Showing 39001 words to 42000 words out of 64131 words
Chapter 14 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf
Shi dai bai tsaya jiran jin karshen zancen anty ba ya, ya rike maryama ba wai dan yasoba, tana
rab'e a kirjinshi ya ziro daya hannunshi ta bayanta ya rike kugunta, karshen kyau ma'auran
sunyi kuma sun hadu duk wanda ya kallesu bazai iya hakuri ba sai yaji ya sake maimaitawa
gwaurayen wurin kuwa take suka fara burin suma kasancewa a irin wannan rana,
Suna shiga cikin hall din kowa da kowa ya mike tsaye, su anty maijidda da anty babba na biye
dasu har suka hau kan dining table,
Sai da shaddad yaje ya zaunar da maryama akan kujera sannan shima ya zagaya ya zauna a
kusa da ita domin wata kujerace ta alfarma aka ajiye musu wadda tasha decoration,
Yanayin kujerar yasa dole sai da suka matsi juna domin bata da fadi sosai girmanta bai kai na
two sitter ba dan haka dole manne suke da juna,
"Ina son kisani na aureki ne kawai domin yin biyayya ga mahaifiyata bawai dan so ba saboda ko
sau daya ban taba jin sonki acikin zuciyata ba kuma nasan bazan sokin ba har abada domin
inada wacce nake so yarinya mai hankali,
Mai nutsuwa mai addini, mai kamun kai, sannan gata yarinya karama danya shakaf yar shekara
goma sha takwas ba irinki ba wacce ta tara shekaru ba aure..."
Duk da taji zafin maganganunsa sai bata ko tanka masa ba saboda nasihar da anty maijidda
tayi mata tun dadewa ita take tunawa inda anty maijidda take cemata,
"Maryama zaki samu shaddad kuma zaki aureshi amma sai kinyi hakuri sai kin jure, ko bayan
aurenku dashi dole sai kinyi hakurin zama dashi har zuwa lokacin da Allah zai karkato miki da
hankalinsa gareki.."
To duk lokacin data tuna wannan maganar ta anty maijidda sai taji sanyi taji cewar zata iya jure
duk wasu miyagun maganganun da zai jefeta dasu,
"Kuma ina so ki sani, wallahi zaman gidana zaman ukuba ne agareki.."
Ta jiyo muryarsa a saitin kunnenta, kai idan ba jin abinda yake fada kayiba zaka zaci wasu
kalaman soyayya yake fada mata ko wasu kalamai masu sanyaya zuciyar masoya saboda irin
yanda sukayi zaman, hatta cinyarta guda daya akan tashi take, gaba daya acikin jikinsa take
shikuma yasa hannushi guda daya ya zagayeta, gashi sai saitin kunnenta yake kai kanshi, dan
kamshi kam yashaki kamshi har ya cika masa ciki domin tako ina kamshi ne yake ambaliya
daga jikin maryama to amma shi shaddad sam ba kamshin ne sababin kai kanshi jikinta ba
asalima yana yin hakane domin ya kuntata mata.....
_Fans ku taya Ummi shatunku da addu'a mura nakeyi duk hancina atoshe, muryata adashe..
Luvs you all._
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_Thanks to my masoya masu yimin fatan samun lafiya, nagode muku sosai especially masu
kirana awaya da masu turo min text da duk wani wanda yadamu dani acikin mind dinsa...one
love_
*_35_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Ita dai maryama shiru tayi tana sauraren bak'ak'en maganganun da shaddad ke faman
fada mata, masu video da camera kuwa sai aikin haskasu suke domin ba karamin kyau suka
yiba,
"And last abinda zan fada miki shine babu zuwa club agidana, babu zuwa stadium sannan babu
zuwa aiki, mutukar kina son auren mu yaci gaba da numfashi to sai kinbar wannan aikin da kike
yi saboda nariga da nadade da sanin duk doctors din wurin abokan mu'amularki ne more
especially ma wannan karamin yaron da kike bibiya wanda baifi sa'an kaninki ba amma tsabar
jaraba irin taki binshi kike.."
