Showing 6001 words to 9000 words out of 23188 words
Chapter 3 - KAI NE GATANA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY FIDDAUSI SODANGI .txt
bacci kake is tym 4 my story, "Tahau birgima ajikinshi tana wakeup, duk da rigar jikinta nada kauri sosai amma yanda take goga mashi jikinta ajikinshi yasa kasala ta saukar mai,
" tunkudata yayi tafadi akasa ya Mike, daidai lokacin Umar Faruq
Ya shigo dakin yana fadin ya Haydar naje har gidan nasu amman tace ita bazata tahoba a can zata kwana, nikuma nayi tahowata,
"Kausar jabaya tafarayi a zaune tana neman hanyar guduwa, amma yariko hannunta yace waike wace irin mace ne? Namiji ne abokin wasan ki?" Yauzakici gidanku
"Waya gaya maki mace na wasa da maza?" Bakisan babu kyau ba! Sorry yaya wlh baxan sake ba.pls. idanuwansa ya kura Mata aikuwa da saurinta ta runtsa ido dan kuwa bala'in tsoron idon sa takeyi.ya Kama kunninta yaja da karfi tasaki ihu wayyo ya Aliyu pls am sorry baxan sakeba pls. Wlh idan kika kuma sai na cire wannan dan iskan bakin naki! Yasaketa aikuwa ta zura da gudu sai da takai dakinta sannan ta tsaya tana haki. Aikuwa tana kwanciya bacci ya dauketa cike DA tsoron Aliyu Haydar gadanga kusar yaki!
"Da safe suna zaune a parlour suna kallo itada mummy kanta na bisa cinyar mummy tanata zuba Mata shagwaba tana bata lbrn cartoon dinda akeyi sunata dariya.saiga Umar Faruq nan ya shigo, da gudu ta mike ta rungume shi tana fadin i miss u bro yau bangan kaba tun dazu Ina kashige? Sorry kausar naje unguwa ne , na manta ne jiya ban fada maki ba. Ta zunburo baki tasake shi ta juya masa baya tace kasayo min ice cream din?" Yace no sai anjima sai muje musayo ko? Tace A'a tare da bata fuska zatayi kuka nidai gaskiya yanzu nakeso mum ba tun dazu nake jiran Saba? Mummy tace gaskiya kuje asayo Mata.
"Tsalle takama yi tanajin dadi ahaka suka fice sanye take da riga da wando kanta ko dan kwali babu, Umar Faruq na rike da hannunta,
"Sun shiga motar zai tada kenan sai ga ya Aliyu nan yace Kai! inazaku haka!?"
Umar Faruq ne yace ice cream zamu musayo Mata. Ice cream?" Bataci abinci bane?" kobabu abinci a gidan ne?" da tsawa yake maganar da allah kufito Ku wuce Jo!!! dubeki!! Kalleki! ko dan kwali babu akanki amman wai ahaka zaku fita! Sai na karya maki kafa idan baki kiyayeni ba wallahi! da gudu ta ruga cikin gidan tabarsu nan tsaye yana cigaba da masifar sa,
"Jikin mummy tafada tasaki kukan ta mai bala'in cin rai da tsuma zuciya.a gigice mummy ke tambayan ta lfy me yafaru ina faruq din yake?" Kuka kawai takeyi itakuwa mummy hankalin ta ba karamin tashi yayi ba suna ahaka yayi sallama yashigo tsit Tayi ta hade kukan nan tamkar ba itabace take ta rusa ihu ba.
" Yace au kuka kikeyi? dasauri ta mike ta rike baki tana girgiza Kai no! Ba kuka nakeyi ba! Abinma dariya yabashi yadake yace tome kikeyi?" Mum tace wai dama Kaine kasata kuka?" Aliyu wai meyasa kakeyin haka ne wlh banajin dadin abinda kakeyi Sam tunda kadawo yarinyar nan atakure take inadalili ni kam banison haka gaskiya! To mummy menayi Mata dan kawai nace baxa a siyo ice cream ba?" Au wai hanawa kayi dama?" to wlh maxa ka tafi kasayo Mata inajiran ka yanzu kuma!
"Harara ya watsa Mata yace Bari kallo na Ana min magana kin tsareni da ido! dasauri ta runtse ido harya fice sannan ta bude.mummy Nata lallashinta.
