Showing 21001 words to 24000 words out of 64131 words
Chapter 8 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf
jini ne yake fita, yana fara dosota ta sake yin baya
tana shirin yin kuka....
*_Ummi Shatu_*í ½í±Œí ¼í¿»
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_Kuna raina akoda yaushe, Basma er lele, Nasma mai Kano, Umma yahaya musa
(marubuciyar goyon kaka), tareda Baby Rasheed...nagode muku Allah yabar zumunci._
aishaummi.blogspot.com
*_17_*
~~~Ja da baya take yana binta tana sake jada baya yana sake matsowa da haka har taje ta
tokaru da wani katon ice,
"Dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan sake ba..." Tafada idanuwanta sunyi jajur suna shirin fitar
da hawaye,
K'afarsa yasa ya take kafarta guda daya nan taji wani radadi ya shigeta, babu shiri ta bude baki
da niyyar kwalla ihu,
Cikin sauri ya katseta,
"Shhhhh, idan kika sake kika yimin ihu wallahi sai na lahira yafiki jin dadi,kin yimin karya kince
zanyi raping dinki to yanzu zanyi raping din naki dagaske...."
Hannu tasa ta toshe bakinta tafara jijjiga masa kai alamun yayi hakuri kar ya aikata abinda yake
shirin aikatawa,
Kafarta ya kama yajawota gabanshi ya direta, rufe idanuwanta tayi saboda ganin abinda ke
shirin faruwa gashi ita ba wani iya addu'o'i tayiba balle ta karanto,
Shi kuwa shaddad zuciyarshi sai angazashi take tana zugashi akan ya aikata hakan amma
kuma wani bangaren na daya zuciyar tashi sai hanashi take tana cewa,
"Haba shaddad kai da baka taba aikata zinaba koda wasa meyasa yanzu zaka aikata baka
tsoron haduwarka da ubangiji? Ko baka tsoron daukar cuta ajikinta tunda dai ba kamilalliya
bace ita..."
Shawarar zuciyarsa yabi na kawai ya kyaleta saboda ko yanzu yasan ta gane kuskurenta
sannan ta fahimci shi ba sa'anta bane tunda gashi nan har hakuri take bashi,
Mayar da belt dinshi yayi ya daura yana kallonta, jikinta inbanda rawa kamar mazari babu
abinda yake yi ta runtse idanuwanta ta gagara budesu,
"Mtsssss Allah ya sawwake na hada jiki da karuwa irinki wacce take bibiyar maza kala- kala,na
tabbata idan na kusanceki sai na dauki cututtuka barkatai...."
Shureta yayi da kafarsa nan ta fadi sharaffff, ko kallonta bai sake yiba ya juya yayi tafiyarsa
mintuna kadan ta daina hangoshi, duk irin radadi da ciwon da jikinta yake yi mata hakan bai
hanata tashi da rugawa aguje ba, gudu take iya fin karfinta kamar zata kifa,tana ji tana tattaka
abubuwa masu tsini suna shige mata cikin kafarta amma hakan baisa tafasa gudun ba,
Ko alamar shaddad bata gani bare ta saka ran zai sake biyota, kafin ta karasa gida tagama
jigata,
Kamar yadda shaddad yabar gidan haka ta sameshi a bude nan ta lallaba ta shige tayi
gaggawar hawa sama ta fada dakinta, kan gado tafada ta kankame jikinta wuri guda tana
kakkarwa,
Gaba daya jinta take ta kasa tuna koda abu guda daya saboda tsananin tsoro da razani hadida
fargaba da suka dabaibayeta,
Ta dade sosai kafin tasamu tadawo cikin nutsuwarta, ganin abinda yafaru take yi kamar acikin
mafarki aka yishi,
Sai alokacin ciwon da jikinta yake yi yadawo sabo nan kafafunta wanda shaddad ya tattaka
suka dauki ciwo gashi ko ina na jikinta radadi yake yi mata musamman ma tafin kafarta wanda
bai saba jin wahala ba gashi yau ta tattaka k'aya da sauran abubuwa masu shiga k'afa,
Tana nan akwance tana tuna yanda abubuwan suka faru har ta jiyo an shiga masallaci sallar
asuba,
"Shin yakamata na sanarwa da father wannan abun da yafaru kuwa..?" Ta tambayi kanta,
juyawa tayi ta sake gyara kwanciyarta,
"Idan har nafadawa Dada wannan abun to nasan bazai taba hakura ba har sai ya dauki
mummunan mataki akan shaddad gara kawai nayi shiru nayi hakuri sannan nabar abin acikin
zuciyata ni kadai.."
