Showing 21001 words to 24000 words out of 24103 words
yake d'auke damuwar. Shiru wurin yayi
kowa yana figar kazar sa. Can ya dube ni, "Samha don Allah kiyi hak'uri mu zauna lafiya acikin
gidannan kamar na da."
Cak! Na tsaya da cin kazar na ce, "Na hanaka zaman lafiya ne Awwal?"
"Baki hana ba, amma kin san yanzu ina da buk'atar ki a kusa da ni amma kuma kin juya min
baya ."
"Wai saunawa ka juya min baya aba ban ce komai ba sai yanzu dan na raba kaina da wahala
shi ne? Sau nawa nake binka ina rok'onka ka saurare ni amma sai dai ka kore ni anyi haka?
Awwal a baya rabon ciki ke had'ani da kai kawai kuma na yi hak'uri na zauna, dan yanzu na
gaza jurewa shi ne kake ganin laifina? Dan yanzu kazo da yawan bukatar ba biyan bukatar ai
awurina duka abu guda ne."
Shuru ya yi kansa a k'asa yana sauk'e lumfashi. Sannan ya ce, "Na ji na d'au laifina kiyi hakuri.
Amma yanzu ya kike son na yi Samha."
"Ai ba wani abu bane magani kawai zaka nema ka zauna dani lafiya."
"Samha maganin nan fa duka tallar k'arya ce ba wani abu da zayyi min fa. Da kin ba ni dama
na kuma jarrabawa muga yadda za'a yi. ...... "
Tsaye na mik'e na ce, "Dama! Har yanzu wata dama kake nema da zaka cutar dani? To wallahi
ba wata dama zan kuma baka har sai ka yi wanka fad'a."
Ina gama fad'ar haka na fashe da kuka mai tsuma zuciya. A mama kance na dago dajin sautin
kukan Awwal a gefe na. Yana zaune gefena shi ma yana kuka kamar yadda nake yi. . kallon sa
na yi tare da goge fuskata na...........
17
"Kai Kuma mene ne abin kuka?"
Sa ke matse hawayen idanunsa yayi ya ce, "Samha ai dole na yi kuka, ace kullum matata tana
kuka saboda ni? Kuma ni na gaza daina saka ta kukan ? Taya zan samu nutsuwa. " "Amma ai
kasan hanyar da za ka bi."
"Samha bansani ba! Bansani ba! Ina zan saka kaina wai."
Ita yanzu abin ma mamaki yake ba ta da tsoro, anya kuwa Awwal d'inne ko dai aljanin ne ya
dawo. Awwal ne zai tsaya har yana kuka a gabana.
"Samha, wallahi abin yana damuna sosai wallahi, kuma ke kina ganin kamar da gangan nake yi
. To yanzu tsakani da Allah mene ne abin yi in ba kukan ba?"
"Cab! nifa wallahi sam ban ma yarda kaine ba, na fi tunanin ko Aljanin ne. " Ta fad'a tana ja da
baya. Hannu ya d'aura akan sa tare da, cewa, "Samha, don Allah ki bar wani zancen aljani. Ko
wancen ma wani shirina ne kawai amma ba gaskiya ba ne."
Idanu ta zaro waje tana kallon sa tare da fad'in, "Shiri kuma?"
"Samha, muje d'aki na sanar miki."
"D'aki fa ka ce? Ai wallahi dukkan abin da zaka fad'a kawai ka fad'a anan, amma ba inda
zanje nikam."
"Haba Samha amatsayinki na me ilimi yanzu ba zaki taimakawa mijinki ba? Ki taimaka ki yi
hak'uri ki kuma ba ni wata damar mana."
"Ai Awwal ya kamata ka fahimci ba wata dama yanzu wacce zan kuma baka. idan har baka da
abin fad'a anan to ka ga tafiyata."
