Showing 21001 words to 24000 words out of 39022 words

Chapter 8 - Gawa Taki Rami Book Complete Writing By Ayuba Muhammad Danzaki.pdf

cewa bai san
muhimmancin tafiyar ba.”
MC ya karva, “A’a kai ma ba ka ci ba,
wrong.”
Alhji Safiyanu ya zauna jiki a sanyaye,.
MC ya miqawa wata yarinya abin magana.

Gawa ta qi rami
106 A.M. Xanzaki

Ta karva ta amsa, “Sunana Aliya Yakubu,
saboda bai iya magana ba, ba ta haka ya kamata ya
gayawa Ogansa ba.”
MC ya karva ya girgiza kai, daga nan jikin
kowa ya yi sanyi aka fara sauqe hannuwa.
MC ya yi dariya ya xaga murya , “Ga alama
dubu xari biyun uwar amarya na cikin aminci.”
Daga nan ya xaga yatsunsa ya fara qirgawa,
“goma, tara, takwas, bakwai, shida, biyar, huxu,
uku, biyu…”
Wata yarinya daga can qarshen layi ta xaga
hannu. MC ya miqa mata abin magana domin a ba
ta.
“Kina da minti xaya,” cewar MC.
“Sunana Zainab Uba Sani, ya rage masa kuxi
ne saboda barci yake yi ba ya aiki, domin ba a
mafarki sai an yi barci, kuma ya qara tabbatar da
cewa da daddare ne ya yi mafarkin.”
Aka qara yin tsit a wurin.
Bayan an dawowa da MC abin magana sai ya
kalle ta ya ce, “Ku tafawa Zainab Uba Sani ta
samu lashe kyautar kuxi zunzurutu har naira dubu
xari biyu don haka ta qaraso dandamali ta karva.”

Gawa ta qi rami
107 A.M. Xanzaki

Zainab ta taso da zumuxi ta tsallako ta taho.
Idanuwa suka sauqa a kanta ana qare mata kallo ta
iso dandamali.
Hajiya Abu ta sauqo da kanta ta miqa wa
Zainab kyautarta sannan ta karvi abin magana.
“Da ma duk wata Zainab tana da kaifin basira, ina
godiya takwarata.”
Zainab ta koma wurin zamanta.
Wani mutum ya shigo da sauri ya taho
dandamali kai tsaye har ya ja hankalin mutanen
xakin taron suka bi shi da kallo.
Ya qaraso gaban Hajiya Abu ya xan rusuna
ya yi mata magana a kunne.
Nan take fuskar Hajiya Abu ta canza ta kalli
mutumin, “Yaushe?”
Hajiya Abu ba ta san maganar da ta yi ta fito
a amsa-kuwwa ba wanda hakan ya sa waxanda ba
su juyo hankalinsu gare ta ba yanzu suka dawo da
hankalinsu nan.
MC ya qaraso ya karvi amsa-kuwwar.
Tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskar
Hajiya Abu sai kawai aka ga ta kalli MC ta yi

Gawa ta qi rami
108 A.M. Xanzaki

masa magana daga nan ta bi mutumin suka fita
tare.
MC ya kalli mutanen taron, “Uwar amarya ta
nemi uzuri, wani abu na ujila ya taso mata, don
haka ta ce a tashi taro lafiya, to yanzu za mu
tsallaka ga agenda ta gaba wadda ita ce duk ta tara
mu a nan…”
***
Hajiya Abu ta kalli mutumin, “Ka ce an kashe
Tanko?”
Ya gyaxa kai, “Kisan gilla ma kuwa Hajiya.
Tun da daddare ne, ko lokacin da aka kai shi
asibiti ma rai ya yi halinsa, xazun nan da Azahar
aka yi jana’izarsa.”
“Amma shi ne ba a sanar da ni da wuri ba?”
ta waiwaya ta kalli xakin taron inda ta ji an saki
sabon kixa ta yadda har ba ta iya jin me baqon
nata yake cewa, ta umarce shi.
“Shiga mota mu yi magana, ta yaya haka ta
faru Xanlami?”
Suka shiga mota suka zauna ta rufe gilasan
taga don kada iska ta kwashi maganar ta kai ga
wanda ba a so ya ji.