Wuta ta kunna saboda taji alamun ankawo, kallon jikinta tayi duk yanda rigar baccinta tayi kaca
kaca da kasa da tab'o,
"Ohhhh yaron nan gaskiya yanada karfi... Kalli fa rik'o daya yayi min nakasa k'wacewa.."
Haka tayita maganganu ita kadai amma ta rigada ta yankewa kanta hukunci cewar bazata
sanar da kowa abinda shaddad yayi mata ba har mahaifinta tunda dai Allah ya taimaketa bai yi
mata komai ba.
Bandaki ta shiga ta tari ruwan zafi cikin baho ta surka da na sanyi tashiga tayi wanka ta gasa
jikinta sosai saboda ko ina ciwo yake yimata,
Alwala tayi ta fito tayi salla sannan ta dauko first aid box dinta ta duba magungunan da ya dace
da ita a yanzu wanda ya kamata tasha,
Zab'a tayi ta dauki ruwa dake ajiye agefen gadonta tasha taja bargo ta lulluba lokaci kadan
zazzabi ya hau jikinta ga wani irin ciwo da kanta yake yi...
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/12, 10:18 AM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_Gaisuwa mai yawa ga masoyiyar ummi A'isha, wato Meenah 4eva tareda Khadija Magaji
bk,da duk masoyana gaba daya.._
*_18_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Kwana tayi da zazzabi ajikinta ga matsanannacin ciwon kai dake addabarta,
Misalin karfe 10 nasafe Dada ya shigo dakin nata saboda har ya kammala shirin tafiya office
rashin jin motsinta yasashi zuwa dubawa yagani ko lafiya,
Ido ta bude tasake rufe jikinta sosai da bargo domin bata son dada ya ga ciwukan dake jikinta,
"Daughter lafiya kuwa?" Dada yafada yana karasawa gaban gadon,
"Dada bana jin dadine yau dinnan da zazzabi natashi ga wani irin ciwon kai.."
Kanta dada ya dafa yana yimata sannu, kuku ya kira yace ya dan hado mata wani abun taci sai
tasha magani, kasancewar akwai wurinda zaije shiyasa yatafi batare da ya tsaya yaga taci
abincin ba,
Dakyar tasamu ta tashi ta zauna saboda radadin da jikinta keyi mata musamman ma tafin
kafarta da kafofinta,
Blessing ce ta kawo mata indomie wacce aka dafa da naman kaza da kwai,
"Sorry anty, meya samu jikinki haka?"
Harara ta wullawa blessing sannan ta nuna mata hanyar fita da hannunta,
"Zo ki fice min adaki, kar ki sake ki dawo har sai idan nice na nemeki..."
Sum sum blessing ta fice daga cikin dakin tabarta tana cin indomie din data kawo mata,
Abincin take ci tana ganin shaddad yana yi mata gizo, wani irin masifaffen tsoronshi ne yake
shigarta wanda ta kasa sanin dalili gefe daya kuma tunanin ta yadda akayi har ya shigo gidan
yafita da ita take yi,
"Koda yake babu mamaki tunda shi ba bak'on gidan bane" ta fadi hakan acikin zuciyarta,
Abincin ta ture gefe ta dauki robar ruwa ta fara sha kafin daga baya ta debi magunguna ta sha.