"Towai mummy meyasa bazai koma gidan saba yake kwana mana a gida?" Ina matar tasa ne?" Nidai gaskiya mummy ki koresa yakoma gidan sa, wallahi ni nafison yaya umar, meyasa kika haifi ya Aliyu mummy bayada kirki fa! Murmushi kawai mummy tayi taka ra rungume ta, kausar takara shigewa jikinta tace mummy kuma kice masa yadaina cemin yar bak'a banaso! Banaso! Wai bak'a! Aidai bak'ina mai kyau ne ko mummy?" Murmushi mummy takuma yi tace ai kinma fishi kyau y'ata,
"Ranan monday misalin 2:30 umar faruq ya daukota daga skul yana ajeta yajuya yace Mata wani waje zashi.
" Jakanta ta goya a bayanta da gudu tashigo cikin gidan mummy nazaune a parlour tana karanta newspaper ta fada jikinta tana fadin am back mum mummy ta rungume ta tana shafa bayanta mum yaufa anbamu assignment bari kigani tasauko kasa ta zazzage littafan duka akasa tana niman book din da assignment din keciki can tace la!!! la!!!! Wlh mum sainabi zainab Muktar gidan su yanzunnan wlh ta dauke min book Dina ta mike ta nufi kofa mummy ta rukota tana fadin sorry my baby Kibari gobe idan kuka hadu a skul sai ki karba kuka ta fashe dashi tana cewa no! Mum no! Niyanzu xani! Mummy Nata lallabata dakyar dai tai hakuri kancewa gobe ta karba din.
Amman wai ita saitaje ta gayata da yaya Umar dinta saiya Zane ta gobe.mum tace to kije kicire kaya idan kikai wanka kikai sallah sai kixo kici abinci kinga sai kije Kai karar ko?" Ina ai da gudu ta fice ta nufi side dinsa, tana tafiya duwai nannan na kadawa kamar wata babbar budurwa, koda yake 16yrs aiba nan kusa bane, Uniform din riga da skirt din Iya gwaiwa sai dan hijabi Karami Iya wuya.kayan sun bala'in yimata kyau kamar ba uniform ba.daidai kwanan daza a shiga side din akwai wani lungu dan karami harzata shige sai taji kamar Ana magana kasa kasa aikuwa lungun ta nufa tana fadin waye ne awajan nan?" Ido hudu sukai da ya Aliyu yana zaune bisa kujerar roba hannunsa daya rike da waya akunninsa alamar waya yakeyi daya hannun kuwa sigari ne yake zuka (Taba) yana wani fesar da hayaki cikin kware wa. Ai kuwa da sauri takama ja baya tana kare fuskar ta da hannu alamar wai ita bata ganshiba. Yace ke!!!! Mekikazo yi anan? Jikinta na kyarma take fadin Allah ban gankaba wlh ko ganinka banyi ba.nibanma ko kallekaba Allah ya Aliyu!!!!
" Dariya ce taso kufce masa yace tocewa nayi kin kalleni?" Ta girgiza Kai yace waya koma inda kika fito! da gudu kuwa ta ruga yace keee!!!! Zonan!! Ta dawo tana jujjuya hannunta alamar ban hakuri sai kuma ta rike kunni tana motsa baki alamar pls am sorry dinnan.yace idan naji kingaya ma wani kinganni inashan wannan ya daga Mata sigarin hannun shi yace sai na yanka maki wuya na huda cikin ki!! Ido ta zaro alamar tsorata tace wlh ni banma gankaba! Yace gud kina Iya tafiya.ta gudu ta ruga ya fashe da dariya abinda baitaba ba.first time in history.......
Fido sodangiš
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] āŖ+234 813 502 2313ā¬: šKAINE GATANAš
4ā£0ā£to4ā£5ā£
NA FIDDAUSI SODANGI
Ā©TASKAR MARUBUTAš
"Tun daga bakin gate kausar ke jin hargowar Aliyu Haydar da alamar ransa a bace take, "dawowar ta daga islamiyya kenan, lefewa tayi a jikin k'ofar tana mai tsoron shiga, "kalaman dake fita a bakinsa yasakata natsuwa tana saurare, "A'a mummy! "Maganar Allah fa ba son zuciya ba, tayaya za ace k'atuwar budurwa kamar kausar ace tana irin wannan sangarta?" Yarinya sam bata san wani wai wannan namiji bane baligi bai kamata inayi masa kaza ba, baidace ni ina kaza ba! Haba mummy! Karfa ki manta yarinyar nan amana ce a hannunki! Na rantse da Allah wannan wasannin banzan dasuke aikatawa itada Umar Faruq haramun ne! Saboda ba muharraman sa bace! "Kai koda ma ace muharraman sace bai dace ba wallahi mace fa take! Gaskiya lamarin gidan nan akwai gyara wallahi sosai aciki dan wannan ba waye wa bace wallahi! Muji tsoron rannan da Allah zai tambaye mu, "mummy kiyi tunani ki duba maganata idan kuma ranki ya baci akan abinda na fadi to Allah ya huci zuciyar ki Amman wannan kam wallahi ba cinye wa bace!