Maryama ji tayi kamar zata fashe da kuka saboda tsabar bakin ciki domin har idanuwanta sun
fara kokarin kawo ruwa, sai dai kuma ta dade da yiwa kanta alkawarin cewa shaddad bazai
taba ganin kukanta ba wannan dalilin ne yasata yin gaggawar hadiye kukan bawai dan
zuciyarta ta daina kuna ba a'a kawai bata son yagano lagonta ne domin tasan muddin shaddad
yagane tana jin dacin maganganun da yake fada mata to zai cigaba da fada mata sune har illa
masha Allah,
Watsi tayi da al'amuransa ta mayar da hankalinta kan program din da aka fara gudanarwa,
Anty karama ce ta bude taro da addu'a sannan aka bayar da tarihin ango da amarya a gurguje,
daga nan kuma aka fara chashewa, ganin su anty maijidda sun fita suna rawa yasa maryama
kokarin tashi domin tana son taje tayi musu lik'i, amma kuma bazata iya tashi ba domin
shaddad ya matseta sosai,
"Zan tashi.."
"Na rikeki ne..?" Ya fada yana dauke kanshi zuwa wani wuri, kokarin tashi tafara ta samu ta
tashi dakyar ta nufi filin rawar tana tafiya ahankali saboda tsinin takalminta,
Liki tafara yi nan da nan wuri ya kancame, tana liki ana yi mata, shaddad yana daga can zaune
yana kallonsu, tashin shima yayi ya sauko ya nufi wurinsu,
Rafar kudi ya ciro daga aljihunsa yafara zubawa jama'ar dake cikin filin, yana tsaye a bayan
maryama sai kudi yake zuba mata, amma ita bata saniba saboda yanda taga yana jin kai bata
zaci zai fito yayi liki ba, daga ita har shi atsaye suke cak babu wanda yake yin rawa sai liki
kawai suke yi,
Kasancewar bata son hayaniya yasa taji kanta yafara juyawa, hakanne ma yasata niyyar fita
daga filin, tana juyawa taci tuntube da kafarshi nan tatafi zata fadi, cikin sauri ya tareta ta fada
jikinsa,
"Ka riketa ku koma sama.." Anty babba tace da shaddad da karfi tana ta faman tikar rawa,
Riketa yayi kamar yanda yayi mata lokacin da zasu shigo cikin hall din, har kan kujerar da suke
zaune ya maida ta ya zaunar sannan shima ya koma ya zauna,
Dafe goshinta tayi saboda ciwon da kanta ke yimata, ita dai kawai tana zaune ne awurin amma
bawai dadin zaman takeji ba,gashi duk ta takura ko yaya tayi motsi jin jikinta take acikin na
shaddad,
Bayan angama cashewa ne aka kira amarya da ango domin yanka cake, tashi suka yi suka
sauka zuwa inda cake din yake suka yanka ya dauka ya bata a baki itama ta dauka ta bashi
bayan ta dan rissina,
Fuskarshi babu yabo babu fallasa yake gudanar da komai, haka taron yaci ya watse,
Karfe 10:30 aka gama dinner din aka fito domin tafiya,yana rikeda ita ajikinsa har wurin motar
da takawosu,har zata shiga anty babba tazo tace,
"Ba a wannan motar zata koma ba, kar ta shiga tazo tare da ita zamu tafi, kai kaje kawai.."
Sakin baki yayi yana yiwa anty babba kallon mamaki ganin yanda taketa kaffa kaffa da
maryama, murmushi yayi yace,
"To shikenan anty sai mun hadu agida"
Saboda yasan dalilin da yasa anty ta hanashi tafiya tareda maryaman tunani take ko zai yimata
wani abu bayan itace bata saniba amma shi babu wannan acikin tsarinsa,
Gaban motar ya shiga sulaiman yaja suka tafi,
"Wallahi Navy kayi sa'ar mata, matarka masha Allah kyakkyawa babu wanda zai ganta yazaci
tayi wadannan shekarun.."