Kwananta biyu akwance tana zazzabi kafin ta Samu ta warware, office ta koma taci gaba da
zuwa aikinta saboda yanzu ta dawo normal sai dai amma duk wanda yasanta ada idan yaganta
ayanzu zai fahimci canjin dake tare da ita, domin yanzu bata doguwar magana gashi jikinta yayi
sanyi komai asanyaye take aiwatar dashi duk da cewar dama can haka take da rashin son
hayaniya to yanzu har gara da,
Tun ranar da shaddad yaso yayi mata wannan cin mutuncin tun aranar taso ta yakice tunaninshi
amma hakan ya faskara,
A kowanne lokaci cikin ganin kyakkyawar fuskarshi take acikin zuciyarta, da farko tayi zaton
abin na wasane sai daga baya ta fahimci ba haka bane,
Gaba daya yanzu tunanin shaddad yagama zame mata dimin da'iman daga baya dakanta ta
fahimci cewar tashiga tarkon so da kauna, ganin zata yiwa kanta illa yasata nemanshi a waya
amma abin haushi koda ta kira bata sameshi ba saboda wayar akashe take.
"Yanzu ya zanyi ni maryama...?"
Ta tambayi kanta tana tallafe da kumatunta acikin office dinta bayan ta kammala duba marassa
lafiyar dake ziyartar office din nata,
"Guy dinnan nasan bazan taba samunsa ba domin ba zai iya aurena ba saboda haushina yake
ji, kawai abinda yafi shine nabawa dr sameer ko dr yazeed dama na auri daya daga cikinsu,
Kai sai dai kuma gaskiya ni basuda wasu qualities din da nake son mijina ya mallaka,
Shaddad dai shi kadai shine namijin da nake ganin zai iya dani sannan zanji dadin zama dashi
duk da nasan baya sona baya kaunata, asalima babu macen da yafi tsana irina...
Waima duk ba wannan ba yanzu a ina zan ganshi har na mallakeshi....?"
Wadannan sune tarin maganganun da take tayi acikin zuciyarta ita kadai sai kace zautacciya...
Sake gyara zamanta tayi ta dafe kanta ta zubawa teburinta idanu,
"Nifa ko sanin garinsu ma banyi ba yanzu wa zan tunkura da tambayar inda yake?"
Dabarace ta fado mata, "koda yake nasan ada shi mutumin dada ne babu mamaki watikil ya
taba sanar da dada sunan garinsu, bari idan nakoma gida zan tambayi dada"
Mikewa tayi jikinta babu kwari tamkar marar lafiya ta nufi dakin yara, round tayi ta dudduba
marassa lafiyar ta kammala ta fito domin yau bata jin zata iya kaiwa yamma acikin asibitin, gida
kawai take son tafiya domin ta samu dada ta tambayeshi labarin shaddad......
*_Ummi Shatu_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/12, 10:18 AM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_*19*_
aishaummi.blogspot.com
~~~Jikinta a sabule ta tashi ta fita tana rikeda key din motarta tana faman karkadashi sai dai
kuma duk jikinta a sanyaye yake, babu wanda tayiwa sallama ta bude motarta ta shiga domin
bata son damuwa,
Driving take hankalinta kwance idanuwanta na bisa titi, wayarta ta dauka ta kira dada ta
tambayeshi ko yana gida, cikin sa'a yace mata yana gida tun rana ya dawo,
Katse wayar tayi ta sake bawa motar wuta ta nufi gida cikeda kwarin gwiwar abinda take son
aikatawa,
Lokacin da ta shiga gida falon dada ta shiga direct ta iskeshi zaune yana rikeda jaridar daily
trust yana karantawa, zama tayi ta yaye gyalen dake kanta ta kalli Dada,
"Barka da hutawa dada.."
"Yawwa barka da dawowa mai sunan mama, ya aikin?"
"Lafiya lau dada..."
Shiru tayi tafara nazarin ta inda ya kamata ta fara, can dai ta daure tayi magana,
"Uhm Dada nace nikuwa wannan sojan wanda da ya yake kaini asibiti da d'an wanne garine...?"
Dago da idonshi yayi daga kan magazine din da yake karantawa ya kalleta,
"Daughter meya faru? Lafiya kuwa?"
"Lafiya lau Dada dama musu muke yi da dr naz shine nace zan tambayeka.."
"Shi nazirun ina yace garinsu?"
