Showing 36001 words to 39000 words out of 39022 words

Chapter 13 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

Ya kuma yin

Gawa ta qi rami
185 A.M. Xanzaki

qara sannan ya yunqura zai miqe, Bilkisu ta
mayar da shi da duka, ya sake bajewa a wurin
numfashi ya bar jikinsa.
Hannatu ta yi sauri ta saka hannu a aljihun
wandonsa ta zaro mabuxan, suka yi saurin mayar
da tufafin jikinsu suka buxe xakin suka fita cikin
sanxa.


Qabusu na zaune ya gaji da jiran abokin
hirarsa sai ya miqe ya shiga cikin gidan shi ma,
bai yi nisa da shiga ba ya hango qofar xakin da
aka kulle su Bilkisu a buxe. Ya tsaya ya qarewa
xakin kallo daga nesa, wiwin da ya gama zuqa
yanzu ta gaya masa wani abu ya faru.
Bai daxe ba a tsaye ya hango gilmawar
mutane biyu waxanda yake zargin su Bilkisu ne
duk da bai san su a fuska ba, domin shi mata basu
dame shi ba.
Qabusu ya fusata ya tabbata wani mummunan
abu ya faru ga abokinsa, lallai bai kamata ya bari
yaran nan su sha ba. ya duba gefe da gefe inda ya
ga wani dogon manjagara ya jawo shi cikin dabara

Gawa ta qi rami
186 A.M. Xanzaki

,ya samu wata kusurwa ya lave yana jiran
qarasowarsu.

Gawa ta qi rami
187 A.M. Xanzaki


_________BABI NA 9_________
ajiya Abu ta danna ham sau biyu, Jibo
maigadi ya fito daga banxaki da sauri
riqe da buta ya ajiye a gefe ya iso ya
buxe mata qofar ta fita ya bi ta da
kallo, duk wanda ya san Hajiya a ‘yan kwanakin
nan ta rame. Jibo maigadi ya tabbata ba batun
vatan ‘ya’yanta ne kaxai ke damun ta ba akwai
wani voyayyen al’amari duk da ya san vatan su
Bilkisu ma babban dalili ne.
Hajiya ta kalli dama da hagu na titin sannan ta
hau a nutse ta ci gaba da tafiya tana bin kwatancen
da aka yi mata ta hanyar rubutun saqon waya
zuciyarta cike da tunani, wannan karon ba ta xauki
lamarin da wasa ba.
Ta ci gaba da tuqi tana tunanin yadda
al’amjra za su kasance, ta tabbata ko ma wane ne a
bayan labulen da ke shirya mata tuggu za ta yi
qoqari ta ga bayansa, duk da cewa idan ta samu
Bilkisu da Hannatu suka kuvuta ba ta da matsala.
A wayar da aka yi da ita an tabbatar mata idan har
ta kawo kanta to tabbas za a saki ‘ya’yanta.
Hakan na nufin duk burin da take da shi akan
‘ya’yanta ya watse ken an? Domin ta yi imanin
H

Gawa ta qi rami
188 A.M. Xanzaki

wani al’amari yana shirin faruwa da ita. Ta da ke
ta ci gaba da tafiya. Tafiyar sa’a xaya da rabi ta ba
ta dama ta bar gari ta fara shiga dajin a hankali.
Wayarta da ke ajiye a gefe ta yi qara ta xauka
ta duba (private number) sannan ta kai ta
kunnenta.
“Kin kusa qarasowa,” aka sanar da ita.
Daga nesa ta hango wani gida shi kaxai
kamar gidan kiwon dabbobi. Ta tabbata nan ne
gidan kuma nan ta nufa.
Ta tsaya da motarta daga gefe tun kafin ta
kashe motar wayarta ta kuma yin qara ta xauka.
“Wani mutum zai zo ki ba shi makullin
motarki sannan ki shigo cikin gidan kai tsaye,”
aka sake ba ta umarni.
Hajiya ta cika da mamaki, sai yanzu ta gane
wautar da ta yi da ba ta sanar da kowa inda za ta je
ba, ta tabbata ita ma saceta za a yi kamar yadda
aka sace yaranta, bambancin xaya ne kawai an yi
amfani da su ne a matsayi qugiyar kama ta. Shin
su wane ne da wannan aikin, kuma me suke so?
Ba ta gama tunani ba aka qwanqwasa mata
qofar mota ta sauqe gilashin motar ta kalle shi, sai
ta samu kanta tana kallon wani mutum kakkaura

