Showing 15001 words to 18000 words out of 24103 words

Chapter 6 - WASU MAZAN Part 1 Complete By Ummu hibbat .pdf

27 Apr 2025

2146

sanadi."
Jin ya yi shuru bai dame ta ba domin ta san halin sa ne. Amma abu mafi firgitarwa shi ne da ya
sa ta ja da baya da shi shi ne............



12


Jin wani irin kamshin turare wanda ba na shi ba shi ne ya sanya ta ta ja baya da ga jikin sa.
Idanu ta kuma warewa sosai tana kallon sa domin tana son ta gane shi. Shi kuwa Mu'azzam ga
ba d'aya ta sincema sa notin kai da na jiki kuma duk ta rikita shi. Ganin Mu'azzam ne tsaye
gabanta tuni ta ja da baya. Yunkurin ta na son fita akitchen d'in ya k'i samuwa don haka sai ta
koma can gefe da shi ta zube tana lumfarfashi . Shi kuwa ganin haka gaba d'aya sai ya rasa
abin yi. Fita ya yi a kitchen d'in ya nufi bakin d'akin Awwal zai buga masa kuma sai ya fasa.
Wani tunani ya yi ya sa shi tsyawar. Domin ya fahimci matsalar ta. Kuma yana tsoran kar Awwal
ya zargi wani abu game da shi. Don haka sai ya wuce d'akin da aka ba shi bakinsa akelum ya
zauna bakin gadon sa. Mamaki yake sosai, daman ana iya samun haka a zaman aure mace har
tana kuka da neman taimakon mijinta amma mijin ya gaza yin hakan? Shi kuwa Awwal wane
irin mutum ne haka? Ko dai wani mummunan lefi Samha ta yi masa wanda bai sani ba? Ganin
ba shi da mai ba shi amsar duka tambayar ta sa ya sa ya kwanta yana juyi da damuwar da yake
ciki ga shi ko shayin bai samu had'awa ba wannan matar ta kuma k'ara masa damuwa.
Alwala ya yi ya fara sallaoli ko zai samu nutsuwa da jin sauki a ziciyar sa. Samha kuwa kusan
awa guda kafin ta d'an samu sukuni ta koma d'akinta. Bacci ne me nauyi yayi nasarar d'aukarta
sosai wanda ya sa har ta makara bata yi salla ba. Ko da ta farka sai take jin kamar mafarki nd
ba zahiri ba. Sassafe Samha ta rasa gane kanta sam, me za tayi yanzu. Ta ya zata iya bud'e idanu ta kalli
Mu'azzam idan har abunnan a zahiri ne ba a mafarki ba? Ganin ba ta da mafita sai Allah ya sa
kawai ta shirya kayanta wanda zai kaita kwanakin da Mu'azzam zayyi agidan ta sulale ta bar
gidan ko abinci ba ta dafa ba. Dirar mikiya ta yiwa gidansu wansa hakan ya sa mama tambayar
lafiya kuwa. Kuka ta saka tare da cewa "Mama har yanzu fa Aljanunnan suna gidan Awwal."
Idanu Mama ta zaro tare da fad'in, "Ke Samha ki rufawa kanki asiri a rayuwa Wallahi, ina