Tana gama fad'ar haka ta wuce d'aki ta barshi zaune a wurin. iya ka damuwa ya shiga sosai
akanta. Kuma ba shi da wani buri da ya wuce ya kasance da ita a wannan dare. Amma ta juya
masa baya.
Ita kuwa tana shiga kan gado ta fad'a tare da fashewa da sabon kuka, duniya ta yi mata zafi
sam! Ba ta san mene ne abin yi ba a yanzu. wa zata tunkara da wannan lamari ba tare da ta ji
kunya ba? Shin ina zata je ta samu nutsuwa a duniya? Da tana da wani wuri da za ta iya
fakewa tabbas da ta gudu ta bar Awwal. Tana tsaka da tunanin sai ta ji wayarta ta yi k'ara bisa ga dukkan alamu sak'on kartakwana
ne. Hannu ta mik'a ta janyo wayarta ta fara dubawa, ganin lambarsa ce ya sa ta gane sak'on
daga gare shi ya fito. Tana bud'ewa taga ya rubuta, 'Don Allah Samha ki taimakeni kizo ina
jiranki.' Tsaki tayi tare da jefa wayar gefen ta. Hannu ta d'aga sama tana fad'in ya Allah ka ga
halin da nake ciki da mijina, Allah karka saka ni cikin sahun matan da tsinuwar ka za ta hau
kansu. Allah rashin yinsa shi ne zaman lafiyata, yin sa kuwa tamkar jefani cikin mummunan
had'arine. Ya ubangijin mu, na kai mak'ura ta yadda ba zan iya jurewa ga kusantuwa ga dukkan
wata mu'alar da babu tsuwa cikinta ba. Allah ka kawo mana mafita a zaman aurenmu.
da irin wad'annan addu'o'in har bacci yayi gaba da ita.
shi kansa cikin damuwa ya kwana a wannan ranar.
da safe kuwa ya dubeta ya ce yau za su je gidan hajiya da yamma saboda gobe Mu'azzam zai
koma garin su.
da to ta amsa masa tare da jin mugun tausayin sa ganin yadda duk girman izzarsa ta lafa a
lokaci guda duka yayi lakwas. lalle ta amince maza ba su kai mata iya jurewa sha'awa ba.
yadda ta shiga ta shin hankali a baya ta shan ye aka wuce wurin idan shi ne ya zayyi, ga shi
na lokaci guda ma ya gaza! Abin karyawa ta yi musu suka karya yara kuma aka kaisu makaranta. Don haka sai ta shiga
aikin gyran gida domin yau d'aya ta ji sauk'in damuwar da take zuciyarta. bayan ta kammala ta
zauna a falo tana chat d k'awayen ta da kuma sister d'inta. ana ma ta samu wani darasi na
musamman wanda take jin in sha Allah zuwa dare za ta jarraba Awwal da shi tun da dai neman
mafita ake.wuraren Yamma ta gama aikinta ita da yaranta suka shirya cikin kaya na alfarma ya
zo ya d'aukesu zuwa gidan hajiya. koda suka je ba k'aramin murna Salma da hajiya suka yi da
ganinta ba kasancewar ta d'an kwana biyi bata zo ba.
suna tsaka da gaisawa Mu'azzam ya shigo falon, wata irin kunya duka ta lullib'e Samha domin
ba za ta tab'a mantawa da abin da ya faru tsakanin su ba. Kuma ba don tana tsoran Allah babu
abin da zai sa ta nunawa Mu'azzam ta gane shi, domin kalar sa shi ne kowacce mace za tayi
mafarkin mallaka a duniya. don haka in sha Allah za ta yi iya ka waje ganin Salma ta amshi
tayin da yayi domin tabbas ta san za ta yi farin ciki nan gaba.
ganin ta tafi duniyar tunani yasa Salma yi mata magan da cewa "Aunty Yaya yana gaida ke."
Jin ta ambaci kalmar yaya yasa ta yi tunani ko da Awwal take nufi. Don haka sai ta d'aga kanta
domin ganin me maganar. gamuwa da idanun Mu'azzam cikin na ta tare da wannan shegen
murmushin na shi shi ne yasan ya idanunta sark'ewa cikin nasa............