"Waini abinda ma ke bani mamaki yarinyar nan fa tashin k'auye ce! To yaushe tayi irin wannan wayewar haka?" Acewai budurwa y'ar shekara goma sha shidda amman tana irin wannan sangarta saikace d'iyar goye?" Hmm! Allah ya kyauta, nabarki lafiya,
"Daidai k'ofar fita yaci karo da kausar wacce ke rakube gefe sai hawaye ne ke gudu bisa fuskar ta, tsayuwa yayi cak yana kare mata kallo,yaji dadin da Allah yasa tajiyewa kunnuwanta zancan sa, dan haka batare dayace mata uffan ba yai tafiyar sa,
"K'arasawa cikin falon tayi ta zube a jikin mummy tana wani irin kuka mai ban tausayi, mummy kanta shuru tayi takasa cewa komi illah bayanta datake d'an bubbugawa, sai da tayi Ku kanta iya son ranta sannan tafara magana cikin rawar murya, "hakika mummy abinda yaya ya fad'a gaskiya ne kuma nayi alkawarin cewa insha Allah zan canza halina daga yau zan gyara, ta tashi da gudu ta shige d'akinta tana mai cigaba da kukan nata,
****************************
" BAYAN SHEKARA UKU"
****************************
"Abubuwa sun faru sosai a wannan shekarun dasuka wuce ciki kuwa harda kammala karatun Kausar na secondary school,
"Kausar anzama babbar budurwa,Allah yayi mata k'ira mai daukar hankali komi na jikin kausar a cike yake,duk kayan data saka sai sun karbeta sunyi mata bala'in kyau gata dai bak'a kirin amman kuma bakin ta mai kyau ne,
"Soyayya suke itada Umar Faruq abin babu kama hannun yaro,wata irin soyayya ce mai wuyar fassarawa, suna bala'in son junansu sosai,
"Zaune suke a harabar gidan akan wasu kujerun roba suna fuskantar juna, "kausar meyasa kikeso ki ringa wahalar da zuciyata ne! Nace maki ki bari insamu abba da maganar mu amman kinki! Why?" Why?" Meyasa kike hanani mekike tsoro ne iyee! Yaya umar dan girman Allah ka rufa min asiri! Wallahi Allah ina tsoron faruwar wani abu, "A fusace ya mike tsaye yana fadin mekike tsoro meye shi abinda kikema tsoron faruwar?" Kausar kodai baso na kike ba! Idan baki sona kigaya min ki daina wahalar da zuciyata da gangan jiki na! Kifito fili ki gaya min cewar baki sona! Amman bawai kiyi tamin wasa da hankali ba ki dubenifa ni ba yaro bane yakamata ace na dade da aje iyali! Amman na tsaya inata jiranki nayi rainonki har kin girma na jure duk wani gori da ake min akancewa naki aure na toshe kunnuwa na amman sai ki zauna kina raina min hankali a banza a wofi! "Fashewa da kuka tayi tana fadin ba haka bane yaya Umar wallahi ba haka bane ina sonka ina kaunar ka bansan yanda zanyi maka bayanin irin sonda nake maka ba! Amman.....katseta yakarayi a fusace jikinsa har wani rawa yakeyi Amman me mekikeso ki gaya min kausar! Yaya Umar ina tsoron ya Aliyu......dasauri ya kuma katseta cikin rawar murya yace bangane kina tsoron Aliyu ba! Mekikeso ki gaya min iyyye!!.......... Gaba dayansu hankalin su yakoma kan gate din gidan da mai gadi ya wangale yana wani rawan jiki, motar sabuwace dal wace tashigo gaba dayan ta tint ce bak'a wulik babu yanda za ayi na waje ya ga naciki, motar tazo ta parka har a gaban su dukda cewar ba wajan parking bane wajan, "kusan minti uku sannan nacikin motar ya fito bayan ya kare masu kallo tas cikin kuluwa ya nufosu, zuciyar kausar tamkar zata tarwatse dan tsananin tsoro da gudu ta nufi cikin gida tabarsu nan tsaye kowanne zuciyar sa na bugawa tamkar zata fito waje................