rabaki da kiyon akuya kina ga kyalla ta haihu.." Zumb'ura baki Samha ta yi ta wuce d'akin mama
bata ce komai ba.
A can gidan Awwal kuwa yana kwance shuru har wajen tara baiji motsin kowa a falo ba, kuma
Samha ba shigi ta gaida shi kamar yadda ta saba ba. Don haka sai ya yunk'ura ya fito falo ya zo
ya ga bata nan, kai tsaye kitchen ya wuce nan ma wayam. Tunawa da yayi da rigimar jiya da
dare sai ya nufi d'akinta nan ma ba ta nan. Mamaki sosai abin ya ba shi. To ina ta tafi a wannan
safiyar ya tambayi kansa.
Wuri ya samu ya zauna akan kujerar falo bayan ya fito a d'akin ya fara gwada lambarta tana
shiga amma bata d'auka. Hankalin sa ya yi matuk'ar ta shi da jin hakan. Tagumi ya yi yana
nazarin abin yi sai ga Mu'azzam ya fito a d'akin sa, wuri ya samu shi ma ya zauna suka gaisa
sannan Mu'azzam ya dube shi sosai cikin kulawa ya ce, "Me yake faruwa ne haka?" "Me ka gani?" Awwal ya maida masa da tambaya maimakon amsa. "Aa na ga ka yi zaman
tagumi ne." "Aa babu komai kawai dai wallahi Samha ce ban gani ba duka gidan, kuma na k'ira
layinta ba ta d'agawa."
"Oh Samha ai tun sassafe na ga fitarta na zaci ma tare kuka fita fa."
"Fita kuma?" Awwal ya tambaya.
"Tabbas! Amma me ya faru. Sanar min na sani."
"Babu komai ni ma ban sani ba." "Haba Awwal taya zaka ce baka sani ba, kai ne babba fa
Awwal. Kuma jiya na ga Samha a cikin wani yanayi na jinya, kuma na ji tana ambatar sunan
ka."
Kai Awwal ya d'aga a fusace ya ce, "Mu'azzam! Me ka ji tana cewa? Sannan kuma me ka fito
yi kai a wannan lokacin?"
Sosai kai Mu'azzam ya yi tare da fad'in, "Ni kuma taya zan san abin sa take fad'a, na fito ne
ina kitchen ina had'a magani kuma kasan dai halin da nake ciki. Dole ma na yi aure na huta."
Mu'azzam ya fad'a yana tsaki tare da juya kansa gefe. Tsakin shi ma Awwal yayi yace, "Banza
mayen mata kawai, wannan dalilin ne ya sa ba zan bari ma Salma ta san kana sonta ba. Bare
kuma ka aure ta."
Dariya sosai ya kyalkyala da ita, "Haba kai kuwu ai asara ce zaka yi mata wallahi. Domin
matan yanzu fa ba sa son auren mata maza, gwanda dai ka ba ni sai kuji mu shuru. Amma idan
ka aura mata wanda yake maza ya rako ko, to tabbas kullum cikin fitina zasu zauna."
Dum! Ya ji da maganar Mu'azzam, domin ji yayi kamar da shi yake. Duk da dai shi ya san ba
ya da ga cikin mazajen sa Mu'azzam yake nufi.
Mik'ewa ya yi tare da cewa, adai bi wani sarkin amma ban da wannan. Ni zanje na nemo
matata kayi mana kirki tunda ka iya daman." Dariya Mu'azzam ya yi ya ce wannan ba matsala
ba ce, kai de ka je ka nemo mana matar tun kan dare ya maka kuma ka bata hak'uri tabbas na
san ka yi mata laifi. Don da gani zata yi hakuri wallahi." Awwal dai bai ce komai ba ya wuce d'akin sa yana kuma maimata k'iran layin Samha.
Ganin dai ba zata d'aga ba kawai sai ya shirya ya d'auki mota lokacin kuma Mu'azzam ya shiga
ya fara girka musu abin da za su ci."
Har k'ofar gidan su Samha ya faka motarsa sannan ya shiga daga zaure yayi sallama aka ba
shi damar shiga. Bayan mama ta ba shi damar zama ya zauna sun gaisa ya ke tambayar ta ko
Samha ta zo? Ta ba shi amsa tana nan. Hakuri ya fara bawa mama akan cewa bai san ta fito
ba. Mama tace karya damu yanzu zata fito su tafi. Mama ta kwalawa Samha k'ira Samha ta fito

sanye da hijabi amma ta na ganin Awwal sai ta fasa ihu ta zube a wurin irin dai yadda take yi
alokacin da Awwal yayi mata wasan aljani.......... Tofa an yanka ta tashi.