Shiru shaddad yayi bai tankawa sulaiman ba saboda yasan shi sulaiman din bai san wacece
maryama ba shiyasa amma shi dayake yasan wacece maryama sam kyawunta baya rudarsa.
Abangaren maryama kuwa da ciwon kai takoma gida saboda hayaniyar wurin dinner dinnan,
Suna zuwa gida khairat ta zuba mata ruwan wanka acikin dakin hajiya, ganin babu kowa acikin
dakin yasa maryama zuwa ta shiga wankan, lokacin data fito khairat na zaune da food flask
agabanta tana jiran fitowarta,
"Adda maryama wai me yaya navy yake fada miki lokacin da ya rikeki acikin mota ya hanaki
fitowa, nasan koma dai menene ba abu mai dadi yake fada miki ba.."
"Ba wani abu bane khairat, wai sarkar da nasa akafata yace sai nacire saboda kar mutane suyi
min mummunar fahimta, nikuwa banga laifin sarka akafa ba saboda wasu kwalliya ce kawai
kesasu sakawa bawai wani abuba.."
"Hakane adda maryam, ai naga kun dade ne baku fito ba shiyasa"
Murmushi maryama tayi ta zauna agefen gado tafara shafa mai marar maiko sama sama....
*_Ummi Shatu_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
*_36_*
~~~Dak'yar maryama ta iya tsakurar abincin da khairat ta kawo mata taci ta nemi wuri ta
kwanta, tun daga wannan lokaci bata sake ganin shaddad ba, hajiyarshi kuwa sai nan nan take
da ita cikin so da kauna domin tana tsananin son maryama,
Kwanansu biyu suka shirya aka yiwa hajiya sallama suka tafi Lagos, gidan Dada aka fara kai
maryama nan suka kule a daki Dada yana yimata nasiha akan tayi kokari tayiwa mijinta biyayya
sannan ta kasance mai rike sirrinta,
Kuka maryama tasha shi kamar ranta zai fita, dakyar anty maijidda ta samu ta banbareta daga
jikin dada, shi kanshi dadan shima saida ya goge kwalla saboda rabuwar da zaiyi da tilon yar
tashi,
Kai tsaye gidanta aka wuce da ita dama shi shaddad ya rigasu tahowa shida su anty Zainab
wadanda suka yi jere suka shirya gidan wasu kayanma basu gama shiryasu ba sai gobe,
"Wallahi ban so zamu kwana agidan nan ba naso mubawa yaran nan wuri su sakata su wala
suci amarcinsu" anty babba tafada tana kokarin zama agefen gadon maryama saboda bazai
yiyu su tafi yanzu ba dole sai dai su kwana tunda dare yayi,
"Babu komai ai iya yaune kadai gobe iyanzu mun dade da bar musu gidansu"
Anty maijidda tabata amsa, ita dai maryama tana kwance tana jinsu amma har ga Allah har
tafara jin tsoron tafiyarsu domin tasan zama zatayi irin zaman k'unci kamar yadda shaddad yayi
mata albishir,
Dayake agajiye take babu bata lokaci bacci ya dauketa tabar su anty maijidda sunata faman
hayaniyarsu suna hira ba ita ta tashiba sai da gari yawaye,
Wanka tayi ta shirya cikin wata dakakkiyar shadda light pink dinkin riga da skirt ne,daga rigar
har skirt din sunyi mutukar amsar jikinta, lokacin da ta fito tasamu har su anty maijidda sun
gyara mata gidan sun shirya sauran kayan da suka rage ba ajera ba sannan sun turare gidan
da turaren wuta mai kamshin gaske ga abinci nan kuma fal cikin kuloli wanda Dada yayi order
aka kawo musu daga wani hotel,
Ruwan tea kawai maryama ta iya sha daga nan bata kara iya cin komai ba har saida anty