18
Ganin idan bata sunkuyar da na ta kanba ba zai dena kallonta ba shi ne yasa ta kalli gefe guda
tare da fad'in, "Lafiya lau bakon mu. Ashe tafiya za ka yi gobe kuma."
"Eh wallahi, zan koma garinmu nima na huta da jarabar mijinki kullum cikin gori nake a wurin sa.
Don haka ina komawa zan fara shirin aure ni ma."
Duka dariya aka yi masa sanna na ce, "Gaskiya dai kam ya kamata ace ka yi aure ka huta da
gorin sa."
Da 'In sha Allah ya amsa min' Muka ci gaba da hira har zuwa dare sannan muka keba da Salma
domin tattaunawa. na dubeta na sanar mata cewa matukar tana son Mu'azzam to tayi k'okari ta
ba shi dama ayi bikin nan da ita, domin ya cancanta ya zama mijinta kuma yana da duk wani
abu da kowacce mace zata so ace mijinta yana da shi. Kallo na ta yi har na kammala zancen
sannan ta ce, "Aunty mene ne halayen sa wanda kika sani kuma wasu abu ne wacce mace zata
so mijinta ya kasance da su da za ta aura? shi kuma duka yana da su?"
Zama Samha ta gyara tare da fad'in, "Salma, yana da addini kuma yana da ilimin boko da na
addini. Sannan ba zaki saka shi cikin munana ba, kuma mutum ne me tsafta, sannan ga
barkwanci . Kuma yana da kud'i daidai gwargwado. Sannan yana a matsayin cikakken saurayin
da ake saka masa ran me lafiya. Salma Mu'azzam yana k'aunarki, to wanne abu zaki ne ma
adukkan wani na miji wanda ba shi ba? Abu guda ne, Sai dai idan bakya son sa a cikin zuciyar
ki. To kinga ana ba wata dabara."
Sunkuyar da kai ta yi bata ce komai ba sannan ta d'ago kai ta dubi Samha ta ce, ""Wallahi ina
son sa sosai har cikin zuciyata, sai dai abu guda da nake tunani shi ne. Idan na aure shi dole
zan barku ne na bi shi. Ni kuwa ba na son rabuwa da ku. Kuma kin san dole bauci zai kaini."
"Haka ne, amma wannan ba wani abu bane da zai hanaki auren sa ba, domin ba kanki a ka fara
auren wani gari ba."
"Haka ne kam aunty, in sha Allah zanyi tunani sosai a kan hakan.
haka dai suka yi ta tattaunawa a tsakanin su har lokacin sallah yayi.
Bayan anyi sallah kowa ya na inda yake basu kuma hallara ba har sai bayan isha. Wanda a
lokacin kuma su Samha suka tattara nasu ina su sukayi bankwana da Mu'azzam suka ta fi.
daga hajiya sai Salma da Hajiya suka rage. Suna ta hira har hajiya ta ce bacci take ji ta tafi ta
kwanta.
ganin haka sai ya zama kamar an basu wata dama ce, matsowa kusa da ita yayi ya sake mata
wani murmushi me narkar da zuciya tare da wani sassanyan kallo na soyayya.
sunkuyar da kai ta yi cikin shagwab'a tare da fad'in " Ya isa haka tom kallon."
"A'a kam, barni na yi ta kallon masoyiyata, domin gobe iwar haka sai dai naga hoto. "
"To yanzu dai goben zaka gudu kenan ka barni?"
"Dole ai, tunda wacce nazo dominta ba ta sona." Ya bata amsa cikin shagwbe fuska.
"Ya Mu'azzam ni ce bana sonka?"
"To ga Shi kin k'i yarda ki sanar da mama batun amin cewar ki."
"Aa kaima ka san ba zan iya ba, yaya ya kamata ya sanar mata."