13

Da sauri shi da mama sukayi kanta, jijjiga ta mama take yi sosai. Awwal kuwa ruwa ya d'ebo na
fara yayyafa mata. Idanun ta ta bude tana ganin sa ta yunk'ura ta fara ja da baya tana fad'in,
"Mama karki yadda da shi ba Awwal ba ne aljanine, zai cutar dake. Awwal ba ya murmushin
nan. Kallon sa mama ta yi ta ce, " Wai me yake faruwa ne? Aljanun ne ko kuma tsora kawai take yi."
Sun kuyar da kai Awwal yayi sannan ya ce, "Mama shi ne abin da na gaza ganewa. Addu'a
sosai mama ta fara yi mata tana gyara mata zaman, amma sam Samha ta k'i amincewa ta
kuma ko sa kallon Awwal. Har mama ta fita a d'akin ta barsu tare. Awwal ya dube ta yace, "
Samha, don Allah ki ta shi mutafi gida, wallahi ba wani aljanin a gidannan kawai ki tsorata ne
tun baya."
"Ba zan koma ba sai sanda zuciyata ta tabbatar da hakan tukunna. Ka bar wurinnan kafin ka
sanya ni cikin masifa."
Ganin babu sarki sai Allah ya sa Awwal yiwa mama sallama ya tafi. Ko da ya koma
Mu'azzam ya na zaune a falo ya gama had'a komai da za su karya yana jiran dawowar sa.
Da ya kalle shi shi d'aya ya tambaye shi ina Samhan take ne. Bai amsa ba sai da ya samu
wuri ya zauna sannan ya ce, "Tana gidansu, kuma ta ce ba zata dawo ba."
"Tofa akan me ya sa to?" Mu'azzam ya tambaya. "Wani shiririta ta ke ji da shi. Wai ba zata
dawo ba gidan akwai aljani." Dariya sosai Mu'azzam ya yi ya dubi Awwal, "Aljani kuma? To kai
kuma sai ka barta ta zauna. Gaskiya ka lallab'ata ta dawo dan dai gaskiya ina jin kawai dan
karta dawo ta ce maka haka. Wata k'ila kayi mata wani laifi ne ba zata iya sanar maka ba shi ne
ta fake da aljanu."
"Ai kuwa za ta ga aljanu, domin ba zan je na dawo da ita ba. Ko wanne irin lefi ne ai ya
kamata ta sanar min ba wai ta tsaya shirme ba. Kuma ma ba wani laifi da na yi mata ni a yanzu.
Don haka na huta ma ta sha zaman ta.
" Aa fa Awwal karka maida kanka gauron k'arfi da yaji a kan abin da bai kai ya ka ba, ya
kamata kaje ku sulhunta." "Sai ka yi ta yi kai wannan ya dama ni bani da damuwa. Daga haka
ya ta fi ya fara zuba abinci. Ganin haka ya sa shi ka Mu'azzam ya bi bayan sa ya zuba na shi.
Suna ci suna hirar su ta abokai har suka kammala. Fice wa suka yi duka agidan, agidan Hajiya
suka ya da zango. Salma ce ta gaida su dukan su sannan yaran suka gaishe su salma ta
tambaye shi yau she zai d'auki su Ameera za ta fita anjima da yamma. Sanar mata yayi anan
zasu zauna har zuwa sanda mamar su zata dawo ita ma ta yi tafiya. Shi dai Mu'azzam bai ce
komai ba da jin k'aryar da ya mata.
Samha zaune a bakin gadon mama tana nazari da tunani har su aunty dija suka zo gidan
yini. Ganinya ya sa suka yi farin ciki da zuwan na su saboda sun jima ba su had'u a gida ba sai
dai kowa yayi zuwan sa daban. A lokacin da suka san dalilin zuwan ta sai kuma suka ka yi mata
nasiha da fad'a akan ta dage da karatun Alkur'ani kuma ta cire komai azuciyarya na batun jinnu.