Gawa ta qi rami
189 A.M. Xanzaki

sanye da baqin takunkumi a fuska amma ya sake
shi a qarqashin havarsa ya miqa mata hannu.
Hajiya Abu ta miqa masa makullin ba tare da
gardama ba.
Ya yi mata alama da ta fito, ta fito ta tsaya
tana kallon sa. Ya nuna mata cikin gidan. Ta miqe
ta fara tafiya zuwa ciki ba tare da ta yi magana ba
tana mamakin ko duk haka mutanen gidan suke
tamkar kurame.
Ta ji qara an tashi motarta, abin daya xaure
mata kai shi ne kawai sai ta ga mutumin ya miqe
titi ya nufi cikin gari wato inda ta fito.
Kamar za ta yi magana sai ta ji motsi a
bayanta. Da sauri ta waiga ta kalli sashen sai ta ga
mutane biyu a tsaye daga tazarar taku goma daga
inda take. Duka mutanen fuskokinsu akwai
bandeji, ta doshi inda suke kai tsaye riqe da
wayarta tana tunani haka nan gabanta yana
faxuwa.
Suka saka ta a gaba tamkar kurame babu mai
magana har suka isa da ita qofar wani xaki, xaya
daga cikinsu ya sa makulli ya buxe xakin sannan
ya bi ta da kallo, sai a sannan ne ya yi magana.
“Ki shiga suna ciki.”

Gawa ta qi rami
190 A.M. Xanzaki

Hajiya ta kalle su tamkar ta zura a guje domin
mutanen sun fi yi mata kama da mala’ikun
mutuwa fiye da shaixanun mutanen da take gani a
fina-finai.
Da wannan tunanin ta sa qafa ta shiga cikin
xakin, kamar wasa sai ta ji kuma an sa makulli an
sake datse xakin. Ta tura qofar a qoqarinta na
buxewa sai kawai ta ji murya daga bayanta an yi
magana cikin rauni.
“Hajiya.”
Ta waiga da sauri sai a sannan ne ta ga
Hannatu da Bilkisu a durqushe a kan gwiwoyinsu
an xaure hannuwansu ta baya, ga alama sun sha
duka ko kuka domin fuskar kowaccensu a
kumbure take. Kawunansu babu xankwali haka
nan kuma babu wadatattun kaya a jikinsu. Ta
sake qarewa xakin da suke ciki kallo ita da
‘ya’yanta sai ta ga alamun jini a wurin, gabanta ya
yanke ya faxi. Ba ta tantama an yi wa ‘ya’yanta
fyaxe ne. Lallai kam rayuwarta ta zo qarshe
domin a yadda aka yi mata wannan cin zarafin ita
da marayun ‘ya’yanta to yau dai kam sai dai a yi
wadda za a yi wai vera ya varar da garin kyanwa.
Da sauri ta qarasa wurinsu ta fara qoqarin
kunce su amma ta kasa don haka sai ta yi zaman

Gawa ta qi rami
191 A.M. Xanzaki

dirshan a wurin tana kuka tamkar wata qaramar
yarinya.
Duniyar ta yi wa Hajiya Abu duhu gaba xaya
ta ji ta tsani rayuwa ta tsani komai nata.
“Me suka yi muku?” ta tambaye su.
“Dukan mu suka yi, mun yi qoqarin guduwa
ne.”
Ta yi ajiyar zuciya da ba abin da take zato ba
ne ya faru. Daga ita har ‘ya’yan suka shiga kuka
ba tare da an samu mai ba wa wani haquri ba, har
zuwa lokacin da duhu ya fara shigowa xakin
alamun rana ta qarasa faxuwa.
Ba su san sa’annin da suka kwashe ba sai ji
suka yi ana qoqarin buxe qofa da makulli. Gaba
xaya suka mayar da hankalinsu bakin qofar.
Mutumin da ya shigo sanye yake da babbar
riga ‘yar ciki da wando da hula zanna (mai mala)
yana riqe da waya a hannunsa ta haskawa. Mutane
biyu da suka rako shi suka koma baya suka tsaya
kusa da qofa kamar wasu ‘yan gadi.
Ganin mutumin ya sa Hajiya Abu ta miqe
tsaye a firgice ta qura masa ido tana fatan a ce
mafarki take yi.

