba Aisha ,ai koda kashe ni zasuyi inshaa Allah zan shiga kuma zan d’auki fansa!!:evil: ta wafce hannun ta tayi ciki duk fadawan suka bita da kallo 🙄


Shiganta kenan su Haidar suka iso gurin ,garin ma shiru kamar babu Kowa , a nan ya iske su Jauda cikin matsananciyar damuwa , suka sanar dashi duk abunda ke faruwa hankalinshi ya tashi Rizwan yace ” yanzu meye abun yi ??¿
Jaseena kuwa da ta shiga kai tsaye fada ta nufa shiganta kenan taji an rufe k’ofa ta juya da sauri don taga wanene daga cikin su, Muryar shi ne ya fara ratsa kunnuwan ta tabbas sarkin yak’i Amjad ne:oops: ta waro ido waje tace ” kai ! Dama Kaine?!! Me kake yi a nan kuma?!!” Ya matso kusa da ita ya makureta a bango kamar me neman kasheta ,sai taji yana mik’a mata abu a hannun ta ,tayi amfani da tunanin ta taji ashe karamar wuk’a ce tayi wata k’aramar dariya yace ” godiya nake” shi kuma ya hankad’a ta gefe ta zube a ‘kasa su Jalalud-deen kuma basu san wainar da suka toya ba sai wani dariyar keta sukeyi. Jalalud-deen ya karaso inda take rik’e da irin kibiyar da aka harbi Hameed yace ” ban sani ba Jaseena ! Ko tayaya zan fara gamawa da ke ! Ko in sambad’e ki da wannan takobin ne kokuma wannan kibiyar wadda itace silar barin ubanki da uwarki duniya?? Ko kuma………… Kafin ya karasa ta buga masa wannan y’ar wuk’ar a daidai mak’ogoro kamar me bud’e madarar peak 😜 tuni ya durkusa kan gwiwar shi ,Jini na malala kamar ruwa, ta zare wuk’ar tace ,ba sai ka za6a ba🙄 take ya fadi ‘kasa ya gama shure shuren sa har ya margaya (Hmmmm duniya kenan budurwar wawa akan son abin duniya har ka kai kanka ga halaka!!) Ta juya ta dubi sarkin yak’i tace” ina Hasheem? ” ya nuna mata k’ofar fita yace ” ya fice tun tuni! Mu bishi!!!!! Jaseena tayi wata muguwar dariya tace Kar ka damu ,yayi gudun gara ne ya tadda zago don nasan yanzu haka jikina yana bani ZAKI NAH!(Haidar) ya riga ya iso 👣


Suka dunguma sukayi waje suma, ko da suka fita basu tarar da Hasheem a raye ba amma kuma kamar mutuwar kasko sukayi da Jauda😭 da gudu Jaseena ta yo kan Jauda da ke Kwance a gurin matacciya ta rungume ta ,kuka takeyi duk ta susuce su Meenah ma na durk’ushe a gaban su suna kukan. Haka ranar Jaseena ta kwana tana kukan zuci wanda yafi kuka ciwo😭……………


🏵Jeeddah ja’o🏵
[4/8, 10:20 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


9⃣6⃣⏭1⃣0⃣0⃣


BAYAN SHEKARA D’AYA


Zaune yake kan kujerar mulkin sa yana magana da waziri Jabeer ,sarki Haidar ne cikin kaya na alfarma na sarauta sai hira sukeyi wanda har masu gadin ma suna saka baki , ana ta raha, chan waziri yace ” Allah ya baka nasara zan iya yafiya yanzu?” Haidar yayi murmushi yace me zai hana ? Ko so kake kayi tafiyar dare baka ga yamma ta kawo kai ba ? Waziri Jabeer yayi murmushi ya mik’e ya nufi hanyar fita.


Dank’o ne a hannun ta irin na Harbin tsuntsaye ta saita shi a kan kujerar ta sake masa daya a hannun shi ,ko girgiza bai yi ba ya basar ,har tayi sau uku ,sannan ya juya don ganin me aikata masa hakan. Had’a idon da zasuyi kuwa ta zaro manya manyan idanuwanta da suka sha ado da kwalli:oops: sannan ta tattare doguwar rigarta ta ruga a guje ta fice zuwa lambu , murmushi kawai yayi ya mik’e ya kwashi duwatsun da ta jefo mar ya fice ,bai ma san inda ta nufa ba shidai kawai yana ta kallon yadda mutane Kowa ke gudanar da alamuran shi cikin lumana wasu yara kyawawa sun kai biyar suka rugo da gudu suka rungume shi suna dariya ,sai d’aga su sama yake yi yana musu wasa wata tazo wucewa dauke da kwando cike mak’il da kayan marmari ya tsayar da ita ta kawo ma yaran ,sai tace ” Allah shi taimake ka Sarauniya JASEENA ke da buk’atar su ” murmushi yayi yace ” ki basu sai a kai mata wasu , tana ina ne itan?” Matar tace tana cikin lambu ” gami da mik’a masa kwandon ta wuce. Shi kuwa ya durk’usa gaban yaran ya ajiye musu kwandon yace ” bismillah! ” kowannen su ya d’eba shima suna ta Saka mishi a baki sai da yaga sai loda mar suke ya mik’e da sauri yace ” Yauwa maza ku cinye kafin na dawo ya wuce ya barsu suna ta fama ,ba ma mutane ba har dabbobi ma sun san akwai y’anci a Ramali:).