Fido sodangiš
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] āŖ+234 813 502 2313ā¬: šKAINE GATANAš
4ā£5ā£to5ā£0ā£
NA FIDDAUSI SODANGI
Ā©TASKAR MARUBUTAš
"Wani irin mugun kallo Aliyu kewa umar wanda zuciyar sa ke tafasa yana kissima wani abu a zuciyar sa, "k'awafa Haydar din yayi sannan yai wani irin taku zuwa gaban sa ya nuna sa da d'an yatsan sa yana fadin nalura kamar kanka na rawa kwanannan ko?" To wallahi wallahi ka kiyayeni! Na rantse da Allah bakin rijiya bawajan wasan yaro bane! Kuma karka manta BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE! "Yajuya a fusace zai bar wajan, Umar Faruq yayi saurin tsaidashi dafadin hyyy!!!! Dakata Malan!!! Ya isa har inda yake sannan yashigar da idanuwansa cikin nasa, cikin d'aure fuska yafara fadin nifa ban fahimce kaba bansan mekake nufi ba ban san manufar kaba wannan tada jijiyoyin wuyan nameye?" Yakama kafito ka fiddani cikin duhu......wani mugun tsaki Aliyu yayi yace lallai yaro wuyar ka ya giga! Tunda har kake iya kallon cikin ido na ka gaya min magana! Yayi k'wafa yabar wajan,
"Kausar jikinta na k'yarma ta shigo falon mummy na zaune tana kallo tazo ta wuce ta a guje zuwa d'akinta, mummy tabita da ido tanason kiranta amman bakinta yai mata nauyi, ajiyar zuciya kawai ta sauke taci gaba da kallonta abinta,
"A fusace Aliyu ya shugo ganin mummy zaune yasashi natsuwa ya d'uka yace mummy barka da maraice kun yini lahiya?" Lahiya kalau ya matar taka?" Wallahi batajin dad'i shinema nazo in dau kausar ta dan tayata dawasu aiyuka kafin Allah yasa ta warware, amman dai kasan kausar bason ta tafi wani waje tabar ni takeba ko?" To mummy ai lalura ne kuma dataji sauki ai saitayi dawowarta ko, to shikenan tana d'aki saikaje ka gaya mata ai amman fa idan bata yardaba baza a takura mata ba sai animi yanda za ayi! Baice komi ba shidai ya nufi hanyar d'akin mata,
"Zaune take rike da wayar ta a hannu ta kura masa ido tamkar meson gano wani abu acikin wayar, saidai da alama hankalinta ba nan yakeba, turo k'ofar da akayi ne yamaido da hankalin ta kan k'ofar, mikewa tayi jikinta na rawa tace ya Aliyu yakamata kayi min uziri haka nan! Karka manta a yanzu nagama makaranta idan kace.......rufemin baki stupid kawai! Mekikeso ki gaya min?" Haka mukayi nida ke?" Girgiza masa kai tayi hawaye na gudu bisa fuskar ta, kausar wallahi wallahi yazama dole ki aure ni koda kuwa baki so! Bawai nace ki soni bane A'a aure nane yazamar maki dole! Idan kuma kince taurin kai zaki min tokuwa zakisha mamaki wallahi Allah kinji na rantse maki! Ke in banda ma rashin hankali Umar Faruq fa kaninane kinsani to danme zaki ringa kulasa bancin tunba yau ba nagaya maki ki kiyayesa sau nawa zangaya maki ne?" To wallahi za ayi yaki a cikin gidan nan duk ranan danakuma ganin ku atare! Kuma ki shirya ki dauki wasu daga cikin kayanki gida na zamu sai inga idan akwai dan iskan daya isa yazo min gida! Wuce ki hada kayanki mutafi karki batan lokaci!
"A razane take kallonsa bakinta na rawa tace ya Aliyu ka rufa min asiri kabarni a gidan nan dan girman Allah..........tsaki yayi yawuce wajan ajiyar kayan nata, wani empty akwati ya jawo yashiga loda kayanta aciki duk wanda hannunsa yaje kai kawai yake jawowa, saida ya cika shi tam ya rufe sannan yajawo hannunta da k'arfi ya fisge ta zuwa falon ganin mummy bata falon yasashi cigaba dajanta har zuwa cikin motarsa, kuka kawai ta fashe dashi tana kallon irin wannan karfin hali da Aliyu Haydar yake gwada mata, k'atuwar budurwa kamarta amman yake yi mata duk yanda yaga dama itakam gaskiya ya takurama rayuwarta yakamata ace zuwa yanzu ya shafa mata lahiya..............