maijidda ta zo ta tisata agaba sannan ta danci faten doya dan kadan,
12 narana nayi su anty maijidda suka fara shirin tafiya ai nan da nan maryama idonta ya kada
yayi jajur kafin wani lokaci har tafara kuka, ita kanta anty maijidda itama kukan take ita dasu
khairat babu mai rarrashin wani ahaka suka kammala shiryawa suka tafi suka barta ita kadai sai
faman kuka take, gashi wani abin karin bacin ranma unguwar barikice babu mai shigar
mata,haka tayi kukanta tagama babu mai rarrashinta, mikewa tayi ta kwanta akan doguwar
kujera saboda ciwon da kanta yake mata daga nan bacci ya kwasheta ba ita ta tashiba sai da
misalin karfe 2 saura yan mintuna,
Bedroom dinta ta shiga tayi salla ta sake yin wanka ta shirya cikin doguwar riga ta material
kalarsa purple, ta fito, dakin dake kusa da ita ta leka wanda su anty babba suka kwana aciki
nan ta ganshi shima ashirye da kaya kamar nata sai dai kawai kalar kayan sun banbanta,nan
tayita bin ko ina nagidan da kallo domin ba karamin kudi Dada ya kashe mata ba wurin zuba
mata furnitures hadaddu,
Daya bedroom din dake can gefe daya tanufa domin dama three bedrooms ne acikin gidan,
ahankali ta bude ta shiga daga ganin tsarin dakin tasan shine na shaddad saboda ga kayanshi
nan aciki sannan ga uniform dinshi nan shima akan gado, karasawa tayi ta debi uniform din ta
ninkesu tasaka cikin drewar ta fita,
Falo ta koma shiru ta zauna, daga karshe ta tashi ta hada kayan kallo ta kunna ta kamo tashar
mbc action nan taji dadi saboda suna nuna wani american film true blood a lokacin,
Tana kwance tana kallon taji an bude kofa anshigo, kanta ta daga ta leka, shaddad tagani ya
shigo yana sanye da kananan kaya,
"Sannu da zuwa.."
Tafada tareda kokarin tashi zaune saboda ita rabon da ta ganshi tun ranar dinner dinsu,
"Yawwa" shine kawai abinda yace ya wuce cikin dakinshi,
Kitchen ta shiga ta zubo masa abinci ta kai kan table ta ajiye tana jiran fitowarsa amma shiru
shiru bai fitoba ganin haka yasata tashi tabishi cikin dakin, kwance ta ganshi yana bacci dan
haka ta juya takoma falo taci gaba da zama,
Har karfe hudu tayi shaddad bai fitoba, tana zaune a falo akan sallaya bayan ta idar da salla sai
gashi ya fito, ganin zai fice yasata dakatar dashi,
"Navy ga abincinka nan akan table.."
"Kidaina raba abincinki da ni saboda baci zanyi ba"
Wannan shine kawai amsar da ya bata yasaka kai ya fice, da kallo tabishi har yafice,
Tagumi ta rafka tafara tunanin irin zaman da zasuyi dashi....
*_Ummi Shatu_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
*_37_*
~~~Zaman kad'aici maryama taci gaba dayi har dare yayi, nan kuma taji zaman yafara
damunta,daki takoma tayi wanka tayi shirin bacci cikin wata hadaddiyar doguwar rigar bacci ash
colour, kwanciya tayi tana jin shaddad ya dawo, a falo ya yada zango ya kunna kallo,
Ahankali ta lab'ab'a ta lek'ashi nan ta ganshi zaune yana kallo komawa tayi ta kwanta saboda
tasan dama babu abinda zai shigo dashi dakinta daga karshe dai har bacci ya kwasheta bata
san lokacin da yabar falon ba.