Gawa ta qi rami
192 A.M. Xanzaki

Mutumin ya bi ta da kallo cike da vacin rai da
tsana a fuska. Har ya qaraso tsakar xakin Hajiya
Abu ba ta dawo daga duniyar ximuwa da ta shiga
ba sai da ya yi magana,
“Gawa ta qi rami zauna mana, kina mamaki
ko?”
Har yanzu ba ta yi magana ba, a lokaci guda
idan ka kalle ta za ka yi tsammanin kana kallon
wata tsohuwa ce ‘yar shekara tamanin.
“Malam ni ban san ka ba ka saki yaran nan su
yi tafiyarsu, ba su da laifi a cikin wannan
sha’anin.”
Ya yi murmushin qarfin hali sannan ya nemi
wuri ya zauna a kan xaya daga cikin kujerun da ke
xakin, “Idan su ba su laifi ai ke kina da shi ko?”
“Laifin me na yi maka? Ni ban san ka ba?”
“Qarya kike yi ki ce ba ki san ni ba, Hajiya
Abu lokaci ya yi da zan karvi dukiyata daga
hannunki na san yanzu kin gama tattala mini ita
kamar yadda na tsammaci haka a farko, lokacin
sake yaudara ya qare, ko har yanzu ba ki dawo
daga lahirar ba ne?”
Bilkisu da Hannatu suka kame jikinsu a gefe
suna kallon yadda hirar take kasancewa tsakanin

Gawa ta qi rami
193 A.M. Xanzaki

mahaifiyarsu da mutumin da suke tsammanin shi
ya sa aka sato su.
“Kamar yadda kika daxe da sani sunana
Alhaji Haruna Tinqwal haka kuma ni ne mijinki
da kika yaudara bayan na ba ki ajiyar gwalagwalai
da hoda mai daraja...”
Ta katse shi, “Kai ba mijina ba ne.”
Ya kalli su Bilkisu sannan ya kalli Hajiya
Abu, “Na ga alama taurin kanki ya yi yawa game
da tonuwar asirinki, abin da ba ki sani ba shi ne na
daxe ina bibiyar lamarinki. Kin tava yin aure kika
haifi yara biyu da wani Dagaci da ke maqwabtaka
da qauyenki Xansarai, labarin mutuwarsa lokacin
kuna tare yana qunshe da munanan abubuwan da
bai kamata na faxe su a nan ba. Ya kamata in
koma ga labarin da nake ba ki.”
Ya gyara zama ya xora qafa xaya kan xaya ya
ci gaba, “Tun daga lokacin da na farfaxo kuma
aka binne ki tare da ni, na samu hotonki a xaki
wanda kika ajiye wata wasiqa a matsayin saqo.
Wasiqar wadda kika bar wa babban amininki Sani
kin adana ta ne a cikin tangamemen hotonki da na
san kin fi so a rayuwa, kina sanar da shi cewa shi
ma ya manta da ke har sai kin neme shi, domin
akwai wata muhimmiyar magana a tsakaninku da

Gawa ta qi rami
194 A.M. Xanzaki

ban san ta mece ce ba. Daga nan kika nemi wanda
zai sayi kayayyakin da kika voye kika sayar a
sirrance da taimakon wani shahararren xan agulla
a Saudiyya, kika shirya tafiya yayin da kika tattara
‘ya’yanki kika kai su qauye. Ban samu labarin
rayuwarki a can ba amma bayan shekaru uku sai
na samu labarin an kamo ki. Bayan dawowarki ne
sai kika nemi Tanko da kika ba wa ajiyar wasu
daga kayayyakin da kika sata shi kuma ya xebo
ajiyarki ya ba ki, Tanko amintaccen yaronki ne
wanda kin taimake shi a rayuwa ta vangarori da
dama musamman kasancewarsa maraya.”
Hajiya Abu ta xago kai ta kalle shi, “Wannan
ne dalilin da ya sa ka kashe shi?”
Ya girgiza kai, “Ba ni na sa a kashe Tanko ba
ban san ta yadda aka yi ya mutu ba, ni dai na ci
gaba da bibiyar ki har zuwa dawowarki daga
Saudiyya inda na ji labarin kin kwaso ‘ya’yanki
kin dawo da su birni kin tare da su a wata unguwa
Nassarawa kika ci gaba da kasuwancinki yayin da
na dasa miki mutum guda don ya ci gaba da kula
da ke. A iyaka nazarina babu waxanda kika fi
qauna sama da ‘ya’yanki don haka na yanke
shawarar in dai ina son samun nasarar karvar
kayayyakina dole sai na yi amfani dasu don haka