Gawa ta qi rami
109 A.M. Xanzaki

Ya yi ajiyar zuciya, “Hajiya sai da aka kwana
biyu ba a gan shi ba har mun zaci ko masu satar
mutane ne suka xauke shi amma da aka kwana
xaya ba a ji an kira waya ba sai hankula suka daxa
tashi aka shige nema sosai, a kwana na biyu da
vatansa ne aka samu gawarsa a tsohuwar Rugar su
Namadi an yi masa yankan rago. Da fari mun
xauka matsafa ne amma da aka tabbatar ba a yanki
wani sashe na jikinsa ba sai aka cire wannan
zaton.”
Ta kalle shi, “An sanar da ‘yan sanda?”
Ya ce, “E an gaya musu amma me za su iya yi
bayan abin ya faru? Suna maganta varna ne yayin
da ba a daxe da aikata ta ba amma fa wannan
kwanansa biyu, shi dai Difi’on garin Xanmushe ya
ce a yi haquri suna ci gaba da bincike yayin da
muka gaza samun cikakken labari.”
Hajiya ta tashi mota ta nufi babbar qofar fita
daga wurin.
Xanlami ya kalle ta, “Ina kuma za mu je
Hajiya?”
Ta yi magana ba tare da ta kalle shi ba,
“Qauyen za mu je yanzu.”

Gawa ta qi rami
110 A.M. Xanzaki

Xanlami ya ce, “Me zai hana mu bari sai da
safe? Dare fa ya fara yi.”
Ta murza sitiyari ta sha kwana ta hau babban
titin fita daga garin, “Akwai abin da ba ka sani ba
Xanlami.”
“Kina nufin kin san dalilin kashe shi?”
Ta girgiza kai, “Ban sani ba amma lallai idan
na je na ga komai da idona zan iya fahimtar wani
abu.”
“Kamar me?”
“Kai kam ka fiye tambaya,” ta katse shi.
Sannan ta lalubo waya inda ta sanar da Hajiya
Nadiya wadda ke wurin fatin abin da ya faru
amma ta ce mata da safe za ta dawo.
Ba su isa qauyen Xansarai ba sai wajen qarfe
goma na dare saboda ba qaramin gudu Hajiya ta yi
ba.
Xanlami ya yi shiru da bakinsa yayin da ita
kuma ta ci gaba da tuqi.
***
Hasken fitilar motarta ta haske qauyen ta
yadda mutane a wuraren hirarsu da samari da suke

Gawa ta qi rami
111 A.M. Xanzaki

wurin taxi da sauran mutane da suka fara barci
kowa ya tashi tsaye suna hangen motar.
Kai tsaye Hajiya ta wuce wurin zaman
makokin.
Ragowar mutanen da suka rage a zaune bisa
tabarmi suka miqe tsaye har zuwa lokacin da ta
buxe qofar motar ta fito, sai a sannan ta lura ashe
ta xebo ‘yan kallo (mutane) tun farkon
shigowarta qauyen.
Wani saurayi mai shegen surutu ya ce, “Ai na
xauka ma ‘yan sanda ne.”
Bayan ta gaisa da mutanen da ke waje ne sai
ta wuce cikin gidan don gaisawa da mata. Da
yawa daga mutanen da suka san an tafi sanar da
ita labarin abin da ya faru sun yi mamakin dalilin
da ya sa Hajiya Abu ta yi gaggawar zuwa qauyen
maimakon ta bari gari ya waye.
A haka ta zauna zuwa bayan sallar Isha inda
ta hau motarta ta wuce gida wurin mahaifinta
Liman Malam Kalla inda suka yi mamakin
zuwanta.
Waxanda suke barci a gidan suka tashi don
jin zuwan Hajiya sannan sai sabuwar hira ta varke