Lek’o ta yayi suna had’a ido ta ruga da gudu ya bi bayan ta sai fama take da doguwar riga hakan yasa ya cimmata ,ya d’aga dutsen data wurga masa kamar zai rama sai yaji daga waje wani mayak’i yace ” Allah ya baka nasara sarkin Kalahari Rizwan ne tafe da Sarauniya Meenah!!!! Jin hakan yasa ya sauk’e hannun shi yace ,a shirya tarbar su ,kuma a sanar da sarkin gida ” mayak’in yace toh ranka shi dad’e! ” sarki Haidar ya maida dubanshi ga Jaseena yace ,kin taki sa’a yau da sai na rama jifan da kika min!!” Ta rungume shi tana ta dariya tace ” kai dai kace kaji tsoro Kar na fille maka kai yanzun nan 😝 ” ya bushe da wata irin dariya yace ” ni din ? Toh ko za’a gwada karfi ne?” Ai ko bamu gwada ba kasan na fika k’arfi 💪🏼” ya sake bushewa da dariya yace ” karfin cin tuwo ba! Yanzu ma naga an taho da k’aton kwando cike mak’il da kayan marmari Wai naki ne 😜 ” Tuni ta had’e rai tace ” toh ai kasan ba ni kadai bace shi yasa 😒 ” ” Ohhhhh na gane !!! Kar kiyi ma d’ana sharri ,ke kad’ai kike cin kayanki ☺” ta bugi kirjin shi da hannun ta tace ” zan rama ai!!!” Ya kama hannunta suka fita suna tafe yana tsokanan ta………..


Haka dai rayuwar su ta kasance cikin farin ciki da kaunar juna ,ga gaskiya da rikon Amana ,sukan ziyarci junansu daga su har su Rizwan ,Aisha ta auri abokin Rizwan ne majeed aka kuma suka zauna a gidan Benaxir don yanzu kam bata nan dama ba gidan ta bane mallakin su Aisha ne ,majeed kuwa likita ne don babu wani magani da bai san amfanin shi da kuma yadda ake hadawa ba!! Saboda haka wannan babban gida ake kiranshi da gidan majeed likita!


Akwana a tashi yaran Jaseena biyu ,na farkon sunan mahaifin ta ne wato HAMEED na biyun kuma mace ce mai sunan JAUDA yara ne kyawawan gaske son Kowa !
Bangaren Meenah kuwa danta daya mai sunan mahaifin Haidar wato MAHMOUD! Aisha kuwa mace ta Haifa sunan ta Sameerah sunan kanwar majeed da ita ,gaba daya suna cikin farin ciki ,nutsuwa da kwanciyar hankali ,zalunci ya kau!!!!


🙏🏽ALHAMDULILLAH🙏🏽


Godiya ta tabbata ga ubangiji Allah mai Kowa mai komai wanda ya kawo ni har izuwa wannan ranar da na kammala wannan takardan nawa mai suna JASEENA !!


Dama ance in kaki sharar masallaci zakayi ta kasuwa ,kuma abunda kashuka shi zaka girbe , masu iya magana sunce RABON KWAD’O BAYA HAWA SAMA!!!
Duk abunda Allah ya kaddara zaka samu tabbas babu makawa sai ka same shi ,amma in kasa son zuciya toh lallai zai zamto sanadiyyar zubar ruwan idanuwa a gareka 😭 Allah kasa mu dace AMEEN


ALL CREDITS GOES TO
MY BESTIES
– Rukayya Abdullahi Kakumi (Rukey kaxs)
– Aishat Muhammad (maman abd Shakur)
– Sufeeyah abdoul
– mah Nancy trbl
-my ‘kawas Zeetu and Zainab Ahmad…..
And Ameener esmael( maman Ilham)
GODIYA TA MUSAMMAN
AJAJIGEEE GROUP
ZINARE BOOKS
SADAU GROUP OF WRITERS !!!
AND OTHER MEMBERS OF JEEDDAH JAO 📚NOVELSTOPIA🏵












DICUMENT MADE BY °°°°√••••°°°°°°SALMA°°√••••

3
4
5

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login