"Wow!" Ya furta tare da kaiwa iska naushi. "Yanzu dai kin amince na zama mijinki ke nan?"
"Yaya, idan ban amince ba ya zanyi da k'aunar da nake maka? Ina maka wani irin so wanda
ban san ta yadda zan misalta shi ba ."
Baki ya saki yana kallon yadda take furta lafuzzan bakin ta.
haka suka yi ta musayar baitukan soyayya har zuwa kusan sha d'ayan dare. Hakan ta sa shi
kusan fita a cikin hayyacin da wanda da kyar ya iya kai kan sa d'aki.
Su kuwa su Samha haka suka ci gaba zama ba wani ci gaba har biki ya zo suka tattara suka
koma gidan su domin a yi bikin.
Tafiyarta gida kuwa shi ne silar sake shigarsa damuwa, ganin haka ya ji ya kamata yayi zama
ko da wasu daga cikin abokansa domin yaji yadda ake zaman aure don ya gyara kafin Samha
ta dawo. Wata k'ila ko akwai wani abu da bai sani ba.
Inuwa abokin sa ya k'ira ya ce su had'u yau da yamma akwai maganar da zasu
tattaunawa........
19
A lokacin da Inuwa ya iso gidan baya gida, don haka sai da ya jira zuwan sa tukunna. Ko sa ya
iso falo suka yada zango, ruwa da lemo ya d'auko masa tare da cake ya ajjiye masa suka
gaisa.
Tambayar sa yayi ya iyalinsa ya tabbatar masa da suna gida sunje biki. bayan dan lokaci da
suka d'auka suna hirar duniya sai Awwal yace da Inuwa, "Wai ni kam na tambaye ka mana, a
cikin zaman aure me da me mata suka fi so ne."
Dariya Inuwa yayi tare da cewa, "Tofa ka ce madam zata sha gata kenan, lalle kana k'aunarta
sosai. A wannan lokacin ina ruwan wasu mazan da abin da matan su suke so."
"Haka ne, amma ina matukar kaunarta, sannan na rasa me zan mata wanda ba zata manta ba.
Wannan dalilin yasa na k'iraka don na tambayeka."
Gyara zama Inuwa yayi ya ce, "To Allah ya bar k'auna. A iya sanina da mata gaskiya suna son
soyayya, musamman soyayya ta fannin yabawa kwalliya girki da sauran su. Sannan mata suna
son kyauta, idan aka ce kyauta to ana nufin ta komai ma.
kuma mata suna son suga ka basu lokacinka ko ta mu'amalar aure ko kuma ta lokacin hira.."
"Okay ma sha Allah da wannan bayanai. Amma naji ka ce lokaci shin akwai wani k'ayyadaddan
lokaci da ake bawa mace a lokacin tarayya ko hira ne?"
"A'a ba ina nufin a k'ayyade ba, sai dai lokacin ya zama an maida hankali akan abin da suke da
buri. Misali idan mace kuna hira to tana son ka bar komai ka saurareta ko da kuw aikin
kasuwanci kake. Haka kuma a lokacin tarayya da kai tana buk'atar dogon lokaci, domin ita
mace tafi na miji wasu lokutan rashin gamsuwa da wuri. Amma dai wannna ya danganta da
yadda kuka san junanku ne, kawai na baka mislani ne."
Shuru Awwal ya yi domin an zo inda yake so azo d'in.
"Haka ne kam Inuwa, kuma na fahimta.
hira suka ci gaba da yi akan zamantakewar aure da yane shi kansa Inuwa yana da mata har
guda biyu. Sai wuraren magrib suka fita a gidan suka wuce masallaci.