Da to ta amsa musu amma ta ce suyi mata uzuri ta samu nutsuwa nan da wasu kwana ki sai ta
koma. Amma a yanzu ba ta da nutsuwa. Ba su takurata ba suka barta da abin da ta ce d'in. Sai
dai sun sanar mata duk yadda za'ayi kar ta bari su baba da yaya Yusuf su dawo daga tafiya
bata koma ba. Wasa gaske kwanan Samha uku bata gidan. Gaba d'aya hankalin Awwal ya fara ta shi da
rashin ta agidan. Tun da sukayi aure bat tab'a tafiyar ko da kwana d'aya ba. Duk da cewa wuri
kwanciyar su ba guda ba amma sam idan dare yayi sai ya shiga damuwa. Yau ma yana kwance
a falo shi da Mu'azzam suna hira ya ce masa zai je ya kwanta. Ko da ya shiga d'akin sa wayarta
ya fara k'ira, kamar ba zata d'auka tukunna ta d'auka. Gaisawa su ka yi sanna ya tambayeta
yau she zata dawo. Amsa guda ta bashi wacce ta sany shi mamaki, wai sai ranar sa ya can ja
hali kuma ya samu lafiya.
Wannan maganr ta jima tana masa yawo a ransa. Wane hali ne da shi wanda zai sauya shi?
Kuma kenan har yanzu tana jin cewa shi ba mai lafiya ba ne? Ba don yana sonta ba da tabbas
zai saketa ta auri masu lafiyar da take buri. Sai dai ba zai iya tab'a sakinta ba. Kuma shi ya san
yana daga cikin maza masu lafiya, amma matan yanzu sam sun damu kamsu da cewa sai na
miji ya sha wani abu na magani sannan zai iya musu, suna so sai sun ga na miji ya fita
hayyacin sa sannan za suyi farin ciki. Ko kuma sai yana zunduma ihu irin yadda masu
magunguna suke yad'awa. Humm aikuwa Allah ya kiyaye shi da wannan aikin. Ba zai tab'a
shan wani abu domin ya birge mace ba, tunda dai ya san yana da lafiya ga shi har ya haifi yara
uku. Lafitar da Allah ya bashi tunda har ta kai ya ba ta ciki ta haifa ai renin hankali ne ma ta ce
wai z ta gamsuwa da shi. Amma zai d'auki mataki akan hakan. Zai bincika komai na d'akinta ya
kwashe magungunan da take sha ya watsar kuma ya mata gargadi na musamman. Da wannan
tunanin ya tafi d'akinta har kuma lokacin Mu'azzam yana falo yana kallon bal, shiga ya yi ya fara
bincike. Sai dai har ya gama bai samu komai ba. Murmushi ya yi tare da fad'in "Mata sun san
munafurci ai ba zata barsu inda zan gani ba.
Hakura yayi ya koma ya kwanta. Ganin da gaske Samha ta k'i dawowa ya sa ya koma gidan
amma yana zuwa ta kuma birkice masa tana ik'irari aljani. Abin ya b'ata masa rai sosai amma
ba yadda zaiyyi. Dole ne ma ya lallab'ata kamar yadda Mu'azzam ya fa'da. Domin yana da
bukatar ta sosai. Zama yayi daga ita sai shi a d'akin ya sanar mata cewa ya sauya saboda ba
na da ba ne shi d'in, kuma in sha Allah za ta yi farin ciki sosai. Allah sarki abin ka da mai
buk'atar hakan tuni Samha ta yarda da roman bakan da yayi mata. Bayan ya fita ta sanar da
mama za ta koma. Mama ta yi dariya ta ce Allah ya kiyaye hanya. Kunya kuma duka sai ta
lullub'eta.
Gidan suka dawo ta shiga kitchen ta shirya masu abincin dare. Shi kuwa Awwal sai fara'a yake
yana ta kaiwa da kawo wa yana mata hira. Dare na yi yaje ya siyo musu nama me laushi wanda
yaji yaji me dad'i tare da kayan sanyin. Samha aka canjad'a ado na musamma saboda yau tana
cikin farin ciki mijinta ya fahimci matsalar sa har ma ya canja yace mata. Abinci suke ci suna
hira kai ka ce wasu daban ne ba su ba. Ba za ka d'auka wannan Awwal d'in bane.
Mu'azzam ne ya shigo ua same su ya gaishe da su, amma ganin yadda Samha take jin
kunyarsa sosai ya sa bai mata magana ba balle ya zolayeta yadda ya sa ba. Kai tsaye ya wuce
d'akin sa domin ya barsu su sake. Bayan sun gama komai Awwal ya shiga ya fesa wanka ya
wuce filin gida ya far motsa jiki, wai saboda ya samu jikin sa ya ware ta yadda zai nuna wa
Samha ainahin k'arfin da Allah ya masa. Bayan ya gama ya samu kankana ya fasa guda ya