Misalin karfe 8 tafito bayan tasha kwalliya cikin dark purple din shadda dinkin riga da skirt,
kitchen ta shiga nan taga buhun semovita guda daya sai ko kayan tea,mamaki ne ya kamata
saboda tasan sai da mahaifinta ya cika mata store da duk wani abu wanda zata bukata, hatta
chocolate da biscuits saida ya hado mata dasu saboda yasan tana yawan mu'amula dasu,
Dakin shaddad ta nufa lokacin data shiga yana zaune a bakin gado yana gyara sumar kanshi
jikinshi sanye da uniform da alama fita zaiyi,
"Ina kwana?" Ta dan rissina tana gaidashi,
"Lafiya" ya amsa a takaice,
"Navy nace ko mukullin store yana hannunka?"
"Meya faru?"
"Zan dora girki ne"
"Baki ga wasu kaya awaje ba?"
"Nagani"
"To sune iya abinda zaki rinka dafawa kina ci.."
"Garin tuwo ne fa kawai sai lipton da sugar.."
"Ehh sufa, ko tuwo ba abinci bane?" Ya tambayeta yana kallonta saboda yadade da sanin babu
abinda ta tsana irin tuwo dan lokacin da yana zuwa gidansu yana jinta tana yiwa kuku masifa
duk ranar da taga ya dafa tuwo,
Bata kara magana ba ta fita zuwa kitchen ta shiga ta dora ruwan zafi,
"Lallai yaron nan mugune, wato nufinshi tuwo shine abincina kullum kenan? Tab"
Tafada ahankali,
Tea kawai ta hada ta fito kafin fitowarta har shaddad ya fita haka ta zauna shiru bayan tasha tea
din, waya tayi ta kira blessing akan tazo, nan blessing ta tattaro kayanta ta taho, adakin kusa da
na maryama ta ajiye kayanta ta fara dan shasshare gidan da goggeshi,daga nan ta shiga
kitchen ta yi musu tuwo miyar kubewa, ita dai maryama da yake ta tsani tuwo baifi lauma biyar
tayiba ta dauraye hannunta.
Suna falo zaune da yamma suna hira ita maryama har ta danji sanyi saboda zuwan blessing,
shaddad ne ya dawo yana shigowa ya tsaya yana kallon blessing wacce ke zaune a kasa ita
kuma maryama tana kan kujera tana yin game a laptop dinta,
"Ke mekika zo yi agidan nan?"
"Anty ce ta kirani tace nazo zan rinka tayata aiki"
"To ba agidan nan ba, baki da wurin zama agidan nan, aikin gidan nan ita zata rinka yin kayanta
idan kuma dole ne sai kinyi mata aikin to sai dai ta tattara ku koma gidansu sai kuje can kici
gaba da yimata aikin..." Yana kaiwa nan ya wuce cikin dakinshi,
Ganin idon blessing yayi rau rau zatayi kuka yasa maryama katseta,
"Babu komai blessing ai ba rabuwa muka yiba muna tare, dauko kayanki ki koma gida, bari na
dauko miki kudin okada"
Duk da abin yayiwa maryama ciwo amma haka ta danne bata nuna ba sannan tasan shaddad
yayi mata hakane saboda ya kuntatawa rayuwarta domin baya son taji dadin zaman gidansa,
1000 ta daukowa blessing ta bata ta tafi tana matsar kwalla, komawa falo maryama tayi ta
zauna tana tuna abinda shaddad ke shirin yimata, nafarko ya hanata aiki, ya kulle store ya boye
mukullin sannan gashi yanzu ya hanata zama da yar aiki yace itace zata yi aikin gidan gaba
daya.
Tun daga ranar maryama ta shiga damuwa kafin sati har ta rame saboda bata cin abinci domin
abincin tuwone ita kuma bata so gashi ya hanata siyo kayan abinci yace wallahi muddin yaga ta
siyo koda indomie ne sai ya dauki mataki, dan haka ta hakura bata siyo komai ba bawai dan
bata da kudiba sai dan hanawar da shaddad yayi, kullum cikin shan ruwan Lipton take ga aikin
gida wanda bata saba ba jikinta ma bai sababa, ga zaman kadaici nan abu yataru yayi mata
yawa, sanin