Dan jim tayi kafin tabada amsa,
"Cewa yayi wai dan katsina ne.."
Jijjiga kai Dada yayi,
"Bana jin wannan yaron dan katsina ne sai dai ko wajen kano ko Kaduna amma ni gaskiya ban
taba tambayarshi sunan garinsu ba.."
Murmushin yake maryama tayi ta mike tana kallon dada,
"Dada bari na shiga ciki nayi wanka..."
Dakinta ta shiga ta zauna ta rafka uban tagumi,tunani take shin yanzu awurin wa zata iya samo
labarin shaddad da garin da yake?
Ganin bata samu mafita ba yasata tashi ta cire kayan jikinta ta shiga wanka, ko acikin bathroom
dinma ganin shaddad tayi yana yimata gizo, dakyar ta samu ta kammala wankan ta fito ta
zauna domin shiryawa,
Komai nata cikin sanyi takeyi domin damuwar dake kwance cikin zuciyarta tafi gaban wasa,
Doguwar riga brown colour tasa ta yafa mayafi ta dauki key din mota ta fita, headquarter din
sojoji take son zuwa domin bincikawa ko Allah zaisa ta dace tasamu wanda ya sanshi,
Koda taje cikin rashin sa'a babu wani bayani ko kwaya daya data samu saboda sojojin da ake
turowa nan Allah ne kadai yasan adadinsu,
Cikeda takaici da bacin rai hadeda kunar zuci ta fito ta koma gida, wani irin jiri taji yana daukarta
sama sama wanda har yana barazanar kayar da ita, dakyar ta fara dafa bango ta samu ta haura
zuwa dakinta,
Har wani kai kawo take ji numfashinta yake yi kamar zai fita daga jikinta babu shiri ta kwanta
akan gado ta dafe goshinta tana kallon sama nan da nan taga dakin ya fara juya mata,
Runtse idanuwanta tayi wadanda suka kada suka yi jajur duk da tsananin farin da suke dashi,
Gaba daya ta gagara samun nutsuwarta balle tasan abinda ya kamata tayi, blessing ce ta turo
kofa ta shigo tana dauke da kayan sawar maryama wanda aka wanke aka goge, drewar taje
tafara jerasu daya bayan daya amma kuma sai take jin kamar nishi nishi,da sauri ta waiwaya ga
maryama,
Ganinta tayi dafe da goshinta idanuwanta arufe tana yin numfashi sama sama,
Matsawa tayi kusa da ita, "sannu anty..."
Kai kawai maryama ta daga mata ta yi mata nuni da ta dauko mata first aid box dinta,
Cikin gaggawa blessing taje ta kinkimo mata shi ta kawo mata, dakyar ta iya yunkurawa ta tashi
zaune ta bude box din ta dauki magani, da gudu blessing taje ta dauko mata ruwa roba daya ta
kawo mata, maganin tasha ta zame ta sake kwanciya tana jin zuciyarta tana bugawa da sauri
saboda tsananin soyayyar shaddad dake azalzalarta, jitake kamar ba zata iya rayuwa ba
mutukar bata mallakeshi ba mallaki na har abada.......
*_Ummi Shatu_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/13, 7:16 AM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: _®MANAZARTA ONLINE WRITERS (MOW)_
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_Fatan alkairi agareki kawata fiddausi sodangi, nasan kema masoyiyar maryama sarauniya ce
shiyasa nabaki wannan shafin kyauta keda maryama Abdul takwarar maryama sarauniya.._
*_20_*
aushaummi.blogspot.com
~~~Wani wahalallen barcine yayi gaba da ita, hatta acikin mafarkin ma in banda mafarkin
shaddad babu abinda takeyi,
Mafarki take wai gashi nan ta ganshi awani gari wanda bata san kowanne bane, tana tsaye kan
wani tsauni shikuma yana can nesa da ita, ahankali ahankali sai kara yimata nisa yake da haka
har ta daina hangoshi,
Tashi tayi firgigit daga baccin da take duk tabi ta hada zufa kamar wacce ta kwara ruwa ajikinta,
"Me wannan mafarkin yake nufi kenan? Kodai shaddad yayi min nisan da bazan iya kamoshi ba
har abada?"