Gawa ta qi rami
112 A.M. Xanzaki

mafi yawa akan marigayin domin kowa ya san
Hajiya ba ta da abokin sirri a garin kamar sa.
***
A daidai lokacin da Hajiya Abu ke fama da
mutane ake kuma karvar gaisuwa tare da ita ne
aka tashi daga wurin fati ana ta hayaniya domin
kuwa wani al’amari ne ya faru da aka rasa gane
mene ne.
Wato misalin qarfe goma na dare ne aka
kammala fatin kuma mahalarta suka fito waje don
tafiya gida.
Amarya Bilkisu, Hannatu da A’isha, Karima
da kuma Binta suka fito waje.
Makulli yana hannun Karima wadda ke
qoqarin tayar da motar bayan ta shiga yayin da
amarya ke waje tana saurare.
Hannatu ta kalli tayar motar daga qasa sai ta
kalli ragowar mutanen da ke tsaye.
“La kun ga tayar ma ta yi faci, garin yaya aka
yi haka?”
Kowa ya tsaya ana tunanin abin da ya kamata
a yi.

Gawa ta qi rami
113 A.M. Xanzaki

Wata mota ta fito daga wani lungu a wurin
qirar Hilux ta qaraso ta tsaya a kusa da su.
Wani mutum kakkaura sanye da baqin
takunkumi a fuska amma ya sake shi a qarqashin
havarsa ya zuge gilasan tagar motar ya leqo ya
kalli amarya da qawayenta.
“Ku shigo mu tafi, tun xazu Nasiru ya ce in
xauke ku a mota saboda dare yana qara yi.”
Suka kalli juna sannan suka nufi motar suka
buxe suka shiga. Karima wadda ita ce mai motar
ta kalle su, “Ni kam zan jira direba ya zo sai ya
kira mai gyara ya zo ya canza mana akwai safaya
a baya.”
Ta juya ta koma ciki.
Mutumin ya karya kwana cikin nutsuwa ya
nufi babbar qofar fita daga gidan gaba xaya.
Akwai wata mota a qofar wurin tana dako, nan
take ta rufa masa baya suka hau titi.
Bai daxe da hawa titi ba sai wata mota ta fito
daga wata kwana gilasanta a rufe ta shiga gabansu
ta sa sigina sannan sai ta ci gaba da tafiya.
Wato motar amarya na tsakiya motocin biyu
sun saka ta a tsakiya.

Gawa ta qi rami
114 A.M. Xanzaki

Cikin motar ya yi tsit suna tunani kala-kala, a
kuma daidai lokacin ne direban motar ya kalle su
ta madubi.
“Ana zafi ko? Bari a kunna muku esi.”
Ya danna wani wuri, nan take motar ta
xumame da xumi yayin da ya saki takunkuminsa
ya rufe hanci da baki. Bai daxe da yin haka ba sai
wani farin abu kamar hayaqi kamar hoda ya fito
daga wasu qananan hudoji da ke gaban motar ya
doki fuskar kowannensu. Amarya da ke gaba ita ta
fara shaqa. Nan take suka ji jikinsu ya mutu sun
kasa motsi. Daga nan sai wani barci mai qarfi ya
kama su.
Mutumin ya kashe na’urar da ya kunna ya
buxe taga iska ta shigo sosai sannan ya xauki
waya ya danna ya saka a kunne.
“Qanqara ta narke,” ya faxa.
Aka amsa masa daga xaya vangaren, “Ka
biyo mu a sannu, ba ka da matsalar ‘yan sanda
kamar yadda na gaya maka da farko.”
Motocin suka ci gaba da tafiya a jere tamkar
ba za su tsaya ba har suka fita daga qwaryar garin
Kano suka miqa tafiya zuwa qauyukan da ke
bayan Kano, suka wuce Jaba suka wuce Fanisau

Gawa ta qi rami
115 A.M. Xanzaki

ba tare da Bilkisu da qawayenta sun san me ake
ciki ba.
Wani gida shi kaxai a tsakiyar daji suka riska
sannan motocin suka tsaya daidai lokacin da qarfe
uku na dare ta yi. motocin duka sun yi buxu-buxu
da qurar kan hanya.
Wani mutum fari kakkaura ya fito daga cikin
gidan, ba ya sanye da komai sai rigar shadda
shuxiya mai haske mai gajeren hannu da
wandonta, kansa babu hula ya dafa makarin
qarfen da ke jikin gidan yana kallon su.
Alhaji Lado ne.
Duka qofofin motocin suka buxe a tare
sannan mutanen da ke ciki suka fito.
Mutum biyu ne a motar gaba; wani xan tsigigi
wanda da alama shi ne direban domin daga sashen
direba ya fito sai wani madaidaici a qiba amma
dogo ne sosai yana sanye da singileti mai kauri
maras hannaye wadda ta bayyana girman
qwanjinsa.
Direban da ya xauko su Bilkisu ya dafa qofar
motar bayan ya fito.
Qofar motar baya ta buxe, wani lukutin
mutum qato ya fito sai faman zare idanuwa yake