Fido sodangiš
Dedicated to
KAUSAR M HASSAN
(Kausar luv)
[12/5, 3:57 PM] āŖ+234 813 502 2313ā¬: šKAINE GATANAš
5ā£0ā£to5ā£5ā£
NA FIDDAUSI SODANGI
Ā©TASKAR MARUBUTAš
"Gudu yake ta shararawa bisa titin tamkar wanda aka biyo, "A tsorace take dubansa ganin fuskar tasa babu annuri yasata saka fuskar ta acikin cinyoyinta, " wai meyasa ya Aliyu yakeda bak'ar zuciya ne?" Ita kam sam baya burgeta.......wani irin burki yataka jikake kuuuuuu!!!!!!!!! "Cikin tsananin firgita kausar ta fad'a jikinsa ta kankamesa jikinta sai rawa yakeyi, "wani irin shock ya ziyarce shi tamkar wutar nepa ne yaja shi, dasauri ya hankad'a ta ke bakida hankali ne! Bakiga tuki nake ba?" Yi hakuri yaya tsoro ne yakama ni, bai kuma cewa uffan ba har suka isa tangamemen gidan nasa,
"Matar gidan ce a hakime cikin daya daga cikin kujerun dake falon, tana wani taunar cingum ta daura k'afa daya bisa daya tana kallon tashar zee aflam, da alama hankalin ta ya dauku bisa kallon, sanye take da riga da wando kanta ko d'ank'wali babu, tasha kwalliya kamar wacce zata gasar kwalliya,
" Aliyu ne a gaba yayinda kausar ke biye dashi a baya, da gudu ummi Aisha ta taso ta rungume mijin ta tana basa kiss a kuncinsa tare da fadin i miss u sweetheart wlh kawai sai tashi bacci nayi naga har ka fice! (Hmm abin kunya tana can tana baccin asara har mijin ta ya tashi ya shirya ya wuce office batama san anyi ba dan tsabagen lalaci! Injini fido)
"K'ara kankameta yayi yana fadin my ummi kin cika lalaci sosai! " turo baki tayi tana cusa kanta acikin k'irjinsa alamar taji haushi, dago kanta yayi ya hade bakinsu waje daya yana tsotsa gaba dayansu sun wani lumshe ido suna jin dadin sak'onnin dasuke aikama juna k'afafuwansu ne suke niman su gagaresu tsayuwa hakan ne yasashi sunkutar matar shi zuwa dakin baccin su,
"Kausar dake tsaye tamkar wata gunki ta fashe da kuka wannan wani irin iskanci ne haka?!! Wallahi itakam bazata zauna ba tafiyar ta zatayi, Ak'watinta tafara ja tana kokarin ficewa a falon,
"Shi kuwa Aliyu Haydar yana d'ire ummi bisa gadon sa tamkar kuma wanda aka tsikara dasauri ya nufi k'ofar dakin ya fice, hangota yayi tana k'okarin ficewa daga gate din gidan, keee!!!!! Cak ta tsaya batare data juyo ba, ina kike kokarin zuwa ne?! Yayi tambayar a fusace, gida zankoma! Tafada batare data dubesa ba, kina wasa dani ko?" Na rantse da Allah saina tattakaki idan baki kiyaye niba Allah kuwa! Hannunta yajawo da k'arfi itada akwatin nata har zuwa cikin gidan.
*****************
"Mummy wai ina kausar ne ni bansan menayi mata ba taketa fushi dani ba inata kiran wayar ta taki ta dauka naje k'ofar d'akinta inata bugawa taki ta bude min......au! Bata sallmeka ba kaima?" Wallahi ni kaina bansan sanda suka fice ba nasan ba son zuwa take ba shiyasa tayi fishi ta tafi babu sallama, ina taje mummy?" Tana gidan Aliyu wai matarsa bata lahiya.......gidan Aliyu?! A fusace ya mike tare da nufar k'ofar fita, cikin rashin gamsuwa da yanayinsa mummy takirasa Umar!! Juyowa yayi ya dubeta, zonan! "A sanyaye yadawo ya zauna zuciyar sa na tafasa, meke faruwa ne kaida Aliyu a yan k'wanakin nan naga kamar akwai abinda kuke boye min a tsananin Ku?" No! Babu komi mummy kawai dai kinsan kausar bawani shiri sukeyi da shi yaya Aliyu ba so bazata wani sake a gidan