shanye domin a tunanin sa ita ma zata inganta masa lafiya saboda magani ce sa ya yarsa da
ita d'ari bisa d'ari. Samha kuwa an sha kayan bacci an sha turaruka ana jiran aji shigowar Awwa
falo. Domin ta ji fitar sa wajen gida, don haka da zarar ya wuce d'akinsa zata bi shi. Kwatsam
sai ga shi ya shigo d'akin yana washe baki ya zauna bakin gadon tare da fad'in, "Baki yi bacci
ba a she."
Mamaki fal ya kama zuciyar Samha bacci kuma wanne iri. Hayewa gadon yayi ya kwanta ya
juya baya tare da fad'in, "Ina jiranki." Mamaki ya kama Samha, lalle Awwal ya sauya yau shine
har sa yana jira? Cab! Lalle yau akwai sauyi tabbas. Hawa gadon ta yi ta kwanta tana jiran jiran
da sai da ta yi nadamar yin sa..........


14

Kamar a mafarki take jin yanayin sa ya sauya irin na da, sai dai kuma ba ta ji yana munshari ba.
Hakan ne ya sa take jin kawai ta tsorata ne amma ba wai ya gama bane. Jin nauyin sa ba
k'aramin tayar mata hankali yayi ba. Ja da baya ta yi ta gyra kwanciya ta k'are masa kallo yadda
yake fidda lumfashi kamar an d'aura masa wani nannauyan dutse. "Awwal wannan shi ne
sauyawar da ka ce min?" Samha ta furta cikin wani rikitaccen yanayi. Sa ke matse idanun sa
ya yi ya ce, "Innalillahi! Samha wai kina nufin har yanzu dai shuru ne....?"
Kuka ta fashe da shi sosai har ta na d'aga murya, "Wallahi Awwal yau kam wallahi Allah ya isa
zan maka na rantse idan har ka ce min iya ka abin da zaka iya kenan.
Cike da ta shin hankali ya ta shi ua zauna yana fad'in, " Samha, don Allah karki min wallahi na
kai k'arshe ban san me kike so na yi ba wanda ya zarce haka. Ina jin dai marsalar nan ke kina
da ga cikin sahun mata ta fannin wannan lamari mataki na k'arshe. Amma don Allah kiyi hak'uri
ki kwanta zuwa anjima zan dan yi bacci idan na farka sai ayi wani abu." "Wallahi baka isa ba! Abun ma har da raina min hankali! Kana farke ma yaya bare kuma ka
yi bacci. Wallahi Awwal na gaji tunda na karanta maka da yaran hausa na yi maka da boko
yanzu kuma na yi maka da larabci amma sam ka k'i yarda, to ka wai ka sawwak'e mun kowa ya
kama gaban sa Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login