Gawa ta qi rami
116 A.M. Xanzaki

yi, sanye yake da riga mai gajeren hannu ya
zagayo ya qwanqwasa gilasan motar ta xaya
vangaren, wani mutumin ya fito sanye da riga ‘yar
kanti mai dogon hannu, sanye da wando yankakke
a qafarsa, shi ma dai kamar xan uwansa qato ne
sai dai yana sanye da baqin tabarau duk da
kasancewar tsakiyar dare ne. Wasu abokansa sun
ce ba ya gani sai da daddare kuma wai da baqin
tabarau, sun ce wai wani zama da ya tava yi a
gidan gyaran hali a xakin duhu ne ya raunana
ganinsa.
Su duka suka nufo inda Alhaji Lado yake
suka rusuna, amma ban da direban su Bilkisu.
Alhaji Lado ya tafa hannuwansa, “Da kyau
Lawurje aikinku ya yi kyau sosai, suna ina
yaran?”
Dogon nan mai qiba wanda shi aka kira da
Lawurje ya nuna motar da ta xauko su Bilkisu..
“Ranka ya daxe suna cikin motar can.”
Alhaji Lado ya nufi motar yayin da suka rufa
masa baya a tare suka doshi motar.
Direban su Bilkisu ya zagayo ya buxe gaban
motar.

Gawa ta qi rami
117 A.M. Xanzaki

Alhaji Lado ya kalli ‘yanmatan da ke ciki ya
qirga su sannan ya juyo ya kalli direban.
“Qabusu a ina ka samo waxannan kuma?”
Qabusu ya gyara tsayuwa, “Ranka ya daxe ba
ni na samo su ba ‘yan rakiyar amarya ne.”
Alhaji Lado ya ce; “Ai kuwa za su ci gaba da
raka ta har lahira matuqar kuka bar su a nan,
amma a daren nan nake so a mayar da su inda aka
xauko su.”
Siririn direban nan ya matso kusa yana
haxiyar yawu, “Ranka ya daxe ‘yanmata ne fa.”
Alhaji Lado ya harare shi, “To sai aka yi
yaya? Tsigi ba ka da hankali idan ba ka nutsu ba
mace ce ajalinka wallahi,” ya kalli ragowar
sannan ya nuna ‘yanmatan da ke faman barci har
yanzu tamkar ba za su farka ba ya ce; “idan
mutane suka taru suka yi yawa mai yiwuwa a
samu mai kaifin basirar da za ta iya ba su mafita
daga hannunmu don haka ya zama dole ku mayar
da su, amma ku bar wannan da wannan,” ya nuna
Bilkisu da Hannatu.
Ya juya ya nufi cikin gidan, “Ku taho da
waxanda ake buqata sauran ku mayar da su birni.”
ya juya ya kalle su sannan ya tsaya cak, “Lawurje

Gawa ta qi rami
118 A.M. Xanzaki

kai kada ka bi su ka zauna nan tare da ni zan saka
ka wani aiki.”
Suka amsa da to sannan suka kinkimi Bilkisu
da Hannatu suka shiga da su cikin gidan.
A cikin abin da bai wuce mintuna biyu ba
motocin tare da mutanen suka miqe tare da
komawa da su.
Alhaji Lado ya qura ido a tsaye yana kallon
su sai da ya tabbatar hasken fitilinsu ya vace
sannan ya juya ya nufi gidan tare da Lawurje.
***
A can wurin fati kuma mintuna kaxan da fitar
amarya da tawagarta ango da abokansa suka fito
suna neman ta.
Lokaci guda labari ya karaxe wurin
musamman da ango ya kira wayar amarya da
muqarrabanta ya ji a kashe. Aka yi cirko-cirko ana
tunanin abin yi.
Karima na can na qoqarin canza tayar mota
bayan da direban nata ya zo sai ta fahimci me
yake faruwa ta qaraso gaban ango.
“Ah! Ba kai ka turo a tafi da su a mota ba da
ma?” ta tambayi Nasiru.