Samha ana gida ana didimar biki har ranar auren ta tabbata aka d'aura auren Yaya yusuf lafiya,
kowa yana saka albarka da ganin kaya, haka suka d'auka suka kai gidan su amarya aka ba da
tukuici suka dawo.
washe gari ma haka suka
Kuma d'aukar wanka kamar su ne amaren ita da yayyunta, kayan maskeru aka kawo masu
suma da yamma. kuloli ne da su kafet da shinkafa had'i da samiru dubulan alkaki da abinci da
miyar sa da ta ji nama, da dai sauransu.
zuwa dare aka watse kowa ya kama gabansa. Su kuwa sai washe garin ranar sannan suka
koma gidajen su.
Tsawon kwana uku da gama bikin ke nan yau.
Samha tana zaune akan d'aya daga cikin kujerun falonta, tana sanye cikin riga da zani ba ko
hota a fuskarta kanta ta yi wani kalar d'aurin d'ankwali a har butse, gefe guda kuwa Awwal ne
yana zaune ya rasa ta yadda zai fara mata magana ta fahimce shi, saboda yana son su
kasance a daren yau amma yana tunanin taya zai mata magana ta saurare shi. Domin a yadda
ya ganta ma yau sam kamar bata cikin nitsuwarta.
Jin sallamar aunty Dija shi ne abin da ya sa su waiwaya wa. Zuwa ta yi ta zauna suka gaisa da
Awwal sai ya tashi ya fita. Aunty ta dubi Samha ta ce, "Muje ciki."
Bata yi mata musu ba suka shiga ciki abakin gado suka zauna.
Aunty ta dubeta ta ce "Tsarabar da aka fidda miki ce ta biki da na koma gida mama tana neman
me kawo wa na ce ta ba ni sai na biya na baki, amma kafinnan Samha me yake damunki? Na
jima da fahimtar ba kya cikin nutsuwar ki, kawai ina barin kine bana matsa maki. Yanzu ki dube
ki, a gaban mijinki kina zaune ba kwalliya bare wani kyakkawan d'aurin d'ankwali. Shin Samha
duk duniya kina da wanda zaki sanarwa da damuwar ki sama da mu ne?"
Shiru Samha tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tare matsar hawayen da ya cika acikin idanunta.
"Aunty wallahi ina cikin tashin hankali."
Ta fad'a tare da fashewa da kuka. Rungume ta Aunty ta yi tare da lallashin ta tace , "Karki damu
sanar min koma mene ne."
Sunkuyar da kai ta yi k'asa cikin matsananciyar kunya ta ce, "Aunty wallahi injin Awwal ne yana
da buk'arar sabis, kuma kullum na yi ta sanar masa ya k'ara karfin injin amma sam yaki
fahimtata.kuma ina tsoran hakan ya jefani cikin halaka. shi ne na yanke shawarar rabuwa da shi
amma sam yak'i ya sallame ni."
Jim, aunty ta yi tajin bayanin nata sannna ta yi murmushi ta ce, "Haba Samha, yanzu wannan
matsalar akan ta ce zaki ce zaki rabu da uban yaran ki?
na sha mamaki da jin cewa wannan ita ce damuwarki. a tunanina sai dai ko haskawa wasu
hanya saboda kasancewar ki wayayya."
"Humm! nayi dukkan abin da zan iya aunty ina yiwa Awwal.........."
Dukkan k'okarin da Samha tayi ta sanar da aunty sai ta ce da ita, "Samha, kinyi k'okari, amma
baki yi abin da ya dace ba har yanzu. kuma kina da laifi kema acikin wasu abubuwan. Don haka
yau in sha Allah k'arshen damuwar ki ta zo, zan sanar da ke abubuwa masu mahimmanci
wanda baki sani ba na zama da irin wad'annan maza. Sanna kuma zan sanar dake abin da
zakiyi ki samu zaman lafiya da gamsuwar aure a wajen mijinki."
Cike da farin ciki ta gyara zama ta kuma matsowa wurin aunty tare da fad'in, "Ina jinki."
"To Samha, abu na farko dai shi ne..............
*To jama'a laifin dad'i k'arewa, anan na kawo karshen free page na wannan labarin. Don