Gawa ta qi rami
195 A.M. Xanzaki

na turo aka shirya sace su a daidai lokacin da kike
shirin kawo tarnaqi ga auren babbar ‘yarki, ban
sani ba ashe ke ma kin shirya sace su ta hanyar
yaronki Bello. Hankalina bai tashi ba sai da su
Alhaji Tanko suka same ni suka yi mini maganar
wai sun samu ganin ki a raye har suka nuna mini
hotunanki ke da ‘ya’yanki a wayoyinsu, wannan
ya tabbatar mini ba ni kaxai ke neman ki ba, su
ma sun gano badaqalar da kika shirya mai kama
da wasan kwaikwayo. Ganin haka ya sa na yanke
shawarar yin mai gaba xaya; a kira ki nan idan
kuma kin qi zuwa a xauko ki da qarfin tsiya a
kawo mini ke, sai ga shi kin kawo kanki duk da ba
ki san wanda yake neman ki ba.”
Hajiya Abu ta yi zaman davaro a sumuntin
xakin tana zare idanuwa, jikinta ya yi matuqar
sanyi, ita da ‘ya’yanta gaba xaya sun daina kuka
suna kallon Alhaji Haruna.
“Na rasa inda kika koyo wannan ha’incin,
amma ban yi mamaki ba musamman da qawarki
Hajiya Hindu ta ba ni cikakken labarin rayuwarki
tun daga nan har Saudiyya…”
Ta xago kai da sauri ta kalle shi.
“Kina mamakin yadda aka yi na san Hajiya
Hindu ko? Za ki iya tuna wata rana da kuka

Gawa ta qi rami
196 A.M. Xanzaki

kevance da ita kika nemi damqa mata amanar
dukiyarki da alqawarin yi mata biza don ta koma
Saudiyya ta ci gaba da kula da harkokinki har ta
ce sai ta yi shawara? To ai bayan rabuwarku ni na
sa aka xauko ta aka kai mini ita gida, inda na yi
mata alqawarin ba ta ninkin abin da za ki ba ta
matuqar ta yi mini abin da nake so. Daga baya ta
koma wurinki ta ce ta amince amma tana son ki
qara mata kaso, ta yi sa’a kika amince, abin da ba
ki sani ba Hajiya Hindu ta fi ki son kuxi za ta iya
cin amanar kowa, abu xaya kika fi ta, qarfin halin
shirya makirci sai dai ba ki da dabarar kare kai.”
“Ni ban shirya komai da Hajiya Hindu ba,”
Hajiya Abu ta faxa,
Ya miqe tsaye, “Ta qare miki Hajiya, yanzun
nan za ki ga abin mamaki,” ya xaga wa su
Qabusu hannu, “ku shigo min da su.”
Qabusu ya sunkuya cikin ladabi sannan ya
juya ya fita, daqiqu kaxan sai ga shi ya dawo
mutum biyu na biye da shi, mace da namiji.
Hajiya Hindu ce da Sani direba.
Alhaji Haruna ya kalli su Qabusu, “Ku koma
bakin aikinku.”
Qabusu da Tsigi suka juya suka fita.