Gawa ta qi rami
119 A.M. Xanzaki

Ya girgiza kai cike da fargaba, “Ba ni ba ne,
wani ya xauke su ne?” ya waiga ya kalli sashen
tarin abokansa yana nazarinsu, “ai kuwa duk masu
motar suna nan.”
Ta kalli wani sashe, “Motata ce ta yi faci shi
ne shi kuma ya zo ya ce ka turo shi ya tafi da mu.”
Nasiru ya daki murfin motar da ke gabansa,
“Oh shet! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ina
aka yi da su?”
Ya juya ya kalli Karima, “Za ki gane titin da
suka bi?”
Ta girgiza kai alamar a’a.
Nan take labari ya yaxu an sace amarya da
qanwarta da qawayenta guda biyu.
Tashin hankali!

Gawa ta qi rami
120 A.M. Xanzaki

__________BABI NA 6___________
arfe uku na dare ta yi amma Nasiru ya
kasa barci sai zirga-zirga yake yi, a
tsakanin awannin da ya dawo gida ya
kira lambar Bilkisu kusan sau xari uku amma har
yanzu amsa xaya yake samu, wato a kashe take.
Ya yi jifa da wayar tasa a karo na barkatai
amma a wannan karon kan tayil ya faxa ta
tarwatse. Ya nemi wuri ya zauna ya yi tagumi
yana ta tunanin ta yadda aka yi haka ta faru.
Sai da aka turo qofar sannan ya tuna ashe a
buxe ya bar qofar xakin nasa tun da ya dawo.
Hajiya Nadiya ta shigo xakin da alamun barci
a idonta.
“Kai mai sunan Baba kada dai ka ce min
wannan lamarin ne ya hana ka barci?”
Ya kalle ta ya kawar da kai.
Ta qaraso bakin gadon da yake zaune ta
zauna kusa da shi ta dafa shi, “Ba na gaya maka
na yi waya da kwamishinan ‘yan sanda ba? Me zai
sa ka damu kanka bayan ka san daga nan zuwa
wayewar gari za a ji labari mai daxi?”
Q

Gawa ta qi rami
121 A.M. Xanzaki

Nasiru ya yi ajiyar zuciya, “Hajiya har fa
gidansu mun je xazu amma an tabbatar mana ba
su je ba, kuma ita kanta Hajiya ba ta koma ba.”
“Hajiya tana qauyen Xansarai inda iyayenta
suke ta ce rasuwa aka yi musu amma da safe za ta
dawo. Ko ba ka yarda da ni ba ne? Matsala a
rayuwa in dai ta shafe ni ba ta haura awa ashirin
da huxu ban warware ta.”
Ya gyaxa kai, ‘Na san haka kike Hajiya,
amma xan adam da qawazuci yake, haka kawai
sai nake fargabar rasa ta.”
“To ka daina,” ta ci gaba da qoqarin kwantar
masa da hankali, “komai ya yi zafi maganinsa
Allah, ka sani akwai muhimman abubuwa da ke
gabanka bana so yawan tunani ya shafi
karatunka,” ta fara share masa hawaye.
“Don haka ka saki jikinka ka samu ka yi barci
da safe za mu yi magana ka ga Asuba ta kusa,
insha’Allahu komai zai zama normal a ci gaba da
shirye-shirye.”
Ta kwantar da shi a kan gadon da kanta ta
lulluve shi, “Ka yi barci lafiya my sweet son.”
Daga nan ta fita daga xakin.

Gawa ta qi rami
122 A.M. Xanzaki

Nasiru ya yi lamo a kan gadon kamar zakaran
da ruwa ya jiqa, ya yi barci kamar ba ya yi ba,
daga qarshe dai barcin ya xauke shi.
***
A can qauyen Xansarai misalin qarfe sha
xaya da rabi bayan kowa ya watse daga Hajiya sai
mahaifinta wanda ke qoqarin bayyana mata halin
da suke ciki a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login