Dafe kanta tayi wanda ke barazanar rabewa gida biyu,
"Ya Allah ka sassauta min, nasan hakkin shaddad ne yake bibiyata, hakkin sharrin da nayi
masa ne shiyasa Allah ya jarrabeni da tsananin sonshi..."
K'walla ce ta cika mata idonta ta dauki wayarta dake ajiye agefen gado tafara trying din number
dinsa amma kamar kullum yau ma wayar akashe take, cigaba da kira tayi har ba adadi daga
karshe ta jefar da wayar akan gado ta kifa kanta jikin pillow tana hawayen bakin ciki masu
cikeda nadama tareda dana sani,
Dakyar ta iya saita kwakwalwarta ta tashi idanuwanta jajur ta lallaba ta sauka k'asa inda Dada
ke zaune akan carpet yana cin abincin dare,
Ganinta yasashi sanin ba kalau ba domin fuskarta da idanuwanta sun sanar dashi hakan,
"Daughter..." Yafada cikeda kulawa,
"Na'am Dada" ta amsa masa tana runtse idonta saboda ciwon da kanta yake yi mata,
"Bakida lafiya ne?"
Daga masa kai tayi sannan tace, "kaina ne yake ciwo.."
"To kinsha magani?"
"Ehh nasha.."
Tashi Dada yayi yabar abincin da yake ci yakoma kusa da ita ya zauna,
"Mai sunan mama kodai kinada damuwa ne kika boye min?
Idan akwai abinda yake damunki ki sanar dani domin nine mahaifinki baki da kowa sai ni,
sannan bakida wanda yafini dan haka karki rufe min abinda ke damunki"
Hannuwanshi duka guda biyu ta kama ta rirrike sai ga hawaye yana bin kuncinta wanda yayi
mutukar razana Dada domin sam yasan maryama ba mai saurin kuka bace sannan akwaita da
dauriya tun tana yarinya karama, ita dai barta da shagwaba amma tanada dauriya akan komai,
Hankalinsa ne yaji ya tashi saboda bai saniba ko wani abune yake damunta haka wanda har
yasata kuka,
"Mai sunan mama kodai mahaifiyarki kika tuno?"
K'wallar idonta ta share ta girgiza masa kai,
"To meyake damunki har yasaki kuka? Ko kina son zuwa kiga yan uwan mahaifiyarki ne?"
Nanma kai ta girgiza masa alamun a'a, take taga hankalinsa yayi kololuwar tashi nan kuma taji
tsoron kar hawan jininsa ya tashi dan haka tayi gaggawar rarrashin tata zuciyar,
Murmushin dole tayi idanuwanta sun kada sunyi ja,
"Father babu fa abinda yake damuna, jikinane duk nake jinsa a daddaure amma yanzu na
wartsake.."
"A,a daughter nasan abinda ke damunki, tunowa kikayi da mahaifiyarki shiyasa kikayi kuka, kiyi
hakuri kiyi mata addu'a akan Allah yayi mata rahama yakai haske kabarinta,
Keda ko zama da itama bakiyi ba bare har kisan halayenta da dabi'unta da mu'amalarta,
Nida nazauna da ita ni nasan wacece ita,ni nasan wacece maryama, shiyasa bazan taba iya
mantawa da maryama ba domin nagartacciyar mace ce mai hakuri mai fara,a mai son mutane
sannan mai tsananin biyayya ga mijinta, sunanta kadai idan naji yakan sani farin ciki, maryama
ta zauna dani a lokacin da banida arziki banida abin duniya a lokacin da ban mallaki komai ba,
gashi dadin dadawa sunan mahaifiyata gareta shiyasa dan haka ko sunanta bana kira wannan
dalilin ne ma yasa kema na kiraki da maryama na rada miki sunanta kuma sunan mahaifiyata,
Maryama ta nuna min dukkan soyayya ta duniya sannan ta rayu dani cikin kwanciyar hankali,
lokacin bana zama agida kullum ina can jeji yawon yake yake haka zan tafi nabarta babu ko