Gawa ta qi rami
197 A.M. Xanzaki

Hajiya Abu ta kalli Hajiya Hindu, “Hindu da
ma ba kya Saudiyya?”
Ta gyaxa kai, “Ai da ma mai yayi aka ba ya
kai gudunmawar gobara.”
Alhaji Haruna ya xaga mata hannu alamar ta
dakata.
A wannan lokacin Hajiya Abu ta daxa
sallamawa, zuciyarta ta gama karyewa ta tabbatar
qarshenta ya zo.
“Hindu yaya za ki yi mini haka?”
Hajiya Hindu ta yi murmushin qarfin hali,
“Ki yi haquri karayar tattalin arziqi ce ta zo mini,
ga shi an janye mini subsidy ta ko ina,
karuwancin da nake taqama da shi a Saudiyya
hukuma ta tsaya tsaiwar daka ta daqile shi, ba ni
da mafita illa na miqa wuya ga duk wata hanya ta
samun kuxi da ta zo mini, kuma mai gwavi na ke
so. Bayan kyautar kuxaxe masu yawa da ya fara
yi mini na fara murmurewa mun yi alqawarin aure
da shi.”
Hajiya Abu ta ji kanta yana juyawa tamkar
duk duniyar za ta ruguzo mata a ka, fata take yi a
ce duk wannan abin da yake faruwa mafarki ne ba
gaske ba, nan gaba kaxan za ta farka ta gan ta a

Gawa ta qi rami
198 A.M. Xanzaki

kan gadonta tana barci a lokacin da Bilkisu da
Hannatu suka tafi makaranta.
Kukan da Hannatu ta saka ne ta dawo da ita
daga duniyar tunani ta yi sauri ta waiga baya.
“Umma kin cuce mu kin zalunci rayuwarmu.
Ashe da ma ha’intar tsohon mijinki kika yi shi ya
sa kika ba mu labarin wai mutuwa ya yi kika ci
gado?”
Hajiya Abu ta matso kusa da su Hannatu, “Ku
yi haquri wallahi ruxi ne kawai irin na…”
“Ya isa haka,” wata kakkausar murya ta faxa
daga bayansu.
Gaba xaya mutanen da ke falon suka waiga
don su ga ko wane ne.
“Yan sanda ne kamar guda biyar kowannensu
riqe da bindiga. ASP Abdulhakim na gaba riqe sa
qaramar bindiga da ankwa (agogon maza) a
hannunsa, a bayansa kuma Alawiyya ce tare da
Zahira cikin yanayin damuwa.
“Kowannenku ya xaga hannunsa,” ya faxa
yana qare musu kallo.
“Yan sandan suka zagaye su gaba xaya.

Gawa ta qi rami
199 A.M. Xanzaki

Alawiyya ta matso ta nuna Alhaji Haruna,
“Yauwa ga shi nan, wannan ne ya sa aka sace ni.”
ASP Abdulhakim ya matso ya kama hannun
Alhaji Haruna Tinqwal zai sa masa ankwa.
Alhaji Haruna Tinqwal ya yi masa kallon
qudan da ya faxa masa a abinci, “Kada ka sake ka
sa mini ankwa, in ba haka ba wannan kakin sai na
raba ka da shi ka qare a gidan maza. Na san
manyan mutane, hasali ma wannan gwamnatin
tamu ce.”
ASP Abdulhakim ya ciro wata takarda daga
aljihnnsa ya nuna wa Alhaji Haruna Tinqwal, “Ka
miqa wuya kawai, abokanka ma sun shiga hannu
bisa zargin dillancin wiwi da hodar iblis, da kisan
wani matashi Tanko a qauyen Xansarai .
Kwamishina ya ba mu umarnin kama su, kai kuma
wannan court order ce ta shiga duk inda kake da
mallaki don yin bincike, ina so in tabbatar maka
kai susupect ne akan laifukan safarar miyagun
qwayoyi, yin garkuwa da mutane da kuma
yunqurin kisan kai, abin da mutane irinku ba su
sani ba shi ne idanuwan hukuma na kan kowa,”
ya saqala masa ankwa sannan ya hankaxa qeyarsa
zuwa waje.

Gawa ta qi rami
200 A.M. Xanzaki

Sauran mutanen da ke cikin xakin aka tisa
qeyarsu zuwa waje.
Sai da suka fito farfajiyar gidan ne sannan
Alhaji Haruna Tinqwal ya san abin ya wuce
tunaninsa domin duk an kame yaransa su Tsigi da
Qabusu da sauransu sannan akwai motocin ‘yan
sanda sun kai guda biyar a waje da qarin wasu
‘yan sandan riqe da makamai.
Ana saka kowa da kowa a mota aka bar wasu
‘yan sandan don gudanar da bincike a cikin gidan.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login